Showing 51001 words to 54000 words out of 84763 words

Chapter 18 - AIMANA Book Complete by MAMI YUSUF DABO.txt

yau harta kwanta barci ta tina da Alhaji Jamilu da sauri ta cire lambarsa daga black list data saka sa bugun farko yaɗaga jiki na rawa ya ce
"Murja nayi kewarki kwana dayawa sau uku ina zuwa kofar gidanku nayita zama amma bana ganin gilmawarki yanzu ina zamu haɗu?"
"Alhaji kana sona zaka aure ni?"
"So! sosaima kuwa nake sonki Murja, aure kuma ko yanzu kika ce na fito zanzo ga iyayanki" Numfashi Murja ta sauke kana ta ce
"Ok kazo wajan mahaifina kuyi magana"
"Nayi matukar farin ciki Murja Allah yabamu zaman lafiya amma dai kinsan sai kinyi istibira'i ko"
"Na riga da nayi free"
"Ok ki gayawa Abba gobe zanzo mu gana"
"Allah ya kaimu" tafaɗa kana ta kashe wayar ta,

"Aimana yanzu in kika bini yaya zanyi da Sumayya?"
"Ni mai yayi ruwana da wata aba Sumayya ni mafita ta kawai nake nema, inka tafi kabarni yaya zanyi, ina zanji kamshinka nidai Allah binka zanyi" tafaɗa tana dire kafafu irin na shagwaɓaɓɓun yara, dariya yayi yana kallon yanda take kamar wata karamar yarinya, rigima da shagwaɓar Aimanah suna kara narkar da shi a kogin sonta
"Ok dariya ma kake min ko, nidai a zubar da cikin nan tunda ai shine yajamin nakeson kamshin turaranka"
"A'a reina kar ayiwa boy ɗina sharri fisabilillahi kwalba nawa ta turarena na ajje maki amma sai kice ke ba shiba na jikina kike so kawai dai nagano wayon so ake ayita zama a jikina"
"Allah ba haka bane" tafaɗa tana faɗawa kan gado haɗe da fashewa da kuka, zama yayi kusada ita ya ɗagota ya haɗata da jikinsa yana kallon fuskarta kana yasa hannu yana goge mata hawaye
"Kinga zaki ɓata min kyakkyawar fuskar nan taki nifa wasa nake maki, tashi ki haɗa kayanki jirgin yamma zamubi motarki da kayan nayi magana da Anty Halima driver ɗinsu zai tafi da su can legos inya kai sai ya biyo jirgi yadawo" tsalle tayi ta ɗane Musty tana ihun murna
"Nikam Aimah zanga randa zaki girma" hara ta masa irinta masoya batace komai ba taci gaba da abinda take, fita yayi zuwa kasa wajan Sumayya

Tana tsaye a ɗakin nata rike da waya suna magana da Amarya, shigowar Mustapha ɗakin yasa ta katse kiran tayi zuru tana kallonsa, zama yayi gefan gado ya nuna mata kusada shi ya ce
"Sumy zoki zauna muyi magana" ba musu ta zauna inda yace ɗin, jimm yayi na ɗan lokaci har saida ta ɗago kanta ta kallesa taga shima ita yake kallo kasa tayi da kanta tana murmushi
"Sumy kiyi hakuri da abinda zan faɗa ki fahimceni please"
"Ina jinka" tafaɗa tana wasa da zoban hannunta
"Zan tafi da Aimanah legos" da sauri ta ɗago ta kallesa sai kuma tayi kasa da kanta hawaye masu ɗimi suka biyo kuncinta
"Shi yasa nace ki fahimceni Aimanah nada juna biyu, tunda ta sami cikin nan take son kamshin turare na, na ajje mata su dayawa amma sai tace na jikina take so yau ranar komawata legos ta tubure saita bini na rasa yanda zanyi da ita shiyasa nazo na roki kimin alfarma natafi da ita"
"In naki yin alfarma fa?"
"Dole ta zauna ai bazan shiga hakkin ki ba"
"Hakki kuma na nawa Musty, ca nake nan kasai mata motar sama da miliyan talatin ni kuma kasaimin wacce bata kai miliyan goma ba"
"Sumy kibar maganar motar nan, kyauta ce na mata tun tuni na kudurce a zuciyata zan mata wannan kyautar tun kafin ki shigo rayuwarmu, Sumy bazan ɓoye maki ba kin rigada kin sani Aimanah itace jini da tsokata itace bugun numfashi na karki soma kwatanta kanki da ita ina matukar iya bakin kokari na na kamanta adalci a tsakanin ku shiyasa kema na sai maki mota" tabe baki tayi ta tashi zata fita a ɗakin sai da takai bakin kofa sannan ta juyo ta kallesa
"Na amince ku sauka lafiya" fita tayi daga ɗakin ta faɗa ɗakinta ta fashe da kuka, tabbas ayau basai gobe ba zata barwa Mustapha gidan sa bazata zauna kishi ya kasheta ba, to in kuma nabar gidan yasakeni ina zan zauna gidan mahaifina ba daɗi Mama tabar gidansu Mustapha ina zan kama tabbas dole na zauna a ɗakin mijina in yaso na nemi mafita kawai, ko Mama zanyiwa magana mu koma wajan tsito a farraka tsakaninsu kai ai kuma komai daɗewa asiri zai karye ga zunibi ga ba biyan bikata, ita kaɗai take ta zancan zuci har barci yayi gaba da ita tanata barci Mustapha suka tafi bata sani ba saida ta tashi a barci taga massages na Mustapha yana sanar mata sun wuce yazo suyi sallama ya tarar tana barci in sun sauka zai kirata a waya

Rayuwa mai daɗi da kwanciyar hankali Aimanah keyi a legos tayi kiba ta kara yin fresh, kullum suna tareda Musty daga yadawo daga office baya kuma fita ko ina yana gida tare da Aimanah kulawa ta misamman yake bata yana, duk friday yake zuwa kano yayiwa Sumayya kwana biyu ya koma legos,

Aimanah ta tsaye a kicin tana soya irish Mustapha ya shigo kicin, rungumeta yayi ya zagaye ta da hannunsa ɗaya ɗayan kuma yana shafa cikinta
Reina yakamata ki rinka samun hutu fa tun asuba kina nan kina fama nace zan samo maki mai aiki kinki yarda"
"Allah ya kiyaye baby inban kula da kai wazanyiwa ni bana bukatar wata mai aiki kawai ta kwace min kai" dariya Musty yayi haɗi da kwantar da kansa a bayanta yana lumshe idanuwansa
"Reina zuciyata taki ce ke ɗaya ko bake a duniyar nan bana jin zan so wata bayan ke, ina sonki ina kaunarki! zuciya da ruhi duka na begenki hmmm reina baki yayi kaɗan ya iya bayyana kalar son danake maki ki kalli cikin idaniya su kaɗai sun isa su bayyana maki kalar so da kaunar danake maki, ko yaushe in ina tare dake ji nake kamar nan duniya gaba ɗaya babu sauran kowa daga ni sai ke Aimah I love you"
"Love you tuch baby" tafaɗa tareda sumbatar hannunsa,
"Kawo na karasa kije ki huta bari zan haɗo komai"
"A'a baby kabarni na karasa ladana"
"Nima ki bari na sami ladan, kije kawai bana son musu Aimah" hannunta tasa ta kunna famfon sink ta wanke hannunta ta fita, tana zuwa wanka ta faɗa ta shirya cikin farin wando dogo da karamar riga black colour ta ɗaure gashinta waje ɗaya bata saka hula ba ta fito falo tana danna wayarta, ya gama haɗa komai yana zaune a danning area yana amsa waya, kujerar kusa da tasa taja ta zauna tana kallon yanda yake dariya da alama ko da wa yake waya wayar na masa daɗi
"Aboki bazaka gane bane abar maganar nan sai anyi bikinku da Surry zaka bani labari" tana jin haka ta gano da yaya Mas'ud yake waya, bataji mai yaya Mas'ud ɗin yace ba taji Musty na faɗin
"Kaga gimbiyya na kusa bazaka cinye mata sauran lokacinta ba in na shigo kano ma karasa maganar amma dai nace ka zaɓi India kasar nada daɗin zama" bai jira abinda Mas'ud zai ce ba ya katse kiran, yaja plate yana zuba mata soyayyan irish ya mika mata gabanta tea ya haɗa mata yasa tea spoon cikin mug ɗin ya ce
"Ha na baki a baki"
"Zan iya jira ka bani kuwa nifa yunwa nakeji sosai" ɓata fuska yayi yana mata hararan masoya
"Nidai saina baki Allah" yafaɗa a shagwaɓe haɗi da ɓata fuska
"To naji gashi na buɗe bakin" Irish ɗin ya ɗiba ya zuba mata a baki ta soma ci a hankali, saida ya tabbatar ta koshi kana ya kyaleta
"Baby nima tsaya na baka" zama ya gyara ta ciyar dashi cikeda kauna, har wajan mota ta masa rakiya tanata masa shagwaɓa harya kusa makara yatafi tana ɗaga masa hannu, sai da get man ya rufe get san nan ta koma ciki, gyara ko ina tayi ta sannan ta shiga kicin ta tarar ya wanke kayan da sukai amfani da shi, ta wanke plate da Mug ɗin da sukai amfani dasu ta wuce bedroom ta kwanta, bata tashi ba sai azahar sallah tayi tai wanka ta zauna suna chat da Rumana datake bata labarin rayuwar da suke itada Abbas tana mata godiya bisa zaɓin data mata, ganin biyu da rabi har tayi yasa ta mata sallama ta wuce kicin, wake ta ɗora a electry kana ta ɗora shinkafa kan gas ta ɗebo kayan miya ta wanke ta saka hand clove ta gyara kayan miyan ta cire dattinsu ta sake wanke su sosai da gashiri kana ta markaɗa su a blandar kafin la'asar ta gama haɗa lafiyaryar shinkafa da wake da miyar dake ta tashin kamshi ta yanka salad tumatir cucumber da albasa har green pepe ta zuba haɗaɗɗiyar kula ta kawo su dannin area ta ajje, salla taje tayi bayan ta idar azkhar na maraice tayi ta ɗau wayarta ta kira Mustapha, bugun farko yai pickin call ɗin
"Barka da aiki Rayuwata"
"Barka dai habibiya"
"Baby inajin yunwa fa baka dawo ba har yanzu" shafa kansa yayi yana murmushi yayinda kujerar dayake kai ke juyawa da shi, sai wani kumshe idanu yake da gani wayar na masa daɗi
"Beb kici kawai, ayyuka sun rikeni Aliyu baya nan ya haɗamin aikin office ɗinsa da nawa gaba ɗaya ni nake yi inaga sai mangari ba zan da wo"
"To abincin fa? haka zakayita zama bakayi lonch ba gaskiyya bazan laminta ba, sai yunwa ta kama min kai,"
" zan.." A'a Baby karka gayamin zaka ci abincin waje, Allah bazan yarda ba, ko nazo na kawo maka nan"
"A'a bari na turo driven mu na office ya karɓar min ki bawa Joseph in yazo sai ya basa" dariya Aimanah tayi tana mamakin kishin Mustapha
"And kisa hijab kuma basai kin masa magana ba zan masa waya"
"Baby"
"Uhmm bebyn baby yane" .
"I love you" kissing wayar tayi kana ta katse kiran, tayi kamar yanda ya ce, bai dawo gidan ba kuwa sai gabda sallar insha, wanka kurum yayi ya fita masallaci dake nan kusada gidan, wajan takwas da rabi ya shigo gidan ya tarar tana zaune a danning area, can ya isketa yana mata sannu, soyayyar taliyar da tayi wadda taji kayan lambu ta zuba masu a plate suna ci a hankali suna hira jefi jefi

A kano tuni aka ɗaura auran Murjana da Alhaji Jamil ta tare a gidansa da yake tare da matarsa anan tarauni , sam bata sami matsala da matar saba mace ce yar ba ruwana aikinta kawai tasa a gaba sai dai ta kula tana yawan tara mata a sashinta datayiwa Alhaji Jamil magana yace ai tana business ne shiyasa, ganin bata shiga sabgarta itama saita kama kanta kusan ma ba zaman kasar suke da ba kullum suna tafe itada Alhaji Jameel data zamo masa jela.

*Gidan Abbas*

Ruma na kwance lamo kan kujera yayinda Abbas ke zaune kan carfet yana aiki a laptop ɗinsa, jefi jefi yake kallon ta ganin yanda take juyi kan kujera
"Rumy yane?" yafaɗa yana barin danna laptop ɗin dayake
"Hayatie cikina ciwo wayyo ƴa'ƴan cikina zasu zubo" da sauri ya mike ya karasa kusa da ita ya ɗagota ya haɗata da jikinsa
"Daman bakida lafiya baki gaya min ba mai yasa kika ɓoyemin"
"Yanzu ne fa, yanzu naji cikina na ciwon wayyo zan mutu" tafaɗa tana juyi tareda wata mika, gaba ɗaya hankalinsa yata shi lambar nurse jamila dake cikin barreck ɗinsu yake kira amma bata shiga, da sauri ya mike ya ɗauki Rumana cak ganin idanunta sun kakkafe, yafita da ita yana kwalawa jakop direver ɗinsa kira da sauri jakop ya karaso inda uban gidan nasa ke kiran sa
"Jakop maza ɗakko mota muje hospital Rumy ba lafiya" yafaɗi haka yana leka idanunta dayaga sun kafe waje ɗaya
"Jakop" yafaɗa da karfi hankali tashe a bayan mota ya kwantar da ita yana tukin da hankasa, mahaukacin gudu yake bisa kwalta yanayi yana juyowa yana kallon Rumana dake kwance kamar gawa....✍🏻
[2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹


Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Ashirin da bakwai*

*Wannan page ɗin gaba ɗayansa sadaukarwa ne ga yan Aimanah real fans group 2 comment ɗinku na matakur sani nishaɗi ina godiya da kulawa mutane na*

Hankali tashe likitoci suka karɓi Rumana akai emargency da ita, tsananin tashin hankalin da Abbas ke ciki yasa ko gabansa baya iya gani, Jakop ya taimaka masa ya zauna a recepsion yadafa kansa yayinda shi Jakop ɗin ke zarya tsakanin inda Abbas yake da inda aka kwantar da Rumana
"Ina yan uwan Rumana Mahmud" da sauri Abbas ya mike tsaye yabi likitan zuwa office ɗinsa, kujera ya nunawa Abbas dake tsaye kikam a kansa, ba musu ya zauna zuciyarsa na dukan uku uku
"Sorry matarka tayi ɓarin cikin wata biyu" a razane ya ɗago idanunsa yana kallon likitan, hawaye suka zubo daga idanunsa shikenan sun rasa wannan cikin da suka kwallafa rai a kansa, ya Hajiya zataji idan taji wannan labarin mai tada hankali
"Kayi hakuri mahaifar Rumana nada rauni koda ta sake samun wani cikin banajin zai zauna sai dai zamu ɗorata kan magani sannan zata cigaba da zuwa ganin likita duk bayan sati biyu" Abbas kansa kawai ya ɗaga alamar yaji, Dr ya mika masa takarda ya ce
"Ga wannan asiyo waɗan nan magungunan da allurai" karɓa Abbas yayi ya fita, Jakop yabawa takardar shi kuma ya shiga ɗakin da aka kai Rumana, tana kwance samɓal saman gado kamar gawa ko motsi batayi a kallo ɗaya daya mata yaga ta rame sosai kamar wacce ta shekara tana cuta, hawayan idanunsa ya share ya sumbaci kuncinta ya fita daga ɗakin, recepsion ya koma ya kira wayar hajiyarsa bugu ɗaya a na biyu ta ɗaga
"Soja mazan fama barka da yamma ya surukata"
"Hajiya" zuciyarsa ce tai wani irin rauni ya na shashshekar kuka ya ce
"Rumy tayi ɓari"
"Ɓari! innalillahi wa'inna ilaihir raji'un yanzu tana ina?"
"Muna hospital"
"Kamata sannu zan biyo jirgi na tawo na kula da ita"
"Hajiya basai kinzo ba zan kula da komai"
"Malam Abbas kabari kawai nazo, kaga yanayin aikin ka yanzu ma ana iya kiranka batada kowa a Abuja wazai zauna da ita kabarni kawai nazo"
"Shikenan Hajiya Allah yakawo ki lafiya" Abbaa komawa ɗakin yayi yaja kujera ya zauna kusada gadon hannunta na cikin nasa, motsi tafara yi kana ta buɗe idanunta, lemar dataji a kasanta yasa ta kankame hannun Abbas dake cikin nata
"Hayatie maiya same ni mai ya sami cikina?"
"Ba abinda ya sameki Rumy kina lafiya, haka cikin ki ma yana lafiya"
"A'a Hayatie ka faɗa min gaskiyya jini ne fa yake bina"
"Kinyi ɓari ne" Abbas yafaɗa a sanyaye
"Cikina ta zube wayyo Allah na"
"Kiyi hakuri Rumy kwana nawa ne zamu sami wani dan Allah karki saka damuwa a ranki Allah shiya bamu wannan lokacin da bamu zata ba ko tsammani, shi zai kuma bamu wani kilama ki mana tagwaye" yakarasa faɗa yana murmushin karfin hali, Rumana maida kanta tayi ta kwantar haɗeda runtse idanu hawaye na zubowa daga idanunta, Hajiyar Abbas a ranar tazo ita taci gaba da kulawa da Rumana.

*Musty Home*

"Baby danna min kafar nan sosai zugi takemin bakaji azaba ba" Mustapha dake matsa mata kafa kara himma yayi tareda aika mata sannu akai akai tausayi take basa sosai ganin yanda ta kumbura musamman kafafunta da suka tasa cikinta mai wata huɗu inka kallesa zakace yakai watanni bakwai sabida girmansa, wayarta dake kusa da shi ce tayi kara alamar kira ya shigo hannu yasa ya ɗauka ya mika mata cikeda ɗoki ta ɗaga ganin Rumana ce ke kiranta,
"Hasbunallahu wani'imal wakil" Aimana ta faɗa a razane tareda sakin wayar tata ta faɗa kan cinyarta, a razane Musty ya ɗago ya kalli Aimanah dake kokarin mikewa tsaye
"Ke maine wai nutsu Aimah"
"Baby Rumana ce a asibiti tayi ɓari" tsaki yaja yana cigaba da abinda yake a fusace ya ce
"Shine kika ruɗe haka, dan tayi ɓari Allah zai basu wani ai" saroro tayi tana kallonsa cikeda mamaki
"Baby Rumana fa!"
"Rumana maizan mata fatan samun lafiya kawai zan mata" fusge kafarta tayi ta mike
"Nidai Abujan zan tafi naga lafiyar yar uwata"
"Kiga lafiyar yar uwarki ko ki gano masoyinki"
"Mustapha" Aimana ta faɗa cikeda mamakin maganarsa, bai ɗago ya kalleta ba saima danna wayarsa daya fara yi ganin bai kulata ba yasa taci gaba da magana
"Nidai wallahi sai naje na duba Rumana yaufa kwananta huɗu a hospital ta kirani ta gayamin sannan kace bazani ba Allah sai naje naga yar uwata" kanzil baice mata ba saima tashi da yayi yabar mata gidan, bai dawo gidan ba sai batan sallar insha abinda bai taɓa mata ba matsawar yana gari baya fita ko ina ko wani uzirin ne ya kamasa na fita tare suke zuwa ko ina ne, a ɗakinsa ta kwanta ya shigo yana ganinta baice mata komai ba yai shirin barci ya kwanta can karshan gado nesa da ita sosai, ganin haka saita juya baya, washe gari kafin ta tashi yagama haɗa break yaci nashi yabar mata nata nan saman danning ya wuce office
"Kam bala'i" Aimana ta faɗa sanda taga abinda yayi agidan kicin ta wuce ta haɗa abinda takeso taci ta ajje sauran, saida ta fuskanci lokacin dawowarsa yayi ta koma ɗaki ta kwanta lamo kamar mara lafiya, tana ganinsa ya shigo ɗakin da sallama kasa kasa, suit ɗinsa ya cire ya ɗaura tawul ya wuce bathroom bai kalli ko inda take ba, yana fitowa daga wanka ya ganta zaune kan gado tana kuka kasa kasa ba karamin juriya yayi ba ganin bai kulata ba, jin kukan yake har cikin ransa, ta gefan idanunsa yake kallonta yayin da yayi kamar baisan tana yi ba, wayarta ta ɗauka ta kiran layin Ammi
"Ammi Mustapha zai kashe ni daga nace zanje na duba Rumana shikenan yaɗau fushi dani ya daina kulani ya daina cin abinci na yama daina kwana a ɗakin danake" murmushin gefan baki yayi yana satar kallonta ganin yanda take haɗa masa karya a gabansa ko kunyarsa bata ji
"Shi mai babban sunan yamaki haka, cab bari na kirasa naji dalilin da zaiwa yar Ammi haka kuma ki soma shiri gobe zaki gano yar uwarki" kwalo tayiwa Mustapha a zatonta baya ganinta, Musty yana ganin kiran Ammi yaki ɗagawa saima barin ɗakin dayayi da wayar a hannunsa, saida ya futa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login