Showing 18001 words to 21000 words out of 56306 words
Chapter 7 - ZAMANI (1 to end) Book Complete by Fiddausi Sodangi .pdf
a jikinta cikin k'arfin
hali tadawo ta kwanta wani baccin yakuma d'auketa.
ko da ta farka da asuba mis calls d'in Aliyu biyar ta gani, sai taji bata ji dadi ba, taji kamar ta
kirasa a lokacin amma tace bari dai tayi sallah tukun.
Da k'yar ta k'arasa saboda yanda cikinta ke wani irin ciwo ga bakin ta bala'in d'aci tamkar tasha
mad'aci gaba d'aya tarasa meke mata dadi a duniyar nan............
[5:34PM, 2/9/2018] Maman twinsí ½í²: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)*
*ZAMANI* 2⃣2⃣
*A TRUE LIFE STORY*
*WRITTEN BY*
*FIDDAUSI SODANGI*
*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*
*KHADIJA SIDI*
*ALLAHU AKHBAR TODAY IS 09_02_2018 EXACTLY SEVEN YEARS TO THE DEMISE OF
OUR CARING MOTHER, WE LOVES YOU BUT ALLAH LOVES YOU MORE THAN US, MAY
JANNATUL FIRDAUS BE YOUR FINAL ABODE LUVLY MUM,YOU ARE THE ONE WE COPY
FROM,YOU ARE INDEED A GREAT MOTHER,OUR ROLE MODEL,WE COPY FROM
YOU,THANKS FOR BEING A GOOD MOTHER TO US, ANA A HABBUKI KASEERAN YAA
NOURO HAYATEE,ANTA HABEEBEE DAA'EMAN.*
*YAA RABBI IGHFIR WAR HAM LI ABEE KAMA RABBAYAANEE SAGEERAA ALLAH KA
JIKANTA DA RAHAMARKA ALLAH KA YAFE MATA DUKAN KURA KURENTA, ALLAH KASA
JANNATUL FIRDAUS CE MAKOMARTA, ALLAH KAI KACE A ROK'EKA ALLAH NA ROK'EKA
KA YAFEWA UMMATA ALLAH KA BATA MAKOMA ME KYAU.*
*KIN TAFI A LOKACIN DA BAMU TSAMMANIN MUTUWAR KI, BUT ALLAH DAYA KARBEKI A
LOKACIN YA FIMU SANIN DALILIN SA, KUMA YA FIMU SONKI, SHIYASA YA KARBEKI A
LOKACIN DA YASO, KO NACE BAZANYI KUKA BA KARYA NAKE, DON BANA DA KARFIN
ZUCIYAN RASHIN YIN KUKAN, A YAU NAJI MUTUWAN TA DAWO MIN SABUWA, WASU
MEMORIES MASU WUYAN GOGEWA A BRAIN D'INA ARE STILL THERE, THOSE ARE
PRECIOUS ND UNFORGETTABLE MEMORIES, RAYUWA KENAN IDAN MUNE YAU BAMU
BANE GOBE,*_*ALLAH UBANGIJI YA JIKANKI DA RAHAMARSA HAJIYA MARYAMA
ALKALI YA YAFEMAKI DUKAN KUSKURENKI*
*MU KUMA IDAN TAMU TAZO ALLAH YASA MU CIKA DA IMANI, EVEN THOUGH BAKYA
RAYE BUT KINA A ZUKATANMU STILL KUMA MUNAYIMAKI ADDU'A, FRIENDS, FAMILIES
ND WELL WISHER'S KOWA YA SAMU WANNAN MESSAGE NAWA INA ROKAN ALFARMA
GUNSA DA YAWA MAHAIFANA ADDU'A YA NEMA MASU GAFARA GURIN UBANGIJI YA SA
WA IN NAN SHEKARUN SUN YISU NE A CIKIN KWANCIYAR HANKALI DA NATSUWA DA
NI'IMA A CIKIN KABARINSU, ALLAH YA JIKAN DUKAN MUSULMIN DA SUKA RIGAMU
GIDAN GASKIYA AMEEN.*
*FIDDAUSI MUHAMMAD SODANGI*
"Aliyu zaman ka haka ne ya ishe ni nayi maka magana fiye da sau goma amman har yau babu
wani magana mai dad'i saidai kullum kace abaka lokaci abaka lokaci har yau lokacin naka baiyi
ba kullum cikin niman k'arin lokaci kakeyi, wannan dalilin yasa naje na nimo maka auren d'iyar
aminina Alhaji Muhammad Kabir daula, yabaka auran d'iyar sa Ramla".
"To da yace nan da wata uku sai ayi bikin amman nace masa a'a gara a had'a ta da yarta
Maryama daza a d'aurawa aure ranan asabar mai zuwa insha Allahu, sai a had'a danaku gaba
d'aya ina fatan kana saurare na naga ka tsareni da ido ne!".
Aliyu dayayi mutuwar zaune komi nasa ya tsaya cak na wucan gadi illah ido daya tsurawa
Abban nasa yana kallo babu ko kiftawa.
Tsawon lokaci sannan yadawo haiyyacin sa jin Ammin sa na fad'in " Aliyu bada kai ake
magana bane kobaka jine?"
Ajiyar zuciya mai k'arfi ya sauke cikin rawar murya yasoma magana "Abba nasamu yarinyar
danakeso zan aura harma mungama magana da ita sunan ta A'isha y'ar asalin yola ce saidai
tana karatu ne a jami'ar Umaru Musa dake katsina, iyayan ta suna can Yola d'in sai dai ita tana
zama da kawun tane anan katsina d'in Abba dama inaso indawo ne sai inyi maku maganar
ta.........."
"Wallahi tallahi Aliyu baka isa ba!".
" baka isa ka maidani mutumin banza magana nariga nagama magana ranan asabar za a
d'aura auran ka da Ramla tashi kabani waje!".
Yafad'i a fusace tamkar zaikai masa duka.
Cikin wani irin yanayi ya mik'e yana layi tamkar wanda yayi shaye shaye ya bugu, sam
baiganin gaban sa sosai tafiya kawai yakeyi.
Bayan ya fita ne Ammin sa ta dubi mijin ta tace "Kodai yarinyar dakake gaya min ne?"
"Itace kuma da raina da lahiyata bazan taba bari d'ana ya auri karuwa ba, gaba d'aya binciken
danayi akan yarinya abinda ya nuna kenan ko jiya sai da Dr Muktar ya kira ni yak'ara jaddada
mani wacece ita yarinyar, dan haka ko bayan raina ban yafe masa ba idan ya aure ta".
*****************
Â
A fusace Aliyu ya fice daga gidan hotel ya nufa ya kama d'aki yasa key ya bude k'ofar ya
shiga, kai tsaye wajan firij ya nufa gorar ruwan swan ya dauko irin babban nan, budewa yayi
yakafa kansa yaringa kwankwada bashi ya ajeba saida yaga ya shanye shi tas! Sannan ya
hakura ya fada bisa kujera yana maida numfashi tamkar wanda yayi tsere,
Yafi minti goma ahaka kafin ya mike zuwa kewaye yayi wanka yayi yaji sanyi kafin yasaka
kayan baccin sa, wasu magunguna ya balle ya hadiya tare da korawa da ruwa sannan ya zauna
kamar minti goma bacci mai nauyi yayi awon gaba dashi.
****************
*BAYAN K'WANA BIYU*
" Hello Aliyu na ".
" uhm A'isha yakike?"
"Lahiya kalau Aliyu yanaji muryar ka kamar bakada lahiya meyasameka?"
"Babu komi Aisha gobe zandawo insha Allahu ya jikin naki kinje asibitin kuwa?"
"Aliyu banje ba saboda naji sauki amman idan ka dawo sai muje d'in".
" Aisha kinfiya taurin kai wallahi!".
"Meyasa kike mani wasa da lahiyar kine wai?"
"Aliyu bahaka bane naji sauki ne sosai shiyasa".
" Toshikenan mekikeyi ne yanzu?"
"babu komi Aliyu yau su _uncle_ sukai tafiya antura su Lagos daga wajan aikin su shida Anty
kuma sati d'aya zasuyi dan haka Aliyu zankoma gidan ka tunda gobe zaka dawo insun dawo sai
indawo nima nagayawa _uncle_ zan koma makaranta in ringa kwana tare da kawata".
" OK to kiyi amfani da mukullin hannun ki kibude gidan in kinje sai na dawo".
"OK bye amman dai wallahi kamar akwai abinda ke damunka Aliyu".
Murmushi kawai yayi mata yace " babu komi"
yakashe wayar sa.
*******************
*WASHEGARI DA SAFE*
"Aliyu kaji nagaya maka babu kai babu yarinyar nan, yarinyar nan karuwace kowa ya shaida
hakan batada kamun kai Allah kadai yasan ko maza nawa yarinyar nan take bi!".
A firgice Aliyu ke duban mahaifin sa yana mamakin ynda akai yasan haka akan A'isha, " shin da
gaske ne A'ishan sa tana bin wasu maza bandashi ko ya abin yake".
Zuciyar sa inbanda bugawa babu abinda takeyi.
"Aliyu bari ingaya maka abinda baka sani ba shi abokin baban nata datake zaune a gidan sa
shi kansa saurayin tane tare suke nabaka dama kaje kayi bincike kadawo ka shaida mani
abinda binciken ka yabaka!".
" Tashi katafi Allah ya taimaka yabada sa'a".
*******************
"OK bazaki gaya mani ba kenan sai kinga abinda zanyi?"
Yafad'i yana k'okarin zare belt din jikinsa, a tsorace Aisha tashiga matsawa tana fad'in "Aliyu
wai meye haka ne Yaya daga dawowar ka zaka hauni da matsifa kanai mani ihu haka da tsohon
daran nan wannan wani irin tambayace haka haba Aliyu mezai had'ani da _uncle_ Abokin
babana nefa saboda Allah yakake irin haka ne?".
Gadan gadan yayi kanta yashiga dukanta babu ji babu gani yana fad'in " bazaki gaya min
meke tsakanin kuba?"
"Nizaki ringa cuta kina ha'inta?"
"Ni zaki ciwa amana A'isha?"
"Wayyo Allah na Aliyu ka tsaya kaji dan Allah wayyo baba na nashiga uku zai kashe ni".
Kam kam tarike belt din nan yasakar mata yaci gaba da bugun ta da hannu da k'afa kamar zai
kashe ta da rarrafe tasamu ta fad'a d'akin sa ta rufo k'ofar da key.
Bugawa yashiga yi yana girgiza k'ofar tamkar zai ballata, daga k'arshe ya hakura ya koma ya
zauna a data daga cikin kujerun palon sai huci yakeyi yana hada zufa dan bala'i duk da sanyin
da ake zuk'awa, yafi minti talatin ahaka daga k'arshe yaciro wayar sa ya hau lallatsawa.
Daga karshe ya kashe ta yanufi d'aya d'akin nasa nan yayi wanka daga shi sai tawul yanufi
palo yaciro wasu magunguna nasa ya balle guda shida ya watsa a bakin sa ya kora da ruwa,
Nan yashiga niman sauran makullan gidan da k'yar yasamu na dayan dakin da Aisha ke ciki
sannan ya maida sauran ya aje.
Kai tsaye d'akin da Aisha ke ciki ya nufa yasa key ya bude, ‘kwance take bisa makeken
gadonsa tana bacci wanda kallo d'aya zakai mata ka tabbatar baccin wuya takeyi duk ta takure
waje d'aya kamar mage.
wata yar guntuwar rigar bacci ce a jikinta gaba daya ya tattare yayi sama, “kyakkyawan fuskar
ta ya tsurama ido na tsawon lokaci kafin ya kashe wutar d’akin, gadon ya haye tare da jawota
jikinsa yafara shasshafata cikin sauri sauri, †a tsorace ta farka tana zare ido, cikin rawar murya
tace "Aliyu dan Allah kayi hakuri ka yafe min bazan karaba _please_ dan Allah!". "Shiiiii!!!!".
Ya dora dan yatsan sa bisa bakinsa,alamar taimasa shuru! †cigaba da shafata yayi yanawani
shinshinarta tamkar wata mage, jin yana kokarin rabata da rigar ta yasa tai saurin rike masa
hannu tana kuka, "Aliyu wallahi na gaji kaga fa yanda ka farfasa mani jiki".
' dan Allah kayi hakuri wallahi natuba bazan kara ba….bakin sa yakai cikin nata yanai mata
wani irin salo, “da karfi ta fisge kanta tana kuka tana fadin "nace kayi hakuri nace kayi hakuri".
" Bazan hakura ba sai kin gaya min meye tsakanin ki da tsohon can!?".
"Ke nake sauraro!".
Kuka kawai takeyi sam takasa magana, daga k’arshe jawota yayi da k’arfin tsiya nan suka shiga
kokawa da karfinsa ya kece rigar ya shiga aiki babu ji babu gani, tun tana daurewa harta fara
zanbada ihu tana niman kufcewa, haka yaita wahalar da ita har asuba,Â
†Dasafe bayan yayi wanka yayi shirin zuwa aiki ya kalleta a fusace fuska babu annuri yace
“kada indawo gidan nan in taddaki tunda ke munafukace............
[10:11PM, 2/9/2018] Maman twinsí ½í²: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)*
*ZAMANI* 2⃣3⃣
*A TRUE LIFE STORY*
*WRITTEN BY*
*FIDDAUSI SODANGI*
*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*
*KHADIJA SIDI*
*WANNAN SHAFIN NAWA SADAUKARWACE GA ZAURAN BIEBIE ISA NAGODE DA
ADDU'AR KU GA UMMA TA NAGODE ALLAH YABAR ZUMUNCI*
Har yakai k'ofa yasake dawowa ya kalle ta da kyau cikin murmushi wanda yak'ara k'awata
fuskar sa yace "A'isha na manta banyi maki albishir ba, ranar asabar mai zuwa in Allah ya
kaimu d'aurin aure na da misalin k'arfe sha d'aya na safe .........."
Wani irin zabura tayi had'e da buga tsalle ta d'ira a gaban sa tare da cin kwalar sa ta shak'e shi
"wallahi tallahi Aliyu baka isa ba kayi kad'an! Na rantse da Allah Aliyu yau koni kokai a gidan
nan sai dai ko ka kashe ni koni in kashe ka amman baka isa kayi aure kabar ni ba na rantse da
Allah!". " bakaji kunya ba Aliyu bakaji kunya ba ni kake gaya wa wannan bakar maganar mara dadin ji
dan ka raina mani wayau?"
"Ni zaka wulakanta ka shammata Aliyu, to wallahi Allah baka isa ba kayi kad'an uban daya
haife kama yayi kad'an bare uwar data d'aure maka gindi kaci zarafina.......".
Wani wawan duka yakaiwa bakin ta tare da hankad'e ta ta fadi k'asa , a gigice ta tashi kamar
wata mahaukaciya ta nufi _kitchen_ da gudu sai ga ta da zungureriyar wuka sai kyalli take
kasancewar ba a aiki da ita,
Tsaye yake kawai yana kallon ta yaga k'arshan haukan ta, aikuwa da gudu tayo cikin sa ganin
da gaske take ne ya tattakura ya hankad'eta ta sai gata ta tafi taga taga ta fad'a bisa teburin
dake d'akiyar d'akin tsinin teburin ya daki cikin ta atake ta saki wani irin k'ara mai firgitar wa
kafin ya ankara sai ganin jini yayi yana binta tamkar an bud'e fanfo, a tsorace yayi kanta yana
kiran sunan ta "A'isha!! A'isha!! A'isha!! Dan Allah A'isha kitashi wallahi wasa nakeyi maki
A'isha ki yafe ni dan girman Allah".
D'aukar ta yayi cak yanufi mota da ita da sauri ya figi motar yafice da gudu bai zame ko ina ba
sai FMC nan aka amshe ta cikin gaggawa, likitoci mata guda
 biyu ne suka rufu akanta cikin kwarewa da aikin su tsawon wani lokaci anata abu daya amman
har yanzu shuru, Â Aliyu kuwa tamkar ya tura kai cikin dakin haka yake ji, Â sai faman safa da
marwa yake tayi a tsakanin reception din, Â tuni yafice a hayyacinsa harma bai san me yake fadi
ba,Â
Likitar ce tafito fuskar ta a daure tace masu tana son ganin sa a _office_ dinta, Â wani irin harara
Aliyu yasakar mata cikin hargagi yake fadin “dallah malama ki fadi duk wani abinda zaki fadi
basai nawani biki ko ina ba amman ki tabbatar bace min zakiyi A'isha ta mutu ba!!â€
cikin rashin damuwa da hayaniyar da yakeyi mata ta fara magana domin kuwa ta kule da
maganar da Alitun yagaya mata.
  “dama so nake ingaya maka Matar ka tayi bari kuma mahaifar ta ta tabu bazata iya kara
daukar ciki ba dan haka munaso zamuyi mata wankin ciki idan ka amince, sai ka same ni a
_office_ d'ina idan kagama shawara.
 ta wuce abinta tabar shi nan sake da baki cikin gigita da kalaman ta kuka Aliyu ya fashe dashi
da karfi tamkar wani yaro karami shikenan ya cucu yar mutane ya gama da ita ya bata mata
rayuwa.
Gaba d'aya Aliyu yarasa awani duniyar yake ciki ne tsabagen kid'ima..........
[9:12PM, 2/10/2018] Maman twinsí ½í²: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)*
*ZAMANI* 2⃣4⃣
*A TRUE LIFE STORY*
*WRITTEN BY*
*FIDDAUSI SODANGI*
*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*
*KHADIJA SIDI*
"A'isha wallahi tallahi anfi k'arfi nane babu yanda zanyi, nayi iya kar k'okarina wajan ganin
rashin yuwuwar abin saidai abin ya faskara bansan yazanyi ba A'isha mahaifina yakasa ya tsare
akan hakan, mahaifina mutum ne mai tsattsauran ra'ayi, baya yin magana biyu, tunda ya nace
saina auri d'iyar nan to fa babu wanda ya isa ya canza masa ra'ayi".
"Aliyu to indai har auran yazama dole to ka had'a mu muduka biyun ka aura mana inaga
adalcin daza ka iya mani kenan, Aliyu idan har baka aure niba ka cuce ni ka gama da rayuwata,
Aliyu kasani ina sonka ina kaunar ka tayaya kake tunanin rabuwar mu zai zama abu mai sauki
Aliyu?"
"Kasani kaine farincikin rayuwata Aliyu kaine jin dadi na ina sonka kamar yanda nakeson raina
Aliyu".
Wani irin tausayin tane yakama Aliyu wannan dalilin nema yasa yaji sam bazai iya gaya mata
abinda ya faru da ita ba, kai hatta cikin ma datayi barin sa baijin zai iya gaya mata.
" A'isha ki kwantar da hankalin ki nayi maki alkawarin cewa zamuyi aure koba yanzu ba da
yardar Allah kedai kiringa yi mana addu'a kawai insha Allahu komi zai zama labari kinji A'isha
na?"
Haka dai yaita rarrashin ta yana bata baki hardai tadan samu sukuni a zuciyar ta, bai boye mata
komi ba dangane da abinda mahaifin sa ya gaya masa akan ta murmushi kawai tayi tashiga
sak'e sak'e a zuciyar ta.
"Aliyu meye yasame ni hakane wai cikina ciwo yake yi sosai yana min zafi?"
"Kin bugu ne sosai a cikin Allah dai ya takaita mana wahala A'isha".
Ido ta kura masa tamkar tana karanto wani abu a fuskar sa.
***************************
*BAYAN K'WANA BIYU*
A'isha tasamu sauki sosai ba laifi harma an sallame su sunkoma gida.
Wani irin zama sukeyi a cikin k'wana biyun nan irin zaman da hausawa ke kira na doya da
manja sam A'isha ta canza masa bata wani kulashi duk abin yadame sa.
Wanka tayi ta shirya cikin wata dogowar riga mai hula, duk da yanda ta koma bai hana
k’yawunta fitowaba, cikinta nata wani irin k’ugi alamar yunwa takeji, yamutse fuska tayi,
"gaskiya banjin zan iya cin komi yanzu"
Tafad'i a zuciyar ta tare da Jan tsaki tayi tamkar zatayi kuka, tace bari inje inyi tea,Â
_Kitchen_ ta nufa ta tafasa ruwa ta juye a kofi tasaka Lipton dad'an suga kadan tafito rike da
kofin a hannu, kofar falon a ka bude a ka shugo kallo d'aya tayi masa ta d’auke kai ta nufi
hanyar d'aki
bazato ba tsammani kawai ya shammace ta saiji tayi yawani fisgota, aikuwa kofin hannunta ya
subuce ya fadi k’asa ruwan ya watse a k’afarta, wani irin ihu tasaki jin tafasashen ruwan a
k’afarta, a tsorace ya rike ta tare da zaro ido yana fadin _"oh! A'isha pls am sorry_ wallahi ba da
niyyar yin hakan nayi ba _sorry pls!â€_
Batace masa komi ba ta rabe ta gefen sa ta wuce, bayan ta yabi da sauri a bakin gado ta
zauna tare da juya masa baya, "kishirya gobe mu tafi Abuja tare ranan Monday saiki dawo
tunda masu gidan ku lahadi zasu dawo".
" Mezanje in maka ne Aliyu?"
"Banaso in barki a cikin wannan halin dakike ciki gara ina ganin ki a kusa dani zaifi