Showing 54001 words to 56306 words out of 56306 words

Chapter 19 - ZAMANI (1 to end) Book Complete by Fiddausi Sodangi .pdf

03 Oct 2025

1686

tace mata tana son tayi mata wata _personal_ tambaya
akanta, mijinta da kuma abokiyar zamanta,

Cikin murmushi Malama Zainab tace "to Aysha da farko dai zanso
Kibani labarin ku, saboda zanfi gane irin hukuncin da ya kamaceku.

" To Malama Zainab indan wannan ai babu damuwa ki kwatanta mani gidan ki sai inzo insameki
a gida inaga zaifi sirri sosai".


Nan Malama Zainab ta ba Aysher _address_ din gidanta da zummar su hadu ranar alhamis
saboda babu islamiyya a ranar,


Haka Malama Zainab ta rage ma Aysha hanya cikin motarta, ta sauketa har gida ita kuma ta

wuce.

* * * * * * * * *

Ranar alhamis Aysher ta shirya taje gidan Malama Zainab, inda ta tarbe ta da arziki da mutunci,

Nan Aysha ta shagalta da wasa da khaleel karamin yaron Malama Zainab,

Ita kuma Malama Zainab, na koya ma Sultan babban yaronta _home work_.
Suna nan zaune aka kira sallar la'asar,
bayan sunyi sallar la'asar ne Aysher ta fara labarta ma Malama Zainab labarin rayuwarsu kaf
babu abinda ta boye mata, ta kuma nemi da tayi mata bayanin *hukincin aurensu a musulunci*,

Takara dacewa "Malama *idan yanzu na tuba Allah zai yafe mani?*".

"sannan ya *makomar aurena da Aliyu yake a musulunci?*, "

*"ya makomar auren Aliyu da saadiyya yake a musulunci?*,"

" *xan iya cigaba da zama da Aliyu a karkashin inuwar aure??"*

" Wadan nan sune tambayoyina Malama."

Tunda ta fara magana Malama ke zambada kwalla har ta kai karshe.

Malama ta gyara zaman gilashinta tace "wato Aysher rabona da jin labari mai tada hankali da
Sosa zuciya tun kan labarin *Mugun Makoci* da naba Fiddausi Sodangi labari don ta rubuta
al-ummarmu su hankalta su kuma amfana sai yau da naci karo da wannan mummunan labari
naku mai hade da dabaibayi."

"Bari In baki amsoshin tambayoyinki a takaice saboda lokaci ya kure Magrib nata gabatowa,"
"amma Tunda kina zuwa islamiyya Alhamdulillahi,"
"a hankali zaki dinga jin wasu hukunce hukuncen da suka shige maki duhu."

"Fadar Allah gaskia ne akan mazinata gashi nan ta tabbata a kanku".
*"Allah SWT a cikin Al-Qur'ani mai girma yace*
*Mazinaci namiji baya aure sai mazinaciya mace ko mushrika( mai hada bautar Allah data wani)
haka kuma mazinaciya mace bata aure sai mazinaci namiji ko mushiriki,an haramta hakan ga
mummunai.*

( _sai Wanda kaddara ta fada mawa don ubangiji ya jarraba imaninshi Allah ya rabamu da
mummunar kaddara_)

Kinga kenan Allah ya hadaku duka mazinata a gidan aure.".


"Zina bala'ee ce, zina masifa ce
*Annabin Rahma a cikin hadith sahih yace yan'wuta a ranar kiyama zasu ji wani mummunan
wari mai tada hankali, idan sun tambayi warin miye ubangiji na basu amsa da warin farjin
mazinata ne*".

"Wa'iyazu bil lah
Allah yayi mana tsari Ameen".

"Hukuncin aurenki a musulunci

Aurenki yana nan da Aliyu saboda lokacin kinyi *istibra'ee* _(jini ukku mace zatayi idan tana
*istibra'ee* tsarki ne mace keyi idan tayi bariki ko ta tara da wani namiji Wanda ba mijinta ba
kafin ayi aure)_
Kince kinyi istibra'ee kinga aurenki da Aliyu yana nan saboda kin tsarkake kanki kafin ki shiga
gidanshi".

"Don haka zaki Iya cigaba da zama da Aliyu a karkashin inuwar aure".

"Aysher ki sani Allah ubangiji SWT ya fada a cikin al-Qur'ani mai girma cewa *shi mai gafara ne
mai jin kai*
Sannan yace *baya yafe ma Wanda yayi shirka amma yana yafe zunubi wanin hakan ga Wanda
yaso*_(Wanda ya tuba ya nemi gafararshi)_
Haka kuma ya fada a cikin wata ayar cewa *duk wanda ya tuba yayi aiki nagari, Allah yana yafe
mai,ya kankare mai zunnubanshi Sannan ya musanyasu da lada*".

*"Annabin Rahma SAW yace idan bawa ya tuba ya nemi gafarar ubangiji Allah yana yafe mai
zunubbanshi koda sun kai yawan kumfar teku*".

"Don haka ina son ki sani Allah ubangiji zai yafe maki zunubbanki idan dai har kinyi tubar
gaskiya kamar yarda Malam mai ahdhari yayi mana bayani
*" yin nadama abisa Abunda ya wuce idan dai mutum ba zai koma ma zunubi ba na cikin abinda
yayi saura na rayuwarshi"*

"Ki yawaita istigfari, haila, hamdala kina azumi, sallar dare ki roki gafara kina mai kaskantar da
kanki a wajenshi, ki dinga ma ubangiji kirari da kyawawan sunayenshi wajen neman gafararshi,
Allah zai yafe maki idan dai har tubar gaskia kikayi Sannan zaki samu natsuwa da sukuni a
rayuwarki gaba daya."

"Auren Aliyu da Saadiyya ya haramta kamar yarda na Ramlat ya haramta saboda sun tara da
mahaifinshi dole Aliyu ya saki Saadiya kamar yarda ya saki Ramlat saboda babu aure har

abada a tsakaninsu,
tarawar da mahaifinshi yayi dasu ya haramta mai zama dasu kamar yarda hukuncin yazo a cikin
fiqhu."


" Zan baki husnul muslimina sannan kiyi downloading dinshi a cikin wayarki, zaki dinga samun
addu'a masu kyau wadanda zasu taimaka maki wajen kyautata tubarki".

"Sannan shawarar da zan baki shine kiyi ma mijinki wa'azi ya dawo hanyar gaskia shima, ya
tuba ga Allah ya dena aikata zina da sauran zunubbai ko kun samu dacewa ranar alqiyama,"

" Sannan akwai majalisu da dama na maza da zai Iya zuwa don neman ilmin lahira, yadda
kukayi dashi idan ya amince sai in hadashi da mijina ya kaishi nasu majalisin yayi register.
Allah yasa mu dace Ameen".


"Sannan ki tabbata kin nemi gafarar Ramlat saboda Allah baya yafe hakkin wata rai a kan wata
Sannan ki yawaita yima su uncle safana addu'a ko Allah zai sadasu da ramarsa."

"Aysher ki sani cewa *Ubangiji da kanshi ya fada Aikin bawa baya shigar dashi aljannah sai dai
rahamar ubangiji*, ki dage wajen aikin kwarai da neman rahamar ubangiji kinji?".

"Allah ya sadamu da rahamarsa
Dukkan abinda baki gane ba sai ki tambayeni idan kuma yafi karfina sai mu tambaya a wajen
na gaba, kinsan ilmi kogi ne musamman na addini."

"Kina iya tafiya gida ko insa direba ya maidake?".

"Tunda Magrib ta gabato sosai ko ki bari kiyi Magrib sai a maidake".


Nan dai Aysha tayi sallar Magrib taci abincin dare, sannan Malama Zainab taba driver motarta
ya maida Aysher gida duk da ba wani nisan duniya bane a tsakaninsu.

Tunda gate ta hango Aliyu yakasa ya tsare yana jiran dawowar ta dan yana hankalce da ita,
yasani tanafita kullum sai shida take dawowa banda bokon datake zuwa amman baisan ina ne
takezuwa ba yaugashi har ana niman takwas na dare bata dawoba.

Gaban Aysha ne ya yanke ya fad'i harsai data rik'e k'irjinta da duka hannuwan ta a zuciyar ta
tana fad'in "nashiga uku ni Aysha mezancewa Aliyu yau na bani!".

Tunkan takarasa fitowa daga motar ya nufo su gadan gadan, da sauri ta fito a motar tayiwa
direban godiya cikin rawar murya.

" Daga gidan ubanwa kike a yanzu?"

"Da izinin ubanwa kike fitama kullum?"

"Dake nake daga gidan ubanwa kike nace!?".

Jikin Aysha inbanda rawa babu abinda yake cikin rawar murya tace "Aliyu mushiga daga ciki
inmaka bayani dan Allah".

" bana sonji Aysha bana sonji".

"Mezaki gaya mani?"

"Kina da abinda zaki gaya mani ne dayawuce kice kintafi yawon kwartanci kintafi aikata zina da
aure na?"

"Inace abinda kuka sa a gaba kenan ko akwai wani abu ne bayan hakan uhm?"

"Aliyu! Aliyu! Aliyu! Wallahi bahaka bane......".

Wani mugun tsaki yaja idanuwansa cike da hawaye ya wuce yabarta anan tsaye cikin mutuwar
jiki.

*********************


Haka rayuwar su yaci gaba da kasancewa a kullum gidan yazama kamar gidan makoki a
hankali cikin siyasa Aysher ta fara ma Aliyu text na wa'azin da taji wajen Malama Zainab tana
tunatar dashi lahira.

Tun baya damuwa da abin hardai yasoma karantawa nan fa wani irin tsoron Allah ya shige shi a
hankali
ya fara kulata yana maida mata amsa rannan dai yace ta bari ya gama abinda yake ya dawo
zasuyi magana ta fahimta.


Bayan Aliyu ya dawo Aysher ta zauna ta Kara fahimtar dashi mahimmancin tuba da kuma ya
kamata su aje komai gefe su raya gidan aurensu.


Daga nan Aliyu ya shiga majalisi, ya koma mutumin kirki kullum cikin neman yafiyar ubangiji
yake.

Nan ya d'auki Aysha sukaje har garin Abuja suka nimi gafarar Ramlat inda tace tayafe masu
harga Allah suka dawo katsina cike da farinciki,

Aliyu ya saki Sadiya ta tattara ta koma gidan su yanzu gida na Aysha da Aliyun tane kawai.

******************
Aysher ta gama karatun ta na boko a wannan shekarar taci gaba da zuwa islamiyyar ta babu
fashi har suka shaku sosai da Malama Zainab.

Da taimakon Aysher da Malama Zainab mahaifiyar Aliyu ta samu lahiya saboda gun manyan
malaman ahlus sunna suke kaita har Allah yasa aka dace.

A ranan data warke tas A ranar ne kuma suka samu labarin gobarar da ta tashi gidan Abban
Aliyu wanda komi ya kone kurumus aciki kuwa harda Abban Aliyu, basu wani girgiza ba haka
dai suka nufi garin Abuja tsawon kwana bakwai nan Aliyu yakuma tarkato iyalan sa suka dawo
garin Katsina.
********************


Aliyu ya gina ma mahaifiyar sa tangamemen gida anan katsina kusa dasu, nan taci gaba da
zama abinta ita da autar ta Fatima.

Aysha tayi tayi Aliyu yafada mata meyasa ya kullaci mahaifin ta amman yaki yace yariga ya
wuce har abada abinda ya wuce kuwa babu kyau anata tono shi musamman ma tunda
yakasance ba abu bane mai kyau, sai a wannan lokacin Aysha ta dauko tsohowar takardar da
baban ta yabata a ranan auranta da Aliyu wanda uncle Safana yabari a ranar da za a kashe shi,
uncle Safana ya baiyyanawa mahaifin Aysha abinda yaringa yiwa d'iyar tasa ne wanda daga
k'arshe yanimi gafarar sa yakuma ce yanima masa gafara a wajan Aysha itama, tana kuka tana
fadin nayafe maka uncle Safana wallahi nayafe maka duniy da lahira Allah yahada mu a aljanna
Firdausi......


*ALHAMDULILLAH*
*ALHAMDULILLAH*
*ALHAMDULILLAH*

*ALLAH NAGODE MAKA DAKA BANI IKON KAMMALA LITTAFIN NAN LAFIYA, KUSKURAN
DANA AIKATA ACIKI UBANGIJI ALLAH KA GAFARTA MANI, INDA NAYI DAIDAI KUMA
ALLAH KABANI LADAR SHI,*

***********

*HAKIKA LABARIN DAKE CIKIN WANNAN LITTAFI NAWA YAFARU DA GASKE A ZAHIRI,
ABUBUWAN DANA KARA ACIKI BAMASU YAWA BANE SABODA LABARIN YAKARA
ARMASHI*

*********

*INA GODIYA GA DUKKAN MASOYANA MASU BIBIYAR LITTAFINA AKODA YAUSHE*

*******

*SADAUKARWA*

*WANNAN LITTAFIN GABA DAYAN SHI SADAUKARWACE GARE KI KHADIJA SIDI, (SALMA
ATIKU) HAKIKA INA ALFAHARI DAKE AKODA YAUSHE KINRIGA KINZAMA JININ JIKINA,
ALLAH YAKARA MAKI LAHIYA DA DAUKAKA, ALLAH YAKARA TSARE MIN KE YARABAKI
DA SHARRIN MUTUM DA ALJAN, INAYI MAKI FATAN ALKAIRI A RAYUWAR KI AKODA
YAUSHE*

********


*JINJINAR BAN GIRMA DA KARRAMAWA*

*NAKINE KAUSAR M HASSAN (KAUSAR LUV) DOLENI IN JINJINA MAKI INMAKI GODIYA
KWARAI DA GASKE ABISA NAMIJIN KOKARIN DAKIKAYI WAJAN RUBUTA WANNAN
LITTAFI NA ZAMANI, HAKIKA KAUSAR BAKI BAZAI IYA BAIYYANA ADADIN GODIYA
AGAREKI BA, INA KAUNAR KI KAUSAR HAR A ZUCIYA TA, UBANGIJI ALLAH YAKARA
DANKON SOYAYYA TSAKANIN KI DA ALIYU YA KAUDA IDON MAKIYA AKANKU YAKARA
MAKI LAHIYA DA ZAMA LAHIYA YA KARA RUFA MANA ASIRI DUNIYA DA LAHIRA
SODANGI TAKICE A KULLUM ANA TARE AKODA YAUSHE KOMI WUYA KOMI DADI
AMINTAR MU DAGA ALLAH NE ALLAH YABAR SO DA KAUNA YAKARA MANA FAHIMTAR
JUNA AMEEN*

*********


*TUKUICI*

*WANNAN LITTAFIN NAWA TUKUICI NE GAREKI ANTY SIS, HAKIKA KINZAMA JININ
JIKINA, KAUNARKI A ZUCIYA TAKE HADE DA BARGON JIKINA, KINZAMA WATA BANGARE
A CIKIN JIKINA, TSAKANINA DAKE SAIDAI FATAN ALKAIRI, ALLAH YAKARA MAKI LAHIYA
DA ZAMA LAHIYA YA RAYA MAKI ZURI'A, ALLAH YAKARA DANKON SOYAYYA TSAKANIN

KI DA ABBAN SULTAN, SODANGI TANA KAUNAR KI IRIN SOSAI DINNAN*

**********

*INA KIKE TAWA*

*UWAR GIDA KUMA AMARYAR ABBAN ZAINAB, MAMAN RABI'A, KECE TA FARKO KUMA
KECE TA KARSHE DA YARDAR ALLAH, MAKIYAN KI TAKALMIN KI, HAKIKA ALLAH NATARE
DA MAI GASKIYA A KODA YAUSHE, ALKAIRIN KI DA KYAUTATAWAR KI GA SODANGI BA
ABINDA BAKI ZAI IYA BAIYYANA WABANE, SAIDAI INCE ALLAH YASAKA MAKI DA GIDAN
ALJANNA YA RAYA ZURI'A, ALLAH YASA KIGAMA DA DUNIYA LAHIYA YABIYA MAKI
BUKATUN KI NA ALKAIRI AMEEN SUMMA AMEEN*

**********


*KUNFI KOWA KAUNAR WANNAN LITTAFI NAWA NA ZAMANI*

*MARYAM SARKI*
*MAMAN RABI'A*
*AYSHAN BICHI*
*MEENA PARROT*
*ANTY SIS*

***********


*INAKUKE AMINAN FIDO SODANGI*

*KHALISAT HAYDAR*
*MAMAN ABD SHAKUR*
*UMMI AYSHA*
*KAUSAR LUV*
*SADIYA LAWAL BALA*

********************



*INA KUKE MEMBERS DINA NA MATAN KWARAI, HAKIKA INA ALFAHARI DAKU AKODA
YAUSHE ALLAH YAKARA HADA KANMU YA HADA MU GABA DAYA A GIDAN ALJANNA
FIRDAUSI AMEEN SUMMA AMEEN*

**********


*YABON GWANI YAZAMA DOLE*

*QUNGIYAR NAGARTA WRITERS ASSOCIATION, ABIN ALFAHARIN SODANGI, A GAISHE
KI UWA MABA DA MAMA UWA MAFI UBA KODA KUWA UBAN SARKI NE!, QUNGIYA TA
KWARARRUN MARUBUTA MASU HAZAKA DA SANIN YAKAMATA, QUNGIYA TA
SHAHARRUN MARUBUTA MASU KAIFIN BASIRA DA KAMALA, A GAISHEKI SHUGABA
BENAZIR OMAR SAURAUNIYA MAI HASKAKA TAURARI MACE MAI KAMAR MAZA WAJAN
KOKARI DA 'KWAZO BISA NAMIJIN KOKARIN DAKIKAYI WAJAN GANIN WANNAN
QUNGIYA MAI ALBARKA TA KAFU YANDA YAKAMATA ALLAH YASAKA MAKI DA GIDAN
ALJANNA, MUNAYI MAKI FATAN ALKAIRI ARAYUWAR KI*


**********

*LITTAFAN MARUBUCIYAR*

*YAR GATA*
*ALIYA*
*KAMILA*
*A ZUMUNTAR MU*
*JAWAHEER*
*WAHEEDA*
*RUGUNTSUMI*
*MARYAMA*
*MAKIRA*
*KAINE SANADI*
*KAINE GATANA*
*GOBARA DAGA KOGI*
*MUGUN MAKOCI*
*ZAMANI*
*REAL AMANI*
*HAR A ZUCIYA*

***********
*SAIKUMA KUN SAKE JINA A SABON LITTAFINA BAYAN SALLAH INSHA ALLAHU*


*NAGODE KU HUTA LAHIYA ALLAH YASAKE SADAMU DA ALKAIRI AMEEN SUMMA
AMEEN*

*NI FIDDAUSI SODANGI NAKE CEWA KU HUTA LAHIYA*

07034992740
*FOR ANY COMMENTS*

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login