Showing 54001 words to 57000 words out of 84763 words
Chapter 19 - AIMANA Book Complete by MAMI YUSUF DABO.txt
compound na gidan kana yabi kiran Ammi daya katse, Aimana batasan ya sukayi ba taga dai yadawo ɗakin ya kwanta baice mata komai ba, sa da tabari yayi nisa a barci ta tashi tsakiyar gado ta zauna tana faman kukan shagwaɓa
"Aimanah baza ki barni nayi barci ba ko?"
"Ba kaine ba kadaina min magana" tafaɗa cikin kuka, dafe kansa yayi gamida zuba mata idanu kana ganin yanda take kukan kasan na zallar shagwaɓa ne, matsowa yayi kusada ita yasata a jikinsa yana buga bayanta a hankali da hannunsa
"Is ok ya isa Reina kece rigimar ki tayi yawa a wannan halin da kike ciki kice wani zakiyi tafi"
"Naga a jirgi zanje kuma ai ba kwana zanyi ba randa naje ranar zan dawo bafa nisa legos zuwa Abuja"
"Hmmm" kawai yace ya kwantar da ita haɗida sata a jikinsa yana share mata hawaye har sukai barci a haka, shiya rigata ta shi yauma yayi abinda zaiyi ya fice sai text messages dayai mata na fatan ta taahi lafiya ya kuma sanar da ita ta shirya zasubi jirgin karfe biyu zuwa Abuja, murna tayi sosai sanda taga sakon cikin lokaci kankani ta gama komai, Aimana maca ce mai tsabta da iya girki ga uwa uba iya ado da kwalliya, ko kafin Musty yadawo tagama komai harta shirya cikin doguwar riga yar dubai tayi matukar kyau, sanda yadawo wanka yayi suka ci abinci ya fita masallaci yai sallah itama tayi nan cikin gidanta yana dawowa suka wuce airport yariga da yasaba indai zaiyi tafiya nan cikin airport ɗin yake varin motarsa inya dawo ya ɗauki abarsa, lafiya suka sauka Abuja duk ɗoki da son ganin Rumana da Aimanah take haɗiye sa tayi dan tunda suka sauka a Airport na Abuja Mustapha ke cika yana batsewa, wani haɗaɗɗan hotal Mustapha ya kama masu can suka sauka a recepsion ya karɓi key na ɗakin ya wuce dan tun a office ɗinsa ya gama komai ta online shiyasa key kawai suka basa anriga da an gaya masa number ɗakin, suna shiga ɗakin Musty tafara rage kayan jikinsa ya rage daga shi sai singlate da gajeran wando ya haye gado yana faɗin wash
"Amma yaya inace hospital ɗin zamuje" kanzil baice mata ba saima gyara kwanciya da yayi yana kallon agogo, ba yanda taso itama kwanciyar tayi nesa da shi ta cure waje guda a haka barci yayi gaba da ita, Kiraye kirayan sallar la'asar ya farkar da Mustapha daga barcin da yayi yaga yanda Aimanah ta cure waje ɗaya, da sauri ya gyara mata kwanciya ya lulluɓa mata blanket ya wuce bathroom yai wanka da alwala ya wuce masallacin dake nan cikin hotal ɗin, harya dawo rike da babbar leda a hannunsa bata tashiba shima bai tashetan ba sai wayarsa daya ɗauka yana dannawa, biyar da kwata Aimanah ta farka taga gari yafara duhu addu'ar tashi daga barci tafara kana ta tashi zaune
"Sannu kin tashi" gira kawai ta ɗaga masa ta mike ta shiga bayi tayi wanka da alwala, futowa tayi tana raba idanu
"Yanzu kayan nan zan maida wai" da idanu ya nuna mata ledar dake ajje saman bedsite drowar buɗewa tayi dogayan riguna ne guda biyu yan maroco ja da baka sai manyan hijabai guda biyu, jar tasaka ta ɗaura karamin mayafin rigar a kanta ta saka hijab ɗin tai sallah, kafin ta idar taga yagama shiryawa cikin bakaken suit sak yafito a kalarsa ta ma'aikacin banki🤭tana azkhair ya zauna gefanta ya ajje likab a gabanta, dariya taso kwace mata amma sai ta shanye ta, ta shafa fatiha tana kallon sa shida likabin gabanta
"Kisa muje hospital ɗin"
"Inajin yunwa, kuma Allah bazan saka abin nan ba, ban taɓa sawa ba dan haka bazan koya yau ba"
"Aimanah ki taimaki zuciyata ki sakaya min kyakkyawar fuskar nan taki"
"Mustapha kar muyi haka dakai duka akan Abbas ne kake wannan abun, Abas Rumana yake aure, na tabbata a yanzu babu wani sauran abinda yayi saura tsakani na da shi, kai nakeso kaine abokin rayuwar da Allah ya zaɓa min koda baka raye nan duniya bana jin zai iya auran wani kisa a ranka ni taka ce har abada na roke ka ka rage kishin nan naka akan Abbas"
Jikinsa ne yai sanyi da maganganun Aimanah hakan yasa yai shuru tareda komawa gefe ya kira a waya aka kawo masu abinci, basu sami fita ba sai bayan da sukai sallar mangari ba sannan suka fita zuwa hospital ɗin da Rumana take
"Baby a ina kasami mota?"
"Munyi magana da yah Mansur shiya saka aka kawo min"
"Mutanan landon ana can"
"Suna can kam ɗazu mukai magana da Mus'ab ma zai wuce Rasha acan zaiyi P h d" taɓe baki Aimanah tayi kana ta ce
"Shikenan gida yazama sai Mah da Ma'aruf kowa yasa gabansa yabar kasar"
"Wanda yasami dama ya dama Aimanah wannan kasar tamu sai dai addu'a kawai nima nafara tunanin komawa jordan can inda nafara aiki"
"Amma badai dani ba"
"Da Sumy" yafaɗa yana hararata sunata hira har suka karasa hospital ɗin
[2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹
Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰
☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation
*Shafi na Ashirin da takwas*
Cikeda tausayawa Aimanah takewa Rumana sannu, tana rike da hannunta
"Hajiya ina wuni" Aimanah tafaɗa tana kallon Hajiyar Abbas data fito daga bathroom, hajiyar Abbas ta rike baki cikeda mamaki fuskarta da murmushi
"Wa idanuna ke gani kamar Aimanah mutanan legos, yar uwarki ta taso ki ko?"
"Nice Hajiya yamai jikin"
"Jiki da sauki gobe ma zasu sallame mu mu koma gida" Aimanah kan tayi magana aka turo kofa aka shigo Abbas nw shida Mustapha sai Ammi a bayansu
"Lah Ammi daman kina nan"
"A'a yanzu nazo Abbas ne ya ɗakko ni a airport ashe kunzo" Musty can gefe yasamu ya zauna saman farar kujera yana kallon Aimanah
"Yaya Abbas ina wuni ya mai jikin"
"Da sauki" Abbas yafaɗa idanunsa na kasa, Aimanah sun jima a hospital ɗin har tara saura, Mustapha yabawa Abbas hannu sukayi musabaha tareda fatan sauka lafiya, Aimanah tabi bayan Muatapha daya fita bayan tayi sallama da su Rumana,
Aimanah da Mustapha kwanansu biyu a Abuja kana suka wuce kano inda aka fara bikin Surayya da Mas'ud, Aimanah bata wani sake sosai a bikin ba duk da dama ba wani shagali aka sha ba to ango yana india wajan karatu can za'a tura masa amaryarsa bayan an ɗaura aure, satin su Aimanah biyu a kano suka koma Abuja,
Rumana sosai take samun kula ta musamman wajan Abbas, Hajiyar Abbas tunu ta koma jigawa vayan taga Rumana ta warware, sauri sauri Rumana ta shiga wanka ganin lokacin dawowar Abbas yayi akuwa tana bathroom ta jiyo karar tsayawar motocinsa, kafin ta fito harya shigo ɗakin sanye ta fito da tawul ɗaure a kugunta yayinda hannunta ke rike da ɗaya tana tsane gashin kanta
"Wellcome sir" tafaɗa tana tsugunnawa a gabansa ta fara cire masa takalmin kafarsa duka biyun ta cire ta ajje su mazauninsu kana ta dawo ta fara rage masa kayan jikinsa, janta yayi sukayi baya suka faɗa saman gado suna dariya
"Mar'atul saliha albushirinki"
"Goro" tafaɗa da sauri
"Gobe sassafe zaki sama sabuwar ɗaliba a jami'ar abuja" makale shi tayi sosai tana ihun murna
"Hayatie da gaske dan Allah wayyo ni ina kasami takardu na"
"Jaheed ya turomin da komai"
"Naji daɗi sosai Hayatie nayi farin ciki yanda kake faranta min kaima Allah ya faranta maka fiye da haka"
"Amin yafaɗa yana sumbatar ta" daga nan salo ya canza suka lula duniyar masoya🤭
Aimanah na vaje a falon tayi ɗai ɗai tana fidda numfashi yayinda Al'Mustapha ke zaune kusa da ita yana yanka kata Apple
"wash" Aimanah tafaɗa cikeda raki
"Sannu reina sannu kinji"
"Baby na gaji da cikin nan gani nake ma kamar mutuwa zanyi" Aimanah ta karasa faɗa tana kuka, ya buɗi baki zaiyi magana wayarsa tayi kara alamar kira ya shigo, Ammi ce hakan yasa ya ɗaga cike da ladabi
"Mustapha zan saɓa maka fa yaushe kadaina jin magana ta" Musty dafa kansa yayi a zuciyarsa yana faɗin wayyo ni
"Ammi kiyi hakuri Aimanah tayi nauyi da yawa idan ta tawo kano a haka zata wahala"
"Ni kuma nace ka kawo min ita yau zuwa gobe nabaka ka wucw wannan wa'adin zan saɓa maka" Ammi nagama faɗar haka ta katse kiran
"Kamaida ni kanon in mutuwa ma zanyi na mutu cikin Ahali na"
"Aimanh ba yanzu ba insha Allah sai kinga auran twince ɗinmu da jikokinsu" murmushin yake tayi tana jin mararta na kullewa, yayin da abinda ke cikinta yayi wani irin motsi
"Ya Allah" Aimanah ta furta a hankali
"Sannu" kawai yake aika mata, a washe garin ranar Mustapha ya maida Aimanah kano suna sauka Ammi taji labari tazo ta wuce da Aimanah gidanta tanata ma Mustapha masifa ganin yanda kafafunta suka kumbura, a daran ranar ta kaita hospital suka dubata sosai haɗeda mata hoton ciki inda suka sake tabbatar yan biyu ne a cikin Aimanah kamar yanda a asibitin da take awo a can legos suma suka faɗa, cikin wata takwas harda sati biyu, Mustapha kwanan sa biyu ya koma legos shida Sumayya cikeda kewar Aimanah,
Rayuwa mai daɗi da kulawa Aimanah keyi a gidan Ammi sai abinda takeso take ci kullum sukam futa da dare suyi zagaye su dawo, Mustapha tunda yatafi sai da yayi kwana goma bai zo kano ba, yau yakasa jurewa ba shiri ya biyo jirgin karfe tara na dare, lokacin daya zo sai Aimanah ita kaɗai a ɗakin Ammi, Ammin bata nan tana wajan Abba, da sallama ya shigo bedeoom ɗin Ammin, Aimanah da barci yafara ɗibanta ta buɗe idaninta a hankali da sauri ta tashi zaune tana mistsika idanunta
"Baby" tafaɗa da muryar barci
"Bakiyi barci ba? ina Ammi?"
"Yanzu ta shiga wajan Abba tace bazata jima ba taje basa tea" dariya Musty yayikan ya ce "Taje basa tea kawai dai ta tafi kula da mijinta ke kuma ta rabaki da naki mijin"
"Oh Baby"
"Gaskiyya fa nafaɗa" dariya tayi, ya zauna kusa da ita ya ruko hannunta
"Nayi missing naki sosai reina" yafaɗa yana sumbatar hannun nata, dai dai nan Ammi ta shigo ɗakin da mamaki take kallon sa ta haɗe rai
"Kai kuma maiya kawo ka da wannan daran?"
"Ammi naji kewar Aimanah ne kawai ba biyo jirgi na ganta" taɓe baki tayi sannan ta juya ta fita daga ɗakin, Musty bayanta yabi yasawa kofar key yana murmushi, gadon ya hawo sosai yasa aimanah a jikinsa yana sauke ajjiyar zuciya a jere kamar wanda yayi gudu, Aimanah ma lamo tayi a jikinsa tsawon lokaci suna rungume da juna ganin time na ja yasa ya cire jikinsa daga nata ya fita daga ɗakin, Aimanah gyara kwanciyarta tayi tana jin kewar mijinta na shigarta, har tayi barci Ammi bata dawo ɗakin ba, sai da safe ta ganta kwance kisada ita, Musty bai shigo gidan ba sai da ya tabbatar Ammi ta tafi makaranta sannan ya shigo sashin Momy ya shiga ya tarar bata nan itama, daɗi yaji sosai hakan yasa ya shiga ɗakin Ammi cikeda karsashin son kaɗaicewa da Aimanah kofar sashin ya fara sakawa key bayan ya shiga haka yayiwa ta falo ma, Aimanah taso kin bashi haɗin kai tana nuna masa rashin dacewar abin a ɗakin Ammi, wasanni daya rinka mata yasa ta bada kai bori ya hau, sai dai suka nutsu kana kunya duk ta kama ta gani take kamar Ammi taga komai da kyar da taimakonsa ta gyara jikinta ya cire bedshet ɗin yasa a wash machine ya wanke ya shanya yana addu'ar Allah yasa ya bushe kafin Ammin tadawo, Aimanah kaɗan kaɗan tafara jin ciwon mara azatonta kaɗaicewa da sukai da Musty yakawo haka take ganin gaba kaɗan zata daina ji, maimakon ciwo yayi baya sai yayi gaba tun tana jurewa harta kasa ta kira lambar Ammi ta sanar mata abinda takeji, Ammi tace mata ta jirata gata nan tana hanya tama kusa shigowa anguwar, Musty na can gidansa yana barci, ko kafin Ammi ta karaso Aimanah tafara fita hayyacinta, tayi sa'a tare suka shigo gidan da Ya Ahmad hakan yasa tasa shi suka nufi hospital, wayar Musty Ammi ta kira tace ya ɗakko masu kaya a ɗakinta suna hospital ruɗewa tasa basuma taho da komai ba ance haihuwa ce, Aimanah na zagaye cikin Asibitin taga shigowar Mustapha ya ruɗe sosai, Aimanah tun tana iya zagayan harta gaji kar finta na neman karewa aka maidata ɗaki har sannan da likita ta dubata a 4 cm take, Musty na rike da hannun Aimanah duk yanda likitoci suka so yafita a ɗakin ki yayi ganin ba wata a ɗakin sai Aimanah kaɗai yasa suka barsa, idanunsa kaɗai zaka kalla kasan yanajin ciwon gaba ɗaya yadamu jiyake ina ma da dama da ya karɓi leboor ɗin nan Aimanah ta huta, Tun safiya Aimanah take abu ɗaya har mangariba bata haihu ba, Musty sallah kawai ke fitar da shi daga ɗakin har kuka ya yiwa Aimanah musamman yanzu data fara kuka tana neman yafiyar mutane tana faɗin mutuwa zatai, Nurse ɗin dake zaune gefansu ya kalla
"Babu wani abu da za'a iya mata ne wai?" ya tambayeta cikeda damuwa
"Babu, zata iya haihuwa da kanta yanzu tana 8 cm nan da ko yaushe zata iya haihuwa" kukan jaririn da sukaji ya karaɗe ɗakin yasa Musty faɗin
"Alhamdulillah Allah abin godiya" da sauri likita dake office ɗinta ta fito ta karaso bakin gadon tana yiwa Aimanah sannu
"Dr ɗaya ne yafaɗo akwai wani a cikin kuma da alama mahaifarsu ɗaya ce, Nurse Musty ta kalla
"Matso ka rike wannan karkayi nisa" matsowa yayi ya karɓi jaririn dake faman tsan yara kuka ya rike idanunsa nakan Aimanah dake kiran sunan Allah ya share hawayan idanunsa yana sauke ajjiyar zuciya
"Sannu Aimah" bata ko iya ɗaga kai ta kallesa ba,
"Aimanah tsaya kar kiyi nishi" likitan ta faɗa tana danna mata ciki a hankali, kamar cirar kaya haka Aimanah taji sanda ta sake jin kukan wani jaririn ciwo ya tsaya cak Murmushi Musty yayi sai sannan ya kalli yaran, da Nurse ta matso ta zata yanke masu cibiya, wani gadon tayi daban da yaran Musty yadawo gefan kan Aimanah yasa hannunta cikin nasa
"I love you Aimanah" murmushi tayi ta kauda kanta Dr na mata dariya
"Ranka yadaɗe zamu kwarfe mata jini yakamata ka bamu waje"
"Baki da damuwa dani Dr kiyi komai ina nan yau nan zan kwana" Dr dariya tayi tana canza safar hannunta
"Wayyo" Aimanah tafaɗa sanda taji hannun Dr a jikinta
"Aimanah mai nake ji kinji wani babyn fa" Dr Rubina ta faɗa tana ciro hannunta daga jikin Aimanah
"Wani babyn kuma?" Aimanah da Musty suka faɗa a tare, kai dr ta ɗaga tareda kokarin yiwa Aimanah scaning hoton baby ya bayyana, Musty Lumshe ido yayi yana jero hamdala ga ubangijin da yayi masa wannan baiwar yara uku rigis lokaci ɗaya kai masha Allah, Aimanah wani sabon ciwon taji yana taso mata, tafara cize baki tana mimmikewa
"Wasa farin girki" Dr Rubina tafaɗa tana kallon Musty
"Dr yanzu wani leboor ɗin kuma zata sake?"
"Da a lama" Awanni biyu suka shuɗe ba alamar fitowar baby har an fara kokarin yiwa Aimanah cs sai kuka sukaji Aimanah ta sauke numfashi tana kallon babyn,
"Maca ce wannan" Dr Rubina ta faɗa tana jijjiga babyn ganin kukanta baya fita sosai kamar na sauran yaran
"Nurse Fatima kai wannan babyn nursery wajan su Dr Auwal emargency bata da cikakiyar lafiya da alama tasha ruwan mahaifa, naɗe yarinyar A tawul nurse Fatima tayi ta fita da sauri ita da Ammi suka nufi ɓangaran yara na hospital ɗin, nan da nan Aimanah tai wanka ta shirya sai sannan Mah tazo hospital ɗin shima Ammi ce ta mata waya anyi haihuwa ta kawo ma mai jego abinci da tea, ɗakin na musamman aka kai Aimanah da babyn ta guda biyu ɗayar na sashin yara ana bata kulawa, Musty har sannan bai kalli yaran ba yana kusa da Aimanah yana dai kallo ana ta ɗaukan babyn wannan yaba wannan dan tuni yan uwa sun cika hospital ɗin kai baza kace dare bane musamman daya kasance haske gashin tar wai ko alluranka ce ta faɗi zata iya ganinta kaɗau kayar ka
"Yayanmu babyn nan da kai yake kama" Ma'aruf yafaɗa sanda ya ɗau babyn a hannusa duka biyun
"Ya Ahmad zokamin hoto da babyn nan a tura a group kowa yaga yau na girma"
"So kake ka tashi hankalin Anty Hasana da daran nan tasa dr neman jirgi" Ammi tafaɗa tana dariya, Mah dai na gefe tana murmushi bata ce komai ba
"Mustapha yaɗau yaran nan kuwa?" Mah ta tambaya tana kallon Mustaphan
"Mah basai na ɗauke su ba tunda ga ku ai shikenan"
"Mu daban kai daban, maza ɗauke su kamasu huɗuba ka masu kuma addu'a" kallon Aimanah yayi
"Da alama dai ranka yadaɗe fushi kake da babys ɗin nan sun wahalar da madam" Dr Rubina ta faɗa tana kallon Mustaphan, dariya yayi
"Aimahh wanne suna za'a saka masu?"
"Daddy da Abba" yana kokarin karɓar yaran Alhaji Kamal da prop Farouk suka shigo ɗakin kana kallon fuskar su zaka hango zallar farin ciki, Musty fasa karɓar yaran yayi ya koma inda yake ya zauna Alhaji kamal ya karaso gaban gadon da Aimanah ke kwance yana mata sannu, yayin da Prop ya wuce ya karɓi yaran, fuskarsa da murmushi yake faɗin
"Masha Allah bakin duniya, Sauda kalli yaran nan kamar Mustapha randa aka haifosa" dariya akayi gaba ɗaya, Alhaji kamal ya amshi guda ɗaya yana masa kiran sallah a kunne, Alhaji Farouk ma hakan yayi kamar yanda sunna take
"Prop sai kayiwa kanku takwara ai"
"To nidai na hannuna nasa masa Umar faroup" Prop ya ce
"Au haka ne bari wannan to na masa huɗu ba da Muhammad Kamal" dariya aka kuma yi Dr Rubina dake haɗa allura zatayiwa Aimanah tana kallon Family ɗin tana yaba haɗin kansu.
"Baby wai wannan allurar ni za'ayiwa?" Aimanah ta tambayi musty rai ɓace kamar zata yi kuka
"bake zata yiwa ni za'ama madadinki"
"A'a kadai faɗawa madam gaskiyya ita zanwa duk kun hanata barci gara tayi barci ta huta gajiyar nan"
"Babban mutum ajjeni gida" Ammi tafaɗa tana mikewa tsaye, da sauri Mah ta tashi
"Mai kike nufi wai na zauna anan Allah ya sauwaka"
"Ai kuwa zama ya kama ki yaya tunda Momy na wajan Babyn can, ke ki zauna tareda Aimanah ni kuma naje gida na kwanta na huta tun rana fa muna nan"
"To daman