Showing 84001 words to 84763 words out of 84763 words
Chapter 29 - AIMANA Book Complete by MAMI YUSUF DABO.txt
nan baya ki share ɗakin ki ki zauna"
"Ammi ya..." Ammi ta katse Mustapha da faɗin
"Yimin shuru Mustapha, ka ɗakko duk wani abu da kasan nakane kabar mata gidan ta zauna tana ɗauke da cikinki har yanzu nauyinta na kanka har zuwa sanda zata haihu ta yaye ɗan"
"Ammi bazan taɓa barin jini na a wajan Wannan bakar kadarar ba, tana haihuwa zata bani ɗana ko nononta bana bukatar ya sha bare ya gado wasu muna nan halinta" Sumayya dai mikewa tayi tana yiwa Ammi godiya tanan cikin gidan tabi kofar da zata sadata da gidan nasu, juyi tayi tai tsalle ta kwanta kan kujera ganin burinta nason komawa Mustapha yafara cika, lambar malam ta kira sai dai taki shiga jiki san yaye ta shiga ɗakinta ta faɗa gado tai kwanciyarta ba sallah bare salati daman tuni ta daɗe da jingine sallah a babin rayuwarta, Ammi tasa Mustapha yaturawa Sumayya dubu ɗari a account ɗinta danta rinka samun abu mai kyau tana ci,
Mustapha rai ɓace ya dawo cikin gidan nasa yaɗau duk wani abu daya san nasa ne ya maida sa ɗakin Ahmad acan yagama week end ɗinsa safiyar Litinin yabi jirgin safe ya koma Abuja, sanda ya koma gida sai yaji gidan yai masa faɗi shi kaɗai ba motsin kowa, ko ina ya kalla sai moment ɗinsu da Aimanah ke faɗo masa rayuwar da suke tare itada yara da yanda yake shiga cikinsu suyita tsalle tsalle wani bin harda tsairan gudu, hawayan fuskarsa ya share yana jin zuciyarsa ba daɗi, ba shiri yabar gidan ya nufi wajan aikinsa, Sumayya tana ganin alart ɗin dubu ɗari daga Mustapha har rawa ta taka tana cewa gobe sai enugu wajan malam, sai dai safiyar litinin ɗin Ammi tazo har gida tasata a gaba sukaje asibiti duk wasu abu daya dace ayiwa mai ciki shi aka mata sannan aka bata ranar dazata dawo awo, safiyar talata kuwa Sumayya sassafe tabi mota zuwa enugu, sai dai tayi rashin sa'a ta tarar bukkar Malam a kone kurmus a wajan wasu take jin labarin ai kawai gani akayi bukkar ta kama da wuta ta kone malam ɗinma a kone aka fito da shi wuta duk ta gama kone sa a haka aka bunnesa, ko kaɗan bataji zuciyarta ta yi laushi ba saima cin alwashi datayi zata nemi wani malamin daga zarar ta koma kano.
Aimanah rayuwarta take ta jin daɗi da walwala tuni ta koma B U K ta ɗora da karatunta, ta koma gidan redion data ke aiki da taci gaba da aiki da su, yara na hannunta shi yasa hankali kwance take rayuwarta har kiba tayi ta kara haske, Yasar ya matsawa rayuwarta duk da ya koma Madina amma kullum yana nacin kira akan ta amince da soyayyarsa ta taimaki rayuwarsa a ɗaura masu aure ta biyosa madina su zauna, ita sam yanzu aure baya gabanta karatu da aikinta kawai tasa a gaba, koda zatayi aure ma batajin zata auri saurayi bare Yasar data ke ma kallon da kaɗan ya girme ta a yanda take zato yasar bazai wuce sa'an Ma'aruf ɗin gidansu ba, har Ɗanbatta taje ta ɗakko Gwaggo Fulani suka ci gaba da zama tare tana kula da yara, Mah na Saudiyya wajan mijinta Tuni suka koma har Ma'aruf da ya kamu da soyayyar Azinatu harma manya sun shiga an tsaida masu ranar biki, shiyasa Yasar yake ta mata nacin ta Amince sai ayi bikin tare danasu Yaya Ma'aruf ɗin, Mustapha tunda ya koma Abuja bai dawo kano ba sai da ya shafe watanni biyu sai dai suyi waya da Ammi yaransa ma yasa an kawo masu waya sabuwa dal a kwali Gwaggo Fulani ke haɗasu da yaran su ɓata lokaci suna hira, Aimanah na kallonsu wani lokacin har vidio call zata ga anayi, Musty yasha kiran wayar Aimanah bata ɗagawa sai dai kullum kamar shan maganin bature sai ya mata tex messages sau uku a rana duk da bata taɓa masa reply ba bai fasa ba, Maza da dama na zuwa wajan Aimanah masu santa da aure amma ko kaɗan bata taɓa bawa wani dama ba, wani Alhaji Sadam ne ma takan ɗanyi waya da su kusan kullum shi tana ganin mutumchi da kimar sa yaransa biyu mata maman yaran ta rasu shekaru biyu kenan bai kara aure ba acewarsa yana neman wacce zata iya kula masa da yara bai samu ba sai da yaga Aimanah yaji a ransa itace wacce yake fata da burin ta zama matarsa yana ganin zata kula masa da yaran sa, ya mata alkawarin da zarar ya aure ta ta tawo da yaranta zai haɗa duka ya rike su.....✍🏻