Showing 6001 words to 9000 words out of 56306 words

Chapter 3 - ZAMANI (1 to end) Book Complete by Fiddausi Sodangi .pdf

03 Oct 2025

1701

_gate_ d'in
gida a wannan yanayin dayake k'ok'arin cinma burinsa.
Har zuwa wannan lokacin ba a bar bugun _gate_ d'inba, a fusace yabud'e yana fad'in "wai
wani d'an iskane zai balle min........",
Maganar tasa ce ta k'arasa mak'alewa a labban sa saboda ido hud'u dasukai da abokin sa
kuma aminin sa, bakowa bane illah *ALIYU KASEEM SHATTIMA* cikin tsananin murna ya
rungumosa yana fad'in amman kaifa d'an iskane wannan wani irin shammata ne haka kojiya fa
munyi waya amman baka sanar dani yaune zaka shigo ba shegen kaya!". Hankad'esa Aliyu yayi ya k'utsa kai cikin gidan, da sauri Bello yarufa masa baya yana fad'in "
A'a kujini da d'an iskan mutum fa ya ture ni zai shige min gida kanshi tsaye.
Dai dai lokacin ne A'isha ta fito daga d'akin tana gyara mayafin kanta, ido hud'u sukai da Aliyu
a take gaban ta yayi wani irin mummunar fad'uwa, kallonta yake tundaga sama har k'asa ita
kuwa cikin rawar baki tace "Aliyu......!".
Wani mugun kallo ya watsa mata tare da jan wani dogon tsaki ya raba ta gefen ta yashige
cikin d'akin abinsa,
Cak ya tsaya a tsakiyar d'akin yana k'arewa gadon kallo wanda gaba d'aya an cukurkud'a shi
zanin gadon ya tattare gu d'aya _pillow_ kowanne yakama gabansa, ga robar _ice cream_ nan
wanda yake kife bisa gadon cikin wani irin bak'in ciki yajuyo zai fice nan yaji k'afarsa yatako
abu, idonsa yakai wajan _pant_ d'in A'isha ne yashe a wajan ya taka batare da sanin saba
wanda tsananin sauri da tashin hankali da tsoron da Bello yabata ta mance bata saba ta fice a
haka, da sauri ya d'auke k'afarsa kamar wanda ya taka garwashin wuta.
Zuciyar sace yaji tanai masa wani mugun zafi da sauri yasa hannunsa na dama yadafe saitin
zuciyar sa yanufi palon gidan ya zauna a d'aya daga cikin kujerun ya dafe kansa da k'arfi, sam
baisan meyasa yashiga cikin wannan yanayin ba, shidai yasan wannan shine karo na farko
dasuka soma had'uwa, idan bai manta ba wata uku dasuka wuce suntaba had'ewa a
_Instagram_ harma suka gaisa yasa ta taturo masa hoton ta shima yatura mata sukai musayar
_number_ ta shaida masa tana karatu a katsina amman ita y'ar yola ce, shima yagaya mata
yana aiki a Lagos shi custom ne, to bayan sunyi kwana biyu suna gaisawa ne yake tambayar ta
aji nawa take ne tace masa 2 nan yaji ya sare dan shi sam baya son hurd'a da yara k'anana yafi
son manyan y'anmata kamar way'anda suka k'are jami'a ko suke aiki to shi datace tana karatu a
katsina yayi zaton shekarar k'arshe take haka ashe shekara na biyu kenan take, sai ya tambaye
ta to shekarar ta nawa ne?
Nan fa tace masa 21 ashirin da d'aya tofa tundaga ranan ne baisake kulata ba kotayi masa
magana baya amsata hardai ta gaji itama ta daina, tofa shine sai yau suka had'e ido da ido

kuma yasame ta a gidan abokin sa a wannan yanayin.

Ajiyar zuciya ya sauke da k'arfi ya runtse idon sa way'anda suka kad'a sukai jawur dasu
tamkar jan gauta.
Bello ne yashigo yana fad'in "Sakarar yarinya ita kullum ba a rabuwar arziki da ita nida zan tafi
gobe ita da tasake ganina sai wani ikon Allah amman shine wai zata bari muyi irin wannan
rabuwar kodayake Haydar duk kai kaja min wannan abin d'an iska kawai kamin asarar jin
dad'i......" Wani irin mugun kallo Aliyu ya d'ago yanai masa da jajayan idanuwansa.........



_Mafi hankalin mutun shine wanda ya bar duniya tun kafin ta bar shi, kuma ya gyara kabarinsa
tun kafin ya shiga cikinsa; kuma yaji tsoron ubangijinsa tun kafin ya hadu da shi; kuma yayi
sallah a cikin jama'a tun kafin su sallace shi; Sannan kuma ya yi wa kansa hisabi tun kafin ayi
masa, domin yau ranar aiki ce, ba hisabi, gobe kuwa Hisabi ne ba aiki ba. Allah Ya sa mu dace_ _BARKA DA SAFIYA_
[6:24PM, 1/28/2018] Maman twins: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)*


*ZAMANI* 1⃣1⃣


*A TRUE LIFE STORY*


*WRITTEN BY*

*FIDDAUSI SODANGI*


*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*
*KHADIJA SIDI*



*WANNAN SHAFIN NAWA SADAUKAR WACE GAREKI FULANI HAFSATU KINFI KOWA SON
WANNAN LITTAFI NA ZAMANI ALLAH YA BAR KAUNA*

Wani irin mugun kallo Aliyu ya d'ago yanai masa da jajayan idanuwansa dasuka koma abun
tsoro, "meye ne zaka wani tsareni da mayun idanuwanka, kaidai wallahi kashiga uku da jaraba,
nasan duk ganin A'isha ne ya gigitaka, kai mayan mata, shege na mamajon banza jarababbe, to
wallahi wannan yarinyar nan gani nan bari sai kallo da hange daga nesa, duk jarabar ka saidai
ka shafa mata lahiya".

Nan fa ran Aliyu yak'ara baci watau Bello na nufin tashi ce shi d'aya shiyasa yake gaya masa
haka, lallai yarinyar nan ta shammace shi.

*******************

"A'isha meyasa bakiso Isa direba yana kaiki makaranta saidai ki ringa hawa mashin ko napep
iye!?",
"Inaji fa _last week_ Antyn ki tana maki fad'a ba harcewa tayi ki ringa amfani da nata motar ba,
meyasa kikeso kizama mara jin magana ne uhm?".
" _Uncle_......".
"Shiiiii! Banason jin komi daga gareki, daga yau bana son in k'ara ganin ki bisa mashin idan ba
haka ba kuwa zaki had'u da bacin rai na kinji nagaya maki!".
Tsareta da idanuwan sa yayi bayan matar sa ta bar wajan, so yake ta d'ago kai amman taki,
murya k'asa k'asa yace " Jeki ki shirya zamu kasuwa".
Dara daran idanuwanta ta d'ago ta tube sa batare data ce komi ba ta mik'e ta nufi d'akin ta,
itakam takura ta kawai za a yi ace ta bar hawa mashin ko napep ita da ta hakan ne take
morewa ranta to itakam sai dai ta ringa amfani da motar Antyn amman bazata yarda Isah yana
kaita ba gaskiya duk dama yanzu Bello baya garin bata da abokin holewa sai _Uncle_ d'in nata
idan yasamu ya saci hanya.

"Abeeda ki shirya muje kasuwa Kinga yau _Sunday_ musamu musiyo kayan abincin nan
Talatu tace sunyi k'asa sosai gara muje yau kawai".
"Kayi hakuri _dear_ kuje tare da A'isha wallahi bacci nakeso inyi yanzu".
" Bacci da yamma d'innan kalli agogo fa k'arfe biyar?".
"Dear Allah bazan iya zuwa ba kayi hakuri kawai kuje kaida A'isha d'in _next time_ munje tare
d'in kaji nawan, haba miji na meye aciki ai abinda zan iya yi shi A'isha ma zata yi duk d'aya ne
kace mata tashiga _store_ d'in ta duba abinda duk babu saitayi _list_ kutafi kawai, Allah
yakiyaye hanya mijina sai kun dawo". Ficewa daga d'akin yayi batare daya k'ara ce mata komi ba dama shi hakan yake so ma yariga
yasan hakan ce dama zata faru ba zuwa zatai ba.

 A'isha sanye cikin riga da siket na atamfa wacce tayi masifar matseta ta fiddo da duk wata siffa
tata abin ba a cewa komi, wani d'an yololon mayafi ta yafa a haka suka fito ita da _Uncle_ suka
shiga mota kai tsaye *DADIN KOWA SUPER MARKET* sukaiwa tsinke, inda _Uncle_ yayi mata
umurnin ta zabi dukwani abu datake so a ciki kafin sutafi kasuwar aifa nan ta shiga jidar kaya
babu ji babu gani, dama ita gwana ce wajan shan kayan zak'i .

_Uncle_ ma yana daga gefe yana zabar abinda yakeso. Charaf idonsa suka fada akan Hafsa,
wata yarinyar sace dasuke holewa tare a da lokutan baya, sanin halinta yasa yayi kokarin
boyewa, amma ina, kamin ya kauce tuni ta hangoshi, iya karfinta ta kwala masa kira
*“SAFANA.!!!”* Da gudunta taje ta rungumeshi, tsoro hadi da razani ya kamashi, Hafsa dai
tsohuwar budurwar sa ce da tayi _Diploma_ a nan katsina _polytechnic_ yar Kaduna ce dama
karatun ne yakawo ta katsina har suka hade ita da shi, daga nan ta wuce _Cyprus_ karatu, tun
daga lokacin basu kara haduwa ba sai yau,  sun gurji duniya ita dashi, Hafsa irin yan matan nan
ne da basuda kunya bare tsoron Allah, ko gaban mahaifinta zata iya rungumar namiji, saboda
bata dauki haka a bakin komai ba illa wayewa, 

   Da sauri yayi kokarin banbareta jikinsa kada A'isha ta gani, amma ina har A'isha ta hangosu,
bata sakeshi ba saida ta sunbaci kumatunsa,  duk a idon A'isha,

ta sakesa ta dafa kafadarsa tana dariya,

    *“SAFANA* kalli yanda ka zama babban mutum,” ta kallesa daga sama har kasa tana
murmushi," 

  “Hmmm naga bakayi murna da ganana ba _at all.”_ 

Ta fada tana lumshe idonta, A'isha ce tayo kansu gadan gadan, da yake ya bata baya so bazai
iya hango A'isha tana tahowa ba, Hafsa ce kawai ta ganta, Hannun sa ta janyo 

  “Dallah muje waje *SAFANA* m miss u much, what of  u?” 

  Ta fada tana janyo hannunsa suka bar layin kamin A'isha ta kawo har sun bar gun, haukace ne
kawai A'isha batayi ba, kamar zararra haka ta biyosu tana wani wawan sauri.

   Hafsa kuwa haka taya kokarin janyoshi suka fita ta sami gu suka zauna cikin fari da ido tace

   “Oya kana mamakin ganina ko shiyasa ko magana ka kasayi tin dazu?"

A hankali ta tashi tsaye ta janyo kumatunsa da hannuwanta ta turo baki alamar tana masa kiss.

  Daidai lokacin A'isha ta kawo zuciyarta tana tafarfasa, bata tsaya bata lokaci ba

 Ta wanke Hafsa da wani bahagon mari.

   Hafsa dagyar ta iya bude idonta sabida saida taga taurari da aka mareta din nan.
A hankali idonta suka bude A'isha ta gani gabanta tana huci tana nunata da yatsa, sam bataji
abinda A'ishan ta fadaba, amma lokacinda ta dawo hayyacinta ta fuskanci cewa magana takeyi,
 saida hafsa ta saita natsuwarta, sannan ta daga kai ta kalli A'isha ta kalli *SAFANA*da yayi
wata uwar zabura ganin A'isha ta mari Hafsa 

*“SAFANA* wacece wannan??” 

Abinda Hafsa ta iya tambaya kenan sabida taga wani abu daya daure mata kai tare da A'ishan.

  Bai bata amsa ba sai wani turus da yayi, cikin daga murya ta sake tambayar sa, daidai nan
A'isha tayi tsaki ta kama hannun sa zasu bar gurin Hafsa da karfi itama ta kamo hannunsa ta
rike, A'isha ta rike Hafsa ma ta rike, suka sakashi a tsakiya, 

Hafsa ce ta maimata tambayar ta 

*”SAFANA* _who is she?” _

 Ta tsareshi da ido, ya kasa bata amsa Hafsa kam ko rashin kunya tasan da zaman ta, A'isha ita
take barikin yaran zamani amman ita kam barikin ta na gogaggune wayanda sukaga jiya
sukaga yau.

  Tana rike da hannun sa ta zagayo gaban A'isha  ta kalleta daga sama har kasa, abu daya ne
data hango a idon A'isha wato kishi karara shi zaisa ta aikata abinda take da niyyar aikatawa.

  ” bansan koke wacece ba, amma ki sani Nice budurwar *SAFANA* da zai k'ara aura kuma ko
kinki ko kinso sai munyi aure sabida soyayyar mu hadice daga Allah, ”

  Ta kamo fuskar _Uncle_ iya karfinta dan kada yayi kokarin kwace kansa tamasa  kiss sosai
sannan ta sakesa, ta waigo ta daddage iya karfinta ta wanke A'isha da mari, 

Jikin _Uncle_ ne ya fara rawa ya daga hannu iya karfinsa zai mari Hafsa amma A'isha ta rikesa
iya karfinta 

  _“Dont do it,_ budurwarka ce fa.” 

Sai wani huci yakeyi har cikin zuciyarsa yakejin marin da aka yiwa A'ishan. Hafsa kam
wucewarta tayi cikin taku na isa. 

   A hankali A'isha ta sake masa hannu tana kokarin barin gurin, rike mata hannu yayi amma ya
kasa magana.

    Wani kallo A'isha ta watso masa baisan lokacinda ya sake mata hannu ba, sayayyar da
ba’ayi ba kenan.

  Mota ta fada ta fara sharara gudu bata nufi gida ba, bata ma san ina zataje ba, saida ta fara
fita cikin gari ta kama hanyar Dutsanma sannan taja gefe ta tsaya.
Duk wannan abinda yake faruwa a idon Aliyu ne wanda shima yakaiwa *DADIN KOWA* ziyara

domin yasai kayan amfanin sa nayau da kullum, anan ya tarar da harkallar dake faruwa a
tsakanin Hafsat da A'isha da kuma _Uncle_ wanda a k'arshe A'ishan tayo nan shima yashiga
mota ya biyo ta ganin dama tasamu.........
 
[12:42PM, 1/29/2018] Maman twins: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)*


*ZAMANI* 1⃣2⃣


*A TRUE LIFE STORY*


*WRITTEN BY*

*FIDDAUSI SODANGI*


*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*
*KHADIJA SIDI*



*WANNAN SHAFIN NAWA SADAUKAR WACE GARE KU GABA DAYA MEMBERS NA
GROUP DINA NA MATAN KWARAI INA ALFAHARI DAKU GABA DAYAN KU MUSAMMAN*

*REAL AMANI*
*A'ISHA (JJ)*
*SUPY*
*MAMAN RABI'A*
*ZEE IBRAHIM*
*NANA FA'AD*
*SHAMSIYYA LAWAL*
*MARYAM SARKI*
*UMMU SAFWAN*
*MAMAN NASIBA*
*AYSHA BICHI*
*MEENAT M SOBA*
*BEE BEE*
*FA'IZA HUSSEN*
*AMEENA ALKALI*
*FATYMA JAWI*

*RAFI'A*
*SALSABILA*
*SMALL UMMI A'ISHA*
*MAMAN HAISAM*
*MAMAN JUHAINA*
*SWEET KHARDY*
*MAMAN MOHA*
*RAMATU HALIDU*
*MEENAT*



  Wani sanyi ya taso mata, wanda yake had'e da tashin zuciya da sauri ta bude murfin motar
kawai ta fara kwarara amai, kamar hanjin cikinta zasu fito waje, har saida ta galabaita ya zama
bata iya komai anan gurin, takai minti goma a gurin  dak'yar ta samu ta daddafa ta shiga mota
sai dai ta kasa tuka motar, tayi kokari ta kashe AC ko ta sami sassauci, tayi baya ta ijiye kanta
wani dogon ajiyar zuciya tayi wanda ke nuna tsananin damuwa da bakin ciki tattare da ita,
shikuwa Aliyu duk wannan abinda takeyi yana kallon ta a take tunaninsa ya canza akan ta bazai
iya aiwatar da abinda yayi niyya da farko ba akanta, ganin bata da lahiya yabarta sai wani karon
kuma in sunada rai da lahiya, a wani bangare na zuciyar sa kuwa yana mai jinjina irin bakin
kishinta wanda ya haddasa mata shiga wannan mugun yanayin.

  _Uncle_ kuwa daga gurin kasa motsi yayi, sai tunani yakeyi wace kaddara ce ta hadashi da
Hafsa a wannan lokacin? 

Yarinyar rabonsa da ita anfi shekara 4 amma yanzu lokaci daya tazo zata bata masa duk wani
_plan_ nasa, 

Har ga Allah baya son bacin ran A'isha, sannan bayason abinda zai taba masa ita ko kadan. 

Jiki a mace ya sami napep ya saukeshi gida, abin mamaki koda yaje bata nan, ya tambayi mai
gadi ya shaida masa batazoba, nan hankalin sa yayi k'ololuwa wajan tashi, a haka ya lallaba ya
wuce masallaci domin yin sallar magrib, koda aka idar da sauri ya shigo gidan dan ganin ko ta
dawo amman shuru bata ba labarin ta, gashi yau Talatu ta tafi garin su balle ya tambaye ta,
haka dai yashiga gun matar sa zaune take bisa darduma da alamar yanzu ta idar da sallah,
"Abeeda haryanzu yarinyar nan batashigo ba?"

"A'a batare kuka fita ba?"
Kanshi ya d'an sosa yace "Eh tare muka fita amman ai bamu samu munje kasuwar ba motar
tayi mana faci, ansamu an gyara kuma nace mudawo gida kawai yamma tayi, sai tace dan Allah
tanaso zata gidan kawarta ta karbo wasu _handouts_ ni bani iya binta nace kawai ta tafi ni bari
indawo gida, to kinga yanzu kusan minti na talatin da dawowa amman haryanzu bata dawo ba
kuma nagaya mata kar ta dade ni bansan meyasa A'isha batajin magana ba yanzu".

" To _dear_ ai bawani dad'ewa tayi ba nasan tana hanya nidai dan Allah idan ta dawo ta had'a
maka _tea_ d'inka ni isha'i nake jira yayi danayi salla bacci zanyi gobe akwai aiki kasani".
Ajiyar zuciya kawai yayi yafice daga d'akin.

yayi kusan awa d'aya yana lek'e lek'e ko zata shigo shiru bata dawo ba har kusan awa biyu bata
ba labarin ta, 

 Ya gama rudewa, ina ta tafi? 

Abinda yake tunani kenan, wayoyinta sam bata d'agawa har ya gaji ya daina kira, ya kasa ci, ya
kasa sha, sai safa da marwa yakeyi a palon, k'arshe sai yadan kishingida bayan yayi sallar
isha'i da yake ya gaji sannan ga damuwa ta mishi yawa,  nan danan bacci yayi awon gaba
dashi.
  A'isha ta kare amaye amayen ta, ta sami dan sassaucin abinda takeji ta tuk’o mota tayo gida,
Aliyu ma sai a lokacin yatafi,
Maigadi ta tambaya ko _uncle_ yadawo nan ya shaida mata nimanta ma dayakeyi,
wani k'ololon bakin ciki ne ya turnuketa da ta tuna yanda Hafsa ta rika tsutsar bakinsa, rufe ido
tayi amma ina! Saida ta sake wani amai nan gefen flowers kamin ta shiga palon a daddafe ta
shigo palon, kina ganin ta zaki tabbatar da tasha wuya sabida gaba daya ta fita hayyacinta,
hatta idanuwanta da suke dara dara duk sun shige ciki.
  Kwance ta ganshi yana sharar bacci abinsa, bata iya karanto damuwa a cikin fuskarsa ba ji
tayi kamar ta rufeshi da duka, cikin sassarfa ta wuceshi dakinta ta nufa, kamar an tsikareshi ya
tashi daga baccin da yakeyi.

   “A'isha kin dawo?" 

Kamar an mata Allura ta tsaya chak, ta kasa waiwayowa kuma ta kasa tafiya, 

  Tafiyanshi taji bayan ta wanda ya tabbatar mata da cewa yana son karasowa gurin tane, wani
haushinsa taji wanda ya saka mata _energy_ tuni ta wuce daki cikin kuzari kamar ba itace ta
sharari amai dazuba.

 Baiyi kasa a guiwa ba ya biyo bayanta saidai kamin ya kawo ta datse kofar da key ta shige
d'akin.

  Samun kanta tayi da rusa wani matsananchin kuka.

 Ita kuwa ya akayi ta bari son wannan mutumin har ya mata wannan mummunam kamu haka ??
tabbas idan tayi wasa zai illata rayuwarta sabida ya riga ya chafko zuciyarta.
Kuma ita kanta tasani ko giyar wake tasha bazata tana auran abokin babantaba.

  Kuka take kamar ranta zai fita.

Yana tsaye

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login