Showing 3001 words to 6000 words out of 84763 words

Chapter 2 - AIMANA Book Complete by MAMI YUSUF DABO.txt

sun kasa sabawa da rashin Mustapha takanyi kuka sosai tana yawan kiran lambarsa bata shiga tayi kuka tayi addu'a harta gaji, yau tana zaune a ɗaki karatun kur'ani take a wayarta karar buɗe kofa dataji yasa tai saurin ɗago dara daran idanunta tana kallon kofar dan ganin mai shugowa Anty Ummi ce shirye cikin doguwar rigar atamfa mayafinta a hannu
"Sannu Amaryar ɗaka, kindai kasa daina tunanin Mustapha"
"Anty kin rigada kinsan komai kinsan irin soyayyar danakewa Musty irinta ba lokaci ɗaya take fita a zuciyaba inajin soyayyar Musty ita zata kaini kushewata" Anty Ummi cikeda tausayawa ta zauna kusa da Aimanah tabbas kamar yanda tafaɗa ne tasan komai tasan zazzafar soyayyar dake tsakanin Mustapha da Aimanah bata misali bace soyayyace mai cike da kauna da aminci dole idan ɗaya ya rasa ɗaya manta sa zaiyi wuya, bata taɓa zaton akwai wani abu dazaisa Mustapha ya juyawa Aimnah baya ba yaje can ya auri wata tabbas da walakin wai goro a miya dawata a kasa ba Hakanan Mustapha zai guji Aimana ba ita tini tafara zargin akwai sa hannun Amarya matar Alhaji kamal a lamarin
"Yi hakuri Aimanah yanzu tashi ki rakani nayiwa su Zayyad siyayya gobe Monday zasu koma makaranta muyi maza mu dawo kafin su dawo daga islamiyya Zaheed yace saiya bimu kinsan baida daɗin tafiya"
"Anty da kinyi tafiyarki insuka dawo gidan bakowa bazasuji daɗi ba kinga leena bata nan"
"Bazan tafin ba dake zamuje kin maida kanki matar ɗaka duk ba rigimar nan nikan Musty bai kyautaba daya canza mana Aimanarmu daga rigimammiyar mai yawan fara'a zuwa wannan mai taurin kan, oya maza maza tashi ki shirya mu fita nabaki minti biyu" Aimanah batan tasoba ta shirya cikin doguwar rigar abaya, sakar egypt hular net tasa a hanta kana ta naɗa ɗan karamin mayafin abayar akanta tana kokarin saka glass a idanunta wanda yazame mata jiki kusan ko yaushe kaganta tana sanye dashi a idanunta, bakaramin kyau yake mata ba, Anty Ummi data sake dawowa ɗakin jin shuru Aimana bata fito ba sak tayi tareda faɗin
"Wow My Aimaah kinga yanda kikayi kyau"
"Anty Plese kidaina faɗar sunan nan Aimaah bansaba ba daga bakinsa kaɗai nakeson jin sunan nan faɗar sunan yana daɗa tadamin mikin dayake cikin zuciyata" Aimanah tafaɗi haka miryarta na rawa kamar zata fashe da kuka
"Ok bazan sake faɗar sunan ba amin afuwa kar ayi kukan nan yaɓata mana wannan special kwalliyar, Allah yasa mu samo wanda zai biya kuɗin kwalliyan nan" murmushi kurum Aimanah tayi ta zura plate shoe tafice zuwa wajan ajje motoci na gidan.

Amota Anty Ummi nata tsokanarta saidai kawai tayi dariya taci gaba da danna wayarta har suka karasa babban kantin siyayya Aimanah tasoma fita daga motar kafin Anty Ummi tafito suka jera zuwa ciki.

Ahankali yake tukin motarsa cikeda nutsuwa da kwarewa karatun kur'ani yake sauraro acikin motar yanabi ahankali jefi jefi yana murmushi shi kaɗai yabuga sitiyarin motar ahankli kallo ɗaya zaka masa kasan yau yana cikin zallar farin ciki, harya gifta shoprite yayo baya kaɗan yayi parking cikin wajan yafuto ya kulle motar yashiga ciki

"Kai Anty Ummi kalli wancan atamfa yayi kyau sosai bari na ɗakkowa Mahh nasan ma nason jar kala" batajira mai Antyn zatace ba tayi gaba takai hannu zata ɗakko shiya yakai nasa da sauri ta ɗauke hannunta wanda shima hakan yayi saboda wani shoking da hannun nasa yayi sanda ya haɗu dana Aimana atare suka ɗago suna kallon juna kusan tare suka furta "Sorry" jin sun faɗa tare sai abin yabasu dariya shi yaɗan dara sosai itako Aimanah murmushi kawai tayi tamaida hankalinta wajan ɗakko atamfar, shiko gefe yakoma yana kallon Aimana yanajin wani iri a xuciyarsa karo na farko kenan daya taɓa jin irin haka a rayuwarsa ta nan duniya sake gyara tsayuwa yayi yana cigaba da kallonta duk inda ta motsa baiyi aune ba yaga tana shirin barin wajan
"Ji mana yammata nace Dan Allah kozaki zaɓar min atamfa da lace zanyi tsaraba" har tayi kamar bata jiba komai ta tina kuma saita juyo ta kallesa kallo ɗaya ta ɗauke ganinta daga kansa tamaida hankali wajan zaɓar abinda yace saita ta kai hannu zata ɗauki wani lace kawai taji bakinta ya furta
"Uwa mata ko kanwa?"
Sarai yagane tambayar amma saiya basar yai kamar baijita ba yaci gaba da danna waya
"Nace ba ina tambayya banida lokaci fa"
"Namaki kala da wanda yake da mata tayar mota ne ni haka kuma banda kanwa" maganar daya faɗa ta fitar da amsar tambayarta hakan yasa taci gaba da zaɓar kaya saida ta ɗauki Lace huɗu atamfa uku mayafai sannan ta ajje masa a gabansa taci gaba da tafiya da sauri yabi bayanta da kayan shirim a hannunsa yai saurin zuba kayan a cikin basket ɗin datake turawa
"Wannan kayan da kika ɗiba yayi yawa banida kuɗin dazan biya duka"

"Bakada damuwa ni ina dasu indai harka ta iyaye ce bama sanya musamman ma mahaifiya ita ɗin ta musammance" murmushi yayi yabi bayanta ganin tasoma tafiya zuwa wajan biyan kuɗi inda ta hangi Anty Ummi tsaye da alama tagama siyayyarta ita take jira, Aimanah na kokarin ciro Atm card ɗinta cikin jaka shi kuma ya ɗakko nasa daga aljihu yamikawa ma yaron dake wajan
"Ga siyayyanmu nan ta ɗauki kuɗin duka" yafaɗi haka yana ajje masa kayan saman canta, Aimanah tayi saroro tana kalon gayan mai karfin hali
"Kaga ba tafiyarmu ɗaya karɓi ka ɗauka anan iya nawa saika ɗauki nasa a card ɗinsa"
"Madam kiyi hakuri narida na shigar" cashiar ɗin yafaɗi haka yana cigaba da danna computer ɗin dake gabansa, aka gama haɗe kaya ko wanne ledarsa daban gayan shiya bikaci hakan ta hanyar ware kayan data basa daban da wanda ta ɗiba, Aimanah a fusace tayi gaba bata tsaya ɗaukar ledar ba Anty Ummi ita ta haɗa da nata ta ɗauka tanayiwa mutumin godiya hartayi gaba yace
"Anty in wani bai rigani ba kibani phone number na kanwar taki" Anty na murmushi ta gaya masa lambar ya loda cikin wayarsa tareda save na number yana tsaye a compount na store ɗin yana kallonsu suka shiga mota sannan shima ya shuga tashi yana murmushi ahankali ya furta
"Fenally yau dai Momy tayi sirika yau zanje Jigawa da daddaɗan labari....✍🏻


07039793439
[2/13, 4:43 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹


Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

Shafi na Uku

Jiki a sanyaye yake tuka motar haka kawai yau yakejin ransa ba daɗi damuwa da baisan ko ta macece ba duk tabi ta addabi zuciyarsa haka kawai yaji baisan komawa gidansa amma ba yanda zaiyi dole yakoma, badan ransa na soba yakama hanyar zuwa gidan, tun daga falon gidan ranshi yakuma ɓaci wani uban kauri daya jiyo daga kicin yasa yai saurin nufar kicin ɗin abincime ake dafawa yakone yayi baki kirin sai hayaki yake gaf yake da kamawa da wuta da sauri yakashe gas ɗin ya sauke tukunyar kasa, jingina yayi da kantar kicin ɗin yadafe kansa yana faɗin "Ya salam" azafafe yafito ya kalli ko'ina kaca kaca komai zaman kansa yake kudaje sai bin falon suke dafe kansa yayi ganin ko kayan dasukai break ba abinda ta ɗauke yana nan ajje a wajan, afusace ya banga kofar ɗakin nata ya shiga amma duk zafin daya ɗakko sai yaji tayi masa wani gingirim tsoro da shakkarta suka shigesa yaji yama kasa faɗar abinda yazo faɗa, asanyaye ya zauna gefan gadon datake zaune sai faman latsa waya take da alama chat take kasa yayi da kansa kana yace
"Yanzu Sumayya kina kallon yanda gidan nan yake amma kike zaune anan kina chat gaba ɗaya gida kaca kaca dan Allah in kikayi baki bazakiji kunya ba" zumburo baki tayi gaba tareda karkata ɗaurin ɗan kwalinta tana harararsa tace
"Aikai kajawo nace maka kasamo mana mai aiki kace bazaka kawo ba basai kayita kallo ba kazanta yanzuma aka fara, ni katashi ka yo mani take away kunya nakeji kuma bazan iya dafa abincin ba" wani kallo yayi mata kamar bazaije ba amma data ɗago ta kallesa ba shiri yamike zai fita saboda wani tsoronta daya shigesa da sauri yafice daga ɗakin yana waiwayanta, amota ya zauna tai shuru yana tinani ahankali yatada motar tasa bai tsaya ko ina ba sai office ɗin abokinsa kuma ɗan uwansa Mas'ud, Mas'ud dake zaune cikin office ɗinsa yana danna laptop yaɗago ya kalli Mustapha daya shigo abirkice bako sallama haka yasami waje ya zauna, Mas'ud ya tura laptop ɗinsa gefe yaja tagumi yana kallon Mustapha dayai wani zuru zuru kamar mara lafiya maganar Mustapha ta katsewa Mas'ud kallon dayake masa murya a raunane Mustapha yace
"Mas'ud na canza ko naga kanata kallo na wai dan Allah nima mutum ne?" aɗan tsorace Mas'ud yasake kallon Mustapha jin maganar data fito daga bakinsa
"Mutum ne kai mana maiya faru kake wannan tambayar?"
"Gaba ɗaya banida nutsuwa Aboki wani iri nakejin kaina gani nake kamar bani ba"
"Aboki anya kuwa kanada lafiya ko asibiti zamuje a duba ka?"
"Bazamu ko ina ba lafiyata kalau kawai kamin addu'a kagayawa Ammi tayafemin nadaina zuwa gaisheta idan natafi gidan sai naga gaba ɗaya na rasa hanyar"
"Mustapha kana azkhair kuwa anya ba aljanu ne suka shigeka ba, kayawaita azkhair sosai sannan kana karatun kur'ani koda yaushe kana sakawa a redion cikin motarka" wayar Mustapha datayi kara tasa ya mike da sauri yafice daga office ɗin, Mas'ud yabisa da kallon tausayawa tabbas bako tantama asiri ne ajikin Mistapha inko har hakane tabbas zaiyi tsaiwa daka wajan ganin yataimakawa abokinsa, yazama dole yaje yasami Ammi suyi magana.

Sumayya ta fito daga ɗakinta tana waya dariya take sosai harta shiga kicin da sauri ta karasa gaban tukunyar dake ajje a kasa ita gaba ɗaya ma ta manta data ɗora girki, da sauri tamaida murfin ta rufe saboda wani kauri daya bigeta ta maida wayarta kunne taci gaba da magana da mamanta Amarya
"Amarya aiki yayi kyau sosai ai kirawa boka tsito kuɗi bakiga yanda Mustapha kejin tsorona ba komai nace yayi jiki na rawa yakemin kawai dai maganar yar aikin nan ce dai yaki yadda ki gayawa tsito yayi aiki dan Allah ya amince nasami mai aikin nan, kinsan dai ni Mama ban saba da wahala ba ko gidam Innah ba abinda nake saida agama naci nabar kwano nan bare wannan gidan mai uban girma bazan iya aikin saba wallahi Mama"

"Ke dayallah raguwa kina nan kina kazantarki ko tabbas ki canza inba haka ba zamu sami matsala dake duk abuna bana zama da kazanta, sannan maganar kuɗin nan kisake masa magana boka ya tabbatarmin zai bayar yau in aka tambayesa yaɗaure masa baki"
"To Mama zan tambayesa yanzu dai na aikesa siyomin abinci"
"Sumayya abinci kuma mai zanji wannan abu ba daɗin ji ke bazaki girka ba kenan gaskiyya ki canza koda asiri fa saida kissa wani abun ke tafiya dai dai adaina siyo abincin nan kina dafawa kinfa rigada kin iya komai nida nakeso ki rike zuciyarsa ta yanda koda asirinmu ya karye yaazama akwai wani abu naki da saboda shi kaɗai zai iya zama dake"
"Mama yakike wannan fatan ai bazai ma karye ba muda muke da boka tsito ai bamuda sauran matsala zama daram a gidan Musty nifa Mama sai yanzu ma naji ina son sa da duk kwaɗaita min daular da kike bana hangowa sai yanzu danake cikinta" shigowar Mustapha yasa ta katse kiran.

*AIMANA*

tagama shirinta na kwanciya ta kwanta kusada Zaheed tana gyara masu blanket wayarta tayi kara hannu tasa saman bedsite drower ta ɗauki wayar tata ganin bakuwar lamba ba suna yasa ta ajje harta katse bata ɗaukaba sau biyu ana kira bata ɗauka ba sai ana ukun ta ɗaga kiran tareda karawa a kunnanta
"_Amincin Allah yatabbata a gareki ya tauraruwa a cikin taurari_" dim taji gabanta yai wani irin faɗuwa ta ciro wayar daga kun nanta ta kalli screen ɗin taga sam batasan lambar ba batama taɓa ganin ta ba
"Afuwan ba wannan layin kake nema ba"
"Shi nake nema mana Hayatie yakike ya daran?" tsaki taja takashe wayar gaba ɗaya tayi addu'ar kwanciya barci ta kwanta da hannun dama rufe idanunta tayi bayan tayi bisimillah ahankali tasoma rero karatun suratul mulik har barci yayi awon gaba da ita.

Abbas ganin ta katse kiran yayi murmushi ya fito daga ɗakinsa zuwa na Hajiyarsa, Hajiya Hafsatu mahaifiyar Abas na zaune cikin bedroom ɗinta tana duba littafin addu'o'i na hislum muslim ɗagowa tayi tareda amsa sallamar gudaliyar ɗannata murmushin fuskarta ta faɗaɗa haɗi da faɗin
"Malam Abas bakayi barci ba nazaci gajiyar hanya zata saka kayi barci da wuri"
"Hajiyata ina zan iya barci banzo munyi hira ba gaba ɗaya aikin nan baya barina sakewa dake sosai kamar da, Hajiya kinsan me?"
"Bansani ba Malam Abas saika faɗa"
"Hajiya kinyi suruka" Abas yafaɗi haka yana sunkuyar da kansa alamar jin kunya
"Nayi farin ciki sosai Malam Abas Allah yasa albarka yatabbatar mana da alkhairi"
"Amin" yace ahankali yakarasa gabanta ya tsugunna yaɗora kansa saman cinyarta "Hajiyata kimin addu'a yarinyar nan tasoni fiyeda yanda nake sonta Hajiya nafaɗa sosayayya mai zafi kowane bugu na zuciyata yana bugawa da soyayyatar ta" Hajiya Hafsa na murmushi tadafa kan yaron nata tana masa addu'a, ba sabon abu bane a wajansa tun yana yaro haka take masa harya saba indai yanason wani abu yakan tsugunna a gabanta yace "Hajiya amin addu'a" ba ɓoye ɓoye a tsakaninsu komai yana iya faɗa mata baya shayi ko shakkar faɗa, Hajiya Hafsatu wayayyar maca ce tana matukar son ɗannata guda ɗaya tak da Allah yabasu itada mijinta Alhaji wada idiris, Hira sosai Hajiya da Abas suke har zuwa sanda Alhaji Wada yadawo Abas yabar ɗakin bayan sun gaisa da Abban nasa...✍🏻

Game bukatar shuga group ko gyara ko wani karin bayani 07039793439
[2/13, 4:43 PM] +234 904 746 4048: Follow this link to join my WhatsApp group: https://chat.whatsapp.com/GMAOuujeP6dLtFTHo1Edxx



🌹 *AIMANA*🌹


Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

Shafi na Huɗu

Ahankali take karanta addu'ar tashi daga barci, idanunta nakan agogon bangon dake manne jikin bangon ɗakin, karfe biyar saura na asuba sakkowa tayi daga kan gado ta shiga bathroom ta ɗauro alwala jin anata kiran sallah raka'anun fijir tasoma yi bayan ta idar ta zauna tana addu'o'i kafin sanda taji anyi assalatu, ta tayar da sallah, tasbihi tayi bayan ta idar da sallar tasoma karanto azkhair na safiya, harta kammala sannan ne Zeeyad yatashi tana kallonsa yashuga bathroom yaɗauro alwala yatada sallah, tamike tareda ɗauke daddumar datayi sallah akai ta linke ta maida ta ma'ajjiyarta, tashin Zaheed tayi ta taimaka masa yayi alwala shima yai sallah wanka tamasu ta gama masu shirin makaranta sannan suka fito, lokacin bakwai saura Leena suka tarar tagama shirya kayan breakfast bisa danning ta koma kichin, Aimanah tana zama ta tina da wayarta ta kalli Zeeyad tace
"My Son ɗakkomin phone ɗina a ɗaki" yamike a nitse ya tafi, dai dai sannan Anty Ummi da Yaya Mansur suka sakko daga sama, Aimanah tagaidasu cikeda ladabi, tare sukayi break fast gaba ɗaya bayan sun gama Yaya Mansur ya wuce wajan aikinsa tareda yara zai ajjesu a school, Aimanah tana buɗe wayarta sako na shugowa kamar daman jira ake ta buɗe wayar

_Amincin Allah yatabbata a gareki tauraruwata fatan kin tashi lafiya, Dan Allah inaso abani dama na kira wayan nan muyi magana bakon masoyi ne,_ Bakon masoyi Aimanah tafaɗa a fili batareda tasan ta faɗa ba Anty Ummi dataji abin data faɗa dariya kurum tayi taci gaba da danna wayarta, minti kaɗan tsakani wayar Aimanah tayi ring kamar bazata ɗaga ba ganin lambar da'akai mata tex ce yanzu, saida ta kusan katsewa sannan ta amsa kiran kara wayan tayi a kunnanta tai shuru batace komai ba
"Haba kyakkyawata kika kashe wayanki jiya"
"Malam mai yasa kake da naci ne bani kake nema ba, wannan ba lambar da kake nema bace nagaya maka tun jiya, Dan Allah kadaina kirana kana takuramin"
"Uhm uhm ke nake nema ba kece jiya muka haɗu a shoprite ba kika bani lambarki?" dariya Aimanah tayi kana tace
"Kaine wai ina kasami lambata?"
"Sirri ne amma ki tambayi Antynki"
"Anty Ummi" Aimanah ta faɗa ahankali
"Indai itace wacce kuke tare jiya to ki tambayeta, Aimanah tsaya ki saurare ni dan Allah nazo da lamari mai girma agareki Anty Ummi tabani labarin soyayyarki da Mustapha da tambarin da kika yiwa maza, ki sani kamar yanda mata ba halinku ɗaya ba haka maza muma ba halinmu ɗaya ba, ina sonki so irin so na aure bada wasa nazo ba dan Allah kibani dama naje ga iyayanki su bani damar zantawa dake mu fahimci juna manya su shiga a tsaida ranar auranmu, niba yaro bane bazanyi soyayya irinta yara ba"
"Soyayya kuma daman har yanzu akwai wannan kalmar, ni babu ita a wajena, a zuciyata da wajena tuni an kashe so" Aimanah na gama faɗar haka ta katse kiran ta ajje wayar ta wuce ɗakinta da sauri, Anty Ummi tabi Aimanah ta kallo tana girgiza kanta hannu tasa ta ɗauki wayar Aimanah dake ring sun jima suna magana da Abas daga karshe tamasa kwatancan gidansu Aimanah dake kano.

Abas bashida kowa daya sani a kano hakan yasa yasha wuya sosai kafin yasamo gidansu Aimanah da Yaya Mus'af sukayi magana ya nema masa izinin ganin Aimaha Daddy yace yabasa dama yaje inhar sun dai daita zaiyi farin ciki da hakan, cikeda ɗoki Abas ya ɗauki hanyar Abuja baishiga garin da wuri ba lokacin dare yayi goma saura na dare hakan yasa kawai ya wuce gidansa, cikeda takaicin rashin shugowarsa garin da wuri,kasancewar washe gari lahadi shiyasa dayayi sallar asuba yakoma barci bai tashi ba sai sha biyu na rana, yayi mamakin irin baccin dayayi "Barcin gajiya" yafaɗa ahankali yana murmushi shi kaɗai, wanka yayi haɗeda ɗauro alwala yafito, tsab ya shirya cikin Sky blue ɗin yadi ya fita masallaci, ahanyar dawowarsa daga masallacin ne yakira wayar Yaya Mus'af bayan sun gaisa ya bukaci yabasa adress na gidan Yaya Mansur yasan koya kira Aimanah ba ɗagawa zatayi ba yana tinanin ma tasa lambar sa a blacklist sabida jiya yayita kiran layin baya tafiya, Ya Mus'uf yabashi adress bayan sun gama wayan ya kira Yaya Mansur yamasa bayani

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login