Showing 63001 words to 66000 words out of 84763 words
Chapter 22 - AIMANA Book Complete by MAMI YUSUF DABO.txt
la'asar a maimakom sallah biyar uku zaki nayi kina jinmu" jikinta na rawa hannunta na kankame da magen da ke ɗan kuka kasa kasa ta ɗaga kanta dan bakinta yakasa furta komai sabida tsoro da firgi cin daina salloli biyu da aka sata, ta fita da baya baya
Shatar mota ta ɗauka a tasha zuwa abuja sassafe ta isa gidan ta dake abuja, tayi nasarar tarar da Mustapha baya nan ya fita aiki, hakan yabata damar saka magen kasan gado ta kuma zuba ruwa a kwalba mai magani da malam yabata ta shanye...✍🏻
[2/13, 4:45 PM] +234 904 746 4048: 🌹 *AIMANA*🌹
Story and writting by
Mamie Yusuf Daboo🥰
☀️ *First Class Writer Asso*☀️
Home Of Qualities And Trusted Writer's Of The Nation
*Shafi Na Talatin da ɗaya*
Aimanah dake kwance a ɗaki gaba ɗaya taji jikinta kamar wacce ake ɗaurewa da igiya duka jikinta yayi sanyi kalau, lamo tayi tana kallon yaranta dake barcin safe, banko kofar da akayi da karfi ita ta farkar da Islam dake rigima daman barcin nata ba wani nisa yayi ba, Aimanah ta ɗaga kai ta kalli Sumayya dake girgiza tana wani fari da idanu
"Ki fito ki gyaramin gida malama" Aimanah ta ɗago da niyya maida marta ni amma wani abu mai kyalli ya fito daga idanun Sumayya ya faɗa idanunta da sauri tayi kasa tareda runtse idanun nata, dariya Sumayya taci gababdayi tana kallon Aimanah data sun kuya tana murza idanunta, da sauri ta ɗago bayan taji idanun nata sun daina zafin amma kallon da Sumayya ta mata yasa gabanta ya faɗi ba musu tabi Sumayya zuwa compound ta soma aikin data saka ta, daga wannan ranar saiya zamana komai na gidan Aimanah keyi ta koma kamar mai aikin gidan, ko abinci ita keyi amma wanda Sumayya ke bata ko yaran baya isa, Aimana na cikin damuwa sosai nan da nan ta rame tai baki sau biyu tana kwada son futa ta gudu daga gidan sabida azabar da Sumayya ke gana mata amma getman ya hanata fita, Maman Hanif makociyar su Aimanah ce tasu tazo ɗaya sosai lokaci bayan lokaci suna zagaya juna su gaisa, Maman Hanif ganin kwana biyu Aimanah bata shigo mata ba hakan yasa yau ita ta shiga gidan, abinda ta gani ya ɗaga mata hankali ganin Aimanah kamar mata yarinyar gida tana rike da moper tana goge compound na gidan da sauri maman Hanif ta taɓa Aimanah, Aimanah ta juyo tana kallon ta, sharr sai hawaye daga idanun Aimanah, gefe Maman Hanif taja Aimanah suka zauna
"Maman Hanif ina cikin masifa kalli yanda rayuwa ta juyamin baya, Mustapha yadaina kulani komai na gidan nan ya canza jibi yanda nadawo yar aiki a cikin gidan mijina nakasa taɓuka komai ko na ɗaga waya zan kira makusanta na saina kasa nayi yunkurin barin gidan nan na tafi namu gidan an hanani fita ina zan saka kaina ban saba da wahala bazan iya wannan bautar ba" Maman Hanif goge hawayan idanunta tayi ta ruko hannayan Aimanah
"Aimanah kina addu'a kuwa kina azkhair yanda yakamata"
"Inayi Maman Hanif ina komai har karatun kur'ani ina yi"
"Aimanah na rantse da Allah asiri aka maku aka farraka tsakaninki da Mustapha, ki tsananta addu'a ki daina barcin dare kina ta shi cikin dare kina addu'a Allah zai fiddaki daga wannan jarabawar daya maki, sannan karki gayawa kowa wannan maganar ki rike sirrin cikin gidanki"
"Maman Hanifa nabar maganar nan fa kika ce karna faɗawa kowa na zauna cikin uku ba da azabar aikin nan harta motocin gidan nan ni nake wankewa"
"Aimanah kiyi hakuri" maman hanif ta faɗa bayan ta mike tun daga wannan ranar Maman Hanif ke kawowa Aimanah abinci a ɓoye wanda zai ishe su, Sumayya duniya ta mata yanda takeso sai facaka take da kuɗi tana abinda take so, tsadaddiyar motar Aimanah yanzu ta zama mallakinta da kanta tasa Al'Mustapha ya karɓar mata key ɗin daga hannun Aimanah yabata, a cikin wannan halin da suke Rumana ta haifi yaranta twince masu matukar kama da Abbas mace da namiji, Hajiyar Abbas jigawa ta wuce da yaran da mai jego acan zasuyi zaman wanka Abbas ma kwana huɗu da haihuwa yabi matarsa wai tare zasuyu zaman wankan, Hajiya Hafsatu mace mai kirki da son mutane ita tayi ta kula da Rumana Ammi da taje ma bata barinta tayi komao harta ɗora ruwa yiwa mai jego da jarirai wanka duk ita takeyi, Aimanah taji labarin haihuwar tayita ɗoki da zumuɗin zuwa suna amma Mustapha yasawa idanunsa toka yace ba inda zata, wannan duk huɗubar Sumayya ce, Aimanah tayi kuka ranar kamar ranta zai fita, ta duba duka account ɗinta gaba ɗaya bata da komai a ciki duka ta cinye su lokacin da Sumayya ta ɗebe kayan abincin gidan, sai da dare yayi kana ta kira lambar Yaya Mus'af bayan sun gaisa ta ce
"Yaya dan Allah kuɗi nakeso"
"Kina matar accounter kike neman kuɗi, ko bashin banki basai yabaki ba" Mus'af yafaɗa yana dariya
"Yaya banaso yasani fa, shiyasa nabari sai yanzu na kiraka, wasu kaya zanyi ordar nake neman kari"
"kamar nawa"
"Ko ɗari da hamsin nasamu"
"Bama masu yawa kike bukata ba, ba damuwa zansa maki yanzu"
"Nagode yaya" Aimanah tafaɗa tana share hawayan idanunta
"Ba godiya a tsakanimu ina mutanan"
"Sunyi barci tafaɗa tana kallon yaran dake barci" basu jima da sallama ba taji alart tana dubawa taga dubu ɗari biyu, murmushi tayi nan take ta yiwa Rumana transfer na dubu ɗari tareda mata messages _kiyi hakuri Rumana bazan sami damar zuwa suna ba anma zan zo daga baya naga babys ga kuɗi nan ba yawa asaiwa yarana riga_ Rumana murmushi tayi bayan ta gama karanta messages ɗin
Hankali tashe Mustapha ke kallon Sumayya
"Ina kika saka min jakar da jiya na shigo da ita,"
"Jaka kuma na rantse ni banga ka shigo da jaka ba gidan nan" Sumayya tafaɗa tana zare idanu, a haukace Mustapha ke bincikar ɗakin ko ina lekawa take ko zau gano jakar, rasa wannan jakar kamar rasa aikin sa ne, ga zargin cin amana da za'a masa kilama takaisa ga birsin hakan ya kuma tasar hankalinsa
"Sumayya ki fito min da jakata nan fa na ajjeta"
"Na rantse ban ɗaukar maka jaka ba, in baka yarda ba muje ɗakina ka bincika daga nan sai a duba na Aimanah" sak yayi yana kallonta jin ta ambaci Aimanah sunan da a yanzu bayajin akwai wani suna daya tsana ko son ji bayayi sama da sunan, ɗakinta aka bincike tas babu jaka ba dalilinta, haka ta tisa Mustapha a gaba aka shiga ɗakin Aimanah, ita tsorama taji daga gansu sun ahigo mata bako sallama mikewa tayi tsaye tana kallonsu
"Kin wani zuba mana idanu kamar na mujiya jaka ake nema a gidan nan ba'a ganta ba, shine nace a bincika ɗakin kowa dan a fitar da ɓarawo, nagodewa Allah an bincika ɗakina bata nan shuyasa na rako sa a bincika nan"
"Ok bisimillah" Aimanah tafaɗa tana matsawa suka shiga ɗakin sosai, bin ciken farko saiga katuwar jakar mai shake da manyan kuɗaɗe a cikin wardrove ɗin Aimanah, wacce tayi tsuru tsuru tsoro duk yakamata ganin abinda bata zata ba
"Ka gani ko kaga gaskiyya ta fito ko, shiyasa nace a bincika ko ina, oh ana zaune da katuwar ɓarauniya bamu sani ba," Mustapha baice komai ba ya rungumi jakar kuɗi zai fita da ita
"Wai kana nufin baza kace komai ba, kana ganin wannan babban zunubin da ta aikata sata fa"
"Maizan ce Sumy tunda sun fito ai shikenan"
"Au haka zakace ai wallahi bazan zauna da ɓarauniya anan ba wataran ni ta sace ni yau yau ɗin nan zata bar wajan nan daga ita har ƴaƴanta amaidata can ɓangaran bayan nan ta karata acan"
"Duk yanda kikai dai dai ne" Mustapha yafaɗi haka yasa kai yafita daga ɗakin, watsi Sumayya tafara yiwa Aimanah da kayan sawarta dana yara tana watso su waje
"A fita afita a koma can aci gaba da sata" Aimanah na hawaye ta fara tsintar kayanta ta ɗago ta kalli Sumayya zuciyar Aimanah ta rauni kawai ta fashe da kuka, kafafun Sumayya ta rike
"Sumy na roke ki da girman Allah da azabar da kike gana mana gara kisa Mustapha ya sakeni na koma gaban iyaye" Sumayya ta kece da mahaukaciyar dariya tana kallon Aimanah
"Saurin me kike ai ana gab da yin hakan zan saka ya baki takarda mai ɗauke da saki uku ta yanda ke da zama da shi har abada amma sai bayan na gama shayar da ke zumar azaba a gidan nan" Sumayya na gama faɗar haka ta juya ta wuce ciki ta rufo kofa, Aimanah kayanta ta ɗiba zuwa bayan wajan yayi datti sosai sabida da Salman ɗan gwaggo ke zaune a wajan babban falo ne sai ɗaki ɗaya mai ɗauke da toleit a ciki, kayanta ta jera a wardrove ta zauna gefan karamin gadon taja tagumi tana hawaye Tasnim na goge mata, Islam da Aslam na kwance lamo a jikinta,
Aimanah duk yanda taso ta gayawa wani halin datake ciki saita kasa kamar wacce aka rufewa baki, hakan yasa ta tsananta ibadarta barcin daranta ya koma rabi cikin dare take ta shi tayi sallah tai kuka ta roki ubangiji ya fitar dasu daga halin da suka shiga, ko kaɗan batajin haushin Mustapha sai ma tausayinsa datake ji daman can tasansa da rauni musamman wajan azkhair sau tari ko addu'ar kwanciya barci ita ke masa ta shafa masa a jikinsa bare kuma azkhair da ada intayi magana sai yace aikine ya masa yawa zai yi, tasani wasa da azkhair da karatun kur'ani da yake shiya jawo masu komai, sabida ta tabbata Sumayya asiri tayiwa Mustapha kamar yanda tayi a baya sanda zata aure sa,
Sumayya shewa sukayi da kawayanta suka tafa
"Gaskiyya lina ina godiya da kuka ɗorani a hanya kuga yanda nadawo wata big girl da na tsaya kaina zai kulle, ai ingaya maku a gidanna mulkina nake yanda naga dama komai na Muatapha yanzu yadawo nawa harta motar Aimanah yanzu ni nake hawa da kaina na koma wajan malam kibauu nasa ya hana waɗan can mutanan dawowa nace a janyw masu hankali daga nan bare su dawo suga abinda ke faruwa atafi a lalatamin aikina yanzu ba gashi ba inata shan sharafi na, boka ya tabbatar min da Aimanah bazata iya barin gidan nan ba inhar ma magen karkashin gado na kunce ba," tafawa suka daɗa yi tareda shewa, Aimanah komawa tayi ta jingina da bango tana hawaye
"Mage mage a karkashin gado ya ilahi" komawa Aimanah tayi da baya daman Islam ke kukan tana jin yunwa ta zo ta roki Sumayya ta taimaka ta bata abinci ashe rabon zata jiyowa kanta ne, wayar maman hanif ta kira mintina kaɗan tsakani Hanifa babban ɗiyarta ta kawowa su Aslam abinci, Aimanah zuru tayi tana kallon yaran ganin yanda suke cin abincin hannu baka hannu kwarya, share hawayanta tayi tausayin yaran suka kamata tamike tana jin zuciyarta na mata wani irin zafi
zagayan neman mafuta a rayuwarsu tafara yi, kakarin aman data jiyo daga bayanta yasa ta juyowa taga islam ce keta amai da sauri ta rungomo yarinyar jikinta tana mata sannu, wajan datai aman Aimanah ta gyara, kafin wani lokaci zazzaɓi mai zafi ya rufe islam sai surutai take,
"Wayyo Ammi zan mutu afaɗawa abie banda lafiya a kaini asibiti wayyo Ammi cikina" islam ke faɗa da muryar yara
"Yi shuru islam bazaki mutu ba, zakiji sauki Aslam ne ya mike da gudu ya fita ya zagayawa wajansu Sumayya bako sallama yafaɗa ɗakin kai tsaye wajan Abie ɗinsa yaje ya ruko hannunsa
"Abie islam bata da lafiya zo kaje ka ganta" Mustapha saroro yayi da idanu yana kallon yaran yana son tina inda yasan sa
"Kai maye baza shi ba, futa ka bamu waje ɗan iska mara tarbiyya" Sumayya ta faɗa a zafafe kamar tana magana da sa'anta, Aslam baya yayi ya fita daga sashin yana legen Mustapha wanda shima yaron yake kallo wanda yake hango fuskarsa a fuskar yaran
Islam tasha wahala matuka maman Hanif ta kawo mata magani harta sami sauki, yau Murja garin abuja suka sauka dawowar su kenan daga dubai jirgi ya sauke su nan abuja, hakan yasa ta cewa Alhaji Jamil ya kama masu ɗaki a hotal su kwana zataje gidan yayarta su gaisa, texz ya ta shiga zuwa Yaya Mustaphan cikeda ɗokin ganin yayar tata da yayanta harma da yaya Aimah, hannu biyu Sumayya ta karɓeta suna hira kan mahaifiyarsu
"Anty Sumy yanzu wai ba wanda mama take jin tsoro yamata magana ta daina harkar datakeyin nan"
"Babu Murjana iyayanta ne to suma sun zuba mata idanu duk da na tabbata basu san mai take aikatawa ba, duk da daman can bata ɗauke su da mihimmanci ba, addu'a kawai zamuyi mata" kai kurum Murjana ta gyaɗa can ta ce
"Yanaji gidan shuru ko Yaya Aimah bata dawo daga aiki ba" dariya Sumayya tayi ta ruko hannun Murjana suka fito can baya karshan gidan Sumayya ta tura kofa suka shiga Aimanah ce zaune saman carfet itada yaran data rungumo su duka a jikinta, Murjana kallon Aimana tayi ta juya ta kalli Sumayya dake ta murmushi
"Murja yaushe kika zo?" Aimanah ta tambayeta a sanyaye
"Yanzu" Murja tabata amsa tana bin ɗakin da kallon mamaki, ta juya ta kalli Sumayya da har sannan fuskarta ke shimfiɗe da murmushi
"Anty Sumy ban gane bafa mai Aimanah take anan wajan da ya dace ace yan aikinku ke wajan"
"Itama yanzu ai batada maraba da yar aikin" Sumayya ta faɗa tana jan hanun Murjana dake kallon Aimanah wacce ke goge hawaye suka fita
"Sakar min hannu Sumy ki sake ni, mai abinda na gani yake nufi"
"Kin rigada kinsan komai Murjana wani malami na samu mai zafi ina gaya maki hmmm ba'acewa komai, aiki yayimin yanda nakeso, kema in kinason kama mijinki kizo na rakaki kiga yanda ake aiki kamar yankan wuka"
"Innalillahi wa'inna ilaihir raji'un, la'ilaha illa anta subahanaka inni kuntu minal zalimin, maine haka wai Sumayya kinyi hauka ne, ina zaki kai wannan zunubin mai girma haka"
"Istigifari ai bai bar komai ba murjana inaka aikata ba dai dai ba saika tuba ka koma ga Allah"
"Sumayya banso ba banso kika komawa harkar asiri ba duk karyan banza ce da ɗaukarwa kai zunubi kisani Allah baya yafe laifin wani daka cuta, Anty Sumy kin cutar da masoya Allah bazai barki ba, kuma da ikon Allah saina tarwatsa komai" Murjana na gama faɗar haka tayi baya ta koma wajan Aimanah da har sannan ta sameta tana hawaye
"Yaya Aimanh bar hawayan nan insha Allah komai zai wuce yanda na tarwatsa wancan asirin haka yanzuma insha Allah saina tarwatsa komai, nasanki ada kinada ibada kici gaba karki daina tabbas nasan ibadarki tasa kika tsaya iya wannan halin, kaico kaicon yaya Mustapha da bai ɗauki azkhair da mihimmanci ba shiyasa daga an masa abu yake saurin kama sa kici gaba da addu'a Yaya Aimaah, ko zaki bini mu gudu na maida ke kano"
"Bazan iya nayita yunkurin yin haka amma sai naji na kasa barin gidan zan so ace zan iya fita daga gidan nan da tuni bana cikinsa" mikewa Murjana tayi tana gyara zaman jakarta dake saɓe a kafaɗarta
"Gobe zan dawo Yaya Aimah da ikon Allah saina fiddaki daga wannan gidan" ɗagowar da Murjana tayi taga Sumayya na tsaye jikin kofa tana kallon su, sa kai Murjana tayi ta raɓa ta gefanta ta wuce tana gafda fita daga gidan taji Sumy ta kira sunanta ta juyo tana kallonta
"Zaki fitar da ita ko? to gara ma kiyiwa gidan nan kallon karshe keda sake shigo sa har abada" juyawa Sumy tayi ta koma ciki, Murjana jikinta yayi sanyi tana mamakin Sumy,
Sumy na komawa ɗakinta malam ta kira ta sanar mata yanda sukayi da Murjana sannan tace tana so yakara mata aiki sosai kan Mustapha taga yafara mata musu kwanan nan
"Dole zai maki masu kishiyarki na tsaye kan addu'a bamuda wani abu da zaiyi tasiri a kanta, kici gaba da rikon magen nan ruhin haɗe take da ruhin Aimanah daga randa kika yi sake magen nan tabar cikin gidan daga ranar Aimanah bazata sake kwana a gidan nan ba, fitar Aimanah daga cikin wannan gida dai dai yake da tarwatsewar komai da kikayi, ga tukunya nan mun saka aljani dundurusu ya ajje maki a kofar ɗakinki ki fito ki ɗauka ki mata ma ajjiya mai kyau karta fashe inta fashe akwai matsala maganar kanwarki kuma yanzu zan mantar da ita komai" sallama sukayi da boka Sumayya ta fita ta ɗauki tukunyar a hankali tasa can wani ɗan lungu dake cikin ɗakinta ta adanata
Kamar yanda malam yafaɗa hakance ta faru Murjana kafin ta karasa hotal ɗin da suka sauka ta manta da wata Aimanah bare kuma alkawarin komawa datayi mata
Yau Aimanah ta tashi jikin Islam ba daɗi gaba ɗaya hankalinta ya tashi musamman ganin yanda take mimmikewa, kafin wani lokaci ta suma yafi sau biyu, a guje Aimanah tafita daga wajan nata tai sa'ar ganin Al'Mustapha tsaye jikin motarsa suna magana da Sumayya da alama fita zaiyi
"Yaya dan Allah dan Allah akai Islam hospital wallahi batada lafiya sumanta uku a safiyar nan, dan Allah Sumayya ki taimakamin" Aimanah tafaɗa tana rike kafafun Sumayya, Sumayya kafa tasa ta take hannun Aimanah wanda har sai da hannun yayi kara, Aimanah tasaki azababban ihun dayasa Mustapha lumshe idanu ya kifa kansa saman motar sa haɗeda rike kirjinsa da hannu ɗaya
"Muna fuka baza'akai tan ba ta mutu mana waye a ciki" Aimanah mikewa tayi daga tsugun nan datayi na rokon Sumayya, hannunta wani irin azabar zafi yake mata tana fitar da numfashi ta kalli Sumayya cikin kukan azaba
"Allah yamaida maki mugun nufinki kanka, Sumayya insha Allah bazaki taɓa gamawa da duniya lafiya, bazan taɓa yafe maki wannan azabar da kike gana min ba, nasani bazan zafi da raɗaɗin haihuwa ba tunda baki taɓa yinta ba, shiyasa bazaki taɓa jin tausayin yara ba nabarki da Allah"
"Ni kike zagi Aimanah ni zakiyiwa Allah ya isa,"
"Ya isa ya isa haka Sumayya akai Islam hospital" Mustapha yafaɗa cikin bada umarni ya shiga motarsa yaja a fusace ya fice daga gidan da mugun gudu
"Bazan kaitan ba idan ta mutu ma nima nayi farin ciki" Sumayya tasa kai ta koma ciki, Aimanah ɗaki ta koma ta kira lambar maman Hanif tana kuka ta gaya mata halinda Islam ke ciki, maman Hanif Dr ɗin dake duba su ta kira a waya