Showing 39001 words to 42000 words out of 84763 words
Chapter 14 - AIMANA Book Complete by MAMI YUSUF DABO.txt
kamshi yake
"Muje falo kisa sim ki haɗa wayan" yana rikeda ita har suka karasa falon ya mata mazauni saman kujera shi kuma ya zauna kasan carfet yana kallonta ta buɗe wayar ta cirota daga kwali farin ciki sosai yagani shimfiɗe kan fuskarta, ya karɓa ya sama mata screen gart da wayar tazo da shi a kwalin ya mika mata ta kunna wayar
"Wow Yah Musty kalli gaskiya wayar nan tayi kyau sosai"
"Nifa banason Sunan nan maye wani yah Musty dan Allah"
"To baby"
"Yawwa na karɓi wanan nice name" rungume Musty tayi ta sumbaci laɓɓansa
"Wow Reina sake sake dan Allah please" Aimanah rufe fuskarta tayi da tafukan hannunta tana dariya, ya hawo saman kujerar ya haɗeta da jikinsa yana sauke numfashi, sun jima rungume da juna, kafin aka fara looking na kofa, ta tashi zataje ta buɗe yadawo da ita ya zaunar da ita saman cinyarsa
"Karki buɗe ko waye zai gaji ya koma baza'a ɓatamin wannan yanayin ba"
"Musty zakuzo ku buɗemin ko saina saɓa maku" suka jiyo muryar Anty Hasana tana faɗa, da sauri Musty ya saki Aimanah ya nufi kofa yama magana a hankali
"Kai Anty kin ragemin jin daɗi fa Allah yasa Dr yau ya tattaraki ku koma inda kuka fito" buɗe kofar yayi ta sakar masa rankwashi a ka tana hararar sa ta wuce sa zuwa ciki, Shaheed da Rumana suka biyo bayanta suna rikeda manyan ledoji a hannunsu
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹
Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰
☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation
*Shafi na Ashirin da ɗaya*
Aimanah ta gyara kwanciyarta saman kujera tana kallon Anty Hasana dake mata kallon tausayi
"Sannu Aimanah" kai kurum Aimanah ta ɗaga tana kokarin tashi zaune,
"A'a Aimanah basai kin tashi ba yi kwanciyarki ki huta, nima ba zama nazo yi ba zuwa nai namaku sallama Dr ya takura sai mun tafi yau ga Rumana nan, na barta gidan Ana zata kara maku kwana biyu kafin agama mata shirin makaranta ta tafi"
"Anty yanzu tafiya zakiyi?"
"Ya zanyi Aimanah, umarni daga sama, ba yanda zanyi"
"To Anty Allah ya sauke ku lafiya" musty yafaɗa yana kallon Antyn
"Daman kai ai so kake na tafi na takura maka ko? toga kanan ga Aimanah nan, Allah yasa nan da wata tara mudawo suna"
"Mom" Rumana tafaɗa tana kallon Anty Hasanan
"To uwata hanani magana" ta tashi tana lekawa ko ina na saman tana dubawa kamar yaune zuwanta gidan na farko, ta juya zata fita bayan tabawa su Rumana umarni subar ledojin anan na Aimanah ne, Aimanah ta ruko hannun Rumana ahankali tace
"Rumana inason magana dake fa"
"To Anty gobe zan zo muyi magana" kai kurum Rumana ta ɗaga tabi bayan su Anty da Musty da suka sauka kasa, Akasa suka sami Sumayya ta fito daga kicin ɗinta batare da Anty Hasana ta tsaya daga tafiyar da take ba takewa Sumayya magana
"Sumayya ga Amarya nan Allah yabaku zaman lafiya sai ayita hakuri mu munkoma inda muka fito" Sumayya batace komai ba tabi Antyn da kallo wacce suka fice tareda Mustapha da alama magana suke mai mihimmanci,
Rayuwa sosai taima Aimanah daɗi a gidan Mustapha sosai yake bata kulawa ko wanne motsinta akan idanunsa kauna tattali da soyayya ba kalar wacce Musty bai bata ba a ƴan kwanakin da sukayi tare, ko ƙasa baya barinta ta sauka da kanta goyata yake a bayanta har kasan, sau biyu idanun Sumayya na gane mata Musty ya goyo Aimanah a bayansa zuwa kasa, takanyi takaici ta shiga damuwa hakan yasa ta nemi izininsa akan tanaso zataje katsina, ba musu ya amince mata, tafiyarta tabasa damar ɓarje amarcinsa son ransa komai tare suke cikin kwanciyar hankali da kaunar juna.
Abas ya kalli hajiyarsa dake kuka sosai ganin yanda Abbas ɗinta ya rame ya yi baki sosai dama can shiba fari bane amma bayada duhu kamar yanzun ya wani tara suma kamar wani ɗan sudan,
"Abas kaga yanda ka koma?" ashe baka ɗauki maganar dana gaya maka ba"
"Hajiyata na ɗauka mana naji maganarki zuciyata ce ta kasa jure rashin Aimanah, Hajiya idan na mutu ki gayawa Aimanah ina mata fatan alkhairi, kice nace tabi mijinta su zauna lafiya" Hajiya tasake fashewa da kuka tana rikeda hannun Abas
"Abas ka dai..."Ya isa Baba kayi shuru dan Allah, karka fama inda kemin ciwo, please Baba" Alhaji wada ya goge kwallar data zubo masa yana kallon yaron nasa cikeda nadama
"A'a Abas ka barni nayi magana, kabarni na nemi yafiyarka"
"Yafiyata kuma Baba, ka isa dani ne shiyasa ka yanke hukuncin da kaso, nariga da na ɗauki kaddara ko haka bata faru ba daman can Aimanah ba matata bace kamin addu'a nacika da imanai"
"A'a Abas kadaina faɗar haka dan Allah, ka mutu ina zansa kaina yaya zanyi da rayuwata, bazaka mutu ba Abas kai zaka sakani a kabarina insha Allah" likitane ya shigo yana sanye da kakin sojoji ya haɗa allura yana kallon Abas ya ce
"Captein zan maka allurar barci"
"A'a Uwaeer karka min allurar nan ka barni na kalli fuskar Hajiyata gani nake kamar yinin yau kaɗai ya ragemin a rayuwar duniya" uweer ya ajje alluran yana kallon Abas
"Captein kadaina faɗar haka cuta ba mutuwa bace anyi nasara jininka ya koma dai dai dan Allah karage damuwa ni dakai duk musulmai ne munyi imani da kaddara mai kyau ko mummuna"
"Nagode Dr, ko nace Captein" dariya Uweer yayi yayiwa su Hajiya sallama ya fita,
Aimanah tasawa kofar shigowa samanta key ta zare kay ɗin ta koma ta zauna kusada Rumana wacce ke kallonta da mamaki
"Wai yaya Aimanah mai kikeyi haka ne kin rufe ko ina kin wani saki labulaye yanzu kuma kin sakawa kofa key Yayanmu fa yana gidan Ammi sanda na fito yana shirin tahowa nan shima fa, ki buɗe kofa karya zo yazaci ma wani abin" Aimanah tayi tagumi tana kallon Rumana hawaye suka zubo daga idanunta ahankali ta goge hawayan
"Rumana inason Abas, nasihar da Daddy yayimin randa za'a kawo ni gidan nan ita tasa na kwantar da hankalina na karɓi Musty a matsayin miji na rungumi kaddarata, Rumana inason sanin halin da Abas yake ciki, ina kuma rokon wata alfarma a gareki" Aimanah ta karashe maganarta tana saka hannuwanta cikin na Rumana
"Rumana ina rokonki alfarma ki auri Abas nasan bakida saurayi bakida kowa wanda ke sonki" jikin Rumana ne yahau ɓari tana kallon Aimanah ta zare hannunta daga cikin na Aimanah ta dafe bakinta🤭tareda zare idanu😳ta mike tsaye tanaja da baya baya
"Ni wai haba Allah ya kiyaye na auri wanda kika so haba Yaya Aimanah" Aimanah mikewa tayi ta dawo kusa da Rumana ta tsaya tana sake haɗa hannunsu
"Alfarma na nema Rumana ki taimaka kimin wannan alfarma tunda abin nan yafaru nakeji inama inada kanwa na bawa Abas na fara hasaso Surayya sai na gano suna soyayya da yaya mas'ud, tunani na karshe kwakwalwata ta tsaya a kanki, zakiyi farin ciki Rumana Abas mutum ne yayi ta ko'ina ina matukar maki sha'awar auransa, kamar yanda na gaya maki a baya har akai kwana biyar da auranmu da Mustapha banji a raina zanyi rayuwa da shiba, na kudurce a raina saina kashe auran nan na auri Abas amma girma da kimar Daddy tasa na manta da komai na jure zan zauna da Musty da ayanzu nakejin sa a zuciyata fiyeda Abas kawai dai ina tausayin Abas daga sanda kika amsamin kin amince da auran Abas zuciyata zata nutsu nasami nutsuwa da kwanciyar hankalin da zan bawa Mijina kulawa"
"Yaya indai har inna auri Abas zakiyi farin ciki a gidan Mustapha na yarda zan aure sa amma inyace baya sona fa?"
"Bakida damuwa da wannan bani wayarki" Aimanah taja hannun Rumana suka zauna saman kujera tana gayawa Rumana lambar Abas tana sakawa a wayarta tai call saida ta kusa katsewa sannan yai picking call ɗin Rumana ahankali ta ce
"Hello" da sauri Abas dake kwance saman gadon asibiti ya mike zaune ya ce
"Haya"..dafe kansa yayi kana yace
"Aimanah" yafaɗa da raunanniyar murya
"Ba ita bace Rumana ce" wani bakon yanayi yaji na daban a zuciyarsa daya kasa banbance na mene
"Ga Yaya Aimanan zakuyi magana"
"Abas" Aimanah tafaɗa muryarta na rawa kamar zata fashe da kuka
"Aimanah ya kike ya mi..." sai kawai yayi shuru yakasa karasawa
"Abas ya kake fatan kana cikin aminci" mikewa tayi ta shige bedroom ɗinta ta zauna
"Ina lafiya Aimana ina mijinki kika kirani a waya?"
"Baya nan"
"Mai yasa zakiyi haka ki fara neman izininsa sai muyi magana"
"Ka bari muyi magana Abas tanada mahimmanci, nasan matsayina a zuciyarka hakan yasa zan roki wata karamar alfarma a wajanka"
"Wacce alfarma faɗi Aimanah ko wacce iri ce zan maki insha Allah"
"So nake ka auri Rumana"
"Rumana" ya maimaita da sauri
"E! Ita"
"A'a Aimanah dan Allah karki ce haka"
"Idan kamin haka raina zaiyi daɗi zata kula da kai nasan Rumana batada wata matsala zakaji daɗin zama da ita" hmmm Abas ya sauke numfashi
"Idan ni na amince ita fa"
"Nagama magana da ita"
"Shikenan na amince Aimanah, Allah yasa tanada halaye irin naki"
"Tanada fiye da nawa ma"
"Ki kasance cikin Aminci Aimanah ki zauna da mijinki lafiya ina maku fatan alkhairi"
"Nagode, wannan lambar Rumana ce dan Allah naji labari mai daɗi da zai sani kwanciyar hankali"
"Kamar ma kin samu ne Aimanah ki saka mana ranar bikinmu"
"Ku fara dai daitawa tukunna san samu karya wuce nan da wata guda"
"Da wuri haka"
"E!"
"Yaya Aimanah kizo ki buɗe yayanmu na buga kofa," tajiyo muryar Rumana tana faɗa daga inda take, saurin sallama tayiwa Abas ta fita, taje ta buɗe kofar, yana shigowa ya eungumeta a jikinsa
"Maye na rufe kofa" yafaɗa yana kallon cikin idanunta kamar mai son gano wani abu
"Kuka! kukan me kikayi?" kokarin kwace kanta take amma ta kasa duk kunya ta kamata ganin Rumana na cikin falon,
"Bazaki ce komai ba Aimah" ta buɗe baki zatayi magana ya haɗe bakinsa da nata da sauri Rumana ta salallaɓa tabar falon kar taga abinda yafi karfin idanunta, Musty zama yayi kan kujera ya ɗorata saman cinyarasa yana cigaba da abinda yake,
"Baby Rumana na nan fa"
"Na ganta na guma ga sanda ta fita" wai gawa Aimanah tayi tana kallon kujerar data bar Rumana a zaune taga wayam ba kowa😂
"Kinsa ta gudu kin bata kunya"
"Kabata dai ta faɗa tana lakace masa kumatu"
"reina na gaji zumu shiga daga ciki mu raba gajiyar nan"
"Gobe sunday fa nasan zakace zaka tafi ga Sumayya bata dawo ba"
"Munyi waya ɗazu sai friday zata dawo, goben ai jirgin dare zanbi ko zakizo mu tafi tare?"
"A'a bazani ba nima monday hutuna zai kare"
"shikenan" musty yafaɗa sanda suka ahiga ɗakin, hannu yasa ya ɗau wayar Rumana daya gani ajje saman gado, ya juya wayar yana kallon Aimanah datayi kasa da kanta
"Wayar wace?"
"Ta Rumana ce"
"Rumana nan kika kawo ɗakin kwanan mu?"
"A'a nina yi waya da ita"
"Ina taki wayar?"dawa kuma kikai waya"
"Yah Mus'af" tafaɗa muryarta na rawa,
"A'a reina nasanki gaba da baya zan iya rantse maki baki faɗa dai dai ba, ba da Mua'ab kikai waya ba, bana son karya akomai ki rinka gayamin gaskiyya komai ɗacinta"
"Da Abas nayi waya" Aimanah ta faɗa kanta a kasa muryarta na rawa, Musty ya mike tsaye ya kama kugu yana kallon Aimanah, jikinsa a sanyaye ya koma ya zauna
"Aimaahh maina maki nai haka kin kasa mantawa da A"
"Ba wani abu nace masa ba nagaya masa ne ya nemi Rumana da aure"
"Bana so karki sake magana da shi"
"Insha Allah, bazan sake ba,"
"And karki sake ɓoyemin komai, mu rinka tattauna damuwarmu mu samu mafita tare"
"Insha Allah baby" tafaɗa tana sake kwanciya ajikinsa.
Abas da aka sallama suka koma gidansa tareda su hajiya komai yagaya mata yanda sukayi da Aimanah
"Kai ya kake gani?"
"Na yaba da hankalin yarinyar, na kuma karɓi rokon Aimanah amma ki gayawa Baba yaje yafara magana da iyayanta, karki gaya masa Aimanah ce tamin tayinta ki faɗa masa ni na ganta nace inasonta zan gayawa Rumanan da Aimanar subar maganar nan a tsakaninmu"
"Shikenan Abas nayi farin ciki da hakan Allah ya zaɓa abinda yafi alkhairi"
"Amin" yace bayan ya kwantar da kansa saman kujera,
Aimanah tunda yamma tayi tafara kukan shagwaɓa musamman sanda taga yana haɗa kayansa cikin trolly, kwanciya tayi saman bed tana fashewa da kuka ganin Musty ya ɗauki jakarsa zai tafi, cikeda damuwa yadawo ya zauna kusa da ita yadafe kansa, can kuma ya mike ya buɗe wardrove yafara zuba kayanta a trolly
"Nifa bazani ba," tafaɗa cikin kuka
"Toya kike so nayi kin tisa ni a gaba kinamin kuka ku tashi kawai mu wuce legos ɗin tare"
"Bazan bika ba hakan ai saiya zama rashin adalci ga Sumayya anan ni nabika can ai bamu kyauta mata ba koni akayiwa haka bazanji daɗi ba....✍🏻
[2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹
Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰
☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation
*Shafi na Ashirin da biyu*
Jiyo sallamar Ahmad a falo yasa Musty ya fito yana rikeda Aimanah a jikinsa,
"Yadai malam dogo ina ɓata lokaci ko?" Ahmad ya taɓe baki yana nuna masa agogo tareda yamutsa fuska
"Saura yan mintuna fa jirgi yatashi" bai tsaya jin mai Musty zai faɗa ba yaja trolly ɗin Mustyn yafita, Musty ya koma ɗaki ya ɗakkowa Aimanah hijab yasa mata
"Reina kimin rakiya zuwa airport"
"Baby, bazani ba kuka zanyi kabarni kawai anan" zare jikinta tayi daga nasa tayi baya tana ɗaga masa hannu alamar bye, tashige ɗakinta ta rufe da makulli ta sulale a kasa tana fashewa da kuka, yana jiyo kukan nata hakan yasa ya juyo zuwa kofar
"reina please ki buɗe mu tafi tare kin sani bana son kukan nan naki" tana jinsa yakaraci bugunsa ta kyalesa, fita yayi inda Ahmad da shaheed ke jiransa
"Yayanmu ka ɓata lokaci da yawa fa, Allah yasa ma ba go slow a hanya karya rike mu"
"Ahmad kabi ta gadon kaya ina jin nan ba goslow sosai" Ahmad baice komai ba aikinsa kawai yake na tuki,
Ammi jin ana kiran sallar insha yasa ta kalli Surayya da Rumana
"kuyi salla kuje ku taya Aimaah kwana" da sauri Rumana ta kalli Ammi
"Ammi mu tayata kwana kuma?"
"E! haka nace Mustapha ya koma legos yau"
"Ammi ai na zaci tare zasu tafi" Surayya ta faɗa tana danna wayarta da murmushi a fuskarta da alama chat take da Mas'ud
"Nima haka naso amma Aimanah ta kawo dalilin dana aminta data zauna anan ɗin" ba wanda yasake cewa komai sai salla da suka muke sukayi abincin dare suka ci sun gama ci kenan wayar Rumana tayi kara, gabanta ne yai wata irin bugawa ganin lambar Abbas na yawo a fuskar wayar, "Abbas" tafaɗa a hankali, mikewa tayi tana satar kallon Ammi ta wuce bedroom ɗin Ammin
"Hello Hayatie" Abbas yafaɗa yana lumshe idanu daga inda yake kwance saman bed dake cikin gidansa
"Uhmm umhnm Rumana ce" Rumana tafaɗa muryarta na rawa
"Na sani ai Hayatie ya kike"
"Anya na can canci wannan sunan kuwa da dai ka daina faɗa"
"Kin wuce haka ma a zuciyata ina kau..." shiru yayi yai saurin saka hannu ya danne kirjinsa dayaji lokaci ɗaya numfashinsa na shirin ɗaukewa
"Na riga na sani daman" Rumana ta faɗa tana dariya
"Kika san me? kisa a ranki Rumy kece madadin Aimanah a zuciyata"
"Anya kuwa zan iya zama madadin nan"
"Zaki wuceta ma insha Allah, karki faɗawa kowa cewar Aimanah ce ta haɗamu ki barshi a nina kawo kaina gareki kema kuma kisa haka a ranki"
"Nasa"
"Kin tabbata"
"Gaske"
"Bani labari"
"Yana wajanku, bari zamuyi waya anjima naji Ammi tana kirana" sallama sukayi da Abbas ta sa wayar a kirjinta kana ta sumbaci wayar ta buɗe idanunta karaf idanunta cikin na Ammi da batasan ta shigo ɗakin ba, murmushi Ammi tayi tana kallon Rumana
"Dawa kike waya? koma dai nasani nayi suruki Allah yasa alkhairi" Rumana da gudu ta fita daga ɗakin tana dariya, tare suka jera da Surayya zuwa gidan Aimanah suna tafe a hanya Rumana taruko hannun Surayya suka tsaya
"Sury mai zakice min idan nace maki Abas ɗin Aimanah ɗazu munyi waya dashi wai! wai!! wai yana sona" Surayya ta dafa kirji
"Kai nayi farin ciki matuka ke kuma mai kika ce masa"
"Bance komai ba kina ganin hakan bazaija cece kuce ba a family"
"Banajin hakan zata faru akwai fahimtar juna a tsakanin iyayanmu maza da mata banaji akwai wata matsala, ina maki fatan alkhairi"
"Nagode matar Yah Mas'uf" dafe kirji Surayya tayi tana dariya
"Ya'akayi kika sani duk ɓoyewar da muke"
"To garama ku fito fili kuyi soyayyarku sabida kowa ya san inda kuka dosa" dariya sukayi gaba ɗaya kana suka cigaba da tafiya, falon a rufe da alama a rufe yake sunyi looking amma ba'a buɗe ba hakan yasa suka kira Ammi wayar Aimanah taki shiga, Saheed ne yakawo masu kay suka buɗe suka shiga.
Amarya na tsaye gaban madubi sai shafa wannan goga wancan take, ta kashe ɗauri ta kalli Murjana batace komaiba ta yafa mayafi tana kallon Murja dake kwance saman gado lamo kamar mara lafiya
"Dan Allah Murja kekam wai mai kike son zama ne kinbi duk kin addabi rayuwarki da tunani" Murjana bata ce komai ba saima gyara kwanciyyarta da tayi ta juyawa Amarya baya tana jinta harta fice daga ɗakin, wata haɗaɗɗiyar mota ce a fake a waje take jiran Amarya cikeda gadara ta buɗe bayan motar ta shiga tana hura baki da hanci, direban motar yaja suka bat layin batare dayace mata kala ba, kofar wani haɗaɗɗan gida motar ta faka Amarya ta fito tana karewa gidan kallo, direban motar ya fito
"Hajiya ki shiga daga ciki, mai gadi zai maki jagora har zuwa cikin gidan" batace masa komai ba ta tura haɗaɗɗan gate ɗin ta shiga bako sallama, getman yataso da sauri yana tambayarta ina zataje, card ɗin hannunta ta nuna masa yace ta biyo bayansa yana gaba tana binsa a baya idanunta na kallon ko'ina na gidan, gida ne haɗaɗɗe daya sha fulawoyi ta ko'ina, kanta bai gama kuncewa ba saida ta gansu tsaye gaban kofar glass ya danna wani madanni kofar ta buɗe suka bayyana a wani kawataccan falo daya gaji da haɗuwa, sakato tayi da baki tana kallon falon da iya tsawon rayuwarta bata taɓa ganin haɗaɗɗan falo irin wannan ba, tayi hulda da manyan mata masu kuɗi na garin nan amma kam bata taɓa ganin gidan daya kai wannan haduwa ba, matar da suka haɗu a wajan boka mai suna