Showing 75001 words to 78000 words out of 84763 words
Chapter 26 - AIMANA Book Complete by MAMI YUSUF DABO.txt
da tasbihi ga ubangiji lalle mutum abin tsoro futowa tayi daga ɗakin tana kalllon Ahmad,
"Muje Ahmad" bata tsaya ba tayi gaba abinta, Alhaji Kamal na tsaye jikin mota yaga futowar Ammi da Ahmad harma da Mustapha da Sumayya, har kasa Sumayya ta tsugunna ta gaida Abba daya amsa fuskarsa ba yabo ba fallasa
"Abba wai dama Aimanah bataje gida ba, tun jiya da yamma fa tabar gidan nan Mustapha ne ya bata takarda sabida ya kamata ta satar masa kuɗi, ba yanda banyi da ita ba akan ta zauna mu basa hakuri ta kafe sai da ta tafi ko ina taje, Allah yasa tana lafiya" Sumayya ta faɗa harda kukanta kamar gaske, kallon mamaki Ammi kewa Sumayya lalle mace shu'uma ce
"Assha Mustapha garin yaya haka ta faru banyi farin ciki da jin maganar nan ba"
"Abba ba wannan ba, bar waɗannan mutanan mu fara kiran yan uwa ko Aimanah taje kano" kusan duk wanda Ammi ta kira amsa ɗaya ce bata zo ba, haka ya kuma tasar hankalin Ammi sosai, hankali tashe suka baro Abuja suka juyo zuwa kano, Ammi kuka sosai take da tunanin inda zasuga Aimanah anan kano bincike sosai akayi har mutuware sai da Ammi da Ahmad suka rinka zuwa suna dubawa wai ko ta taho sukai hatsari ta mutu, wasa wasa tun ana ɓoye magana har magana ta fito sarari Aimanah ta ɓata, hanakali tashe yayu da iyayan Aimanah suka duro kano, Mus'af kamar yayi hauka lokacin da labari yaje masa yana sauka a nageria Abuja daman ya sauka sawa yayi yan sanda suka kama Sumayya da Mustapha da zargin sun ɓatar da yarinya, anan sell na yan sanda yabarsu ya hau jirgi ya wuce kano, sai da Sumayya da Mustapha suka kwana biyu a cell sannan Mus'af yafaɗa yasha faɗa a wajan Daddy shiya tilas ta sa aka sake su suka koma gida Sumayya na daɗa cin alwashi...✍🏻
[2/13, 4:46 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹
Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰
☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation
*Shafi Na Talatin da biyar*
Hajiya Zainab zaune gaban gadon da Aimanah ke shimfiɗe kamar gawa, Muhd na gefanta yana dannan waya yayinda Azinatu ke zaune itama kan gadon daga gefan Aimanah, gaba ɗaya sunyi shuru abin duniya duk ya dami Hajiya Zainab zuciyarta fal da zulumin kar yarinyar nan ta mutu
"Moha a fara binciken daga ina yarinyar nan ta fito, na tabbata zuwa yanzu iyayanta na cikin tashin hankali yau kwana shida fa kenan"
"Mom wannan fa daga gani irin yaran nan ne dake aiki a gidajan masu kuɗi kilama sata tayi aka koreta daga inda take aikin" Azinatu ta faɗa tana hararar Aimanah wacce bata san tanayi ba
"Wannan ce tai maki kama da masu aiki, ke dai kawai kin saba saikin ai bata mutum, ke bazaki canza hali bako, bar asibitin nan ki sani ɗan adam ba abin wulakantawa bane kilama tafi ki gata" Azinatu hararar yayan nata tayi tareda kyauda kai gefe
"Moha bana son hayaniyar nan taku kuje gida dan Allah"
"Gaskiyya Mom anemo wacce zata kula da yarinyar nan ki koma gida yaufa kusan sati kenan rabonki da gida, ga ranar Anty Ramla inda tana nan da tini ita ke kula da yarinyar nan" Muhd kallon Azinatu yayi ya fice daga ɗakin batare daya ce mata komai ba, da sauri ta mike tabi bayan Muhd tasan ba karamin aikinsa bane ya tafi ya barta anan, Hajiya Zainab mikewa tayi ta shiga bathroom tayi alwala ta tada sallah nan cikin ɗakin, tana zaune saman dadduma tai nafila raka'a biyu ta soma jero addu'o'i har barci ya ɗauke tana nan saman daddumar
SUMAYYA
Suna komawa gida daga stesion wanka kawai tayi ko magana da Mustapha batayi ba tai shirin tafiya enugu, gaba ɗaya ma ta manta da wata amarya dake kwance a asibiti ba lafiya, ta isa enugu lafiya ta zube gaban malam har kuka saida ta masa akan yataimaka mata kar asirinta ya tonu, wasu ɗalasimai yafara karantawa take wata tukunya ta bayyana a gabansa yacewa Sumayya leka kiga kanta tai kasa da shi tana leka cikin tukunyar Aimanah ce ta bayyana cikin tukunyar kwance kan gadon asibiti
"Mu muka sakata wannan dogon barcin muna jiran kizo muji mai kike so a mata"
"Malam amata duk abinda yadace nidai so nake Mustapha yazama nawa ni kaɗai"
"Hhhhhjj shikenan zamuyi, zamu tashe ta daga dogon barcin da take aljani zai shafe tunaninta bazata iya tuna ita wace ba sai nan da wata uku sannan ta zama ba matar mijinki ba zata dawo hankalinta,muddin tana hankalinta asirin jikin Mustapha zai karye, Mijinki kuma mun rigada mun gama komai a kansa kije sai yanda kikayi da shi yanda kika dama haka zai sha ko kara kika ajje kika ce karya tsallaka bazai tsallaka ba"
"Yawwa malam nagode,"
"Ba'a mana godiya kije, wannan tukunyar zansa aljani yanzu ya ɗauke ku keda tukunyar ya maida ku gida ki ajjeta waje mai kyau inhar ta sake fashewa to bani da abinda zan maki kuma ki kula sosai sannan in kina son magana da ni ki leka tukunyar nan ki kirani zan bayyana, rufe idonki" da sauri Sumayya ta rufe idanunta jikinta na karkarwar tsoro, tsawon lokaci idanunta na a rufe can taji kamar wacce aka ajje kan wani abu ta buɗe idonta tana buɗewa taganta zauna kan gadonta, zabura tayi har tana buge Mustapha dake barcin safe
MURJA
Kuka sosai take sanda taga Mama kwance a gadon asibiti ko zama bata iya yi, Alhaji Jameel shi yayi komai aka mata hoto wanda ya nuna lakarta ta rigada ta tsinke ba ita ba sake iya zama sai dai kwanciya, Amarya tayi kuka tai nadamar abinda ta aikata da bin son zuciyarta da tayi, Alhaji Jamil yadamu sosai ya rinka tambayar Dr ɗin ba yanda za'ayi ko zama a samu tarinka yi suka ce basuda kwarewa a wannan harkar sai dai zasu turasu kano asibitin kashi dake dala, a motar asibitin aka kawo Amarya asibitin kashi anan kano, bayan hotunan da sukai mata suka ce zasu mata aikin da zata iya zama amma itada sake taka kasa har abada, sanda aka gayawa Murja kuɗin aikin hankalinta yatashi naira miliyan huɗu da rabi, Alhaji Jamil shiya biya kuɗin yai komai aka mata aiki, alhamdulillah aiki yayi kyau sosai tana iya zama amma sai an taimaka mata sai dai bata iya tashi da kanta komai a inda take zaune take hakan yasa aka saka mata ledar fitsari, sanda aka sallamesu rasa inda zasuyi da Amarya Murja tayi, Amarya ma kuka tayi sosai na nadama yau sai gashi ta tina da iyayanta dake katsina can Murja da Amarya suka tafi a motar da Alhaji Jamil yasamo masu a tasha ya biya kwana ɗaya yabawa Murja ta dawo sabida jibi zasuyi tafiya,
Dakyar da lallashi iyayan Amarya suka karɓeta dan har rantsuwa sai da Babanta yayi baza ta zauna masa a gida ba sai da Murja ta nemo wani wan baban yayi masa magana kana aka bata ɗakin da zata zauna, Murja ta kira Sumayya tana kuka ta gaya mata halin da mama ke ciki, hankalin Sumayya yatashi hakan yasa tabi jirgi zuwa Katsinan itada Murja suka shiga suka fita suka samo wata tsohuwa da za'ana biyanta zata kula da Maman tasu dan mahaifiyarta rantsuwa tayi da abinda zai kasheta bazata taɓa Amarya ba, washe gari Murja da Sumayya suka baro katsina, kafin wani lokaci Amarya baya ya rarake yayi wani zurfi sai wari da yake fitarwa ko ɗakin ba kowa ke iya shiga ba duk da kuwa tsohuwar na matukar kula da Maman, Sumayya ita ta koma aka samu nurse ɗin dake zuwa tana wanke wajan kullum, daya warke kuka sai wasu tsutsotsi yan mitsi mitsi da suke futowa daga gabanta cukus ba kyan gani Amarya ta rame ta kanjame duk da kuwa su Murja na matukar kula da ita suna ajje mata komai na amfani
AIMANA
Sai da tai sati guda bata ko motsi sai yau data cika sati guda sannan ta buɗe idanunta, lokacin Mom na ɗakin da sauri ta mike ta kira Dr ta cikin telephone ɗin dake cikin ɗakin nan da nan sai ga Dr da Nurse a tare, Dr yakarasa gaban gadon da Aimanah ke kwance wacce keta dube dube
"Sannu yaya jikin?"
"Da sauki ta faɗa a hankali"
"Ya sunanki,kinsan wannan?" Dr ya tambayya yana nuna Hajiya Zainab
"Ban san sunana ba, itama ban santa ba"
"Yasalam" Nurse tace tana komawa gefe ta tsaya, Hajiya Zainab ta share hawaye tana zubawa Aimanah idanu
"Hajiya abinda muke gudu yafaru fa sai dai zamu ɗorata akan magani mu gani"
"Yanzu ina ne ke maki ciwo"
"Bako ina" Aimanah ta faɗa a hankali
"Hajiya zamu sallame ku ku koma gida sai dai zakuna zuwa ganin likita duk sati, sannan ayi kokari a samo yan uwanta ina zaton in taga wani nata komai nata zai dawo dai dai"
"Insha Allah zamu bincika Dr" Hajiya Zainab ta kira Moha yazo ya ɗauke su, Aimanah da idanu kawai take binsu, sosai Mom ke kula da Aimanah gefe guda tana binciken yan uwan Aimanah, wasa wasa Aimanah sai da ta shafe watanni biyu da wani abu tana cikin wannan halin,
Zaman Aimanah a gidan zama ne na gata sosai Mom da Muhd suke kula da ita, a wajan Azinatu kawai take samun damuwa, Aimanah shuru shuru ta koma bata cika son zama cikin mutane ba kusan ko yaushe tana ɗaki, cin abinci wanka sallah komai sai Mom tace tayi sannan take, yau gidan antashi sosai da murnar dawowar ɗan Hajiya zainab tun safe Ramla dake aure a kaduna tazo, sai ɗorawa da saukewa ake
Hajiya Zainab haifaffiyar nan garin Abuja ce, mijinta tuni Allah ya masa rasuwa tana zaune gidanta itada yaranta guda huɗu Muhd shine babba sai Yasar Ramla sai auta Azinatu, Ramla an mata aure tuni tana kaduna tareda mijinta Allah bai basu haihuwa ba, Muhd baiyi aure ba andai saka masa rana da yar kanwar babansa, Yasar shekarunsa bakwai kenan rabonsa da nageria yana zaune a madina inda yayi karatu tuni harya fara lacture a jami'atul madina, takurawar da Mom ta masa na rashin zuwa gida yasa zai kawo ziyara ya koma, sai da suka gama komai suka gyara gidan yanata tashin kamshi sannan Muhd ya zo suka tafi airport ɗakko sa sabida jirgin da yasar ya biyo na gafda sauka, Ramla Azinatu su suka tafi ba yanda Mom batayi da Aimanah ba wacce suke kira da Aysha ba kan tabi su tace bazata ba hasalima komawa tayi ɗaki ta kwanta,
Yasar rungume Muhd da Ramla yayi yana kissin ɗinsu ta ko ina
"Nayi kewarku sosai, Yaya Moha ka kara girma, Anty Ramla tawa kin kara kiba" dariya duka sukayi banda Azinatu dake can gefe tana taɓe baki, dariya Yasar yayi sanda ya hangi Azinatu
"Autar Mom sarkin rigima haka kika kara tsayi, amma dai taliya Mom ke baki ko"
"Kaifa daman bakinka baya shuru, wuce muje" Moha yafaɗa yana rike da jakar kayan Yasar, tunda suka shiga mota bakin Yasar bai yi shuru ba sai surutu yake dan dama shi ba baya ba wajan magana, har suka karasa gida suna yi da Ramla Moha sam baya saka masu baki danshi mutum ne ba mai son magana ba,
"Our wellcome ustaz" Mom tafaɗa sanda ta rungume Yasar, Sun batar ta kawai yake ta ko'ina yana rungume da ita
"Mom nayi kewa" yafaɗa yana share hawaye
"Nima nayi kewar surutun nan naka, ince dai larabawa basu canza min kai ba"
"Ai wallahi ko kaɗan Mom ɗanki bai canza ba, tunda fa muka tawo yake surutu shida Ramla, surutu cai cai kamar yaci aku nifa harya samin ciwon kai, Dan Allah Mom kar a ce ya zauna a ɗakina kamar yanda muke da, ga ɗakin Ramla can ya sauka anan, bazan iya da surutun Yasar ba"
"Caii wai nine mai surutun, Mom inama ɗakin Yah Moha ɗin yake tabbas can zan sauka yau kwanan hira zamuyi anjima ba'ayi hirar zumunchi ba"
"Mom ina Aysha ne, banga motsinta ba" Moha yafaɗa yana kallon kofar ɗakin Mom
"Tun bayan fitar ku ta kwanta barci, ke Azinatu taso ta, tazo aci abinci da ita"
"Mom wace Aysha ko anyi bikin Yaya Moha ne banda labari"
"Wata yarinya ce fa Mom ta kaɗe ta wata uku kenan amma an rasa iyayanta take zaune anan" Azinatu ta faɗa tana taɓe baki, hararta Anty Ramla tayi kana ta shiga ɗakin Mom inda Aimanah ke kwance
"Anty Ramla kun dawo?"
"Mundawo Ashanty Mom tace ki fito aci abinci ga Yasar ma yadawo" mikewa Aimanah tayi tana gyara zaman doguwar rigar dake jikinta tabi Ramla suka fito tare, da sauri Yasar ya kalli yarinyar da ta fito tareda Ramla zaro idanu yayi sanda idanunsu suka gauraya dana juna
"Kambu, Mom maza bani ruwan zam zam a jakata" da sauri Aimanah ta juya zata koma ciki, caraf yayi ya ruko hannunta ya zaunar da ita nan saman tiles yana zare idanu,
"Kai ɗago ka kalle ni," yafaɗa da karfi yana zare idanu, kai Aimanah ta fara ɗagawa,
"Azinatu Ramla kubar falon nan" Yaseer yafaɗa cikin bada umarni
"Wai Yasar ban gane ba mai kake wa yarinyar nan haka ne, maca ce fa kake kiranta da kai"
"Zauna Mom da aljani kuke tare, asiri ne a jikin yarinyar nan bani zam zam dan Allah" Sim sim Azinatu tayi ta fice daga gidan gaba ɗaya jin an ambaci aljani, Anty Ramla zama tayi tai tagumi tana kallon Aysha dake bubbuga kafa
"Bazaka ɗago ka kalle ni ka gaya min waya turoka ba" nan ma kai Aimanah ta kuma ɗagawa kanta na kasa
"Anty bani cup" ta tashi ta ɗakko cup ɗin a kicin ta dawo ta basa, zam zam ɗin hannunsa ya fasa ya tsiyaye a cikin cup ɗin ahankali yafara karatu cikin ruwan, tsawon lokaci kana ya kalli Mom
"Mom rike min cup ɗin nan ki rike sosai, zan matse bakinta ki zuba mata ki rage min kaɗan" Mom tayi yanda yace ɗin sauran daya rage ya cewa Ramla zoki shafa mata a jikinta, Ya soma karatun suratul bakara a hankali cikin kira'a mai daɗin sauraro
"Wayyo wayyo ku daina zamu fita zamu fita, daman aiko mu akai turomu akai mu shiga jikinta mu ɗauke mata tunaninta ta manta komai har zuwa sanda zatayi idda ta zama ba matar Mustapha ba, yau kwana huɗu kenan data kammala daman muna shirin tafiya, kana kona mu kana konamu kabari zamu tafi"
"Zaku tafi kamar ya ku zauna, ina mijin nata yana ina"
"Yanzu haka yana wajan aikinsa"
"Mai sukai maku da zaku rana auran sunna"
"turomu akai kishiyarta ce ta turo mu"
"To ku fita kuma ku karya asirin da kukai masu, kuna jina"
"Munji zamuyi yanda kace"
"Nafa sanku bakuda alkawari, in bakuyi abinda nace ba zansa a kawo min ku nan kuna ji"
"Zamuyi komai yanzu ma" shuru Aimanah tayi tareda jero atishawa, can kuma ta buɗe idanunta ta mike a guje zata fita, rike ta yayi gam yana kallonta
"Kinga nutsu kina cikin aminci" Wani kuka ta saki tareda kokarin kwace rukon da yayi mata
"Musty ka sake ni barin gidan nan zanyi, kariga da ka yanke igiya ɗaya ta auranmu ka sake ni nasamu na fita daga wannan gidan na bala'i"
"Kinga buɗe idanu ki kalle mu sosai nan ba gidan ki bane, Mom ta bike ki kusan wata uku kenan" da sauri ta buɗe idanunta tana kallonsu ɗaya bayan ɗaya
"Ya sunanki" Moha ya tambaya a hankali
"Aimanah Farouk mai naira ni haifaffiyar kano c.........nan ta basu labarin ta da abinda ya fito da ita daga gida, Mom sosai ta tausaya mata anan take Aimanah ta bada lambar Ammi aka kirata a waya, Ammi dan Murna ji take kamar ta fasa wayar ta shigo ciki, cewa ma tayi gatanan zata biyo jirgi tazo Abujan, Mom ta hana ta tace su yakamata suzo gobe zasu biyo jirgin safe, Yasar mikewa yayi ya shiga ɗakin Moha yayi wanka kana ya fito, kallon Aimanah yayi yana murmushi
"Sannu Ummu ya kike ji, kanki baya ciwo ko" kai ta girgiza alama e
"Ba da kai zaki min magana ba baki zaki buɗe kimin magana ɗago ki kalli idanuna naga wani abu" ɗagowa tayi tana kallonsa da fararan idanuwanta, wani abu yaji ya tokare masa a kirji, ya lumshe idanu yana ambaton Allah a hankali, yana buɗe idonsa sukai ido huɗu da Mom murmushi mom tayi tana bin Yasar ɗin da kallo yanda ya kafe Aimanah da idanu, kallo ɗaya inkayi masa fuskarsa zata fallasa asirin zuciyarsa....✍🏻
07039793439
[2/13, 4:46 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹
Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰
☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation
*Shafi Na Talatin da shida*
"Kazo ka zauna kaci abinci sai kaje ka kwanta ka huta" Mom tafaɗa tana kallon Yasar daya kafe Aimanah da kallo,shafa kansa yayi kana yaja kujera ya zauna,
"Ummu kinci abinci" Aimanah tayi murmushi batare data ce komai ba, Anty Ramla da Moha suka kalli juna suka fashe da dariya, Aimanah gaba ɗaya ta kasa sakewa idanun Yasar take ji a ko ina na jikinta, bata wani ci dayawa ba ta mike zuwa ɗaki
"Ummu ki tsaya na baki habbatus sauda ki turara, sannan ki maida hankali sosai wajan yin azkhar na safiya da maraice ki yawaita karanta kur'ani kina kuma yawan saurara a wayarki"
"Batada waya ai" Anty Ramla ta faɗa tana kallon Yasar
"Bari inna fita anjima gaida gwaggo mariya zan taho mata da waya"
"Da wuri haka" Moha yafaɗa yana dariya
"Kasanmu a lamarinmu ba ɓoye ɓoye, sak muke tafiya ba kwana kwana"
"Yanzu dai so kake kace kaga mata"
"Ta aure ma insha Allah" ya maidawa Anty Ramla martanin maganarta
"Tana dai da mijinta, kajira kaga yanda zata kaya" Mom tafaɗa tana kai lomar abinci bakinta
"Mom tariga tayi idda fa, ba wata uku tai a gidan nan ba"
"Hakane tayi idda yau kwana biyu kenan datai wanka, amma dai kabi a sannu karka zurma
"Mom nafa riga na shiga irin sosai ɗin nan" yafaɗa yana dariya, Barci Yasar yayi na awanni sai yamma yatashi ya sake wanka ya fita ya zaga su gaisa da yan uwa, sai bayan sallar insha yadawo a hanyarsa ta dawo wa ya tsaya babban shagon sai da wayoyi ya saiwa Aimanah waya Infinix hot 50 pro, da sabon layin