Showing 60001 words to 63000 words out of 84763 words
Chapter 21 - AIMANA Book Complete by MAMI YUSUF DABO.txt
Sumayya da mamaki
"Wai yanzu Sumy wannan ce kishiyar taki daman?"
"Ita ce" Sumayya ta faɗa a san yaye
"Cab tabbas zaki ga takaici jibi yarinya sai iyayi kalli uban kuɗin da ta fito dasu daga ɗakin mijinta"
"Mijinta kuma" Sumy ta kuma faɗa cikin sanyinta
"To mijinta mana Sumayya ke kina zaune anan bazar kin saki jiki kina zaune da kishiya lafiya waya gaya maki ana zama da kishiya nifa nan da kika ganni sanda zan auri Alhaji na shiga malamai nayi na rabasa da matarsa da yayansa ya kaɗa ta can aka koma gida akaci gaba da cin tuwon dawa, na kama abina ram na rike yanzu in gaya maki daga ni sai ɗana muke abinda ranmu yake so mota sai wacce naso nake hawa, yanzu ki duba misali ace yau Mustapha ya mutu mai zaki samu a dukiyar sa sai dai fa aɗan tsakurar maki ɗan kaɗan, kizo muje inda za'a maidaki tauraruwa a idanun mijinki ya zama sai abinda kika ce shi za'ayi a gidan nan"
"Bazan bi malamai ba, inkai zunubin ina" raɗa Lima tayi mata a kunne komai suka cewa Sumayya oho tadaiyi murmushi tai shuru tsawon lokaci kana ta ce
"Ina son Musty tabbas nima zan so na haihu da shi zanyi abinda kuka ce yau she zamuje wajan malam ɗin?"
"Basai munje dake ba can enugu ne wajan da nisa sosai indai zamuje kwana biyu muke yi, Mustapha zai barki kiyi tafiyar kwana?"
"Zai bari mana, zan masa karya zani Kaduna gidan yayar babanmu nasan zai amince, ban taɓa ce masa zani wani waje ba ya hanani"
"Yawwa yar gari toki tanadi kuɗi, Malam yana aiki kamar yankan wuka amma fa sai yaji dumus" Lina tafaɗa tana dariya
"Banda matsala da kuɗi Mustapha nasamin kuɗi a acount ɗina duk wata bana amfani dasu tarawa kawai nake yanzu zasumin rana" nana suka rabu akan jibi zasu tafi enugu, koda Al'Mustapha yadawo ta gaya masa baiyi musu ba sai fatan sauka lafiya da yayi mata, sanda yace zai sai mata ticket anan ne tace bata son zuwa a jirgi mota zata bi, washe gari ta kira yar uwar babansu tafala mata tafiya zatayi ne bikin kawarta a enugu tasan in Mustapha yasan ga inda zata bazai bari ba tace masa nan zata zo, koda wata magana ta taso tace nan ta zo, jiki na rawa Matar ta amsa mata da to sukayi sallama Sumy ta tura mata dubu hamsin, randa sukai alkawari ranar suka tafi gaba ɗayansu ukun, Sumayyya tun tana tafiyar marmari harta fara galabaita sabida a enugun ma inda sukaje can wani kungurmin daji ne ba gida gaba ba gida baya, sai wata bukka saman tsauni haka su Sumayya suka hau tsaunin nan kafin suka rufe idanunsu lina na karanto masu wasu ɗalasimai wata guguwa ta ɗebe su, tai kamar zata buɗe idanunta taji anan faɗin
"Karki soma kada ki sake ki buɗe mana idanunki anan, kina buɗe su sun zama banaki ba mallakin aljani tsunju" ai kara damke idanunta tayi har zuwa sanda taji guguwar ta tsaya taji wata murya mai kamar ana busa usur tana masu magana, Feena ta zungureta ta buɗe idanunta tai tozali da wani ramamman mutum dogo sosai ga rankwameman kai zaune saman fatar damisa" shekewa yayi da dariya yana kallon Sumayya
"Yarinya burinki ya gama cika tunda kika zo nan ungo wannan" yafaɗa yana wullo mata wani kullin magani kulle cikin kyallan atamfa
"Kimasa lemu ki tabbatar kinsa garin maganin nan to daga ranar sai abinda kika cewa mijinki duk abinda kika ce masa shi zaiyi zai manta da kowa da komai sai ke, hakama kishiyarki kowa nata zai manta da ita sannan zamu kafe ta a gidan komai zakiyi mata bazata iya barin gidan ba, gaba ɗaya dukiyar Mustapha ta zama taki sai abinda kika ga dama kika ce yayi shi zai yi" ranta ne yayi wasai taji gaba ɗaya kamar an yaye mata damuwar dake ranta, saidai jikinta ne yayi sanyi sanda taga Malam na saduwa da Lina ta bayanta anan ne hankalinta yata shi taga lina bata ko damu ba, agabanta ya kuma biyan bukatarsa da Feena, jikinta ne ya hau ɓari ganin malam na kallonta yana lashe baki
"Ki nutsu bazanyi komai dake ba, bama bukatar irinki akwai sauranki sai nan gaba kema zakiyi abinda suka yi juye mana kuɗin jakarki" gaba ɗaya ta zazZzage masa kuɗin cikin jakar suka fita da baya da baya"
"Lina mai naga kunayi da mutumin nan"
"Wannan ba huruminki bane Sumayya kiyi kallo kawai kuma karki sake ki bawa kowa labarin abinda kika gani mun aikata da boka, wannan wata bukatar ce daban" hotal suka kama suka kwana...✍🏻
[2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹
Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰
☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation
*Shafi Na Talatin*
Musty ke zagaya falon da gudu, yara da Aimanah na biye da shi suna dariya, kallo ɗaya zaka masu su matukar baka sha'awa Gwaggo Fulani na can karshan falon tana kallon ahalin dake cikin zallar nishaɗi, dukan su ba wanda ya iya kama Mustapha, zilliya yake masu kamar a filin kwallo, sai da yagaji dan kansa kana ya zube kan kujera Aimanah da yaran gaba ɗaya suka faɗa kansa suna faɗin
"Yee mun kama Abbie mun kama abie"
"Abie ni coculate zaka bani" Islam tafaɗa tana taɓe fuska kamar zatayi kuka
"Abi mu kuma sweett muke so ko Aslam" Tasnim yafaɗa yana kalllon Aslam
"Ba wanda zan bawa komai, sabida ba wanda ya iya kama ni"
"Harni?" Aimanah ta faɗa tana taɓe fuska kamar wata karamar yarinya
"Ni na'isa nace har ke, in ban baki sweet ba yaya zanyi da ita" yafaɗi haka yana shafa mararta, bakinsa kan kunnanta yake mata raɗa
"reina inajin kishi fa, kizo muje ki bani ruwa" yafaɗa da wata irin murya da sauri ta ɗago kai ta kalli cikin idanunsa waɗanda suka tabbatar mata da abinda yafaɗa
"Baby yara na nan fa?"
"Ni ba ruwana da wasu yara" yafaɗa yana mikewa tsaye, kallonta yayi da runan nun idanunsa da suka fara canza launi, lumshe su yake a hankali yana buɗe su akanta, bayansa tabi ganin ya nufi ɗakinsa, yaran ma suka bi su, cak suka tsaya daga bakin kofar ɗakin Mustyn sanda Mustapha ya shiga
"Amma, Abie ya shige bai bamu sweet ɗin ba, kuma kin hanamu shiga ɗakin sa" haɗa yaran tayi gaba ɗaya ta rungume su, dai dai nan Musty yafito da alawa da coculate yabawa kowa
"Mungode Abie Allah yakara arziki" yaran suka haɗa baki suka faɗa gaba ɗaya
"Amin maza ku wuce wajan Gwaggo ta ɓare maku sweet ɗin" da gudu mazan suka tafi, Islam ta makale jikin Aimanah tana yamutsa fuska
"Ammi na wuce kije kinji bazan jima ba, Abie zan sa yayi barci ya huta yanzu zan zo wajanki" sakin Amman tata tayi ta tafi tana waigenta, Mustapha jawo Aimanah yayi suka faɗa ɗakin
"Baby ka fiye rigima fisabilillahi da tsakar ranar nan"
"Aimah bazaki gane ba" yafaɗa sanda suka faɗa gado, ta buɗi baki zatai magana ya haɗe bakinsa da nata yafara aika mata da zafafan sakonni masu wuyar karɓa🚶♀️
Sumayya basu shigo Abuja ba sai dare hakan yasa bata sami damar aiwatar da aikinta ba ta bari sai washe gari, ai kuwa washe gari sai dare kana Mustapha yadawo yariga da yafaɗa mata, tun yamma ta gama haɗa komai har lemun daya sha maganin da malam yabata ta jere komai bisa danning jiran dawowarsa kawai take, bai shigo gidanba sai bayan sallar insha yana shigowa ɗakin yara yafara shiga ya duba su kamar yanda ya saba, cake ya basu sunata murna sannan ya fito Aimanah na zaune a falon tana aiki a systam ɗinta, ya tsaya ɗan nesa da ita kaɗan
"Sannu da dawowa Baby"
"Sannu fa, ya kike ya gida da yara?"
"Alhamdulillah gida lafiya" gaba yayi ya shiga ɗakinsa yai wanka ya shurya cikin jallabiya marun kana ya shiga ɗakin Sumayya dake kwance tana chat dasu lina,
"Sannu da zuwa"
"Yawwa"
"Muje ko abinci na danning" jerawa sukai zuwa wajan damning area ɗin yana cin abincin a hankali yana satar kallon Aimanah dake can nesa da su ta dukufa tana danna systam da alama aiki take mai mihimmanci, murmushi Sumayya tayi sanda taga yakai cup ɗin lemu bakinsa, nan take yaji kansa ya wani sara masa, yai lu zai faɗi, Sumayya ta tallafo sa kamar wani mai jin barci ta gaban Aimanah suka zo suka wuce Sumayya na rike da shi, maimakon ta kaisa ɗakinsa saita shiga da shi ɗakinta ta kwantar da shi kan gadonta tana murmushi ganin yanda yai lamo kamar mara lafiya,
Rawa tayi tai juyi ganin aikin ta yayi kamar yanda malam ya shaida mata, tana kallon yanda yake barci, malam ya tabbatar mata Wannan barcin idan yayi sa to yana farkawa zai manta da kowa, komai sai tace yayi sannan zaiyin, aiko hakance ta faru da asuba ya farka sai dai ji yayi jikinsa ya masa nauyi ya kasa ta shi, sai da Sumayya ta ce
"Kaje kayi sallah" kana yasami kwarin gwiwar mikewa yai alwala yatafi masallaci, ko acan wani iri yarinka ji Allah Allah yake a idar da sallar ya dawo gida yaga Sumayya
A ranar gwaggo fulani tasami labarin rasuwar babbar yarta tafiya ba shiri lokacin Mustapha na barci ɗakin Sumayya, ta kira wayarsa yafi a kirga bata shiga haka yasa tai Kncking na kofar Sumayya, lekowa Sumayya tayi tana kallon Aimanah a wulakance
"Barka da safiya Sumy, dan Allah ki faɗawa Baby Anma Gwaggo rasuwa zata wuce kano"
"Barci yake kuma yace kada a tashe sa" Sumayya nagama faɗar haka ta maida kofarta ta rufe tabar Aimanh baki buɗe, jiyowa tayi tana kallon gwaggo daketa rusar kuka Salman na lallashinta
"Salman zaka iya tuki zuwa kano?" Aimanah tafaɗa a sanyaye
"Bazan iya ba Anty bana cikin nutsuwa"
"Shiryawa gwaggo kayanta, saina kaiku tasha" Aimanah da kanta takai su Tasha ta biya masu mota shata ta ɗaukar masu sukai ciniki ta biya kuɗin motar, gefe sukayi da Salman ta basa Atm card ɗinta
"Salman karike wannan a hannunka dan Allah duk wata harka ta kuɗi inta taso ayi amfani da kuɗin ciki suna da yawa nasan zasu isa komai daga anyi bakwai ka dawo sabida makarantarka Gwaggo kuma ta zauna in mukazo kano nida Baby sai muje mu tawo da ita zuwa sannan ta gama amsar gaisuwa, motar har ɗanbatta zata kaiku na biyasa kuɗin sa"
"To Anty Mun gode Allah yasaka da alkhairi" Salman yafaɗa yana share hawaye
"Kadaina kuka Salman ka lallashi gwaggo Allah ya mata rahama ya raya abinda tabari"
"Amin" yafaɗa tana kallonsa ya shiga motar suka tafi tana ɗagawa gwaggo hannu, sai da taga futarsu daga tashan kana ta shiga tata motar taja itama ta tafi gida,
Aimanah canji tagani daga Mustapha daya zama ko kallon inda take bayayi bare kuma yaran, kwanaki huɗu kenan ko gaida sa tayi baya amsawa kullum yana ɗakin Sumayya daga yadawo a office ya shiga bazai sake futowa ba sai safiya, ko abinci Sumayya bata bari yaci nan falo sai dai a ɗakinta, tunda gwaggo ta tafi bataje aiki ba daman gwaggo take bari da yaran yanzu kuma bata nan, yau ta tarawa dawowar Mustapha haka yasa ta zauna nan falo tana jin tsayuwar motarsa ta fita compound ɗin da sauri dai dai zai shigo ita kuma zata fita, gefe tayi ganin yana kokarin ture ta, ta tsaya gefe
"Yaya Mustapha yaya zanyi da yaran nan inason zuwa wajan aiki fa"
"Kiyi duk yanda zakiyi da su, ke kada ma ki kara fita wannan aikin naki, and dan Allah ki rinka nesa dani banason ganinki" cak ta tsaya tana kallon Mustapha dake faɗar maganar nan cikeda mamaki, Sumayya dake tsaye jikin kofarta dariya ta saki tana tafa hannuwa kamar wata sabon kamu, hannun Mustapha taja suka faɗa ɗakinta, Aimanah bata gama shan mamaki ba sai washe gari da Sumayya ta risketa a ɗakinta lokacin ta idar da sallar asuba kenan tana azkhair na safiya,
"Mustapha yace ki wanke masa motar sa, sannan ya ce nagaya maki duk wani aikin gidan nan daga yau ke zaki rinka yi kama da gyara compound wanke motocin gidan nan bawa fulawowi ruwa dan na sallami mai kula da fulawoyin jiya" Aimanah a fusace ta mike tana kallon Sumayya sama da kasa
"Kije ki gaya masa bazanyi ba, ba aiki nazoyi gidan nan ba, ke Sumayya ki fita a idanuna miji ne kin janye sa nabar maki ki jiƙa abinki ki sha amma ki sani kinyi tsararo wallahi kisa na maki bauta a cikin gidan aure na" Aimanah na gama faɗar haka ta fice daga ɗakin zuwa kichin ta ɗorawa yara abin break, wayam taga store ɗin babu komai, afusace ta fito ta banka kofar ɗakin Sumayya ta shiga, Mustapha na zaune gefan gado yadafe kansa da'alama da abinda ke damunsa,
"Malama ina kika kai mana kayan abincin cikin store" Aimanah tafaɗa tana kallon tsakiyar idanun Sumayya
"Shi yace na kwashe su ana masa ɓarnar Abinci"
"Mustapha kai kafaɗi haka?" Aimanah ta tambayesa tana kallon sa, kai kurum yaɗaga alamar e
"Fine" Aimanah ta faɗa tana ficewa daga ɗakin, yaranta ta ɗiba suka fita babban store ta je tayo siyayya sosai ta jibge su a babban kicin ɗin dake comopound nan take komai nata daga ta gama tasa key ta rufe ta koma ɗakinta, Sumayya bayan Mustapha ya fita ɗaki ta koma tasa key ta kira lambar malam da fina ta bata bayan sun gaisa take masa bayani kan Aimanah
"Ranka yadaɗe malam yarinyar nan fa sam bata tsorona in na bata umarni bata yi, ɗazu fa kawai dan nace ta wanke mana motocin gidan nan baka ga yanda tayo kaina ba kamar zata dake ni"
"Sumayya yarinyar tanada hatsari banajin zan iya komai a kanta sabida a tsaye take kan ibada da azkhar amma zan duba inga ta inda zamu ɓullo mata"
"Yawwa malam ka duba ɗin dan Allah nasan dai ai babu abinda ya gagare ka" shekewa da dariya malam kibauu yayi kana ya kashe wayar sa.
Murjana kuka sosai take tana kallon Amarya dake zaune da wata yaloluwar doguwar rigar barci da alama bata jima da tashi a barci ba
"Mama banajin daɗin ganinki da nake a wannan gidan da aka maida tsaɓon Allah ado a cikinsa, Mama dan Allah kizo muje ki bawa Abbanmu hakuri yamaidaki ɗakinki, inma bazaki koma gidan ba ki koma katsina gaban iyayanki please mama, abinda yakamata ace mu mukeyi kina mana faɗa shi kike yi mama" Mirja tafaɗa cikin matsanancin kuka
"Murja ki fita sabagata kin riga kin girma kinyi hankalin kanki ki zaɓi rayuwar dazakiyi nima na zaɓi tawa, ca nake nan nazo maki da zaɓi na kika nuna ban isa ba kika zaɓi wanda ranki yake so, kije ki zauna da shi, yanda bana zuwa inda kike nima dan Allah ki nesanta kanki dani, basu Saudatu kika maida iyayanki ba to kije na bar masu ke"
"Mama...Murja ki fita nace kafin na saɓa maki" murja mikewa tayi ta futa tana kuka, motar Alhaji Jamil dake jiranta a kofar gidan ta buɗe ta shiga ta zauna a mazauni gaba tana ci gaba da kukanta,
Ahankali Alhaji Jamil ke tuki har cikin ransa yake jin kukan da Murja keyi hakan yasa ya faka motarsa gefan hanya ya kashe ta yai shuru yana sauraron shashshekar kukan Murja
"Murjana dan Allah ki daina kukan nan, nasan dai akan mama taki amincewa ta koma gidan Abba ne, kiyi shuru kuka baya maganin damuwa kiyi addu'a itace maganin duk wata masifa" Kai kurum ta ɗaga alamar to kana ta ɗago fuskarta tana share hawayanta da hijab ɗinta
"Haba ko kefa, jibi yanda kika ɓata min kyakkyawar fuskar nan taki" Murmushi Murja tayi tana daɗa jin son mijinta can kasan zuciyarta, Alhaji Jamil tukinsa yaci gaba jefi jefi yana kallon Murja, tausayi take basa sosai, ganin yanda batai dacan uwa ba, a zaman da yayi da ita ya fuskanci tanada saukin hali rashin dace da mahaifiyar kwarai da batayi ba shiya jefa ta ga rayuwar bariki wacce ta dalilinta har tayi rashin mahaifarta, yana matukar tausaya mata musamman ganin yanda take matukar kulawa da yaransa uku gaba ɗaya komai nasu itace tun sanda ya aureta kulawarsu gaba ɗaya ta dawo kanta musamman in suna kasar, daman Mamansu ba wani kulawa take da su ba aikin ta da kasuwancinta su kawai tasa a gaba nanny ke kula da su da ita suka saba sai bayan zuwan Murja suka san daɗin uwa.
Abbas ya shafi cikin Rumana mai watanni biyar, yana murmushi
"Kana son cikin nan dayawa Hayatie"
"Sosai nake son sa, karo na farko ciki ya kai wata biyar a mahaifarki insha Allah wannan zai zo duniya"
"Allah yasa Hayatie, ni duk bansa rai ba kawai ji nake a kowanne lokaci zamu iya rasa sa kamar yanda muka rasa guda uku a baya"
"Ki daina faɗar haka dan Allah masoyiya insha Allah zamu ga ƴaƴanmu harma da jikoki"
"Anya kuwa, kasan yanda nakeji kuwa ni kaɗai nasan azabar da nake sha gani nake kamar mutuwa zanyi hayatie" Rumana ta faɗa tana fashewa da kuka, gaba ɗaya hankalin Abbas yatashi ya rungumota jikinsa ahankali yana share mata hawaye
"Ki daina ambaton mutuwar nan Rumy ki daina bana so, in kika ci gaba wata rana zakisa zuciyata ta buga na rigaki barin duniyar, zuciyata zullo take aduk sanda kika ambaci mutuwa, muna tare ni dake zamu rayu tare zamu mutu tare Insha Allah rana ɗaya lokaci ɗaya zamu mutu amma ba yanzu ba" yafaɗa yana sumbatar kumatunta.
Sumayya malam waya yayi mata akan tazo ga aikinta ya gama ta karɓa, hakan yasa washe gari ta ɗauki hanyar enugu, a jirgi taje shiyasa bata wani ɓata lokaci ba tana zuwa tsaunin da malam yake tahau kamar yanda sukayi wancan zuwa wannan karan ma hakan tayi malam wata koshashshiyar mage ya wullo mata ta cafe
"Kishiyarki nada hatsari sosai, indai wani abu zamiyi mata bazai taɓa kamata ba, sai dai na biyo mata ta bayan gidan, wannan magen da kike gani kisata a karkashin gadonki kar ki bata abinci ba ruwanki da ita, ga wannan" yasake wulla mata garin magani a cikin kwalba
"Ki jika shi ki sha, sanda zaki sha ki ambaci sunan kishiyar taki zata rinka jin tsoronki kuma duk umarnin da kika bata zata bi, hhhhhhh gida ya zama naki yarinya sai dai mumada sharaɗi zaki daina sallar asuba da