Showing 15001 words to 18000 words out of 84763 words

Chapter 6 - AIMANA Book Complete by MAMI YUSUF DABO.txt

ne tareda kaunarka , Abas naroke ka karka yaudare kar..." Saurin katseta Abbas yayi tahanyar faɗin "Aimanah ki manta da wata yaudara banzo nan danna yaudareki ba naroke ki kimanta da *Mustapha* da yaudarar dayai maki ki ɗauki abin a matsayin kaddara da kuma dama can ba rabon aure a tsakaninku, bantaɓa soyayya ba sai akanki kece first love ɗina, uwar ya'yana insha Allah murmusa mana uhmm"

Dariya Aimanah tayi tareda saka hannu tarufe fuskarta tana dariya sosai, Abbas ya kalli agogon dake sanye a tsintsiyar hannunsa yaɗago yana kallon Aimana wacce yanayin fuskarta ya canza, idanunwansa yabuɗe sosai yana kallonta tareda ɗaga gira "Aimanah tafiya zanyi kinsan yau zan koma koma Abuja bana son tafiyar dare Hajiya faɗa takeyi, kwara na tafi da wuri, nabaki amanar zuciyarki, ki kularmin da kanki please"

"Kema haka My Abas ka kularmin da kanka ka tsare idanunka, karka kalli ko wacce mace"

"Kallo?" kallofa love ai daga kanki nagama kallon wata ɗiya mace kema kin sani nafaɗa maki ba sau ɗaya ba biyu ba" sallama sukayi Aimanah ta wuce cikin gida shi kuma yahau motarsa yatafi, ahankali yake tuki cikin zallar nishaɗi shi kansa yakasa gane shin wanne irin so yakewa Aimanah wani iri yakeji idan yana tareda ita jinsa yake kamar nan duniya babu kowa su kaɗai suka rage lumshe idanu yayi yana murmushi tareda tuna ranar farko daya fara gani Aimanah, da wani yammaci da bazai taɓa mantawa ba.


MUSTAPHA
Wata iriyar rayuwa yake shi ɗaya a india ko kaɗan yaki sabawa da mutane ko yaushe yana gidansa idan ba makaranta ya shiga ba to zaka gansa manne da Sumayya wacce akoda yaushe sonta karuwa yake a zyciyarsa da wani irin matsanancin tsoronta dayake ji Yauma kamar kullum dawowarsa kenan daga makaranta yana shigowa gidan yaji kansa ya sara masa, saurin zama yayi a kasa yanajin ɗakin na juya masa....✍🏻
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹


Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Tara*

*Assalamu alaikum masoya barkanmu da safiyar Juma'a, rana mai daraja idin musulmi, kar amanta dayiwa Annabimu salati a wannan rana haka ma kar a manta da karatun suratul khafi*


.......Abas agajiye ya sauka a gidansu can jigawa, bai sami Hajiya a gida ba bata nan taje wajan walimar bikin yar kawarta, bazai iya zuwa ya wuce batare daya ga Hajiyansa ba hakan yasa dole ya kwana a can ba damar komawa Abuja a ranar dole sai washe gari, baisami zama da Hajiya ba sai bayan sallar insha a gaba yasata da hirar Aimanah
"Abas ka zurfafa a soyayyar nan fa, ina jiye maka tsoron kazo baka aureta ba"
"Hajiya kima daina faɗar haka dan Allah, daman ɗazu wanta yake cemin yakamata na turo manya a tsaida ranar biki"
"Hmm jiya muka gama maganar nan da Alhaji, harma yabawa Alhaji Baita dama shida Alhaji Habu yaje suyi komai tunda baya nan"
"Masha Allah Hajiya naji daɗi sai dai banso a saka lokaci mai yawa ni zanso ma asa wata guda, daman karatu ya hana komai kinga kuma yau kwana uku kenan da sukayi gradution"
"Duk bazai gagara ba daga garemu ba wata matsala sai daga su bansan ko sun shirya ba"
"Hajiya sun shirya nifa banason sumin komai zanyi komai da kaina ko ɓangaran Amarya ma Aimanah kurum nakeso kuma ita kaɗai nakeso su kawomin batare da komai ba, ni zan sai komai na gida"
"Hakan yayi Allah yasa yanda kake kaunar yarinyar nan kaima tana sonka haka" dariya kawai Abas yayi yana shafar sumar kansa,sallama yayiwa hajiyar ya wuce ɗakinsa yai shirin kwanciya.

*Mas'ud*
.......Gaba ɗaya bayajin daɗin komai wani iri yakeji idan yaga Abas yazo wajan Aimanah ji yake kamar ya kore sa, haka kurum baisan Aimanah ta auri wani ba Mustapha ba, gaba ɗaya ya hana kansa barcin dare raya darare yake yana addu'ar Allah ya dawo da Mustapha hayyacinsa, yau bayan an fito daga masallaci sallar asuba yabi bayan limamin unguwarsu yayi masa bayanin halin da Mustapha ke ciki, Liman yayi jim kana ya ce
"Masa'udu shi wani bin asiri idan anyi wasu binne binne baya sakin mutum har sai anje an tone abubuwan da aka binne, irinshi ne mai wuyar karyewa gashi kace Mustaphan baya kasar nan da sai a haɗa masa ruwan addu'a yasha mugani"
"Limana bazaiyu a haɗa ba saina kai masa can kasar dayake" Liman yadafa kafaɗar Mas'ud ya ce
"Kayi hakuri kaji kaci gaba da addu'a muma zamu tayaka, idan yadawo kazo ka gayamin akwai abinda zanyi" Mas'ud yayiwa Liman godiya ya wuce gida yanajin zuciyarsa ba daɗi, yinin ranar haka yayi sa gashi nan shiba mai lafiya ba shiba mara lafiya ba, har aka tashi daga wajan aikinsu sanyi kalau da shi, ahanyarsa ta komawa gida kawai yasami kansa da canza hanya zuwa gidansu Mustapha bai shiga gidan ba yafaka motarsa a kofar gidan ya kira wayar Surayya kanwar Mustapha karamar ƴar Momy, yarinyar slantyly yana hango tahowarta ta gilashin motar sa, yanayin yanda take tafiya a nutse yaji wani abu ya daki zuciyarsa murmushi yayi tareda dukan sitiyarin motar, hannu yasa ya buɗe mata murfin motar, bata shiga ba ta ɗan durkusa cikin sanyin murya ta ce
"Yayanmu ina yini" haka take gayawa Mustapha shima Mas'ud sau tari hakan take kiransa,
"Lafiya kalau Sury, shigo magana zamuyi"
"Yaya dadai ka fito Ammi ta hanani shiga mota fa"
"Motar samarinki ba, niba saurayinki bane dan Haka ba zance nazo ba" dariya tayi ta shiga motar ta rufe fuskar ta
"Yayanmu ka bani kunya ina naga saurayi ni"
"To bani kunyar tawa na tafi da ita"dariya ta kuma yi tana sake saka hannunta daya sha jan lalle ta rufe fuskarta
"Sury kinsan halin da Musty ke ciki inata ƙoƙarin ganin na fitar dashi amma nakasa yau wani malami yafaɗamin abun da zuciyata takasa nutsuwa" nan yagaya mata yanda sukayi da liman, shiru Sury tayi tana goge hawayan dake zubowa daga idanta
"Nifa ba kuka na kiraki kimin ba" Mas'ud yafaɗa da wata murya da ban wacce shi kansa baisan yanada ita ba😂
"Yayanmu dole nayi kuka, jiya nan fa na shige ta kofar ɗakin Amarya naji tana wayada Murjana tana gaya mata ta binne layar nan a kasan murhun mai kosai, kawai jikina yabani kan Yaya ne zasu binne layar" Sury tasake fashewa da kuka
"Sury please stop craying, zakisa zuciyata ta buga fa" da sauri ta ɗago ta kallesa, yai saurin basarwa ya ce
"Yanzu Amarya tana nan?"
"Bata nan ta fita tun safe sai Murjana"
"Yawwa kiramin Murjana nan amshi wannan ki goge face ɗinki, duk kin ɓata kwalliyarki da hawaye sai saurayinki yazo yaga fuskarki a haka yamaki dariya"
"Yaya Nifa Allah vana da saurayi"
"Najib fa?" Saurin amsar hankacif ɗin tayi ta fita tana dariya, yaɗan jima a motar kamar yatafi jin shiru Murjana vata zo ba, yana kokarin tada motarsa ya hangonta ta fito ko mayafi bata saka ba yana hannunta ta rikesa, kai tsaye ta buɗe motar ta shigo bako gaisuwa ta ce
"Surayya tace kana kirana"
"E! dan Allah mai kike so namaki nima inada abinda nakeso kimin" shiru Murjana tayi alamar tana nunani can taɗago ta kallesa
"Kafara faɗar abinda kakeso na maka saina faɗi nawa daga baya sabida nawa yanada girman daba lalle ka iyasa ba"
"Nima nawa babba ne"
"Zan maka komai kake so matukar zaka aure ni" dam gaban Mas'ud yafaɗi yaɗago ya kalleta ta kashe masa ido ɗaya
"Naji zan aure ki indai zaki min abinda nakeso"
"Faɗi kawai ko menene zanyi"
"So nake ki rakani inda kuka binne asirin da kuka yiwa Mustapha"
"Waye yafaɗa maka wannan maganar?"
"Narida nasan komai wallahi indai aka tone tona rantse maki zan aure ki" Shiru tayi na mintina can ta ce
"Zan tone komai yau da daddare kasani inka yaudare ni komai zai iya faruwa"
"Ba abinda zai faru sai alkhairin aure na dake" fita tayi a motar ta koma cikin gida yana kallo harta shiga gidan yatashi motarsa yanajin nutsuwa a zuciyarsa, Surayya tana gayawa Murjana Mas'ud na kuranta ta wuce ɗakin Ammi, ƴar ɗakin Ammi ce sosai kusan komai nata yana ɗakin Ammi, zama tayi saman kujera rufe idonta ta ɗora Hankacif ɗin da Mas'ud yabata a fuskarta tana shakar daddaɗan kamshin turaran Mas'ud, wani bakon yanayi takeji a zuciyarta gameda Mas'ud
Mas'ud koda dare yayi kasa nutsuwa yayi har saida yakira lambar Surayya wacce har varci yafara ɗaukarta cikin mayan barcin tai picking call ɗin
"Hello" tafaɗa da muryar barci
"Haɗani da Murjana ko ki bani lambarta"
"Bani da lambarta, naga fitarta ɗazu wajan tara na dare"
"Ok" kawai yace ya kashe wayar, Ammi dake zaune kusada Surayya ta kalli Surayya ta ce
"Dawa kike waya?"
"Yaya Mas'ud ne Murjana ya ke tambayya" Ammi dafe kirji rayi tareda zaro idanu
"Wayyo ni Saudatu shikenan shima ya shiga komar su wayyo Allah na"
"Ammi vana tunanin wani abu tsakanin Murjana da Mas'ud akwai dai abinda yakawo sa wajanta inaga akan Yayanmu ne" Ammi ta sauke numfashi ta maida kanta ta kwantar jikin filo,Murjana dare tabi ta tone komai batareda Amarya tasani ba saida ta haɗa dukkan abubuwan da suka binne ta kira Mas'ud, yazo ya karɓa cikin dare ya kone gaba ɗaya layun.

Alhaji Habu da abokinsa sukaje suka zo kano aka tsaida auran Abas da Aimanah nan da wata uku...
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹


Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi na Goma*

*Wannan page ɗin gaba ɗayansa sadaukarwa ne ga Chamsiyya Louwali Rabo (Mrs Sadauki) Mafiya*


*Mustapha*

.....Idanunsa yabuɗe waɗanda yaji sunyi masa wani irin nauyi zabura yayi ya fisge kanula ɗin karin ruwan dake hannunsa yamike yana kiran "Aimanah! Aimah!!!" yafaɗa da wani irin sauti da yai amsa kuwa a cikin asibitin, nan da nan likitoci sukayo kansa, wani jirin ne yasake ɗibansa yai luu zai faɗi kafin ya kai kasa ɗaya daga cikin Nurse ɗin dake ɗakin yai saurin tare sa yafaɗi a jikinsa
Sumayya gefe ta koma ta ɗora hannu aka ta fashe da kuka ta fita waje ta kira Amarya a waya "Wayyo Amarya na shiga uku shi kenan na kaɗai komai ya warware muna asibiti Mustapha ya birkice sai faman kiran sunan Aimanah yake, Mama dan Allah ki koma wajan boka tsito komai fa ya ruguje"
"Sumayya garin yaya kikayi wannan gangancin?"
"Mama banida masaniya akan komai kawaifa yadawo gida yafaɗi na kira asibiti suka zo suka ɗaukemu yanzu kuma ya farka yana kiran sunanta"
"Bari na shirya naje wajan Tsito muji wannan masifa daga ina da rana tsakan nan"
Sumayya ta koma ɗakin da Mustapha ke ciki ta tarar har anyi masa allurar barci cikin turancin daya daga cikin Likitocin yake gaya mata ta zauna nan kusa da shi ta kula da shi yana tashi ta kira su, Mustapha ya kwashe awanni yana barci kafin yabuɗe idonsa karaf idanunsa kan fuskar Sumayya saurin mayar da idanunsa yayi ya rufe yai shiru kamar mai barci, komai yasoma dawo masa a kwanyarsa "Nooo!!!" yafaɗa da ihu tareda mikewa duka a lokaci ɗaya, wuyan Sumayya ya shaka
"Ke kika ja komai ina Aimanah ina Ammi?" Sumayya idanu zare ta kasa magana saboda shakar dayayi mata wanda takeji kamar za'a zare mata rai magana takeso tayi ta roke sa yayi hakuri ya kyaleta amma ta kasa, dan kansa ya saki wuyan nata tareda haɗata da bango, gefan gadon ya koma ya zauna tareda dafe kansa yana fitar da numfashi da sauri sauri
"Ina wayata?" yafaɗa yana kallon Sumayya data koma can gefe ta tsugunna har sannan tana rike da wuyanta, mika masa wayan tayi ta koma nesa da shi ta tsaya tana kallon sa, lambar Ammi ya loda sannan ya danna call, bugun farko Ammi ta ɗaga wayan gabanta na faɗuwa ganin kira da wata lamba ta wani kasa
"Ammi kiyafemin" abinda Mustapha yafara faɗa kenan bayan Ammi tai picking call ɗin
"Mustapha kaine Alhamdulillah Allah na gode maka" Ammi tafaɗa da muryar kuka
"Ammi ina Aimah"
"Tana nan kalau"
"Ammi gida zan tawo"
"Mustapha ka zauna ka karasa abinda yakaika India kwanki fa suka rage maka"
"Ammi Aimah fa bazan iya zama anan ba Aimah ba" hmmm Ammi taja numfashi tana goge hawayan tausayin ɗanta dasuka zubo mata
"Karka dawo Mai babban suna ka zauna kamar yanda nace maka Aimanah tana nan har kadawo"
"Shikenan Ammi zan zauna ki turomin lambar Aimah na kira naji muryarta" Ammi ta katse kiran ta ɗora kanta saman kujera ta fashe da kukan tausayin Mustapha, "Mustapha kadawo hayyacinka a kurarran lokaci yamzu Aimanah tazama ta wani" kuka tayi sosai sannan ta mike ta fita daga ɗakinta zuwa na Momy, Mustapha yamaida kansa ya kwanta saman bed na asibitin yanajin zuciyarsa kamar zata fasa kirjinsa ta fito, wata iriyar soyayyar AIMANA ce ketasowa tun daga kasan zuciyarsa
"Ammi bazan iya ba, bazan iya jure zama anan ba Aimah ba, mikewa yayi yana kallon Sumayya data haɗa kai da gwiwa ta zafga tagumi
"Ke kisa a sallameni gida zan koma" asanyaye tamike ta fita shi kuma ya koma ya zauna yana tinanin irin hukuncin da zai yankewa Sumayya, saki shine babban abinda zuciyarsa ta amince dashi

A can gida kano kuwa gaba ɗaya hankalin Amarya yatashi da kyar ta lalubi hijab ɗinta ta saka tana kokarin fita daga ɗakin Murjana ta shigo ɗakin, kallo ɗaya Amarya tayiwa Murjana ta ɗauke kai tana tsaki
"Mama ina zaki?"
"Wajan boka Tsito zani komai ya warware"
"Mama dama kin zauna basai kinje ko ina ba ni na tone komai"
"Na shiga uku" Amarya tafaɗa tana ɗora hannu aka "Murjani ke kika mana wannan ɗanyan aikin, na shiga uku ni naja'atu Allah ya wadaranki Murja" Amarya ta fice fuu daga gidan gaba ɗaya.

Aimanah da Abas soyayya suke sosai da sosai ko yaushe suna manne a waya ayyuka sun masa yawa sosai sakamakon karin girma daya samu a wajan aiki hakan yasa bai zuwa kano sosai sai da waya, tuni Aimanah tafara aiki a ɗaya daga cikin gidan redion dake cikin garin kano, sosai tamaida hankali wajan aikinta, yau agajiye ta dawo daga wajan aiki gaba ɗaya bata jin daɗin jikinta kamar mai zazzaɓi haka takejin jikinta wanka kurum tayi ko abincin dare bata tsaya taci ba ta wuce ɗakinta zata kwanta barci, harta gama addu'ar kwanciya barci ta lulluɓa da blanket taji alamar shigowar sako wayarta, da sauri ta ɗauki wayar tana murmushi "Abas farin Masoyi" tafaɗa afili tana kokarin cire key na wayar
_"Fatan alkhairi tareda fatan kina cikin aminci ina mai neman afuwa bisa tarin ɗimbin zunubin dana aikata a soyayyarki_ mamaki tayi ganin bakuwar lamba da bama ta wannan kasar ba goge massages ɗin tayi taja tsaki ta koma ta kwanta tana mai cewa kilama saɓanin number aka samu, Abas ne ya kurata suka sha soyayyarsu har tayi barci sannan ya kashe wayarsa ya kwanta.

Mustapha gaba ɗaya baya cikin nutsuwarsa gaba ɗaya hankalinsa yayo gida kano nageria, sam yafita harkar Sumayya ayanda yaso tun acan zai yanke igiyar auransu gaba ɗaya amma yakasa saboda tausayinta da yaji ya jinkirta sai yadawo gida,yau cike yake da murna da ɗokin gobe zai bar india zaiyi ido huɗu da sarauniyarsa Aimanah murmushi yayi sanda ya tuna Aimah ya tina tilin tex masaages daya ke aika mata amma bata taɓa dawo masa da reply ba, shi duk azatonsa fiahi tayi baisan cewa batama san shi bane, ita kuwa Aimanah ko sau ɗaya bata taɓa kawowa wai Mustapha nw ke aiko mata da sakonni ba waɗanda tana ganin shigowarsu wasu ta karanta wani ma ko buɗewa batayi zatayi delate ɗinsa, dan yanzu ba kowa a gabanda da zuciyarta sama da Abas wanda takewa wani irin so, sosai take son Abas a yanzu a cewar Aimanah yanzune tai soyayya, soyayyar Mustapha datayi a baya ba soyayya bace idan ta haɗata da ta Abas,
Abas ɗan soyayya ne ya iya soyayya da tattalin mace kusan ko yaushe suna jone a waya motsi kaɗan ya kirata ya ce yayi kewarta, yau Aimanah ba inda taje kasancewar lahadi ce tana gida bata fita, azaune suke a falo itada Mahh suna kallon Arewa 24 Aimanah na tsotsar alawa ahankali kamar wata karamar yarinya Mahh ta kalli Aimanah tai murmushi
"Hmm Abas zai sha yarinta dan Allah jibi yanda kike ta tsotsar alawa mai tsinke kamar wata yarinya" Aimanah ta ɓata fuska kamar mai shirin kuka
"Mahh nifa yarinya dika shekaru na basufi goma sha bafa"
"Kice ma baki shekara ba" Mah tafaɗa tana maida hankalinta kan shirin da ake haskawa a arewa, wayar Aimanah tayi kara alamar shugowar kira kallo Mah tay taga hankakinta ba akanta yake ba hakan yasa tai pickin call ɗin
"Hello Masoyi" Aimanah ta faɗa a hankali tana satar kallon Mahh
"Masoyiya ya kike, kawau naji kewarki na kiraki"
"Kewa niko bana kewarka saboda ko yaushe kana maƙale a zuciyata"
"Nima haka, gabana faɗuwa yake Masoyiya yanzu Kanol ya kurani zamu shiga daji, tsoro nakeji gabana faɗuwa yake Aimanah ji nake kamar wani abu zai sameni nifa gani ma nake kamar mutuwa zanyi....😰
[2/13, 4:44 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹


Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰

☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation

*Shafi Na Goma Sha ɗaya*

"Mutuwa kuma? haba masoyi tabbas mutuwa wajibi ce akan dukkan mutum bawa mai numfashi amma bazaka mutu yanzu ba, masoyi bansan ka da sarewa ba kaida kake karfafawa wasu gwiwa kuma yau kazo da wannan maganar insha Allah nasara ke tare da kai, katashi kai shiri ka haɗa rundunarka ku tafi Allah yana tare dakai Masoyi"
"Na gode masoyiya kin karfafa mun gwiwa, duk na sare inda zamuje ba sarvice kwana uku zamuyi ki kularmin da kanki, ki adanamin soyayyata can kasan zuciyarki, kiyi barci sosai banda tunani mai yawa, Ina fatan duk sanda kika tina ni kimin addu'ar samun nasara"
"Insha Allah nasara na tare damu" kashe wayar yayi naja ajjiyar zuciya ina ɗago kaina muka haɗa ido da Mah wacce bansan tsawon lokacin data shafe tana kallona ba
"Masoya, in anyi magana kice ke yarinya ce gashi har kin

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login