Showing 9001 words to 12000 words out of 56306 words

Chapter 4 - ZAMANI (1 to end) Book Complete by Fiddausi Sodangi .pdf

03 Oct 2025

3361

bakin kofar yana jiyo sautin kukan ta, amma kofa a kulle, zagayawa yayi ta dayan
kofar d'akin Talatu wacce take shigowa dakin nata, yayi sa’a a bude take tanan ya shigo. 

  Halin da ya ganta a ciki bama gaskiya bane, sabida bai taba tunanin haka ta hargitseba.

Yazo kusa da ita zai zauna cikin tsananin kuka harda majina tace dashi

  _“Get out_ *SAFANA*! _I said get out i dont wana see u again”_

  Bai tsaya sauraren ta ba ya nufota ya kamata.
dukda yayi mamakin yanda takirasa haka gatsau.

Yana kokarin rungumeta tana dukan sa a kirji, tana kuka tana fadin ya fitar mata a daki.

 Wani Kukan ne mai tafasa zuciya ta fashe dashi

  “Na tsaneka _uncle_ banason ganinka! na tsaneka banason ganinka!! Na tsaneka bana son
ganinka!!!” Abinda take maimatawa kenan tana wani irin kuka mai tsuma zuciya, gaba daya
_uncle_ ya rude, ba abinda ke masa dadi musamman ganin A'isha tanai masa wannan kukan
tabbas yasani a haife ya haifeta dandai shi Allah bai nufesa da haihuwar bane.
 amma itace take masa wannan kukan kamar ranta zai fita, 

  Sam batajin rarrashin da yakeyi, sai fadar take ta tsaneshi, wannan kalmar ba karamin
wargaza masa tunani takeyiba, 

   ” ka sakeni _uncle_ bana son ganin ka” 

  Wata irin tsawa ya daka mata wacce ta aiko mata da mala’ikar natsuwa, tuni ta natsu tayi
shiru, ta lafee a kirjinsa, a hankali ya fara bubbuga bayan ta kamar ana rarrashin yaro karami.

A hankali taji natsuwa tana sauko mata, yaci gaba da mata waiwayi, ko minti uku ba’ayiba sai
bacci ya d’auketa ba karamin wuya tasha ba, tsayawa yayi ya kare mata kallo, tabbbas wannan
yarinyar akwai kishin bala’ee, sai kace ta gansu turmi da tabarya,
guntun tsaki yaja, a hankali ya zame jikinsa ya janyo pillow ya daura mata ya fito dakin, ko minti
biyar ba’ayi ba sai gata ta tashi kamar an tsikareta,

Sai kace wacce tayi wani mafarki, ko ina ta zagaye bata ganshi ba, chan ta hangoshi hanyar
kitchen yana waya, kuma ga dukkan Alamu wayar ta munafunci yakeyi, zuciyarta take cewa taje
gurinsa wata zuciyar na ce mata kada kije ki jiyo bakin ciki, a hakan ta tsaya amma wayar taki

karewa, bugun zuciyarta yake dad'uwa duk lokacinda ta waigoshi, sai taga kamar ma yana
dariya............
[12:42PM, 1/29/2018] Maman twins: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)*


*ZAMANI* 1⃣3⃣


*A TRUE LIFE STORY*


*WRITTEN BY*

*FIDDAUSI SODANGI*


*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*
*KHADIJA SIDI*


*WANNAN SHAFIN NABAKI SHI KYAUTA MY SADNAF INA JIN DADIN YANDA KIKE BIYE
DANI A WANNAN LITTAFI NA ZAMANI TO INA AFATA ALLAH YARABAMU DA SHARRIN
ZAMANI YASA MUGAMA DA DUNIYA LAHIYA AMEEN SUMMA AMEEN*


Kalmar data fito daga bakinsa neyasata mutuwar tsaye jikin ta ya hau rawa zuciyar ta tamkar
zata fasa k'irjinta ta fito dan takaici.
   Wani bakin ciki ne ya tokareta,  bata san lokacin da ta fizge wayan ba da k'arfi ta wurgar
ak'asa, wanda tuni ya fashe a gurin,  tana hushi kaman mayunwacin zaki, domin ji take kaman
ta rufe shi da duka , shi kanshi  ya tsorata domin bacin ran da yagani a fuskanta dazu bai kai na
yanzu ba, jikinshi  ya fara rawa kaman wanda aka kama yana sata. _“Uncle_ ni kake cewa zaka barni koda zaka mutu?” 

Ta fada da wata irin raunatacciyar murya mai ban tausayi, ta dago kai ta kalleshi, 
Cikin rawar murya yashiga fad'in "Aisha ki natsu ki saurari abinda zangaya maki kina ji nako?"
Cikin tsawa mai k'arfi ta katseshi wanda ya hartsine zuciyar sa ransa ya baci sosai jikin sa har
kyarma yakeyi, sam idanuwanta sun rufe bata lura da halin da yake ciki ba tashiga fad'in
"mayaudari! Ma ha'inci! Azzalumi! Me.........",
Wani irin gigitaccan mari yasakar mata yaci gaba da dukanta sosai tana ihu iya k'arfin ta kuma
bakinta bai bar surfamasa zagi ba shi kuwa a haukace yaketa kai mata duka yaza ai ace d'iyar
cikin sa take zagin sa haka.
Cikin bacci Anty Abeeda ta farka a firgice jin har yanzu ihun A'isha k'aruwa yakeyi, da gudu

tafito palon ba k'aramin kad'uwa tayi ba ganin yanda yadage yana jibgarta ita kuma tana
zaginsa zagi mafi k'ask'anci kuwa, cikin tsananin tashin hankali ta nufesu tana salati, " meye
haka meye haka dear meke faruwa haka, da k'yar ta amshi A'isha a hannunsa wacce sama
sama take numfashi bakinta na furta kalmar Allah ya isa na Allah ya isa na Azzalumi!!!!!". Cikin kallon tuhuma matar tasa ke dubansa ko kallonta baiyi ba yashige d'aki abinsa ransa a
matukar bace.
Taimaka ma A'isha tayi taje tayi wanka ta had'a mata shayi tasha ta kwanta sannan ta turke ta
dambayar meye had'in ta da mijin ta datake masa irin zagin wulakancin nan, "haba A'isha
wannan wani irin rashin mutunci ne zaki ringa zagin mutumin dayake matsayin uba agare ki!?"
"Aminin mahaifin kine fa!".
" Tare suka tashi da mahaifin ki kinsan komi mezaisa kiyi haka, sam wannan ba tarbiyyar arziki
bane ina jinki meya had'a ku meyayi zafi?"
Cikin sauke ajiyar zuciyar A'isha ta kalli Anty Abeeda cike da rashin kunya irin ta yaran
*ZAMANI* tace "Anty mijin ki niman mata yakeyi waya na kamasa yanayi da budurwarsa suna
shirya yanda za ai su had'u gobe, nikuma naga rashin dacewar hakan shine nashiga yimasa
nasiha waifa shine yakama dukana bayan ni duk inayi ne saboda Allah kuma saboda ke!". Murmushi Anty Abeeda tashiga yi mai kama dana rainin hankali, ita dai ba yarinya bace
k'arama, a haife ta haifi A'isha dan haka bazatayi mata wayau ba duk kuwa da tana d'iyar
*ZAMANI* dan haka zata saka ido sosai akansu harsai tagano komi da izinin Allah, da wannan
tunanin tayiwa A'isha godiya ta mik'e ta fice bayan ta kashe mata wutan d'akin.
**************************

K'wance tasame shi haryayi wanka ya kwanta kansa na kallon sama alamar tunani yake,
dasauri ta rungumosa sosai a jikinta tana fad'in dan Allah kayi hakuri ni banaso inji meya
had'aku haka amman koma meye kayi hakuri dan girman Allah kasan halin yaran *ZAMANI* sai
ana kauda kai daga garesu, ba a biye masu saidai mu ringa binsu da addu'a dakuma nasiha!". Bud'e baki yayi daniyyar yin magana dasauri ta maida bakinta cikin nasa taki bashi damar yin
magana, nan tashiga yimasa salo salo tana fad'in,
   _“Oh my dear!_ Bakasan yanda nayi missing dinka ba, _plaese_ kada ka kara mun nisa, idan
baka tare dani ban san yanda rayuwata zata kasance ba.”

  Janyota yayi jikinsa, 

  “Abeeda bakisan irin azabar da nasha ta rashin ki kusa dani na wannan lokacin, sati biyu ne
_but_ jinsa nakeyi kamar shekara biyu.”
"Dan Allah kada ki k'ara yimin laifin dazakisa inyi nisa dake dan Allah".
  Tallabo fuskan ta yayi da hannayensa duka biyu ya fuskanceta, idon sa cikin idonta

  _“I luv u_ Matata!!” 

_“Luv u too”_ abinda ta fada kenan,"

 A ranar dai sun nuna ma juna yanda sukayi kewar junansu, sabida ita kanta Anty Abeedar
saida taji ta gaji a ranan duk da kasancewar ta jaruma a wannan harkar amman saida ta
gaza.............
[9:47PM, 1/29/2018] Maman twins: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)*


*ZAMANI* 1⃣4⃣


*A TRUE LIFE STORY*


*WRITTEN BY*

*FIDDAUSI SODANGI*


*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*
*KHADIJA SIDI*



*WANNAN SHAFIN NAWA SADAUKARWACE GARE KI HAUWA SHEHU (JIDDA ALIYU) KIN
CANCANCI KOWANI IRIN YABO A WAJAN SODANGI, INA SONKI SOSAI INA KUMA
ALFAHARI DAKE, NAGODE DA KAUNAR DAKIKE NUNAWA WANNAN LITTAFI NAWA NA
ZAMANI, INA JIN DADIN YANDA KIKE BIYE DANI KIKE KUMA COMMENT A KOWANI PAGE
INAYINKI SOSAI SOSAI KAWATA ALLAH YABAR KAUNA*




Tundaga wannan ranan A'isha tashiga taitayinta da _uncle_ safana wani irin mugun
tsoronsa take na ban mamaki, shikuwa dokoki ya kafa mata masu yawa acikin gidan sa aciki
harda na rashin fita ko k'ofar gida indai ba makaranta taje ba, gaba d'aya batada sukuni a cikin
gidan abu kad'an zatai ya hantare ta komi fad'a komi tsawa da tsangwama, wannan dalilin yasa
Anty Abeeda watsar da makaman yakin ta dataci alwashin samasu ido tagano abinda ke
gudana a tsakanin su.

************

Cikin takunta ta tak'ama da gadara ta k'araso bakin _office_ d'in k'yawawan yatsun ta tasa
tashiga k'wank'wasa k'ofar, sau uku ta buga daga ciki akace mata "shigo mana".

A hankali ta murd'a hannun k'ofar ta kutsa kai tashiga had'e da sallama da sassanyar muryar
ta,
Gaba d'aya su biyun dake zaune suka amsa mata saidai shi d'ayan inbawai bakin sa ka kalla
ba bazaka gane ya amsa ba.
Kai tsaye ta zauna a kushin d'in dake cikin _office_ d'in ta kame tare da d'aura k'afa d'aya bisa
d'aya, sanye take cikin wata doguwar riga ta kanti wacce tayi bala'in matse ta tamkar tayi nishi
ya yage, kanta wani bakin mayafi ne d'an guntu ta nad'e kan dashi, sai wani uban takalmi mai
bala'in tsini datasaka, fuskar ta taci wata uban kwalliya tamkar wacce zata gidan biki.
" Ina yini Malan?"
"Lahiya kalau A'isha ya karatu?"
"Lahiya kalau Malan wajan ka fa Nazi", tayi maganar tamkar zatai kuka cikin muryar shagwaba.
" To A'isha ina jinki lahiya dai ko?"
K'ara shak'e murya tayi ta mik'e tsaye ta matsa inda yake sai a lokacin sukai ido hud'u da
d'ayan abokinsa dake zaune wanda da alama ziyara yakawo masa, gaban tane yayi wani
mummunar fad'uwa, shi kansa tunsanda tayi sallama yaji muryar ta ya tabbatar da itace saboda
yabawa k'ofar shigowar baya, wani irin muguwar harara ya sakar mata ya d'aure fuska tamau
tare da d'auke kai tamkar bai ganta ba, itama hararar ta watsa masa tare da murgud'a masa
baki a ranta tace maye! Duk inda nayi sai na gansa!
Bata damu da ganin sa datayi a wajan ba cikin k'asa da murya tace "Malan dama zuwa nayi
akan exam's d'inka, wallahi Malan banyi wani abin kirki ba nasani saboda tambayoyin dana zata
basu kayi ba Malan wallahi ka shammace ni shiyasa bansamu na rubuta abin kirki ba, Malan
ina niman taimakon ka banaso in samu c,o a _course_ d'inka wallahi sabida kasan..........." Katseta yayi da fad'in "To A'isha yanzu mekike so inyi maki uhm?"
"Malan kagane mana so nake kayi......."
Karar wayar sa ce ta katseta daga abinda take fad'a, dasauri ya d'auka nan yasa a kunni yayi
d'an magana can yace to ganinan zuwa yanzu ranka ya dad'e, ya kashe wayar ya mik'e ya kalli
abokinsa dake zaune yana ta danna waya yace Aliyu ina zuwa dan Allah, ya rabata ya wuce
batare dayace mata komi ba, bayan sa tabi da kallo can ta koma ta zauna inda ta taso ta bud'e
Jakarta taciro cingum ta bud'e ta jefa biyu a baki tashiga taunawa baka jin komi sai karar
taunawar da takeyi k'as! K'as! K'as!
Hankalin ta kwance take taunar tana hura kwai dashi tana fasawa da hakoran ta.
Gaba d'aya bakincikin ta yagama kashe Aliyu Haydar ji yake tamkar ya shak'e ta, can da abin
ya ishe shi ya mik'e a fusace cikin hargagi yashiga fad'a "Ke banza karya jakka karuwa
dak'ik'iya sakara wacce batasan ciwon kanta ba!".
Wallahi kin rako mata duniya! Sam bakici wannan suna naki ba wallahi, wawuya kawai!".
" kowani jaki da doki da kare da biri duk latsaki suke son ransu suna abinda sukaga dama
dake kaico! kaicon ki wallahi kinyi babban asara a rayuwar ki, wallahi kinyi arha dayawa sam
bakida tsada kin fad'i k'asa warwas!".

A fusace ta mik'e jikin ta har rawa yake ta d'aga hannu da niyyar kai masa mari tuni ya murd'e
hannun nata yasakar mata wani gigitaccan mari dayasata sakin ihu mai k'arfi, cikin tsiwa
tashiga fad'in "banza d'an iska dan uwarka menayi maka ina ruwana dakai dazaka k'wad'a min

wannan shegen hannun naka mai kama ta katako....."
Bakinta yakaima wani wawan duka "uwata kika zaga!?"
"Uwata?"
"Na rantse da Allah saina koya maki hankali saikinyi dakin sani akan wannan furuccin naki
uwata dai ko!?".
"Zaki gane bakida wayau zaki gaya min idan naki uwar.... "
A fusace ta d'auki jakar ta daya fad'i k'asa sai data bud'e k'ofar tasaka k'afar ta d'aya a waje
sannan tace "shege matsiyaci mai shiga shirgin da ba nasa ba, tsinanne mai kama da aljanu
Allah ya Isar min mugu insha Allahu saika hadu da ajalinka a hanya macuci azzalumi
kawai......... [11:41AM, 2/4/2018] Maman twins: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)*


*ZAMANI* 1⃣5⃣


*A TRUE LIFE STORY*


*WRITTEN BY*

*FIDDAUSI SODANGI*


*DEDICATED TO*
*MY MENTOR*
*KHADIJA SIDI*



*INA BAWA DINBIN MASOYANA HAKURI ABISA JINA SHURU DAKUKAYI KWANA BIYU,
HAKAN YA FARU NE SABODA BIKIN KANWATA DA AKEYI AMMAN INSHA ALLAHU
ZAKUCI GABA DAJINA KULLUM DAGA RANAN MONDAY INSHA ALLAHU KAMAR YADDA
AKA SABA*


Da k'arfi ta rufo k'ofar tamkar zata balla, a fusace ya koma ya zauna tare da dafe kai da
duka hannuwan sa, zuciyar sa tamkar zata faso k'irjin sa tafito saboda tsananin bacin rai, yama
rasa irin tunanin dazaiyi, sam yarasa gano irin hukuncin daya dace da ita, shi yarinyar nan
zataiwa wannan rashin mutunci. Tabbas yazamar masa dole ya d'auki mummunar mataki akan ta.
Yana cikin wannan halin ne sai ga abokin nasa yashigo, _sorry_ mutumina na barka kai d'aya

yanata magana yaji yayi masa shuru, candai ya d'ago jajayan idanuwansa ya watsa masa wani
kallo cikin kakkausar murya yace "Fahad itace yarinyar danake gaya maka, ita ce yarinyar da
muke magana akai kace baka gane taba".
" Fahad na tsani yarinyar nan na tsaneta tsana mai tsanani".
Murmushi Malan Fahad yayi yace "Aliyu A'isha tawuce tunanin ka, ta wuce duk yanda kake
tsammanin ta, yarinyar batajin magana sannan kuma baka san wani abu ba, wallahi yarinyar
tana da ilimi fiye da zaton ka, gaba d'aya ko wani bangare Allah yabata kaga tanada ilimin
addini sosai tanada sani yarinyar sosai halaiyan tane kawai sai a hankali, amman Aliyu mezai
hana ka nimi soyayyar ta Ku dai daita?"
Wani mugun kallo Aliyu yayi masa yace "kaifa dama baka da hankali ince maka na tsaneta
tsana mai tsanani sannan kake min wannan maganar banzar kasan abinda yarinyar nan tayi
min kuwa yau?"
"Uwata fa ta zaga wallahi yarinyar nan saita raina kanta na rantse da Allah saita gane bata da
wayau wallahi sainayi mata fata-fata dan uban......."
Wani mugun dariya Malan Fahad yayi yace "Aliyu fata-fatan me kake tunanin zakai mata
yarinyar da tariga tasaba da..."
"Hmm Fahad ka manta da waye Aliyu Haydar inaga shiyasa kake fad'in haka.

*******************

K'arfe shida dai-dai suka fito lectures sauri kawai take ta isa gida dan taji alamar zuwan
_period_ d'inta, gudu take tayi a motar gashi taci sa'a titin babu kowa saboda ta baya ne,
Kuuuuuuu!!!!!!!!!!!!! Taja wani wawan burki saboda wata motar datasha gaban ta sai walainiya
takeyi gata bak'a wuluk mai ban sha'awa, kiris yarage ta buga masa, tsorone karara a fuskarta,
k'am ta k'ame tare da rik'e numfashin ta k'am, sassanyar ajiyar zuciya ta sauke a lokacin dataji
motar ta tsaya cak. Lokaci d'aya suka fito daga motar kuwanne fuskarsa sanye da safar fuska, sanye suke da
k'ananan kaya kai tsaye motar da take ciki suka dinfaro, zuciyar tace tayi mummunar bugawa
tare da tsayuwar lumfashin ta lokaci d'aya, nanfa jikinta ya d'auke rawa dan kuwa duk iskancin
ta tana da bala'in tsoro. D'ayan ne ya bud'e gaban motar ya fisgo ta yayinda d'ayan ya shiga yaja motar yabar wajan,
Dak'arfi ya tura ta cikin motar ya rufe ya zagaya yashiga ya rufe,
Da k'arfi ya fisgi motar yabar wajan sai ihu takeyi tana bubbuga _glass_ d'in motor, da
hannayan ta sai dai duk a banza takeyi domin kuwa motar yaci tint baki wuluk.
Wani wawan ihu yayi mata wanda yasa tayin tsit tamkar ruwa yacita, a haka har suka isa inda
zaikai ta bancin sunyi tafiya mai nisan gaske.

A dai-dai wani tafkeken gida ya tsaya mai gadi ya wangale masa _gate_ yashiga da motar
wajan aje motoci ya paka yafito cike da gadara hankalin sa kwance
ya bude k’ofar motar tare da fadin fito! Cikin daure fuska, a rikice A'isha ke dubansa,
tsawa yakuma daka mata "bazaki fito ba saina sabeki a wuya na!?".
Dasauri ta sauko tana raba ido, hannunta ya jawo da k'arfi har zuwa cikin gidan, a palon gidan
ya wurga ta sannan yakoma ya rufe kofar harda saka _key,_ nan fa A'isha tashiga cikin

tsananin rudani hankalinta ba karamin tashi yayi ba ganin palon dawani irin duhu sosai, ”
hijjabin jikinta ya fisge yai wurgi dashi lokaci d'aya kuma yacire safar dake fuskar sa, ido ya kafa
mata yanai mata wani irin wulak'antaccan kallo,
Hantar cikin tane ya wani karta tare da curewar yan hanji waje d'aya, tsoro mai tsanani
yakamata cikin rud'ani tashiga fad'in
"wayyo Allah na nashiga uku na dan girman Allah kayi hakuri menayi maka Aliyu?”

"Au! Bama kisan mekikayi min ba saboda kin dauke ni takkwali ko!?"
"Me har kin isa kiyimin rashin mutunci uwata zaki bud'e k'azamin bakin ki kizaga dan rashin
mutunci ko!?".
To yau zanyi maganin iskancin ki karamar y'ar iska kawai!".
Yau zan dasa maki wani miki a zuciyar ki wanda zaki ringa yawan

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login