Showing 33001 words to 36000 words out of 56306 words
Chapter 12 - ZAMANI (1 to end) Book Complete by Fiddausi Sodangi .pdf
biyu bamu had'u ba yaje gida watau Abuja tsohuwar sa ta kirasa wai, to abinka ga
masoya dole muka tsaya muka gurji juna son rai kafin na taho amman afuwan Alhaji!".
“Sannan nayi ta k’ok’arin naga na sameka a waya amman inaaa sam hakan ya faskara, kayi
hakuri Alhaji nasan ban kyauta ba amman na sauke hakkin masoyi nane kokaga laihina?".
" Abinne saida kula saboda shidin yakasance mai kyau sosai kamar ka dai to kaga dole ayi
rububinsa ba matan ba, ba mazan ba .........".
Takare maganar tana murmushi had'e da kallon cikin idonsa.
"Alhaji muje ka zauna inaga zai fi dan karka fad'i dajin abinda zan shaida maka".
Ta fada tana kokarin tallabo habarsa, tana mai murmushi.
A kujerar daya tashi tasashi ya zauna tasa aka kawo masa lemu, gaba d'aya jikinsa yagama
sanyi, izuwa yanzu kam ya tabbatar dacewa ba aljana bace mutum ce saidai yana jinjina irin
k'arfin halin ta da tsaurin idon ta.
Cikin wani irin rikitacciyar murya tasoma magana saikace wata boss bayan ta bashi baya,
ma'ana ta juya, shikuwa bayan nata kawai yake kallon ko kiftawa ba yayi.
*"ALHAJI ABUBAKAR KASEEM SHATTIMA* kana magana ne da *AYSHA YUSUF GIDADO*
wacce ka hana d'anka Aliyu ya aureta, ka aibantata ka muzantata a idonsa kake kiranta da
karuwa y'ar iska lalatacciya! Bancin d'an iskan d'anka Aliyu shiya soma lalata rayuwar A'isha ya
maida ta tamkar matarsa ta sunna, yayiwa A'isha ciki yayi mata dukan mutuwa hartayi b'ari
wanda a sanadiyyar haka likita yace A'isha bazata iya haihuwa ba har ta mutu! Sannan har
zaka bud'i baki kace bazai auri A'isha ba dan mugunta da son zuciya irin taka wacce kasaba
!?".
Bari ingaya maka abinda baka saniba wallahi Aliyu bazai iya rayuwa babu A'isha ba tazame
masa k'arfen k'afa idan kuma Kanada ja kaje ka tambayi bokanka yagaya maka gaskiya daga
abinda yasan ya boye maka!".
"Wallahi ka kasance azzalumi mai son zuciya shiyasa ka aura masa natsatsiyar yarinya acewar
ka".
" To bari kaji nasaka kayi mata fyade da kanka ne saboda kaji irin bakincikin danaji a lokacin
dana samu labarin auran da kaiwa Aliyu dukda cewar kai abin kunya baya ka bashi!".
"Nasa kayi mata fyade ne saboda tafita a ran Aliyu idan ma har ta shiga kenan, inaso Aliyu ya
tsaneta tsana mafi muni saboda nasan kishi irin nasa!".
" ina so auran daka d'aura masu ya haramta ta sanadiyyar ka kaida ka d'aura shi da kanka!".
"Alhamdulillah buri na ya cika saura burina na k'arshe a duniya shine kasa Aliyu ya aure ni
sannan kuma inaso kayi duk yanda zakayi kasa Aliyu yasaketa tunda babu aure a tsakanin su
kuma batare da ya fahimci akwai saka hannu na a ciki ba".
"Idan kayi hakan to tabbas Aysha Yusuf zata rabu da kai tashafa maka lahiya, wallahi nayi
maka alkawarin cewa zan rike sirrinka babu maijin sa har abada indai daga bakinane"........
[9:40PM, 2/21/2018] Maman twins: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)*
*ZAMANI* 3⃣4⃣
*A TRUE LIFE STORY*
*WRITTEN BY*
*FIDDAUSI SODANGI*
*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*
*INA GWANAR WATA GA TAWA!*
*WANNAN SHAFIN NAWA DAMA DAI DA DUKKA LITTAFIN MA NAKI NE AI GWANATA!,
UWAR D'AKIN FIDO ABIN ALFARI TA A KODA YAUSHE HAKIKA SHEGE SHIKE MANTA
ALKAIRI HAKA KUMA D'AN HALAK SHIKE YAWAITA TUNAWA DA ALKAIRIN DA AKAI
MASA, INA YINKI SOSAI TAWA ALLAH DAI YAKARA TSARE MINKE TAWA MAKIYANKI
TAKALMIN KI......KIYI SHA'ANIN KI BAKOMI TAWA KIYI KOMI BA KOMI, ALLAH DAI YAKARA
BASEERA DA DAUKAKA TAWA MASOYIYAR SODANGI ALLAH YABAR SO DA KAUNA
TAWA.* *KHADIJA SIDI (SALMA ATIKU*
Zufa yashiga keto masa ko ta ina, cikin k'ankanin lokaci ya jik'e sharkaf da gumi.
Hular kansa ya cire yashiga fifita dashi, a zuciyar sa kuwa fad'i yake ana dara ga dare yayi,
wannna wace irin shu'umar yarinya ce haka?
Tabbas yarinyar nan ta wuce tunani na in banyi hankali ba watan tonuwan asiri nane yakama,
tabbas da kunyar duniya gara ta....... (Tirrr!!!)
"Haba d'iya ta haba! Ai ba a yi hakan ba, indai dan Aliyu ne karki damu bakida matsala kota
sisin kwabo ai ni bansan haka abin yake ba shiyasa ma nashiga wannan magana amman karki
damu ki saurare ni (indai da ranki da lahiyar ki tabbas saikin mallaki Aliyu nayi maki wannan
alk'awarin, indai da ranki zaki same shi, sai dai idan baki raye!)
Murmushi A'isha tayi tace "Alhajin Allah kenan, ai da izinin Allah A'isha bazata bar duniyar nan
ba sai burinta na mallakar Aliyu yacika, wanda k'wanan sa ya k'are shi zai bar duniya ta wannan
dalilin, sannan kuma da izinin Allah zanbaka mamaki!".
" A'isha kenan nayi maki alk'awarin cewa da izinin Allah zan bar maki babban tarihiyi a rayuwar
ki idan har kikai kuskuran tona asiri na bayan na mallaka maki Aliyu".
"A'isha Yusuf tanada amana tana cika alkawari saidai idan aka saba mata nata alk'awarin
tofa.....".
***************************
Aysha ce zaune bisa gadon Aliyu bayan sungama watsewar su yashiga wanka yabarta nan
k'wance tanata sak'e sak'e a zuciyar ta.
wayar Aliyu dake gefen gado ne yayi kara, bata kulaba dan ya mata kashedi akan kada ta
kuskura taringa taba masa waya, mamaki ma take ya akayi ya bar wayarsa ya shiga wanka,
Bata kula ba haka har akayi Kira Na biyar, ta tashi ta dauki wayar ta nufi hanyar bayi ganin an
sake Kira Kuma an rubuta *Ammi* yasa ta daga wayar dansu gaisa da surukar tata.
“Hello Hajiya Ina wuni”
Gaban Ammi ne ya fadi jin muryar wata mace daban ba Ramlat ba.
“Lafiya yau, Ina Aliyu yake ne”
“Eh yadan fita ne yanzu zai dawo Amma”
“Ok” sai ta kashe wayar.
Bata natsu ba sam ta kara Kira,
A'isha cikin ladabi ta kara daga wayar,
“Yarinya wacece ke?”
Murmushi A'isha tayi wato dai Ammi naji da Aliyu, Sai taji ko wacece,
“Hajiya nice fa.”
“Nice A'isha surukar ki ta gaba,”
“Ke wace A'isha ce Kuma, ”
” Hajiya nice fa Aysha Yusuf Gidado”
Gaban Hajiya ne ya fadi tuni idonta suka chanza,
Aliyu ne ya fito ya kalleta mika masa wayar tayi tana kokarin goge masa ruwan jikinsa da towel.
Dakatar da ita yayi hadi da daka mata wata irin tsawa,
“Uban wa ya Baki damar daukar min waya harda fadin ke ce A'isha danma rashin mutunci wai
surukar ta tagaba".
Wannan tsawar tayi sanadiyar murdewar cikin A'isha tsoro yakamata mema yakaita d'aukar
wayar sa ne ita kam.
Bai kashe wayar ba Kuma Ammin ta jiyo abinda yafada.
Wurgi yayi da wayar ya fara safa da marwa a dakin, idonsa sun kankance lokaci daya,
hannu yasa ya dafe kansa, "Tashi ki fice a gidan nan kafin in tattaka ki! Wawuya kawai
_stupid_!".
Murgud'a masa baki tayi tashiga saka kayanta a gaggauce bayan ta gama ta kallesa tace " ai
dai ba k'arya nayi ba, ba surukar tata ce insha Allahu!".
Duka yakai mata ta fice da sauri tana fad'in masifaffe kawai.
A Palo ta wuce Ramlat tana kallo tace "Amaryar mu natafi sai kuma gobe"
Tsaki Ramlat tace tare da fad'in "Banza sakara asararra kawai karuwa mara aji! Allah wallahi
kinyi arha dayawa a cikin karuwan ma ke mara aji ce wallahi mai kyawun d'an maciji a haka zaki
kare ai da bibiyar mazan mutane".
Murmushi A'isha tayi tace nagode Amaryar mu a haka mijinki ke bibiyata yake jin zai iya
mutuwa duk ranar da bai kusance niba, nazame masa tamkar bugun numfashin sa, baya iya
rayuwa batare da A'isha Yusuf ba, sai ki d'au hakuri tunda ke mata kika rako duniya, yanda kika
san namiji d'an uwansa haka yake kallon ki shiyasa har yau yakasa rike koda dan yatsan ki,
sam baki cikin y'an kayan sa dake da babu duk uwarsu d'aya uban su d'aya, dama ai wasu
matan sunan mata kawai garesu amman da k'aton gardi dasu sam babu maraba......"
Ganin Aliyu ya fito ne yanai mata wani mugun kallo ta fice abinta tana dariya.
Zuciyar Ramlat kuwa bakikkirin itakan wannan abin ya ishe ta dole ta d'auki mataki akan
iskancin nan da ake mata.
****************************
*K'ARFE BIYU DA RABI NADARE*
K'arar bindiga ce ta farkar dasu _uncle_ Safana gaba d'aya suka hallara a Palo cirko cirko
kowanne jikinsa inbanda k'yarma babu abinda yake, hankalinsu ya dugunzuma yatashi tuni
A'isha tasoma sakin fitsari daga tsaye tabbas ture ne wannna tasani tabbas akwai wani abu a
k'atsa wata zuciyar tata ce tace A'isha yanzu fa ba lokacin tunani bane nimi mafita ki tsira da
rayuwar ki ina haka ba zaki iya rasa ranki a yanzu basai wani lokaci ba, da gudu tanufi d'akin
tama rasa abinyi a daidai lokacin da akaiwa k'ofar palon wata kyakkyawar bugu sai gata a k'asa
ta fad'i Tim!!!!.
A'isha ta fashe da kuka cikin kid'ima ta fad'a kewaye kwandon kayan wanki tafad'a bayan ta ciro
kayan gaba daya tashiga ta maida ma kanta kayan ta jibga babu yanda za ai kace akwai mutum
aciki sai kayan wankin.
Su shida ne suka shigo kowanne fuskar sa lullube da safar fuska, jibga jibga ne tamkar autan
samudawa dan girma, tuni Anty Abeeda ta kankame mijin ta, tana sakin fitsari daga tsaye.
Ogansu ne cikin kakkausar murya yace "ba tashin hankali mukazo yiba, mai gadi ma mun
kashesa saboda taurin kansa ne",
A gigice suka zaro ido tamkar dasu fad'i k'asa, " eh kuma idan kuka ki bamu hadin kai yanzu
zaku ziyarce shi!".
Hoto yaciro ya nuna masu yana fad'in ina wannan yarinyar take ita aka aikomu mu kashe idan
kuma kunki bada hadin kai wallahi gaba d'ayan ku saikin bakunci lahira......
[6:27AM, 2/23/2018] Maman twins: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)*
*ZAMANI* 3⃣5⃣
*A TRUE LIFE STORY*
*WRITTEN BY*
*FIDDAUSI SODANGI*
*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*
Shuru sukai gaba d'ayan su babu mai alamar cewa komi, tsawa ogan ya buga masu da fad'in
bazaku gaya mana inda takeba?
Da hannu _Anty Abeeda_ tayi masu nuni da d'akin A'isha zuciyar ta na bugawa, kallon ta
_Uncle_ Safana keyi irin kallon _why_ d'in nan, k'asa k'asa tace "Safana ai gara a kashe
A'ishan da a kashemu baki d'aya".
Murmushi ogan barayin yayi kafin yayi ma yaran sa umurni da su zaga ko ina a cikin gidan su
fiddo masa da Aysha.
Cikin bin umurninsa suka raba kansu gaba d'aya, shikuwa ya tsaya a palon tsare dasu _uncle_
Safana da bindiga,
Sukuwa nan suka shiga bincike kowani lungu da sak'o na gidan saidai tsawon minti ashirin
basu gano taba kuma har cikin kewayan sun shiga amman babu Aysha babu alamar ta, nan
suka sake hallara a palon kowa yayi cirko cirko.
" To tunda munrasa Aysha to ku zaku zama madadin ta danni dai bazanyi zuwan banza ba dole
inji dad'i sannan kuma bindiga ta tayi aiki, zan sadu da matar ka sannan acikin yara nama duk
maiso ya d'ana sai yayi, daga k'arshe sai mu aika daku lahira kuje can kujira zuwan Ayshan
itama dan wallahi bantaba rashin sa'a a aiki naba, duk abinda nasawa gaba sainaga bayan sa,
saboda haka bisimillah Hajiya cire min kayan jikin ki, ki kwanta bisa Capet dinnan in lalle ki na
tsawon minti goma idan sh'awata ta motso sai inyi shagali na idan kuma baki burge niba sai
yara na su duba".
Kuka tashiga yi sosai tana rok'on su shikuwa _uncle_ Safana sai fad'i yake "A'a Abeeda A'a ba
a yi masu musu kiyi yanda sukace kawai idan Allah yayi da sauran kwanar mu a gaba sai kiga
sun barmu",
Jin hakan datayi ne yasata saurin cire kaya haka tayi zindir a gabansu ta kwanta bisa Capet din
kamar yanda ya umurceta, kiri kiri babu kunya babu tsoron Allah katon gardin nan ya
tumurmushe ta na tsawon lokaci mai yawa, sannan ya mike inbanda kuka babu abinda takeyi, a
haka gaba d'ayan su sukayi amfani da ita su shiddan izuwa lokacin kuwa tuni ta daina motsi
babu alamar numfashi a tare da ita.
_Uncle_ Safana yanaji yana gani suka sakar mata harsashi bisa kanta, cikin gigita ya fashe da
kuka mai ban tausayi gaba d'aya yagama firgicewa sai rokon su yakeyi dasu kyale shi karsu
kashe shi.
Takarda da biro ya mik'o masa yana fad'in " amshi ka rubuta wasiyya ga yan uwanka da abokan
arziki, ko kuma wani sako mai mahimmanci dakake so ka isar ma wani naka, karbi kana bata
mana lokaci Malan!".
Yadaka masa uban tsawa mai firgitar wa.
Jiki na rawa _uncle_ Safana ya karba yashiga rubutu cikin rawar jiki hawaye najika fefar, rubutu
mai tsawo yayi ya nad'e ya mika mashi, amsa yayi ya aje bisa tebur sannan yayi masu umurni
dasu tafi, saida suka fice gaba d'aya sannan yabisu a baya yana kaiwa k'ofa ya juyo ya sakar
masa harsashi a k'irjinsa yasa kai ya fice.
Mak'ocin su _uncle_ Safana daya kasa samun natsuwar yazauna a cikin gidan sa saboda gaba
dayan su a waje suke a tsakar gida circo circo, matan shi na fad'in karya fita suna rike shi
dayake kwanan sa sun kare haka yafita yana fad'in Allah zai tsare.
Yana fita dai dai bakin _gate_ d'in gidan _uncle_ Safana ya had'e dasu suka sakar masa
harsashi shima suka kara gaba abinsu.
Matan mutumin da sauran mak'ota suka fito nan da nan unguwar ya hargitse, kafin kace kwabo
y'an sanda suncike ko ina...........
[9:48PM, 2/23/2018] Maman twins: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*ZAMANI* 3⃣6⃣
*A TRUE LIFE STORY*
*WRITTEN BY*
*FIDDAUSI SODANGI*
*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*
*WANNAN SHAFIN NAWA NAKI NE MARYAM ZUBAIRU SODANGI TANA JINKI A ZUCIYAR
TA ALLAH YABAR KAUNA*
*YA ALLAH KA JIBANCI LAMURA NA KA YAYE MANI DAMUWATA KA KAWO MANI MAFITA A
CIKIN LAMMURA NA KA BIYA MANI BUKATOCINA NA ALKAIRI TARE DA DUKKANIN
MUSULMI AMEEN SUMMA AMEEN.*
Tunda Ammi ta cire wayar a kunnin ta tashiga safa da marwa, "watau har yanzu Aliyu bai rabu
da yarinyar nan ba kenan?".
" To waima a ina suke kenan shi da ita da har hakan ta kasance?".
Waje ta fita tashiga kwallawa sarkin gida kira, da gudu ya k'araso har k'asa ya zube yana
fad'in "ranki ya dad'e gani".
"inaso ka ciro mani camera dake sama na wajan gidan nan zanga abu ne".
"To Hajiya bari aciro dama Alhaji ya dad'e bai duba ba da duk sati yake gani amman kusan wata
d'aya ma kenan bai sa anciro ba ni ko mantawa yayi ne inaga".
"Duk sati fa kace?".
" eh Hajiya amman yadaina dubawa yanzu".
"Ok ciro mani".
A palon ta zauna tana jira yakawo mata, bai dauki lokaci ba yaahigo dauke dashi karba tayi tai
masa godiya, yana fita ta had'a tasoma gani, ma ai kata ne keta shiga da fita, ko wanne yana
hidimar gabansa, bata dade da fara kallon ba taga motoci biyu sunshigo sai ga Abban su Aliyu
ya fito ya tare su cikin murna, samari ne guda biyu masu kyau, sai wasu Alhazawa guda biyu
suma, kudi masu yawa Abban su Aliyu yaciro ya ba Alhazawan nan suka ja motocin su suka tafi
shikuma yanufi sashin baki dasu.
Kan Ammi ne ya d'aure sosai.
Haka abin yacigaba har zuwa safiya sai ga Alhazawan nan sundawo nan samarin nan suka fito
Abban su Aliyu nata shafa kansu yana murmushi, suka tafi
Haka yan aikin gidan keta hidima har dai zuwa ranan auran Aliyu.
Bayan ankai Amarya kowa ya watse can taga wucewar Abban su Aliyu ya nufi bangaran Aliyu
din, abin ya daure mata kai tare da bata tsoro, sai can bayan wasu awanni saigashi da saurin
sa ya fito tamkar zai kifa.
Tsaye Ammi ta mike zuciyar ta na bugawa, nan taga shigowar su Aliyu da fitowar shi dauke da
Ramlat a hannu shida Bello da fitar su a gidan.
Tashin hankali.
Cikin rawar jiki tasake kiran sarkin gida tace yaciro mata camerar dake palon, nan yaciro ya
bata tasake had'a shi, abu na farko shine can tsakar dare taga shigar Alhajin d'akin da tun
tsawon zaman su a Abuja baitaba yarda wani mahaluki ya rabe shiba a cewar sa akwai
abubuwan sa masu mahimmanci a ciki. Cikin wasu jajayen kaya yashiga tsawon awa daya sannan taga fitowar shi ya cire kayan yafito
dawasu daban.
Da gudu Ammi ciki fitar haiyaci ta nufi d'akin cikin hukuncin Allah tana murd'a k'ofar ya
bude.............
*Kuyi hakuri da wannan wlh ina cikin damuwa banida natsuwa haka nan dai nake rubutun nan
dan kar inbarku kuyita jira, ina barar addu'ar ka allah yakawo mani mafita acikin lamari na.*
[9:51PM, 2/27/2018] Maman twins: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*ZAMANI*3⃣7⃣
*A TRUE LIFE STORY*
*WRITTEN BY*
*FIDDAUSI SODANGI*
*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*
Kutsa kai tayi cikin d'akin cak ta tsaya tana k'arewa d'akin kallo zuciyar ta tamkar zata fasa
k'irjin ta tafito dan bala'in bugawar datake, a hankali tashiga k'arewa komi na d'akin kallo d'aya
bayan d'aya, idonta ya sauka bisa k'waryar dake tsakiyar d'akin cike da wani jajawur d'in ruwa
wanda bayada banbanci da jini, koma