Showing 21001 words to 24000 words out of 56306 words
Chapter 8 - ZAMANI (1 to end) Book Complete by Fiddausi Sodangi .pdf
mani
kwanciyar hankali".
Murmushi tayi a zuciyar ta kuwa taci alwashin saitaga bayan baban Aliyu insha Allahu tunda har
yayi yunkurin rabata da farincikin rayuwar ta tabbas shima saita raba shi danasa bazata kyale
shiba, kallon Aliyu tayi tace " Allah yakaimu lahiya".
Kewaye ya fad'a domin yin wanka inda ita kuma taciro wayar ta ta latsa wasu lambobi cikin
kankanin lokaci aka d'aga daga d'aya bangaran "Da girman kujerar ki ranki ya dade shuru
kwana biyu kin boye?"
Dariya tayi k'asa k'asa tace "dafatan kana lahiya?"
"Lahiya kalau ranki yadade tasamu ne?"
"Kwarai kuwa mugu tasamu!"
"Inajin ki uwar d'akina yanda kikeso haka za a yi anyi angama menene kikeso ayi maki".
" Ba wani aiki mai yawa bane inaso kashiga ka fita kasamomani rahoto akan *ALHAJI
ABUBAKAR KASEEM SHATTIMA* Ina so insan sirrin sa na fili dana boye, ina so insan waye
*ALHAJI ABUBAKAR KASEEM SHATTIMA* Cikin sa da wajan sa!".
"Uwar d'akina ai wannan ba k'aramin aiki bane domin kuwa babban mutum ne shi d'an siyasa
wanda ake damawa dashi a fannoni da dama sannan mutum ne shi mai fuska biyu wand inba
irin mu ba idon duniya babu wanda yasan da hakan".
Dariya ta kwashe dashi tace " saina jika mugu bakada haufi indai nice ba yau muka saba ba
kasani ai, kasan bani wasa a irin........."
Aliyu ne ya fito daure da tawul yanai mata wani irin kallon tuhuma.
Da sauri ta kashe wayar tana kallon sa alamar rashin gaskiya tattare da ita.
"Dawa kike waya A'isha!?".
Ya tambaye ta cikin kakkausar murya ransa a bace
" Aliyu Yaya Abba nefa".
Fisge wayar yayi yashiga dubawa, "Mugu! Mugu! Mugu!?".
"Yaya Abban ne mugu?"
Murmushi tayi tace "bari incanza masa suna kai bakasan muguntar Yaya Abba bane shiyasa".
Jawo shi tayi ya fado jikin ta nan tashiga batar masa da hankali.
**********************************
*WASHEGARI RANAN ALHAMIS*
Garin Abuja sukaiwa tsinke inda yakama masu wani hadaddan hotel,
Bayan sunci abinci sun huta yace mata zaije masallaci yayi sallah daga nan zai je wani waje
amman bazai dade ba zai dawo,tace to adawo lafiya, sai wani dadi takeji tana murna dan duk ta
kosa yabata waje tayi waya.
kallonta kawai yayi tare dayin murmushi ya fice abinsa.
Ledar dasuka shigo dashi ta jawo tashiga dudduba kayayyakin ciki can ta jawo kwalin wayar
data siya yar karama ta bude bayan ta saka sabon sim card dinta data siya a ciki kunna wayar
tayi gajeran tsaki tayi data tuna cewa sai anyi cajin sabuwar waya sannan ake fara amfani da
ita.
jonashi tayi dan yadan yi cajin sannan ta shige kewaye tayi alwala tazo ta tada sallah.
Bayan ta sallame tayi yan addu’ointa sannan ta mike ta nade daddumar,
wayar tace tashiga k’ara alamar kira ya shigo, dasauri ta isa wajan wayar tashiga kallon
_screen_ din har ya tsinke bata daga ba,
wani kiran ne yakuma shugowa d’aukar wayar tayi ta saka a kunni muryar Mugu taji yana fadin
"Ranki ya dade kina ina yanzu?”
" ina cikin Abuja yanzu haka ya ake cikin ne?"
Bayani yashiga yi mata wani irin dariya tashiga yi daga karshe ta gaya masa abinda zai mata.
k’arar bude k’ofa taji da alamar Aliyu ne yadawo, dasauri ta cire wayar a kunninta tana so ta
boye shi ,
bude kofar yayi ya shugo kallo daya yayi mata ya d’auke kai tamkar bai ga metake yiba, kai
tsaye wajan kayansa ya nufa ya bude jakar yaciro wasu kaya sannan ya rufe ya shige kewaye
abinsa,
Ajiyar zuciya tasauke mai k’arfi sannan ta mike ta boye wayar ta koma ta zauna.
“Shirye yafito daga cikin kewayan cikin k’ananan kaya yayi k’yau sosai abinsa sai k’amshi
yakeyi, yace A'isha zan fita zani _club_ sai can cikin dare zan dawo dan sai gobe zanshiga gida
basusan nashigo gari ba ki kular min da kanki pls!”
Kallon shi kawai tayi ta bata rai, yace "menene kozaki bini ne".
da sauri ta girgiza masa kai tace Allah ya tsare ni nikam, yan’iska ke zuwa wajan ai kasani
nikuma ai kaga ba yar’iska bace ko?”
Ta fadi tana murmushi.
Harara ya watsa mata yace "kenan nine dan’iskan ko?”
Kewaye tashige da gudu ta rufo k’ofar, yadade a cikin d’akin sannan zuwa can taji fitar sa,
wanka kawai tayi abinta sannan tafito tasaka kayan bacci cikin wayanda suka saya dazu,
ta feshe jikinta da turare, sannan ta nufi inda ta boye wayar ta dazu ta dauko takira Mugu
takarasa maganar ta ta dazu sannan ta kashe ta hau kan kujerar tayi addu’ar bacci sannan ta
runtse idanuwanta tana sauke ajiyar zuciya, tana fadin Aliyu bazan jiraka ba idan kazo ka
maidani gadon. ahaka bacci yayi awan gaba da ita lokacin karfe sha daya darabi na dare.
Acan bangaran Aliyu kuwa can ya hade dawata tsohuwar budurwar sa ko ince karuwar sa, inda
taita dura masa kayan maye yanasha suna ta watsewar su, daga karshe ta mike taje ta juye
masa k’wayoyin maye danasaka k’arfin sha’awa a cikin wani dan lemu, tadawo ta mik’a masa,
dasauri yasa hannu ya k’arba ya kafa kai ya shanye shi tas yana tunde baki, ba a fi minti biyar
ba ya rungumota yana bata wani irin sunba gaba d’aya ya soma fita haiyacinsa, sunkutar ta yayi
ya nufi d’aya daga cikin d’akunan dake cikin wajan,suna shiga ya wurgata akan gadon ya bita,
wasanni yashiga yi da ita baji ba gani tamkar wani maye, zuwa can tamkar wanda aka tsikara
ya mike dasauri yasaka rigarsa ya nufi k’ofa dasauri itama tasha gabansa tana fadin lafiya
sweetheart menayi maka ta fashe da kuka dan ta kamu dayawa,yace sorry sweetie wallahi
k’anwata na tuna nabarta ita daya kuma na manta ban rufe mata k’ofar da key ba, shuru tayi
kawai tana kallon sa dasauri ya fice abinsa.
Dasauri ya tura k’ofar ya shiga ya rufe da key,tsaye yayi cak a tsakiyar d’akin numfashinsa na
k’okarin dauke wa, A'isha ce kwance akan kujerar doguwar rigar baccinta ya tattare yadawo
cinya, gashin kanta ya barbazu ko Ina, nan take sha'awar sa ta karu daukan ta yayi cak ya nufi
Kan gadon da ita, a tsorace ta bude idonta wayyo meye haka Aliyu!? ”
banza yayi mata ya shiga k’okarin cire mata rigar jikin ta,
ihu ta kwalla masa yasaka hannunsa ya toshe bakin ta dan karta tara masa jama’a,
kuka da ihu take yi saboda sam yau bata bukatar hakan daga garesa.
Amman sam Aliyu bai rangwanta mata ba,……..
[1:08PM, 2/14/2018] Maman twins: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)*
*ZAMANI*2⃣5⃣
*A TRUE LIFE STORY*
*WRITTEN BY*
*FIDDAUSI SODANGI*
*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*
*KHADIJA SIDI*
*INABAWA DUKKAN MASOYA NA HAKURI ABISA JINA SHURU DAKUKAYI KWANA BIYU
KUNSAN JIKI DA JINI SAI ANAYI ANA HUTAWA, NAGODE DA KULAWAR KU AGARE NI*
*CIGIYA*
*DAN ALLAH JAMA'A INA CIGIYAR MARUBUCIYAR WATA RAYUWA WATAU MURBASH,
DAN ALLAH DUK WANDA YASANTA KOYAKE DA NUMBER TA TA ASALI YA TAIMAKE NI
DASHI DAN ALLAH KO YA HADANI DA ITA, NAGODE*
*SAK'O*
*SAK'O ZUWAGA MARUBUCIYAR WATA RAYUWA WATAU MURBASH, DAN ALLAH IDAN
SAKONA YA ISO GARE KI KITAIMAKA KI NIMENI, DOMIN KUWA MASOYAN KI MASOYA
LITTAFIN KI SON DAMENI AKAN INSAMO MASU LITTAFIN KI NA WATA RAYUWA HAR
K'ARSHE, SAIDAI HAR IZUWA YAU NAKASA SAMU SANNAN NAKASA SAMUN NUMBER KI
SAIDAI WATA NUMBER DAKIKASAKA A LITTAFIN NAKI WANDA INA GANIN KUSKURAN
NUMBER KIKAI DOMIN MAI NUMBER TASHAIDA MANA CEWA BA ITA BACE MURBASH
KUMA MUTANE SUN MATSA MATA DA KIRA DA MESSAGES, TO DAN ALLAH Y'AR UWA KI
BAIYYANA MANA KANKI KAUNACE SILA BAKOMI BA, GA NUMBER TA NAN IDAN SAKONA
YA ISKOKI SAI KI NIMENI 07034992740. SODANGI CE TAKE MAKI FATAN ALKAIRI A
RAYUWAR KI NAGODE*
K'ofar gidan *Alhaji Muhammad Kabir Daula* jama'a ne damk'am kuma daga dattijai y'an
kasuwa masu kud'i damasu rik'e da k'usoshin gwamnati da matasa tsan tsan y'an boko way'an
da suka rik'e boko da gaskiya da larabawa harma da sauran yararraki da Allah ya halicce mu a
k'asa guda dasu to duka a yau gasu a k'ofar gidan *Alhaji Muhammad Kabir Daula* sun had'u
domin gudanar da d'aurin auran *Aliyu Abubakar Kaseem Shattima* da *Raulat Muhammad
Kabir Daula*.
Daga can gefe guda yan maula ne da munafukai da 'yan tsurku 'yan saka ido sun baza ido da
kunnuwa.
Gefe guda kuwa iyayan yaran ne a zaune domin su nuna ikon su akan y'ay'an nasu,
Daga can gefe guda cikin _laud speaker_ wani maroki yake kuma jaddada d'aurin auran da aka
d'aura shi akan sadaki na naira dubu hamsin lakadan ba ajalan ba yake kuma k'ara jaddadawa
Amarya tayi goshi takumayi darajar da shari'a ta yarda da ita.
Duk wannan abu yafaru ne bayan an d'aura auran yayar ta *MARYAMA* .
Aliyu ya kasa tantance a wani yanayi yake shin farinciki yake ko bak'in ciki shidai gashi nan ne
kawai sai yak'e yakeyi cikin abokan sa, ana tayi masa Allah yasanya alkairi.
K'anin ango *Yusuf Abubakar Kaseem Shattima* soja mazan fama ya ratso taron mutane ya iso
inda angwayan suke cikin rad'a yace "Yaya Aliyu Abba yace kazo ku gaisa da wasu baki zasu
tafi ne".
Da sauri Aliyu ya bishi suka bar wajan har gaban Abban nasu suka isa mutane duk sun
yanyameshi har k'asa Aliyu ya duk'a ya gaida su, hannun sa _Governor_ d'in Kaduna ya rik'e
yana fad'in tashi tashi ai yau ba ranan durk'uso bace ai sai ka bata kayan ka, dama y'an uwan
mahaifin matar kane zaku gaisa kasan kai ba a sanka ba tunda komi a sauwake yazo maka
bakai gaishe gaishen iyaye ba.
Nan dai Aliyu ya matsa suka gaggaisa sunatayi masa Allah yasanya alkairi sai yake yaketayi shi
kam, masu hotuna sai d'aukar su suke tayi saboda tarihi.
Haka dai taron d'aurin aure ya watse kowa na cikin farin ciki kwarai da gaske.
Angwaye kuwa motoci ne sukai ta jidar su domin zuwa wajan walimar da abokan angon suka
shirya.
Shima mai gayyar mai mai komi, wanda kuma ya isa da duk wani maiji da kansa dashi ba a isa
dashi ba mai magana d'aya babu k'ari watau uban ango *Alhaji Abubakar Kaseem Shattima*
nan shima yashiga gudanar da tasa walimar tare da abokan sa a ciki harda uban amaran da
nashi tawagar.
Abindai yayi k'yau sosai a bangaran mazan.
*****************************
_CIKIN GIDAN SU AMARYA RAMLAT_
Komi ya tsaru bisa tarbiyyar islama, dan kuwa Amarya tayi k'yau tayi k'yau harta gaji duk da dai
tasha kuka ta gode Allah tundaga ranan da uban ya shaida mata had'in da za ai masu da d'an
aminin nasa, dayake yarinya ce mai biyayya sam bata wani ja da maganar uban nata ba atake
ta mika wuya duk da cewar bata san Aliyun ba bata taba ganin sa tunda shi bai cika zama ba
Yusuf kawai tasani sai Auta Fatima.
Sanye take cikin tsadaddan shaddar gizna kalar tuffa, wacce akai mata d'inkin y'an Mali k'afarta
da hannunta sun d'auki zanen fulawa irinta indiyawa abinka da farin fata ai walainiya takeyi, shi
kanshi gashin kanta kafin a d'aura mata d'an kwalin kanta mai kama da nad'in goggoro saida
akaiwa gashin nata gyara na musumman da tufka mai k'yau, aka saki gashin a bayanta yana ta
reto abinka da mai gashi, sannan aka d'aura d'an kwalin yanda zai zauna da kyau batare da
wani tangard'a ba.
Fuskarta ma abin kallo ne domin ta gogu ta gogu iya goguwa tayi sumul tamkar ta jariran da
aka haifa yau d'innan.
Gawani kalar k'amshi dake tashi a jikin ta sam baka iya tantance wani irin k'amshi ne haka mai
bala'in dad'i da bazaka iya banbancewa ba, Amarya dai kam tayi k'yau sosai abinta na ban
mamaki.
Mahaifiyar ta Hajiya Nafisa y'ar boko uwar zamani mai jawo y'ayan ta a jikin ta sune k'awayen ta
abokan hirar ta da su take shawara sugaya mata matsalar su tagaya masu nata.
Tajawo d'iyar ta ta rungume tayi murmushi tayi dariya sam tarasa wani irin farinciki zata nuna
ne.
Tace Ramla inama na iya bud'a yau in rangad'a maki bud'a.
Wata abokiyar wasan ta tace dabaki iya bama ni ai sai in tayaki yi, nanfa ta nare harshe tace
"Ai yiri - yiri - yiri - yirrrrrrrrrr.
" Yau Allah ya nuna mana auran *MARYAMA MUHAMMAD KABIR DAULA* DA *FAHAD
SALIS MASHASHA*",
*"DAKUMA RAMLAT MUHAMMAD KABIR DAURA DA ALIYU ABUBAKAR KASEEM
SHATTIMA*".
"Mak'i gani ya kauda idonsa abin na Allah ne had'in Allah babu wanda ya isa yaja da ikon sa, ta
Allah batakuba Ramlat karbi sadakin ki kirik'e a hannunki kisake kirgawa dubu hamsin ne
Alhajin ku yace abaki kuma kuma kizama a cikin shiri da k'arfe biyar na yamma za a kaiki gidan
su Aliyu Haydar".
" A bisa tsari da al'adarmu wanda da mun d'aurawa y'ayan mu mata aure tofa basu k'ara kwana
a gidan iyayan su sai d'akin mijin su to kuma yau zaku isa ga gida mafi daraja da d'aukaka ga
dukkan matan duniya, dan haka sai aita hakuri kuma a juri zaman aure, dan a baiwa marad'a
kunya, Aliyu dai yazama naki shi aure zaman ibada ne kuma anayinshi ne dan raya sunnar
manzo, dan haka saiku zage ku zage damtse ku bautawa Allah a cikin lamarin ku, Allah yabada
zaman lahiya da zuri'a d'aiyyaba."
Nan wata goggon su itama ta d'aura, ta shiga haska masu wasu abubuwa acikin zaman aure
kamar kula da miji da bukatunsa a kowani lokaci, tsaftar jiki da muhalli, iya girki da canzashi
nau'i kala kala, girmamashi da dangin sa da abokansa, k'yautatawa mak'ota, da duk wani mai
sonka inhar yazama mutumin kirki ne na Allah, ware lokacin mai gida dana baki, duk abin
kulawane ga macan da take niman aljanna mafificiya wajan Allah, kaucewa fushin miji koda
kuwa shine mara gaskiya, akan abinda ya hada ku, tausaya masa cikin al'a muran gida da
kuma tattala masa kayan abincin sa, banda almubazaranci, da nuna masa cewa ku masu
wadata ne, in kuka rike wannan acikin zaman auran ku tofa zaku samu kwanciyar hankali.
Cikin k'awayan su suka koma akaci gaba da gudanar da sha'ani anata hutuna ana jin dad'i,
Anci ansha Amare sai sai shiga da fita suke cikin d'inkuna masu kyau da tsadar gaske,
********************
Da misalin k'arfe biyar aka shiga shirin tafiya da amare bayan kowa ya shirye Amare suka fito
cikin shiga ta alfarma,
Nan kishiyar Hajiyar Nafisa matar babansu wacce ake tayiwa habaici tuntuni ta kama hannayan
su tayi sama dasu wajan mahaifin nasu domin su gana, inda sauran mutane suka isa jikin
motocin dasuke Jere kamar wani kamfanin saida motoci,
Nan mahaifin nasu yayi masu nasiha sosai mai ratsa jiki sai kuka suke babu ma kamar Raulat
ita batasan waye mijin nata ba.
Ahaka suka tafi inda aka fara kai Maryama sannan daga k'arshe aka kai Ramlat inda akai masu
tarbar mutunci da karama daka k'arshe aka kai Amarya bangaran Aliyu daya ke can bangare
guda tare da jaddada masu cewa kawayen Amarya bazasu kwana ba yau Ango zaishiga d'akin
Amaryar sa, ahaka suka juya suka tafi suka barta tanata faman kuka ita d'aya tare da jinjina
yanda akace sati daya zasuyi sukoma katsina tare wajan aikin sa.
************************
A gigice *Alhaji Abubakar Kaseem Shattima* yakira number dake jikin file d'in sai zufa yake yi
dukuwa da sanyin ac dayaso yayiwa d'akin nasa yawa.
Jikinsa sai kyarma yakeyi kallo d'aya zakai masa ka tabbatar da a tsorace yake.
Kusan sau uku yana kira ba a d'auka ana ukun ne aka d'auka cikin gigita yasoma fad'in "waye
kai mekakeso atare dani gaya mani biliyan nawa kakeso ka goge wannan sirri nawa a rayuwar
ka?"
Wani irin shu'umin murmushi A'isha tayi a bangaranta tashiga karkad'a k'afafunta cikin narkar
da murya tace *"Alhaji Abubakar Kaseem Shattima"!!* meyasa ka gigice akan d'an wannan
abin?"
"Kaifa namijin duniya ne wanda yaga jiya yaga yau, baikamata ace d'an kankanin abin nan ya
rud'a ka haka ba, to idan kuma na tono babban sai kayi yaya kenan iye Alhajin Allah!?"
Ajiyar zuciya yayi yace "waye ke!?"
"Sanin ko wacece ni bazai k'are ka da komi ba face kashiga rud'u wanda zaisa ka iya rasa
ranka dankasan ka kwana biyu a duniya kasha miya!".
" bawai cece kuce nakeso muyi nida kaiba umurni ne zanbaka kuma dole kabi idan kina kaki na
rantse da Allah nan da awa biyu sunan ka zaigama baci a duniya kasani tunda nasan wannan
sirri naka dababu wanda ya sani a duniya tofa tabbs kasancewa nasanka cike da waje!".
"Inajinki fad'i inji".
Wani dariyar mugunta tayi tafara zaiyano masa abinda takeso yayi, cikin tashin hankali ya mi'ke
yana fad'in "kinsan abinda kike fad'i!?"
Cikin k'wantar da murya tace "haba Alhajin Allah karfa ka manta kasha aikata abinda yafi
wannan munifa ko in tuna maka ne?".
A rikice yace "A'a 'A'a naji shikenan kawai zanyi hakan, amman yaza ai kisancewa na aikata
hakan?"
Murmushi tayi tace "karka danu ina kallon duk wani taku naka!".