Showing 36001 words to 39000 words out of 56306 words

Chapter 13 - ZAMANI (1 to end) Book Complete by Fiddausi Sodangi .pdf

03 Oct 2025

1687

ince kai tsaya za a kirasa da jini.
A hankali tashiga takawa har ta isa jikin lokar dake cikin d'akin, cikin rawar hannu ta bud'e
lokar, tsananin ratsana datayi ne yasata kurma ihu had'e da fad'in
"Inna!!",
Wani irin tsawa mai k'arfi taji daga tsakiyar kanta ana fad'in " fita! Fita! Fita! Karkiji karki gani
kar kwakwalwarki tasake aiki kizamana dake da babu duk d'aya har k'arshan rayuwar ki fita!!!!".

A firgice tabar d'akin gaba d'aya ta fice a haiyyacinta sai shashek'a takeyi kamar wacce tayi
gudun fanfalaki, a lokaci d'aya kuma taji wani dummmm a kunnuwan ta gaba d'aya jinta ya
d'auke, haka kuma wani irin bala'in duhu ya mamayewa ganin ta d'if ganin ta ya d'auke kwata

kwata, haka kwakwalwarta ta tsaya cak bata iya tuna komi bare tayi tunanin wani abin.

dakansa k'ofar d'akin data baro ya koma ya rufe ruf kamar ma ba a taba bud'e shiba.


*******************************

Y'an sanda suncigaba da binciken su harzuwa washe gari inda labarin kisar gillar da akaiwa su
_uncle_ Safana da matarsa da maigadin sa da mak'ocin sa ya zagaye ko ina a fad'in kasar nan,
a ranan iyayan matan dana mijin suka iso inda gidan ke a cike babu masaka tsinke, sai a
lokacin ne aka ankare da ba aga Aysha bafa, nan jami'an tsaron suka shiga bincike sosai sosai
a cikin gidan nan suka samo Aysha a cikin kwandon wanki babu rai a tare da ita gaba d'aya ta
sandare haka aka kinkimeta zuwa asibiti.

**************************

Wayar ce ta subuce a hannun Hajiya Amina ta tarwatse a k'asa.......
Salati ta keyi tana k'arawa duk ta gigice, sai juya Kai take tana tafa hannuwa, "Ni Amina wani
irin abu ne haka nake shirin ji," sambatu kawai take tana zagaye palon tuni d'an kwalinta ya fita
daga kanta amman sam bata shi take ba.

Sam dama batada natsuwa a kwanakin nan, kullum mafarki takeyi da d'iyar tata masu muni
tayiwa uban magana yafi a kirga amma sai ya hauta da fad'a yana fad'in ai a gidan aminin sa
take ba a wani waje ba shiyasan Safana zai rik'e ta da gaskiya tamkar tana gabansu ne.

Yaya Abba kuwa dake tare da mahaifiyar tasu k'okarin had'a wayar yakeyi wanda ya tarwatse
a k'asa, hannunsa sa rawa yake dak'yar yasamu ya isa _recieved calls_ ya kira _last call._ duk
da yaga sunan Abban sune bai hanasa tsinkewar zuciya ba.

Abinda Abban ya sanar da Umman tasu shiya k'ara sanar masa,
Nan hantar cikin sa ta cure gu guda wani irin zufa tashiga keto masa ta ko ina hangin cikin sa
ya hautsina nan yadafe ciki yayi k'asa yana kiran sunan Allah.

Cikin kankanin lokaci uban ya iso
Atake suka d'auki hanyar zuwa Katsina wani irin tuki Ya Abba yake yi wanda Allah ne kawai
ya kaisu lahiya, a take sukaiwa gidan uncle Safana tsinke inda suka tadda jama'a dankare a
gidan duk da cewar cikin dare suka iso, Abban su Aysha yayi kuka sosai na rashin aminin nasa
inda aka bashi takardar da aminin nasa yabari, saboda sunan sane a jiki.
Bayan sungama yiwa iyayan mamatan ta'aziyya ne sukaiwa asibitin tsinke, a take kwamishinan
yansanda yayi masu jagora harzuwa _mutuary_ saboda har yanzu ba a bada gawarwakin ba
anaci gaba da bincike.

Allah mai girma da babu kamar sa, kunfa yakun ne wanda yayi alkawarin "Kullu nafsin
za'ikatul Maut!!"
_uncle_ Safana kwance sambal tamkar akira sa ya amsa sai Anty Abida da maigadi tareda
mak'ocin nasu suma dai hakan ne,

Kwamishinan yan sandan ne yakara da fadin "Ita yarinyar akwai _hope_ na samuwar ta,
saidai tana cikin mawuyacin hali saboda ta kwana ta wuni acikin kaya babu iskar dake shiganta.

Likitoci dai sunata iyakar k'okarin su wajan ganin ta farfad'o.

Tuni Hajiya Amina ta sulale ta zube a k'asa inda itama aka d'auke ta aka shiga bata
taimakon gaggawa,
Cikin k'arfin hali da dakewar zuciya Ya Abba yashiga niman layin abokin sa Aliyu wanda yake
nan Katsina yana aiki yaje bikinsa dai kwanaki a Abuja.

Aliyu wanda tun safe yake jin faduwar gaba tamkar k'irjinsa zai sauko k'asa ko aiki bai iya fita
ba tun jiya da Aysha ta d'aga wayar Ammin sa yakejin wani irin bacin rai haka ya kasance suku
suku har zuwa yanzu da wayar sa ke kuka.

Cikin sanyi jiki ya d'auka yasa a kunnin sa yana fad'in "zaki zaki zaki".
" Shege kayi shuru kwana biyu ba a jinka tun biki",

Muryar Ya Abba a sanyaye yace "abokina ina Katsina fa".

Wani ihu Aliyu yayi ya mik'e zaune daga kwance dayake, " zaki bakada mutunci fa mekazo yi
Katsina baka nimeni ba sai yanzu da dare haka?".

"Aliyu kasan nagaya maka akwai k'anwata dake karatu a nan Katsina tana wajan abokin baban
mu, to wlh jiya da dare barayi suka shiga gidansa sukai masu kisan gilla harda mak'ocin sa, da
maigadin sa, to ita k'anwar tawa boyewa tayi basu ganta ba harta kwana ta wuni acikin
kwandon wanki to yanzu dai tana asibiti cikin mawuyacin hali gamu nan bamu samu ganin
tabama, gashi itama Umman mu ta yanke jiki ta fadi itama an kwantar da ita abindai babu dadi".

"Subhanalillah....."
"Wallahi Sam bansamu wannan labarin ba dayake tunjiya wayoyina ke a kashe ko aiki banfita
ba yau wallahi shiyasa banjiba, wani asibiti ne in iskoku?"

Nan yagaya masa a gigice yataho asibitin.

Gaban Aliyu ne yayi mummunar fad'uwa sanda yayi arba da baban abokin nasa *Dr Yusuf
Gidado* mutumin da bazai taba mancewa ba a tarihin rayuwar sa lallai wannan shine dara taci
gida! Ga koshi ga kwanan yunwa!

*************

Kafin kace me, tuni asibitin ya cika fam da al'umma ciki da waje, jami'an tsaro ta ko ina
kasancewar mai girma gwamnan Katsina ya dad'e da k'arasowa dan ganin mamatan da kuma
ita kanta Ayshan.

Cikin kankanin lokaci mutuwar _Uncle_ Safana da matarsa tareda makocin sa da maigadin
sa ya zagaye kafafen yad'a labarai, da lungu da kowani sako na gida _Nigeria_


*WASHEGARI*

Mai girma gwamnan Katsina yasa an bada gawarwakin inda aka nufi gidan _uncle_ Safana
aka had'ashi da matar sa, yawan d'inbin jama'ar dasuka halarci jana'izar bazasu lissafuba.

Zaman makoki aka shiga yi,
K'usoshin k'asar nan ciki da bai duk sun samu halar ta, har akai kwana uku.

Sai a yau Aliyu yasamu zuwa gidan yasha mamaki dayaga gidan su Aysha ne kansa ne yayi
bala'in kullewa atake yashiga niman layinta saidai baya shiga, atake yasoma fad'in Aysha Yusuf
Gidado, Yusuf Yusuf Gidado, Dr Yusuf Gidado!

**********************

Harzuwa wannan lokacin Aysha bata farfado ba,
Ranan da akai sadakar bakwai aka sallamo Hajiya Amina wacce jininta yayi bala'in hawa,
daga asibiti takasance bata uhm bata um um, ido kawai take bin kowa dashi, daga k'arshe ne
tace akai ta taga halin da d'iyar ta take ciki,
Lokacin da suka isa tuni numfashin ta ya daidai ta, an cire _oxygen_an bata d'aki a _aminity_.
Tuni Hajiya Amina tasanya kuka dan ganin halin da Aysha ke a ciki, ga karin ruwa dana jini,
da gudu ta fice tana kuka sosai, shi kansa Ya Abba kuka yake banda Aliyu da zuciyar sa ta
dake jikinsa sai rawa yake ganin Ayshan sa a wannan hali.


********************

*BAYAN WATA DAYA*

Jikin Aysha kullum jiya iyau wannan dalili yasa Aliyu yanke shawarar fidda ta waje, nan yayi
magana da likitocin nata, suka shirya takardun komi, ya hada _passport_ din Hajiya Amina
dana Ya Abba wanda yace zashi shima yanadai ta mamakin yanda Aliyu ya tsaya sosai a
lamarin ciwon nan na Aysha.

Haka sukai sallama da kowa ranan wata Alhamis suka d'aga Amurka.
Sun sauka a birnin _New York_ jirgi ya huta, sannan suka d'aga _Los Angeles_ a yammacin
ranan juma'a.
Lafiya suka sauka a babban _airport_ d'in _Los Angeles_ .

Motocine suka zo suka d'auke su, wanda tuni Aliyu yagama tsara komi.
Tun a cikin _airport_ din _Ambulance_ yazo daga wani bababn asibitin k'asar aka d'auki
Aysha aka wuce da ita.

Kulawa sosai take samu daga kwararrun likitocin nata masu jajayan kunnuwa, a hankali sauki
yake samuwa a gare ta.


***************************

*BAYAN WATA UKU*

Tuni Aysha taji sauki jiki ya warware sai dai muce Alhamdulillah.
Nan ta soma rigimar su koma gida haka nan itakam tagaji da zaman asibitin tunda tasamu
lahiya,
Nan likitocin suka dage kancewa sallama sainan da wata biyu sun tabbatar ta warke sarai
sannan subata sallama.
Tuni Aliyu da Yaya Abba sun dade da juyawa saidai duk wata yake zuwa dubasu, kira kuwa
saiyayita takai sau goma a rana, bama kamar yanzu data warke sumul hardai Hajiya Amina ta
tsare ta da tambayar meye alakar ta da Aliyu ne.........
[4:09PM, 2/28/2018] Maman twins💞: *NAGARTA WRITERS ASSOCIATION*


*ZAMANI* 3⃣8⃣



*A TRUE LIFE STORY*


*WRITTEN BY*

*FIDDAUSI SODANGI*



*DEDICATED TO*

*MY MENTOR*




*WANNAN SHAFIN NAWA NAKI NE UWAR D'AKIN SODANGI, KHADIJA SIDI, INA ALFAHARI
DAKE AKODA YAUSHE UBANGIJI ALLAH YABAR KAUNA YAKARA TSARE MINKE
MAKIYANKI TAKALMINKI..........*



"Umma wallahi babu komi ni dai baitaba cemin komi ba gaskiya".
Jinta kawai uwar tayi amman bawai dan ta yarda da abinda tace d'inba.

Hakadai abin yaci gaba da kasancewa har zuwa lokacin da likitocin suka ga ya dace su
sallameta,
Wannan karan ma Aliyu ne yazo da kansa yayi masu cuku cuku suka koma _Nigeria_ murna a
gun Aysha ba a cewa komi saidai data tuna dasu _uncle_ Safana saitasha kuka tamkar zata
shid'e da kyar ake iya rarrashin ta.

A yola suka sauka kai tsaye inda Aliyu ya wuce Abuja kai tsaye batare daya bari sun had'e da
mahaifin Aysha ba tun wancan had'uwar dasukai dama suka shaida juna shidai Dr Yusuf kawai
kallon Aliyun yake da duk wata hidima dayakeyi a matsayin sa na abokin d'an nasa saidai daga
baya sarai ya fahimci dan Ayshan takeyin komi.
************************

"Dan uban ka ni zaka maida mutumin banza?"
"In rabaka da yarinyar amman dan baka d'aukeni a bakin komi ba shine ka fitar da ita waje ita
da iyayan ta saboda bata lahiya ga kannan uwar ka ko?"
Duk wata sai ka niki gari ka tafi yimasu bauta to wallahi tallahi ka kiyaye ni Aliyu wallahi ka
kiyaye ranar dazaka kaini mak'ura shashasha kawai ka uwar kanan batada lahiya tsawon
watannin daka d'auka kana bautawa wasu shegu, baka taba tunanin fita da uwar kaba saiwata
karuwa! Mutumin banza da wofi!".
Fad'an k'arfin hali tundaga ranan da abin nan yasami Ammi har yau d'innan babu wanda yataba
iya bud'e baki yace wani abu game da ciwon ta babu wanda yakuma maganar ta tundaga
y'ayan ta har kowa da kowa ma bakin kowa a rufe yake ruf hatta auta datake cikin gidan
batasan a wani hali uwar ke ciki ba tana d'akin ta a kulle duk safiya shike shiga ya bata abinci a
baki ya kalleta yayi dariya yace uban dayasaki kiyi min bincike gashi nan ai kingano abinda zai
kasheki har lahira, haka zai fice ya rufeta sai kuma da daddare zaishigo ya bata abincin dare
yafice, rayuwar ta tazama abin tausayi kwarai da gaske idan mutum yaganta saiyayi mata kuka
ta fige ta lalace ta fita haiyyacinta, bazaka ganta kace itace hajiyar nan ba maishanawa uwarsu

Aliyu ba, sam kamannin ta duk ya canza tayi bakikkirin gwanin tausayi.

**************

Aysha ce keta shiri zata koma makaranta dan hutun da a ka je yakare tun wancan satin zataje
ayi mata tata jarabawar wanda akai bata nan tunda mai girma gwamnan Katsina yasa baki a
lamarin nata.

inda Yaya Abba yasa Aliyu yagama yi mata komi na cuku cukun hostel a can zata ci gaba harta
k'are.

Haka uwar da y'ar suka rabu cike da begen juna duk da bawani jituwa sukeba dama tun asali,
uban kuwa nasiha sosai yayi mata daga k'arshe yayi mata fad'a sosai tare da jan kunni mai
tsanani.

siyayya sosai Yaya Abba yayi mata a hanya kayan k'walama kala-kala sai ci take suna hira
abinsu a haka har suka isa garin Katsina bancin sun d'auki awowi masu yawa bisa hanya.
Kai tsaye jami'ar Umaru Musa Yar'adua University ya nufa da ita har bakin hostel din yakaita
sukai sallama yace mata zashi ya kwana gidan Aliyu da asuba zai dauki hanyar yola, nan sukai
sallama ya wuce itakuma tashige.


*********************

*WASHEGARI*


Aysha ce ta shirya cikin shiga ta alfarma kai tsaye gidan Aliyu tayiwa tsinke kasancewar yau
asabar tanada tabbacin cewa yana gida, ko wayar sa bata kira ba dan so take tayi masa zuwan
bazata taga wace wainar suke toyawa shida matar tasa tunda bata kusa tsawon watanni biyar
kuma tasan halin Aliyu sarai da jarabar tsiya bai iya kawar da kai tsawon wannan lokaci mai
tsawo.


Matar gidan ce a hakimce cikin d'aya daga cikin kujerun dake palon, tana wani taunar
cingum ta daura k’afa daya bisa daya tana kallon TV, da alama hankalin ta ya dauku bisa kallon,
kallo d'aya zakai mata ka tabbatar jindadi da hutu sun samu waje a gun, k'yakkyawa ce ajin
k'arshe irin matan nan ne dasuka amsa sunan su na mata, sanye take da doguwar riga ta leshi
wacce ta dace da kalar jikinta tayi wani irin d'auri irin na yan matan *zamani* tasha k'walliya
kamar wacce zata gasar kwalliya,

Kallo d'aya mai gadin Aliyu yayiwa Aysha a zuciyar sa yace "to wannan mara kunyar yarinyar ta
dawo kenan, kwana da yawa mun huta daganin fitsara".

Aliyu ne yafito daga d'aki daga shi sai gajeren wando da riga mara hannu sai wani shan k'amshi
yakeyi yanawani cika yana batsewa dan bakin hali.

da gudu- gudu sauri_sauri Aisha ta taho tayi masa wata wawuyar runguma tana basa kiss a
kuncinsa tare da fadin _i miss u sweetheart_

K’ara kankameta yayi yana fadin Aysha ta nima wallahi sunan ina Katsina ne kawai amman
gaba d'aya hankalina yana wajan ki,

turo baki tayi tana cusa kanta acikin k’irjinsa.
d'ago kanta yayi ya hade bakinsu waje daya yana tsotsa gaba dayansu sun wani lumshe ido
suna jin dadin sak’onnin dasuke aikama juna k’afafuwansu ne suke niman su gagaresu tsayuwa
hakan ne yasashi sunkutar ta zuwa dakin baccin sa gaba d'aya ya manta dawata Ramlat dake
palon ma. Ita kanta Aisha sam bata lura da ita ba tanata hidimar gadanga kusar yaki idanuwanta sun
rufe.


Ramlat dake zaune tamkar wata gunki ko ince tamkar wacce aka dasata ta fashe da kuka
wannan wani irin abu ne haka Aliyu yakeyi akan karuwa ya maidata tamkar wata matarsa sam
bayajin kunyar uban kowa akan waccen kilakin, wani irin rayuwace wannan ba a d'auki zina a
bakin komi ba, idan ita bayajin kunyar ta da shakkar ta ai yakamata yaji tsoron ubangijin sa,
watan nin da Aysha ta dauka bata nan tasamu kwanciyar hankali duk dadai bata gaban Aliyu
din amman hankalin ta yana a kwance ba kamar sanda Ayshan kenan ba, to gashi ta dawo
itakam sam bazata iya zama da fasiki ba sam dolen sama ya sauwake mata takara gaba
abinta.

Wani irin bakinciki takeji harcikin zuciyar ta, ita kanta batasan meyasa take jin hakan
ba.

Wallahi itakam bazata zauna ba tafiyar ta zatayi Abuja ta koma wajan iyayan ta, takarawa kukan
ta sauti.

Shi kuwa _Aliyu_ yana d’ire Ayshan sa bisa gado yashiga sarrafata son ransa tanata taimaka
masa sosai ya gigice ya d'imauce, sai ihun dadi yake mata yana sambata.

Saida suka dirji juna son ransu suka fanshe watannin dasukayi basu tare sannan suka hakura
da kyar tamkar zasu cinye junan su.


Ramlat kuwa baiwar Allah taci kukan ta harta gaji ta bingire a wajan bisa kujera tawani takure

waje d'aya alamar sanyin ac din yayi mata yawa.


Haka su Aliyu suka sameta sunyi wanka sun canza kaya sai kyalli sukeyi saikace wasu
ma'aurata.

a haka suka same ta a palon dunkule tana baccin ta sai ajiyar zuciya take alamar taci kuka ta
gaji, da sauri ya k'arasa ya d'aka mata duka a k'afa

"Ke! Ke! Ke!".

A hankali ta bud'e k'yawawan idanuwanta ta sauke su acikin nasa, bata rai tayi ta tsuke fuska
daga k'arshe ta fashe da kuka tana fad'in wallahi Aliyu ka sauwake mani auran ka ka sallame ni
in koma gidan mu nafasa zama dakai dama ai bani na zabarwa kaina ba to banyi nafasa zama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login