Showing 51001 words to 54000 words out of 56306 words
Chapter 18 - ZAMANI (1 to end) Book Complete by Fiddausi Sodangi .pdf
akan kujera ya fito kamar zai tashi sama Aysha ta banka masa harara ta dauke
kanta.
koh kallon ta baiyi ba shima ya fice abinsa.
Tuki yake tamkar baisan akwai wasu motocin akan titin ba sai nasa saboda irin tukin
gangancin dayakeyi,
Yana isa location din wani yaro ya mika mishi Disc bai tsaya wata wata ba ya ruga da gudu
abinsa.
hankalin Aliyu ya kara tashi.
Aysha kuma Aliyu na fita ta sa dariya dan tasan hakon ta yakusa cinma ruwa.
Ta tashi tana yan wake waken ta ta shiga _kitchen_ tasoma shirya abincin dazata ci dan Sam
bata cin girkin Sadiya acewar ta jagwalgwalo ne, bayan tagama kamshi ya bade ko ina ta zauna
falo ta baje tana ci tana yada habaici.
Sadeeya ta fito tana wani shan kamshi,
Aysha koh ko a jikin ta tace "kanwata an tashi lahiya?"
Tana maganar ne tana murmushin mugunta.
A ranta tace yau karshen zaman ki a gidan nan ya kare Aliyu nawa ne ni kadai babu wacce ta
isa taji dadin Aliyu sai ni.
Aliyu ne ya shigo gida da gudu ya shiga dakin shi ya rufe kofar da key ya dauku laptop dinshi ya
saka disc din ya fara kallo kanshi ne yayi mugun bugawa nan yaga
Baban a ranan auran sa da Ramlat, tundaga lokacin dayake labe labe har lokacin daya kashe
wutan gidan har sanda ya shiga dakin, zuwa lokacin idon Aliyu sun firfito waje sunyi jawur
sosai ranshi ya bacci matuka harma yanaji tamkar zai mutu ne.
ya shiga dayan file din yaga Sadiya da Baban shi kwance suna aikata masha'ar su hankalin su
kwance,
Dayan file din kuwa Baban shi ne tube haihuwar uwarsa suna aikata luwadi shida wasu samari
dabasu fi shekara 20 ba.
(Subhanallah)
dayan file din kuma kuma yadda Babban shi yake magana da wanda zasu je su kashe Aysha
ne yanda aka shirya komi harma da yanda suka dawo basu ci nasarar kashe taba.
Aliyu ya runste idon shi yayi wani irrin kara sai da Aysha take falo tana cin abinci girgiza ta
taho da gudu sai ji tayi dakin a rufe.
Bugun kofar take da iya karfinta amman ina, sai can ta tuna tanada wani mukullin, nan tasa ta
bude tana shiga hankalin ta yayi bala'in tashe data ga Aliyu a sume ta rasa yadda zata yi ta
zauna ta fara kuka, zuciyar tace ke fadin
"Aysha meyasa kika sa a nuna mishi
Video din nan".
ta kara sautin kukan ta tana girgiza shi da karfin ta.
"Aliyu dan Allah ka tashi Aliyu kar ka mutu ka barni wallahi bazan iya rayuwa babu kai ba,"
chan dai dabara ya fado mata ta fita dakin Sadeeya da gudu suka taimaka aka sashi a mota
Aysha gudu take tana kuka kamar ranta zai fita har dai suka isa asibiti nan aka shiga bashi
taimakon gaggawa.
***********************
Kwanan Aliyu biyu kafin ya farfado, Aysha bata da aiki sai na kuka duk ta rame kamar ba ita
ba,
Sadeeya koh tunda ta bar asibiti iyakacin ta kiran Aysha taji koh ya farfado.
***************************
Yau dai Ramlat ta shirya ta tafi gidan su Aliyu takanas.
Tana tafe tana tunanin abubuwan da suka faro a daren ranar,
nan ta tuna ai ta cici mutumin cizo mai tsanani kuwabwanda tanada tabbacin tabar masa
mugun tabo.
Tana shiga cikin gidan ta samu Abban Aliyu zaune da vest yana karanta jarida, kallo daya yayi
mata ya dauke kansa dasauri.
Nan suka gaisa tace masa tazo daukan wasu kayanta ne da suke gidan, tana cikin gaya masa
ne aka kira shi a waya yasa hanu zai dauki wayan sai ga tabon cizo ne wawakeke a hannun sa
ga shedun hakora nan tamkar yanzu akai cizon.
Da sauri ta fice abinta.
side din Aliyu ta koma a take tagama fahimtar komai.
zama tayi ta fasha da kuka mai karfi tafi minti talatin a wannan halin kafin ta mike ta tafi gida.
A zuciyan ta tana saka irin yadda zata ma Aliyu rashin mutunci Ashe Uban shine kawarto kai
wallahi anyi asara uba kwarto da kwarto, tana isa gida tayi wanka tayi sallolin da suke kanta ta
shiga fada ma umman ta tanaso a hadata da direba gobe zata katsina akwai abu mai
mahimmanci dazatayi.
*****************
Aliyu tunda ya farko sukayi ido hudu da Aysha yaketa yi mata kallon kurullah.
Sam yakasa magana sai hawaye dayake yi.
Aysha ma kukan take daga k'arshe ta rungume shi kaman za'a kwace shi, ahaka har bacci ya
fara gaba da ita taji muryar Aliyu kamar daga sama yana fadin
"Aysha dan Allah ki fada min gaskiya waye babana me kika sani game dashi ne?"
kuka ne ya kufce mata tace "Aliyu ka bari idan kaji sauki zan fada maka komai na maka
alkawari".
yace "wallahi idan baki fada min ba rayuwata tana daf.....",
Aysha ta rufe bakin shi tace "Wallahi duk abunda zan fada maka babu karya a ciki Aliyu, amma
lallai sai ka daure, kabar kuka kayi hakuri,"
nan Aysha ta fara bashi labari yadda tasa aka mata bin cike da yadda sukayi da Abban nashi
da yadda yasa aka kashe su Uncle Safana da yadda tasa aka rubuta lbrn a jarida da yadda
baban yasa akai auran su, takara dacewa tunda tagano halin ubansa take bibiyar sa duk inda
yayi dakuma duk wani motsi nashi saboda ta tsira da rayuwarta....... [8:01PM, 3/17/2018] Maman twinsí ½í²ž: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*ZAMANI* 4⃣9⃣
*A TRUE LIFE STORY*
*WRITTEN BY*
*FIDDAUSI SODANGI*
*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*
*DAN ALLAH AIMANI HAKURI DA JINKIRIN DA AKE SAMU HAKAN YANA FATUWA NE
SABODA TAFIYAR DANAYI AIMANI AFUWA LABARIN YAZO KARSHE*
Tunda Ramlat ta taso daga Abuja take ta sake sake a ranta na irrin rashin mutunci da zata ma
Aliyu, koda suka iso garin Katsina dare yayi har tayi bacci sabida jiya kwana tayi batayi bacci
ba. Suna isa hotel din da dama tun kafi su tasu Maman ta tasa aka mata booking d'aki suna isa
ta fada gado tana kukan bakin cikin Aliyu da mahaifin shi, can dai ta tashi tashiga bayi tayi
wanka ta dauro Alwala ta fara aikin biyan Sallah .
Sadeeya koh tunda suka kai Aliyu asibiti ta bude sabon pagen iskanci dan koh kwana ta daina
yi a gidan, dama tsakanin ta da Aysha sai waya kwanan Aysha biyu bata dauki wayan ta ba
yasa ta koma gida har yanzu dai babu kowa gidan, hakan yasata wucewa asibitin, tana zuwa ta
wuce dakin da Aliyu yake, nan aka hanata shiga a cewar su Aliyu yace kar a bar kowa ya shiga
inda yake.
haka dai ta Karaci magiyar ta karshe haka ta tafi bata gan shi ba koda ta bar asibitin wani
_appointment_ ta hada da tsohon saurayin ta.
************************
Tunda Aysha ta gama ba Aliyu labari ya ture ta tafadi kasa tana kuka tana bashi hakuri, kota
kanta baibi ba ya fita yaje _office_ din Dr. yace a sallame shi yaji sauki.
Dakyar Dr. yabashi hakuri a cewar sa bai gama warkewa ba kuma yana bukatan hutu sosai da
kyar dai Aliyu ya yarda yace sai dai da sharadin baza a bar kowa ya shiga inda yake ba har
matan shin gaba d'ayan su, haka suka rabu da Dr.
yana komawa dakin ya fara ma Aysha wani mugun kallo yana cewa "Wallahi daga yau idan na
sake gannin ki inda nake sai na babbalaki wallahi kinji nagaya maki, wuce ki fita min ki bace
daga ganin idona!.
Aysha da kuka yaci karfinta ta kasa cewa komai ta fita ta zube a kasa tana kuka kamar ranta zai
fita.
Tun daga ranar aka hana kowa shiga sai Aysha itama saboda tsananin nacin tane da kafiya
yasa sai yayi bacci likitocin suke barin ta tashiga, haka zataci kukan ta ta fito, duk ta rame
kamar ba Aysha Sholy ba.
************
Toh yau dai za a sallami Aliyu, Aysha tun da safe take ta zarya a cikin asibitin daga karshe tayi
zaune kofar dakin da Aliyu keciki tana sana'ar tana kuka, koh da Aliyu ya fito koh kallon inda
take baiyi ba ya wuce dama tuni yayi waya azo a dauke shi daga wajan aikin su, bai zame koh
ina ba sai Abuja, koda ya isa dare yayi, kwana yayi yana tunane tunane har dai asuba tayi, tunda ya tashi Sallah bai koma ba yayi shiri ya fita, yana zuwa kwanan gidan su yaga Abban shi
shima ya shawo kwana abinda bai taba gani ba kenan mahaifin shi yana tuki da kanshi,
nan yasamu kanshi da binshi a baya har suka iso wani gidan baban dake bayan gari.
Baban ya bude gate ya shiga sai chan ya fito ya shiga mota ya juya Aliyu dai yana ta binshi a
baya nan baban ya tsaya ya dauki wata a bisa hanya wanda bayanta kawai Aliyu yake iya gani,
suka wuce bai zame koh ina ba sai wani gidan nashi dake wani unguwa mai nisan gaske.
suna isa aka bude mashi gate suka shiga, shikuwa Aliyu sai yayi parking motan shi can bakin
titi ya karaso da kafa yana zuwa ya kwankwasa mai gadi ya bude suka gaisa, yace "Abba naciki
ko?"
Dan Jim mai gadin yayi kafin yace "eh yana ciki amman yana tare da baki ne".
Aliyu yace " ai babu damuwa yanzu zanfito nima", daga haka ya shige abinsa batare daya kuma
sauraran mai gadin ba.
Ido baba maigadi yabishi dashi a zuciyar sa yace " toh fa yau dai dubun Alhaji ya cika kenan
Allah ya kyauta yasa ba karshan aikina tare da Alhaji bane yazo Allah kadubeni".
Aliyu kuwa yana shiga palon tun daga bakin kofa ya fara cin karo da bra da pant kafa yasa ya
ture gefe yana yatsine fuska, gaban sa sai faduwa yake zuciyar sa na tsinkewa a hankali ya
karasa d'aya daga cikin d'akunan, yana dosan kof'ar d'akin ya fara jin nishin su alamun sun lula
duniyar jin dadi.
Kafarsa yasa ya banka kofar ya shiga, da k'arfi ya runtsa ido saboda ganinsu dayayi tsirara
haihuwar uwar su da ubansu, zuciyar sa tamkar zata buga dan azabar tashin hankali.
Sukam basu ma san ya shigo ba ogan kawai kokarin saka kwallonsa a raga yake gaba daya
idonsa ya rufe, sai kawai ji suka yi ya finciko ta yashiga burma mata ruwan ashar, suna hada
ido wa zai gani, Sadiya ce gaba d'aya tagama gigicewa ta fita haiyyacin ta, nan ya shiga dukan
ta da duka karfinsa yana hadata da bango, ihu take tana kuka tana rokonsa amman ina ransa
yagama back hankalinsa yatashi ba kadan ba, haka yaringa bugunta tamkar yana bugun kato
har saida ya tabbatar bata motsi ta suma sannan ya kyaleta, nan yabarta nan a sume.
Abban sa kuwa tunda Aliyu ya fisgo Sadiya ya kafe ya gagara koda motsi,
Aliyu bai ce dashi komai ba ya juya ya fita bai zame ko ina ba sai gidan baban dake bayan gari
wanda dazu ya ganshi ya shiga
yana shiga ya wuce har cikin gidan, abin mamaki key najikin kofar anrufe amman ba a cire
mukullin ba a jikin, yanashiga palon numfashin sa yakusa daukewa.
Tashin hankalin daya baiyyana a fuskar Aliyu baya misiltuwa.
Kayan tsafin Abban sane baje ko ina harda wasu irin abu kamar kwarangwal.
Gasu jini nan su k'oko da kayan tsafi dai kala kala.
Zaman dirshin Aliyu yayi yaci kukan sa tamkar zai shide sannan ya tashi ya bar gidan.
********************
Bangaran Aysha kuwa tunda Aliyu ya bar garin ta koma gidan ta ta share koh ina tayi sallah tayi
wanka ta dafa abinci amma ta kasa ci sai kuka take yi a haka dai har bacci ya dauke ta.
Washe gari ta koma makaranta ta zama saliha bata kula kowa idan ba kyakkaywan sani kayi
mata ba baza kace ita bace,
ta zama shiru shiru harta shigo makaranta ta fita baza tama kowa magana ba abinda yakawo
ta shi take yi, tana tashi daga makaranta kuma gida take wuce wa abinta.
ta zama wata sukuku bata da aiki sai na kuka.
Aliyu kuma yasa duk inda Aysha ta shiga a riga binta ana ganin movement dinta.
Saboda lamarin ya tsoratashi ba kadan ba.
*******
Aliyu tunda ya tafi bai sake bibiyar taba dan koh ta kira shi a waya baya dauka haka take kuka
har bacci ya dauke ta haka dai rayuwar ta ya kasance a cikin wannan kwanankin.
**************
Ramlat kuma tunda tazo take safa da marwa gidan Aliyu amman kullum taje babu kowa,
ranan nan dai taci sa'an samun Aysha ta fito zata tafi makaranta,
Kamar daga sama Aysha taji ana fad'in "ke kilaki ina zuwa haka, ko yawan karuwancin za a fita
da sassafen nan!?"
rashin mutumci tashiga yi mata tana zagin ta na fitar hankali.
Ba karamin cin mutunci Ramlat tayiwa Aysha ba ta zage ta tundaga biri har wutsiya.
tace kuma saura Aliyu,
Aysha dai batace da ita komai ba rannan dai makarantan da bata je ba kenan ta koma gida
tana kuka kamar ranta zai fita cike da bakin ciki da kunar zuciya saikace ba Aysha ba.
Haka dai Ramlat ta karaci zaman ta a Katsina harta koma Abuja ranta baisu ba dan taso ta
hadu da Aliyu tai masa wankin babban bargo.
***********
Tunda Ramlat ta koma Abuja ta kasa samun nutsuwa a ranta burin ta mezatayiwa Abban Aliyu
ta rage jin radadin abinda yayi mata.
rannan dai ta shirya dan taje ta same shi suyi wacce zasuyi ko ita ko shi.
tana zuwa gidan koh bata yi kasa a guiwa ba ta samu baban Aliyu a kofar shiga Palon gidan
cikin d'aga murya tace "kai tsohon najadu tsohon banza!".
Da sauri ya juyo ya zuba mata ido a tsorace dan yazama kamar wani tababbe tababbe.
nan ta fara surfa masa zagi da cin mutunci ta inda take shiga bata nan take fita ba,
Aliyu ne yaji hayaniya yana fitowa suka yi ido hudu da Ramlat haba nan shima ta shiga zazzaga
mishi rashi mutunci hardai ta karaci masifar ta Aliyu baice da ita komai ba bare kuma uban nasa
mai gayya mai aiki.
Tunda Ramlat ta tafi Aliyu ke kuka da hawayen sa wannan wace irin rayuwa ce.
****************
Tundaga wannan rana Aliyu ke wasan buya da baban shi, kuma yasa ana mishi bincike mai
tsauri akan shi dan haka ma ya gano komai dake faruwa cikin sauki,
nan Abban nasa yasoma tsorata dashi dan yanzu koh karan abu yaji sai ya tsorata.
Kiri kiri Aliyu yace kada ya sake zuwa inda maman shi take.
Ana haka ne Aliyu ya dauke maman shi da kanwar shi ya maida su Katsina uban yanaji
yanagani babu yanda zaiyi dan yanzu Aliyu kam yafi k'arfin sa.......
[11:23AM, 3/18/2018] Maman twinsí ½í²ž: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*
*ZAMANI 5⃣0⃣*
*A TRUE LIFE STORY*
*WRITTEN BY*
*FIDDAUSI SODANGI*
*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*
*KHADIJA SIDI*
*K'ARSHE*
Bak'aramin kulawa Aysha keyiwa mahaifiyar Aliyu ba wanda hakan bawai yana d'ad'a Aliyu
da k'asa bane, yashare su tamkar baisan Allah yayi ruwansu ba a cikin gidan daga ita har
Sadiyar wacce ta dawo babu kunya babu tsoron Allah duk da a d'ar d'ar take zaune, Aliyu yayi
kamar baisan tana cikin gidan ba dan kuwa har yau d'innan baice mata uffan ba akan dawo
masa gida datayi ba.
Ana cikin halin nan, Aysher ta yanke shawarar shiga islamiyyar unguwarsu saboda tsoron
Allah ya shigeta musamman da taga halin da mahaifiyar Aliyu take ciki, kuma ta kudira ma ranta
neman gafarar Ramlat.
Tarasa tayanda zata tunkari Aliyu da wannan maganar, saboda rabon dasuyi magana ita kam
harta manta wallahi.
Yaudai ta yanke shawarar kiransa tagaya masa ta waya.
Ta kira sa dan ta shaida masa
amma yaki d'aukar wayarta, gashi hankalinta ya karkata sosai kan komawa islamiyya saboda
akwai abubuwan da take neman karin haske a kansu na rayuwarta da Aliyu harma da Sadiya.
Tsawon kwanaki Aliyu yaki d'aga wayar tata, wannan dalilin yasata tafiya kawai taje tayi
_register_ a wata islamiyya kasan layinsu mai suna *Sheikh Abubakar Mahmud Gumi
islamiyya.*
Inda aka kaita ajin Malama Zainab Inuwa saboda tace tana da bukatar sanin hukunce
hukuncen addini.
Makarantar ta yamma ce daga Karfe 4:30-6pm na yamma hakan yasa bai shafar karatunta na
boko saboda yawancin malaman makarantar ma'aikata ne.
Sai da ta d'ebi sati tana zuwa Sannan ta fara tunanin kebewa da malamar tasu don ta yaba da
hankalinta,
mutuncinta da karamcinta.
* * * * * *
Ranar da ta yanke samun Malama Zainab da damuwarta sai da ta bari an tashi makaranta
Sannan ta tsaida Malama Zainab