Showing 72001 words to 75000 words out of 84763 words
Chapter 25 - AIMANA Book Complete by MAMI YUSUF DABO.txt
kuɗi ya ce yaje gidan abinci mafi kusa ya yo masa take away ya juya ya koma ciki
"Yaya Aimah wai ina yayanmu"
"Shaheed muna cikin matsala" karo na farko data buɗi baki ta iya gayawa wani halin datake ciki a gidan kuka sosai Shaheed keyi, kamar wani karamin yaro
"Sannu yaya sannu yaya Aimah insha Allah saina fitta ki daga wannan halin, yanzu bazaki iya fita daga gidan nan ba, muje ki ga ya mike shiya taimaka mata tasa hijab ya ɗauki islam da jikinta ya saki sosai ga zafi da jikin yayi, ya ruko hannun Aslam da Tasnim cak taja ta tsaya lokacin da suka je bakin get
"Shaheed gasu nan za su kashe ni, Shaheed mage ce gata can a kofar fita bazan fita ba katafi da yaran kaje ka sanar da halin da nake ciki, ga wasu nan zasu hanaku tafiya shaheed fita da sauri" hannu tasa ta tura su waje ta mai da kofar ta rufe gam, tana jin sanda Shaheed ke faman kwaɗa mata kira, zama tayi jikin get ɗin
"Shaheed ka kai yaran nan wajan Ammi ku maza ku tafi kafin Sumayya ta dawo bazata bari ka tafi da su ba" Shaheed jiki a sanyaye ya saka yaran cikin motar data kawo sa a ciki ya basu abincin sukaci sosai har mamakin abincin da sukaci yake, ya kalli agogon hannunsa yaga jirgi tuni ya tashi kusan da mintina biyar kenan
"Baba kaini tashar da zan sami motar da zata kaini kano" kai kurum baban ya gyaɗa yana cigaba da tukinsa har yakaisu ta sha kuɗi sosai Shaheed yabawa driver ɗin ya sami wata motar su kaɗai yabiya suka ɗau hanya, yana rungume da Islam wacce yakejin kaunar yarinyar ta daban data yan uwanta, Tasnim na gefansa na dama yayin da Aslam ke gefansa na hagu sun kwantar da kansu a jikinsa sunata barci, gafda zasu shiga kano Islam ta fara kelaya amai kamar zata amayar da hanjin cikinta jikinta ya ɗauki rawa idanunta na kafewa, gaba ɗaya hankalin Shaheed yatashi sai cewa mai motar yake
"Dan Allah ka taka motar nan sosai mukai yarinyar nan hospital karta mace min" Aminu kano hospital suka je da wayar driver ɗin yayi amfani ya kira wayar Ammi, Ammi dake tsaye gama wayarta kenan da Ahmad wanda ke sanar mata jirage biyu kenan na sauka daga Abuja amma ba shaheed a ciki zai taho gida, gaba ɗaya hankalinta ya tashi tunani take maiya sami autan nata a yanda suka lissafa karfe sha ɗayan rana a kano zatai masa gashi yanzu magana ake ta huɗu harda kwata na yamma, jikinta ya kuma yin sanyi ta zurfafa cikin tunani har tsorata tayi sanda taji wayarta tayi kara, kamar bazata ɗaga ba ganin lamba ba suna sai kuma ta ɗaga sanda kira na biyu ya kuma shigowa wayar
"Ammi ina hospital kiyi maza ki zo dan Allah"
"Shaheed kana lafiya wanne asibitin maiya sameka yimin bayani"
"Ammi ina lafiya, kizo dai nan Aminu kano" cikin ruɗewa ta fito, tareda Momy suka tafi bayan ta mata bayanin Shaheed ya kirata, Ahmad ta kira tace su haɗu a can Ammi duk gudun da Momy keyi da mota gani take kamar sanɗa take ta kagu taje taga maiya sami ɗanta, yana tsaye sanda suka karasa a wata farfajiya ko gama dai daita motar batayi ba Ammi ta fito tana taɓa Shaheed
"Lafiya mai kake a hospital," baice komai ba yaja hannun Ammi suka shiga wani ɗaki, gaba ɗaya yaran suna kwance a gadajansu harsu Aslam yasa a binciki lafiyarsu
"Ammi kuna kasar nan amma yaya Aimah na cikin wani hali ba wanda ke bin ta kanta kun mata adalci kuwa?" Ammi kanta ne ya sara tai saurin dafa kan tareda dafa bango
Aimana tana turasu wajan get ɗin ta zauna wajan tareda fashewa da kuka wasu halittu ke mata gizo a idanunta kamar zararriya ta kwasa a guje ta shige gidan dan zamanta a wajan jitake kamar ana ɗaureta da igiya ɗakinta ta shige ta kwanta ta lulluɓa cikin blanket rufe idanu tayi har sannan tana hango haluttun nan na mata yawo cikin idanu buɗe idonta tayi tar wai tana karanto suratul bakara da karfin gaske, batayi nisa tana karantawa ba barci yayi awon gaba da ita tsawon awanni tana barci mai daɗi wanda ta jima batayi irin saba sai yamma sosai ta farka, durowa tayi daga gadon ta shiga bayi tai alwala ta tada sallah tai azahar kana tai la'asar tana nan zaune tana azkhair wanda ta jima sosai batayi ba taji an buɗe kofar ɗakinta, kallon kofar tayi Mustapha ne da Sumayya Musty na gaba rikeda takarda a hannunsa Aimanah ta kallesu kallo ɗaya ta ɗauke kanta har sanda taji Mustapha ya ajje mata takarda a gabanta
"Ga shi Na sake ki saki ɗaya" lumshe idanu Aimanah tayi a zuciyarta take faɗin alhamdulillah, juyawa Musty yayi ya fita daga ɗakin, Sumayya ta kece da dariyar mugunta tana kallon Aimana
"Yau dai mun yarda kwallon mangwaro mun huta da kuda, kici gaba da zama anan ke da yayanki nasan yunwa ce zatayi ajalinku, kina nan ba iya fita zakiyi a gidan nan ba sai sanda naso naga dama, kasar ma zamu bari zamu zaga duniya kafin mudawo nasan kin rigada kin zama ba matar Mustapha ba daga nan zan fitar dake daga wannan gidan" Sumayya ta fice tabar Aimanah saman darduma tana ambaton Allah da rokonsa akan yafitar da ita daga wannan ukubar da take ciki, zurawa takardar idanu tayi ta warwareta rubutun Mustapha raɗau saman farar takardar ninke ta tayi ta ajje ta saman gado, tana nan zaune ta jiyo futar su a mota bayan mintina taji an kuma shigowa ɗakin nata wannan karon Lina ce ta shigo ɗakin jikinta ne ya ɗauki mazari sam bata kauna ko san ganin wannan matar, wani kallo take bin Aimanah da shi kafin kuma ta ce
"Zo muje," Aimanah ba musu ta mike tabi bayanta suka fito daga ɗakinta, ɗakin Sumayya taga sun shiga maida kofa lina tayi ta rufe batare data saka key ba, ɗaga katifar dake shimfiɗe saman katakon gadon Sumayya Lina tayi wata mage ta bayyana ramammiya da ita idanunta ja jawur da su ko kyan gani bata da
"Kinason fita daga wannan halin da kike ciki, kinga wannan itace akayi asiri aka haɗa da ruhinki indai har magen nan na kulle anan bazaki taɓa iya barin gidan nan ba, ki bani dama da ƴan mintina na kashe kishi na dake ni kuma na maki alkawarin saina karya duk wani asiri da Sumayya ta maki," Aimanah baya taja ganin Lina na kokarin cire kayan jikinta, sai da lina tai tik ta ɗago tana kallon Aimanah dake makure jikin bango, jikinta gaba ɗaya karkarwa yake ambaton Allah kawai take a fili da zuciya, Lina ta tsugunna tana karkaɗa jiki a tunaninta zata ja hankalin Aimanah, kunce magen Lina tayi, cak Aimanah ta tsaya daga karkarwar da jikinta keyi, yanayin yanda take ji a jikinta taji gaba ɗaya ta sauya ta dawo Aimanar ta da, lokaci ɗaya taji kamar ana kunce ta daga ɗauri, juya idanunta kawai take a ɗaki tana neman abin dazata kare kanta daga Lina wacce ke kusanto ta, kan wata yar tukunya idanun Aimanah ya sauka batayi wata wata ba tasa hannu ta fusko tukunyar kasar ta bugawa Lina a fuskarta Lina ta saki wata karar azaba ta sheme anan, da gudu Aimanah ta fito daga ɗakin batayi wata wata ba ta fice daga gidan gaba ɗaya, gudu take sosai har batasan inda take jefa kafafunta ba sai ji tayi anyi sama da ita...✍🏻
07039793439
[2/13, 4:46 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹
Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰
☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation
*Shafi Na Talatin da Huɗu*
ji kake keeeeeeeeeee matar dake jan motar tai saurin taka burki, Aimanah da motar tayi sama da ita ta dawo kasa kanta ya bugu da kwalta take yanke kan yafashe jini yafara zuba, nan da nan yan sanda dake kusa da wajan suka karaso ba'ayi wata wata ba akayi hospital da Aimanah wacce ko motsi batayi, matar data bige Aimanah kuka take sosai tana addu'ar Allah yatashi kafaɗun yarinyar data bige, hankali tashe ta kira babban ɗanta ta sanar da shi halin datake ciki, cikin kankanin lokaci sai ga shi a Hospital ɗin shiya rinka kwantar mata da hankali har zuwa sanda aka turo gadon da Aimanah ke kai daga emargency zuwa word, ruko hannun mahaifiyar tasa yayi suka bi gadon
"Dr ya ake ciki"
"Hajiya muje office na maki bayani" juyowa sukayi suka bisa zuwa office Muhd ya zaunar da mahaifiyarsa saman kujera ya tsaya jikin kujerar hannunsa cikin na maman nasa
"Hajiya gaskiyya yarinyar nan na a cikin wani yanayi mara daɗi, ta bugu sosai a kanta a yanda muke tunani koda ta farka to zata manta komai nata, sai dai lamari na ubangiji komai na iya canzawa tsaɓanin binciken mu, a karshe dai muyi addu'a"
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un na shiga uku ni Zainabu yau kuma haka Allah yai dani kaico"
"Mom please ki daina kiran shiga ukun nan komai zai zo da sauki insha Allah muyi addu'a kamar yanda Dr ya ce, Muje a kira Azinatu tazo ta kula da ita ke ki koma gida, mu kula da komai"
"Muhd bazan iya komawa gida ba hankalina bazai kwanta ba tsoro nakeji karta mutu na shiga uku"
"Mom zan kira Dr Fawas ya maki allurar barci fa kinsan yanayin ciwonki dan Allah ki cire damuwa, muje na taya ki kiyi alwala ki sallah kiyi addu'a Mom"jiki sanyaye ta mike tabi bayan ɗan nata
Mustapha kwantar da kansa yayi jikin kujera, haka kurum yake jin jikinsa ba daɗi har wani zazzaɓi zazzaɓi yake jin na shirin kamasa
"Sumy mu koma gida bazan iya tafiyar nan ba banida lafiya" harara ta wurga masa
"Sabida kawai bakada lafiya zamu fasa tafiya holewarmu" mikewa yayi ya ajje mata takardunta a kan cinyarta ya mike zai bar wajan ganin da gaske tafiyar zaiyi yasa ta ji gabanta na bugawa tabbas wani abu na faruwa a gida, wayarta ce tayi kara alamar kira ne ya shigo zaro idanu tayi tana kallon Mustapha da har ya fita daga recepsion, hannunta na karkarwa ta ɗaga kiran Malam daya shugo wayarta
"Kinyi sake, Lina ta ruguza komai harta tukunyar ki ta fasata" hannu Sumayya ta ɗora aka zata saki ihu ta tina a inda take cike da damuwa ta ce
"Ran Malam yadaɗe yanzu yaya zanyi nasan dai tunda ina da kai banida sauran damuwa"
"Komai ya rushe Sumayya, mijinki na gafda dawowa hankalinsa hakan dai dai yake da barinki gidan sa"
"Shikenan na shiga uku ni Sumayya kayi wani abu dan Allah malam"
"Zanyi akan mijinki Aljani shinzu zai shiga tunaninsa bazai dawo hankalinsa ba kafin muga mai zamuyi amma dai kisani komai ya rushe kishiyarki ta bar gidan, gobe ki shirin karɓar baki daga kano" yana gama faɗar haka ya katse kiran wayar, a mota ta tarar da Mustapha yana zaune da alama ita yake jira, tana shiga yaja motar suka bar aiport ɗin suna shiga gida ya kwanta barci ba sallah bare salati, zuciyar Sumayya tai sanyi ganin Mustapha baice komai ba ta daɗa kiran malam sukai waya ya gaya mata lalle jibi tazo a sake wani aikin akan Mijinta, gyara ɗakin nata tayi ta kwashe komai sama ko kasa ta duba magen nan bata ganta ba, rai ɓace ta nufi gidan Lina a motar Aimanah wacce yanzu tazama ta hawan Sumayya, Lina na kwance saman doguwar kujera da kumburarran goshi zuciyarta fal takaicin abinda Aimanah ta mata ga ba biyan bukata ga ciwo ga kuma ɓarnar datayiwa Sumayya na ruguza mata komai, ga bakin cikin shikenan ba ita ba zuwa taron gobe da zasuyi a kaduna to ina zata da wannan katon goshi, gabanta ne yafaɗi dataji sallamar Sumayya, tsaye kam Sumayya tayi a kanta tana aika mata banzan kallo
"Kin kyauta akan wata bukata taki shine kika so ki ruguzamin rayuwa to ta Allah ba taki ba, yar akuya mai bin mata" dariya Lina tayi tana tashi zaune da kyar
"Gara ma ni nice yar akuyar ba uwata ba tsohuwar najadu"
"Lina ya isheki fa dani kike bada mahaifiyata ba ki tsaya a ni ɗin idan kika sake taɓo min mahaifiya inada makamin da sai na girgiɗe maki wannan auran wallahi"
"Kin daɗe baki kashe min aure ba, anan anan ɗina kike" Lina tafaɗa tana nuna tafin hannunta
"Ok haka kika ce to muzuba mu gani" Sumayya ta faɗa tana ficewa daga ɗakin, kai tsaye data fita wajan mai gadin gidan ta tsaya suka gaisa ta basa kuɗi masu yawa akan yabata lambar mai gidan, get man baiyi wani tunani ba ya bata lambar tasa a wayarta tai save ta fito ta shiga motar ta taja, kai tsaye gidan Feenah ta nufa a mutumce suka gaisa sun jima suna hira kana Sumayya ta faɗo kan zancan daya kawota,
"Ni kuwa Feena ina vidio ɗin nan da kikaiwa su Lina itada malam randa mukaje ɗin nan?" Feena na dariya ta ce
"Yana cikin wayata duk sanda naso nishaɗi kun nawa nake na kalla nayita dariya ni kaɗai"
"Ki turo min ta whatsapp"
"Ok bari na turo maki yanzu" ta kunna data ta tura mata, tana ganin ya shigo tai dariya bata jima sosai ba ta tafi.
KANO
Ammi gaba ɗaya hankalinta ya gama tashi da jin labarin da Shaheed ke bata kuka take sosai a cikin hospital ɗin, Momy da Yaya Ahmad ke lallashinta
"Naso na gano wani abu sanda naje Abuja amma danayiwa Alhaji magana sai yace ba haka wai na cika zargi daga nan nabar maganar, kaico kaico da wannan auran na Aimanah tabbas gobe saina je abuja sai Mustapha ya saki yarinyar nan, hmmm Mustapha Allah ya.."
"A'a Ammi dan Allah karki yiwa ɗan uwana baki"
"Ko kusa Ahamad bazan taɓa aibata ɗan wani ba bare ɗana dana ɗauki cikinsa tsawon wata tara na shayar da shi na watanni goma sha tara ba baki zan masa ba Allah ya shirye sa zance" Aslam da Tasnim Momy ce ta wuce gida da su binciken likitoci ya tabbatar lafiyarsu kalau, Islam ce dai maleria da typod suka ci karfinta, saiko olsa data kamata hakan yasa aka ɗorata kan magunguna da allurai amma sun kwantar da ita a hospital ɗin danci gaba da kwaje kwaje, Alhaji Kamal ma yaji haushi da bakin cikin abinda yafaru hakan yasa yaɗau alwashin kafarsa kafar Ammi gobe da shi za'ayi tafiyar nan zuwa Abuja,
AMARYA
Shiri suke sosai na tafiya taron da zasuyi a kaduna Hanne an kasa zaune an kasa tsaya kasancewarta babba a harkar shiyasa take ta amsa kiran waya kala kala, wajan tara na safe suka ɗauki hanyar kaduna a motoci uku Hanne da Amarya da Rahila sai wasu matan guda biyu sune a sahun farko, driver ɗin Hanne ke jan motar tasu, kaguwa da Hanne tayi ta ganta a kaduna yasa ta azalzali driver ɗin dayayi gudu sosai suna gafda shiga zariya sukai mummunan hatsari ba kyan gani Hanne tuni ta amsa kiran Allah sakamakon kanta da babbar mota ta taka yai kaca kaca akan kwalta, Amarya kuwa a sume akayi hospital da su itada sauran yan motar, abin Allah driver ɗin ba abinda yasame sa sai buguwa da yayi a gefan kansa mota kuwa tuni ta tashi a aiki, Amarya lokacin data farfaɗo ta dawo hayyacinta shuru tayi tana kallon yan asibitin ba inda ke mata ciwo amma tayi tayi ta tashi ta kasa hakan yasa ta ɗaga hannunta ta kira wani likita dake tsaye kusada gadon wata mara lafiya da alama duba ta yake, sai da yagama da ita kana ya karaso inda Amarya ke kwance kan gado
"Sannu kin farka kenan, ya kike jin jikin?"
"Ba inda ke min ciwo sai dai nakasa ta shi zaune" zaro idanu likitan yayi alamar firgici ya ɗauko allura ya caka a kafarta yaga ko motsi batayi ba
"Bakiji zafi ba"
"Ba zafi, ji nake kafar kamar ba'a jikina take ba"
"Hajiya ina yan uwanki, sai an maki hoton baya muga ya lakar ki take da alama fa kinsamu tsinkewar laka, hoton zai nuna mana in wanda zai gyaru ne sai ayi gyara" hawaye Amarya ta soma musamman bayan tafiyar likitan da driver ɗin su ya shigo shi yake shaida mata mutuwar Hanne da halin da sauran ke ciki, tayi kuka sosai tai nadamar wannan tafiyar tana faɗin data sani bata zo ba, shi ta bawa lambar Murja ya kirata ya gaya mata Mamanta tayi hatsari tana asibiti ana bukatar ganin wani nata, hankali tashe Murjana ta kira Sumayya ta gaya mata, ita kuma ta fara shirin tafiya zari'a itada Alhaji Jamil
Ammi nayin sallar asuba bata koma barci ba ta hau shiri karfe shida na safe suka ɗauki hanyar Abuja itada Alhaji Kamal da Ahmad saiko driver ɗinsu, wajan sha ɗaya da wani abun na safiya suka shiga abuja gaban Ammi bugawa yayi sanda driver ɗinsu ya faka motar a cikin gidan Mustapha, jiki sanyaye Ammi itada Ahmad suka jera zuwa ciki musty na zaune saman kujera yayinda Sumayya ke tsaye tana danna waya murmushi shimfiɗe a fuskarta kamar ba ita Murja ta kira tana gaya mata mahaifiyarsu na hospital ba, ɗagowa tayi ta kalli su Ammi da suka shigo da sallama, daga kallo ɗaya bata sake yi masu wani kallon ba ta maida kallonta ga madubin wayarta tana cigaba da murmushinta
"Ammi barka da safiya kune da safan nan, Ahmad bisimillah zauna" Mustapha yafaɗa yana nunawa Ahmad kusa da inda yake zaune,
"Bazama mukazo yi ba, Mustapha ina Aimanah?"
"Aimanah ai bata gidan nan Ammi tun jiya na sallameta na bata takarda ko Honey" yafaɗa yana kallon Sumayya
"A'A kaga ba ruwana, karka sako ni a zancan ku yanzu matar nan ta ce na maka asiri ka rabu da matarka, bayan ni banma san anyi ba"
"Ke!!! shiga hankalinki kisan da wacce kike magana" Ahmad yafaɗa a zafafe harda mikewa daga inda yake zaune yana huci kamar zai kai mata duka, Ammi kasa magana tayi sai ma buɗe ɗakin Aimanah da tayi ta shiga, shuru ɗakin sai darduma a shimfiɗe, takardar dake ajje saman gado ta ɗauka hannunta na karkarwa ta buɗe ta karanta
_Ni Mustapha Kamal Sareena na saki Aimanah saki ɗaya_ dafa bango Ammi tayi tana hailala