Showing 42001 words to 45000 words out of 56306 words

Chapter 15 - ZAMANI (1 to end) Book Complete by Fiddausi Sodangi .pdf

03 Oct 2025

1692

zaton ko ya makance ne,

" Uwar ka Aliyu!, na ce uwar ka!".

"Ni zaka kalla kace min bazaka auri karuwa ba ka fasa auranta, dan ubanka ita dawa suke
karuwancin bada kaiba!?".

" inace kaine babban kwarton nata daya soma batata?"

"Oh kana zaton bansan komi bane?"

"Wallahi tallahi sai ka auri yarinyar nan indai nine ubanka yazama dole ka aure ta, sannan kuma
kaje ka sakar masu yarinya zan turo direba ya d'auke ta tunda ba zaman aure kake da ita ba

takawo karar ka yafi a kirga dan haka daka koma ka sako ta kaji nagaya maka !".

" Tashi kabar gidan nan tun kafin raina yagama baci inyi k'asa k'asa dakai anan wajan sakaran
banza da wofi munafuki ko kunya baiji ba mugu kawai, kagama da y'ar mutane shine zaka dubi
idona ka gaya min maganar banza da wofi!ka tashi nace kafin inci uwar ka! Da shegen idon sa
kamar na mashaya shashasha!".
Kamar wani mashayi haka Aliyu ya mik'e yana layi ya bar palon zuciyar sa tamkar zata fito waje
dan bacin rai.
[9:33PM, 3/4/2018] Maman twinsí ½í²: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



*ZAMANI*4⃣1⃣



*A TRUE LIFE STORY*



*WRITTEN BY*

*FIDDAUSI SODANGI*


*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*



*INA KIKE UMMY JA'EH*

*NABAKI KYAUTAR WANNAN SHAFI NAWA NAYAU SABODA KAUNAR DAKIKEYIWA
ZAMANI, HAKIKA KALAMAN KI DAKIKAI AMFANI DASHI WAJAN NUNA YABAWAR KI AKAN
LITTAFINA NA ZAMANI YAK'ARA MANI K'WARIN GWIWA WAJAN RUBUTU NA, NAGODE
SOSAI ALLAH YABAR KAUNA*


Lokacin da Aysha tasamu labarin auran ta da Aliyu bakaramin farinciki tayi ba dan saida ta daka
tsalle ta d'ire tace "woo ni Aysha wayace dani ba ni ba, wallahi duk wanda yaja da ikon Allah sai
yayi kuka dan zakaran da Allah yaso saiyayi cara".

"Alhajin Allah Alhaji Abubakar Kaseem Shattima, ya akai kayi saurin karaya haka, ai wallahi
dabakayi min abinda nakeso ba babu abinda zai hana in watsaka a duniya inyaso ka had'iye
zuciya ka mutu wannan ruwanka!".

" Allah ya rufa maka asiri amman duk da haka wlh bazan k'yale kaba sai na d'auki fansar kisan
gillar dakasa akaiwa su _uncle_ Safana, wallahi jinin su bazai tafi a banza ba sai ka gane
kuskuran ka!".

_Number_ Aliyu tashiga nima dan taji irin farincikin dayake ciki, sai dai taga _Number busy_
bayan minti uku tasake kira still dai _Number busy_ tsaki taja bayan minti goma tasake kira _still
Number busy_ tsaki taja tace "wai Aliyu da uban wa yaketa waya haka ne tun d'azu?".

Bayan minti talatin takuma kira, _Number busy_ nan ta tabbatar dacewa ba waya yakeba
_Number_ ta ce aka saka a _black list_ "kuttt lallai Aliyu yaci uwar rainin wayau ma meye
nufinsa to?"

Tayiwa kanta tambayar cike da bacin rai sosai.

Cikin hostel takoma ta ari waya tasaka _number_ sa bugu d'aya ya d'aga yana fad'in _hello_

A fusace tace "Aliyu wani irin kuturun iskanci ne zaisaka kasa _Number_ ta a _black list_ wani
irin rashin mutunci ne haka, meye nufin ka nayin hakan ma kokuwa wani salon wulakanci ne
kakeso ka tsiro dashi wanda tunda bakayi ba sai yanzu iyee!!?".

A zafafe yace " kizo ki shak'e ni ingaya maki dalili, nace kizo ki mak'are ni uwata, sainaji shak'a
da mak'ara sannan zanhid'i maki kinji ko?".

"Ke inbanda ma jahilci da duhun kai irin naki tayaya za ai ni Aliyu in aureki Aysha, to wai in
aureki ince na auri wa uhmm?".

" mezance na aura, abu nayi nayi nayi harma ya gundire ni to meye sabon abu aciki meye abin
zakwad'i aciki".

"Wallahi gara tun wuri kiyiwa kanki fad'a ki kama kanki karkiyi gangancin aure na dan wallahi
shine kuskure na k'arshe dazakiyi a duniya dan saikin gwammace kid'i da karatu wallahi Allah
kinji nagaya maki".

" ke bama kiji kunya ba kinzama abincin kowa kowani biri da kare da jaki da doki duka
shinshinar ki suke kingama rabawa yan bariki kanki shine ni zan aure ki!?".

"Wallahi bakiyi tsadar da Aliyu zai iya auran kiba aikin sani kema basai an hid'i maki ba".

Dariyar rainin hankali Aysha tayi sannan tayi wani juyi tai fari da idanuwan ta tamkar yana
gabanta tace " Aliyu Haydar mijin Aysha Yusuf Gidado!".
"Wallahi Aliyu karya kake baka isa ba, wallahi kayi kad'an, ai Aysha batada mijin dayawuce
Aliyu Aysha taka ce anyi Aysha domin kane, ai mazinaci sai mazinaciya!, nazame maka
k'adangaran bakin tulu, nazama d'uwawu dole a zauna dani ko anki ko anso, dan haka kasawa
ranka ruwan sanyi mutaru murufawa kai asiri, munzama kaddarar juna, sai muje mucigaba da
gurzar juna kamar yadda aka saba ina fata ka fahimce ni da kyau!".

Ta kashe wayar ta tagoge _Number_ Aliyu daga wayar saboda kishin kada yarinyar tabi sahun
sa, ta bud'e jakar ta taciro kud'i masu yawa tahada da wayar ta mikawa yarinyar tace " gashinan
kisai kati kisa nacinye na wayar taki daga hakan tafice abinta zuciyar ta babu dadi.

Tundaga wannan rana Aysha ta kame kanta babu ruwanta da duk wani d'a namiji, kullum
hijjabinta har k'asa, ta maida hankalin ta akan karatunta dakuma niman yafiyar ubangiji.


******************************


"Sadiya!! Sadiya!! Sadiya!!".
"Na'am Umma".

"Gani Umma",
" Sadiya wai mike damunki ne k'wana biyun nan duk kinzama wata sukuku dake baki walwala
ko d'an hiran damuke yanzu baki fitowa saidai kawai ki kunshe a d'aki in rasa abinda kike
kunshewa a d'akin, haba Sadiya yanzu idan baki hid'i mani matsalar kiba kinada wacce zaki
hid'imawa ne wacce tafi ni, nifa uwar kice kuma babu abinda kike boye mani amman ni narasa
gane kanki anya kuwa kinyi mani adalci y'ar nan?"

Sallamar k'awar Sadiyar ce ta k'atse Umma daga maganar da takeyi.

"Umma ina yini munsameku lahiya?".

" Lahiya kalau Sumayya ya Maman taku?"

"Lahiya kalau umma tama ce a gaidaki".

" To masha Allahu ina amsawa".

Janta d'aki Sadiya tayi nan Sumayya taja ta tsaya tana karewa Sadiya kallo kafin cikin mamaki
tace "Sady meke damunki haka kinga yanda kika rame kuwa?".

" kekuwa meyayi maki zafi haka sabida Allah wai kingan ki kuwa?".

"Hmm"
Sadiya ta sauke ajiyar zuciya.

"Sumayya ina cikin damuwa wallahi narasa yanda zanyi kwata kwata banida natsuwa wallahi".

Nan tashiga bawa Sumayya labarin had'uwar ta da Aliyu dayan da sukai da yanda take
azabtuwa da soyayyarsa tun ranan dasuka hadu dayanda takasa kiran sa.

" kuttt!".
"Amman Sady wallahi bakida hankali, shine zaki kashe kanki a banza a wofi bancin ga mafita a
tare dake amman kinki kiransa lallai sannun ki da k'okari.

Jiki a sanyaye ta tashi ta d'auko katin daya bata, fisgewa Sumayya tayi tashigar da _Number_
cikin wayar Sadiya d'in, ta danna masa kira, bugu d'aya ya d'auka yana fad'in _hello_ mik'a
mata wayar tayi da sauri ta k'arba tasa a kunna
ta cikin sanyayyar muryar ta tayi masa sallama,

Ajiyar zuciya ya sauke mai k'arfi danjin muryar ta mai kama da busar sarewa, kobata fad'a ba
yasan itace dama yadade yana jiran takira sa d'in .

" Amincin Allah ya tabbata agareki yake tauraruwa mai haskaka taurari, farin wata sha kallo".

"Tare dakai da y'an gidan Ku baki d'aya".

hak'ika wannan sanyayyar murya taki ta tsaya mani a zuciya harma ta kidima ni narasa abinyi
yanzu haka tsaye nake nakasa zama.

Murmushi tayi mai sanyaya zuciya, tace "kai Yaya Ali kanada ban dariya wallahi".

Tofa nan hira ta balle tsakanin su kamar irin sundade da sanin juna dinnan, sam tama manta
da Sumayya dake zaune, haka Sumayya tagaji da zama tayi mata sallama ta tafi ko albarkacin
rakiya bata samu ba daga wajan Sadiya, illa hannu data d'aga mata, alamar _bye_ _bye_
murmushi kawai Sumayya tayi tana mai jin dadin kawar tata tasamu kwanciyar hankali da
natsuwa.


***********************


*BAYAN WATA D'AYA*

Soyayya tsakanin Aliyu da Sadiya babu kama hannun yaro sunyi wata irin shakuwa mai ban
mamaki, sun aminta da juna sun yarjewa juna zasuyi aure bisa ga amana.

Umman Sadiya tace Aliyu yafito hakanan Indai da gaske yake auranta zaiyi.

Batare da bata lokaci ba yaje yasami mahaifinsa da maganar baiwani jaba ya amince Inda
yatafi shida mutanan sa suka nimo masa auran tare da tsaida rana daidai dana Aysha, duk
wannan hidimar da ake Aysha batasani ba tana can ta maida hankali a karatunta ta tattara Aliyu
ta watsar tana jira sai ta shiga gidan sa tagamu dashi.

****************************


*BAYAN WATA UKU*


Aliyu ne zaune bisa _dinning_ yana karyawa da sauri da sauri saboda yariga ya makara zuwa
aiki gashi sai waya ake ta yi masa tun d'azu.

Tsaye tayi bisa kansa tanai masa wani irn kallo na kaskanci,

"Aliyu takardata nazo ka bani nagaji da zaman gidan ka nagaji da wannan kaddararran auran
naka Aliyu nagaji nagaji wallahi nagaji!".

Ko kallon ta baiyi ba balle ya tankata, ranta ne ya baci sosai, da karfi race " Aliyu da kai fa nake
kanajina, Idan kanaiwa Allah kasake ni Aliyu kasakeni".

"Aliyu Indai har ka haifu cikin uwar ka da ubanka kasake ni bazan iya zama da mazinaci ba
maha'inci mugu azzalimi, d'an isk....

Wani irin gigitaccan mari yasakar mata tare da mikewa tsaye, a haukace taci kwalar rigarsa
tana fadin wallahi tallahi baka isa kabar gidan nan ba saika bani takardata.

Tad'iyeta yayi ta zube k'asa ya rufa mata baya ya danneta yasakar mata nauyin sa gaba d'aya,
bakinshi yasaka cikin nata yaringa tsotsa cikin mugunta yana yamutsata, da karfi ya tuge rigar
jikinta nashanunta suka baiyyana nan yahau aiki akansu babu ji babu gani cikin mugunta sosai,
bakaramin gurzar ta yayi ba kafin ya barta cikin wahala kirjinta kamar zai cire dan zafi da
rad'ad'i.

Wani mugun kallo yayi mata yace kije na sakeki saki biyu dan nima bazan iya rayuwar aure da
fasika ba wacce ta baiwa kwartonta kanta a daran amarcin taba, kuma wallahi bazan taba yafe
maki ba sai Allah yasaka mani azzalima kawai!".

Yafice abinsa yabar ta nan kwance cikin ciwon jiki da na zuciya.


********************



“Sady wai babu wasu _programs_ dazakuyi ne keda kawayanki?†Naji bakice min komi bane?â€

Murmushi tayi wanda ke k’ara rikitashi, tace "Yaya Ali kasanfani bancika son bidi’a ba gaskiya,
dan haka babu abinda zanyi dayawuce walima kawai, saboda inaso auran mu yayi albarka,"

dariyar jin dadi yayi yace "masha Allah! †gaskiya nagode Allah daya had’a ni dake, inayiwa
Allah godiya daya mallaka min salihar mata irin ki, da ace y’anmata zasuyi koyi da k’yawawan
halaiyar ki masu k’yau aida an rage barna a doron k’asa, ubangiji Allah yayi maki albarka
yabamu zama lafiya da zuri’a d’aiyaba,"
“cikin jin kunya ta rufe fuska tana fadin ameen ya rabbi,

Wasu mak’udan kud’ad’e yaciro ya mik’a mata yana fad’in gawannan a k’ara ayi hidimar
walimar da shi,  cikin sunnar da kai k’asa tasa hannu biyu ta k’arbe tana fadin "Yaya Ali irin
wannan d’awainiya haka jiya jiyan nanfa kabani wasu kudin yanzu kuma ka k’ara min wasu,"

murmushi yayi yace to "Sady idan banyi makiba wazai maki?â€
Karfa kiman ta ke *“TAWA CE!!* ked’in *YAR GATA* ce awaje na, gaki kuma *“KAMILA*" mai
addini, ai yanzu munriga munzama d’aya *†ZUMUNTAR MU* mai d’aurewace insha Allahu, yayi
murmushi yace naji kawar ki *“JAWAHEER* tana fadin cewa †*KAUNAR MU* daga Allah ne, a
lokacin har naso inbata amsa sainaji *WAHEEDA* tariga bata amsa shiyasa kawai nayi shuru,"
" hmm! Yaya Ali kenan,"
"yauwa Sady baki k’arasa bani labarin wannan littafin ba dakika fara bani, yama sunan shi?â€

Murmushi tayi tace auwai *“GIMBIYA AMEENATUâ€*  kabari agama hidimar biki insha Allahu
zankarasa maka,"

"alkawari fa kikayi Sady?â€
" Eh aini nace so insha Allahu zankarasa maka kasan ai bana wasa da bukatar ka, dan bukatar
ka shine nawa dankuwa *“KAINE GATANAâ€*"

dariyar jin dadi yayi yace "to Sady ni bari inkarasa gida dan Allah ki gaishar min da kawayan ki
idan kin shiga *“ALIYA* da d’ayar yama sunanta?†Ya tambaya cikin tsokala,

murmushi kawai tayi tace so nawa zangaya maka sunanta?â€

" Sorry d’an gaya min kuma,"

cikin sanyin muryar ta mai kama da busar sarewa tace "sunanta *MARYAMA* "

Yace "d'ayar fa?"

Tace *REAL AMANIâ€*

Daga yau bankara tuna maka.


******************************


*BIKI WAN SHAGALI*


Yautake juma’a ranan daurin auran Aliyu da Aysha za a daura auran ne da misalin karfe biyu da
rabi na rana bayan an idar da sallar juma’a,

An d'aura na Sadiya ko tun goma na safe, yanzu haka kuma karfe sha biyu ne na rana inda za
a gabatar da walima na mata zallah! Wanda mahaifiyar Aysha tashirya a garin yola.

Kowa yayi shigar sa cikin abaya wasu lafaya, kowadai yayi shigar mutunci a harabar gidan za a
gudanar da walimar, inda amarya tafito shar cikin shigarta ta lafaya ko ina na jikinta a lullube
yake fuskarta kawai ake gani,
“kowa yazauna a inda aka tanada domin zama, amarya ma ta zauna bisa wata doguwar kujera
ta alfarma, malama *KAUSAR M HASSAN* itace zata gabatar da wa’azin, sanye take da
hijjabinta har kasa da likaf dinta. Tsaye take agaban tarin jama’ar dasuka halarci wannan taron
walimar, hannunta rike da abin magana, tafara ne da sallama bayan an amsa mata kamar
yanda addini ya tanada saitayima jama’ar dasuka halarci taron barka dazuwa, daganan
tafarayima amarya nasiha masu ratsa jiki da tsuma zuciyar mai saurare, acikin nasihar
datakeyima amaryar ne naji tanacewa,
“Yake wannan amarya Aysha  ki kasance mai ladabi da biyayya ga mijinki! Duk abinda yanuna
yana so to kizama kinfishi son wannan abu, idan yanuna maki baya son abu to kiyi kokari ki guji
abinnan, kizama mai kyautata ma mijin ki, kizama jaruma babu batun Aysha yimin kaza kice
wallahi kai ni kam na gaji! Sam karkizamo mara tarbiyya kizamo mai kare hakkin mijinki! Ki tsare
masa mutuncinsa banda almubazaranci! Banda kazanta! Kizamo mai tsananin tsafta acikin
gidan ki, kiringa kyautata ma yan uwansa banda rowa da shan kamshi agare su, kizamo mai
yawan fara’a ga yan uwan mijin ki, babu ruwanki da yawo mara dalili, ki zauna acikin gidanki
kiyi zaman aure, babu fita batare da izininsaba, kada kisake mijin ki ya gaji dake ya kosa

dayawan bani bani! 
“Kizamo mai yawan kwalliya da ado, kamshi! Yazamana duk sanda mijinki zaikai hancinsa a
jikin ki to kamshi zaiji ta ko ina ki ringa kulawa  da buka tunsa ki bashi hakkinsa duk sanda ya
nima kuma kizamo mai juriya babu yawan fushi da bacin rai agaresa, kizamo mai boye sirrin
mijinki babu zancan surutu mara ma’ana, sai abu na gaba shine yawan yin lalle!  “Lalle dai da farko wani sinadari ne mai dauke da alfanu iri iri, kuma addini ya kwadaitar damu
cewa lalle akwai sirrika acikin sa, 
“Nafarko dai lalle kariyace daga sihiri,

“Kariyace daga aljanu,

“Sannan kuma kariya ce daga cututtuka da dama!

“Yin lalle a kafa yana zuke cutar dake kafar, sannan yana maintaining dumin mace, bi ma’ana
yana reserving ni’imar mace ba tare daya gusheba, 
“Yawan shan fruits, ki yawaita shan fruits sosai, yana taimakawa sosai ajikin mace, yawan shan
fruits nasanyawa kizama fresh akoda yaushe, gakuma tarin ni’ima,
“Haka dai malama *KAUSAR M HASSAN* taci gaba da yima amarya nasiha harna tsawon awa
biyu da rabi, inda taro ya watse cikin kwanciyar hankali, sai a lokacin jikin amaryar yai sanyi
harda dan guntun hawayenta........
[10:02PM, 3/5/2018] Maman twinsí ½í²: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*



*ZAMANI* 4⃣2⃣


*A TRUE LIFE STORY*


*WRITTEN BY*

*FIDDAUSI SODANGI*


*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*



Bayan d'aurin aure ne Aliyu yace ma Yaya Abba dan Allah yayi masa magana da Aysha, harara
Ya Abba ya wurga masa yace "kai d'an iska nifa surukin kane yanzu karka rainan hankali, uban
me zakai mata da baka iya hakuri har gobe, naga dai gobe iwar haka kuna tare".

" kai shege, bawani abu bane inaso inmata maganar Sady ne kasan bata sani bafa tsoro ma
nake wallahi kasan kanwar taka tacika rigima".

"Kuttt!! Ashe yau zaku kwashi y'an kallo bari ma inbar gidan nikam, katafi side d'ina zanturo
maka ita can".

Daga haka ya wuce abinsa shikuma yanufi bangaran Ya Abba d'in.


Cikin wani irin taku mai d'aukar hankali ta iso gefen Ya Abba, cikin sanyin murya tayi sallama ya
amsa mata tashiga ta turo k'ofar.

Da gudu tafad'a kansa tana fad'in " Aliyu yau ina cikin farinciki ina cikin jin dadi Allah ya mallaka
mani kai matsayin miji na Aliyu kaifa wani irin farinciki kakeyi uhm?".

"Aysha ai ni nafiki farinciki yau d'innan Allah ya mallaka mani mata biyu a lokaci d'aya ga y'ar
hannu ga sabuwa fil a leda, yarinya k'arama yar sha takwas, d'anya jagaf, sonkowa kin wanda
ya rasa, Aysha a yau ina farincikin shaida maki an d'aura aure na da Sadiya Lawal Bala, yarinya
mai ladabi da biyayya yarinya wacce tasan darajar kanta dana iyayan ta, yarinya yar gidan
mutunci, ubanta har ya mutu baida wani aibi uban ta ba mutumin banza bane, baya bibiyar
y'ayan jama'a Malami ne me koyar da addini yana da almajirai wayanda har gobe suna alfahari
dashi, ba malamin jami'a bane shi mai bata yaran mutane ba, yanada tsoron Allah kowa ya
shaida hakan shiba azzalimi bane mai keta y'ayan jama'a yana ganin shi ya killace nashi, babu
mai taba waba, bai san ba a yiwa Allah wayau ba".

Wani irin gigitaccan ihu tasaka ta zube

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login