Showing 1 words to 3000 words out of 288773 words

Chapter 1 - JARUMAR UWA Complete Book by Merhreeyaertou.txt

13 Oct 2025

226

20/03/23, 7:36 pm - Messages and calls are end-to-end encrypted. No one outside of this chat, not even WhatsApp, can read or listen to them. Tap to learn more.
24/03/23, 1:57 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA* 🧕
( _Romantic luv storie_ )


_(Under the pens of✍️ Merhreeyeart lerwerl & doctor Ferhyeez m usmern/ as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyert lawal*



_*BISMILLAHIRRAHMANIRRAHEEM*_
Dukkan yabo da godiya sun tabbata ga Allah subhanahu wata'ala, wanda ya bani ikon kammala wancen littafi nawa na Ahali d'aya har yanzu nazo muku da wani sabo mai suna *JARUMAR UWA🧕* littafin jarumar uwa wani salon labari ne me d'auke da So, k'auna, cin amana had'e da sadaukarwa, sannan labari ne daya had'a al'adar k'asashe biyu, hausa Fulani da kuma larabawa, Ina fatan zaku kasance tare dani don jin yadda wannan labari zai kasance, kada ku manta dai tare da Alk'alamin👇



_Merhreeyeart lerwerl_ 🌹



Page one 1️⃣


Nigeria, Abuja state, garki area one.
Kyakkyawar farar balarabiya ce doguwa take tafiya janye da trolley k'atuwa k'afarta ko takalmi babu, yayinda ruwan hawaye yak'i tsayawa daga kwayar idonta, sanye take da tsadaddiyar doguwar riga bak'a wadda ta wadata musamman wajen b'oye kyakkyawar surar jikinta, gashin kanta ma'abocin kyau da shek'i ya futo kad'an ta saman goshinta sakamakon zamewa da d'an gyalen da tayi rolling kanta yayi kad'an, tafiya take cikin sassarfa tana huce tsilli tsillin motoci da suke shige da fuce a cikin layin, ko kad'an bata tsaya ba har saida takai k'arshen layin, ta juyo da gefen fuskarta kamar zata waiwaya bayanta amma bata k'arasa waiwayawarba, tayi magana cikin harshen larabci, kamar haka👉🏻"kamar yadda nayi alk'awari Suraj! kamar yadda ka buk'ata! zan tafi na bar rayuwarka kuma bazan sake dawowa ba har abada....... kayi abubuwa da yawa na dai dai da akasin shi, haka ka kasance babban b'arawo tunda har ka iya sace rufaffiyar zuciyar surayyah ma'abociyar tsoro da d'ar d'ar ka jefa mata dafi ciki da waje, ka illata ta, ka ragargaza rayuwarta da sunan soyayyah, ka keta iyakar daba taka ba, ka ruguzani sooraj ta yadda rayuwata gaba ta kasance k'ark'ashin sarrafawarka! to ka sani itama surayyah bata kyaleka haka ba, kada ka d'auka Kai kad'ai kayi nasara, a yau surayyah zata tafi maka da abu mafi tsada da daraja wanda zaka dawwama kana bege da mararin had'uwa dashi har k'arshen rayuwarka, something precious and rare more lyk a diamond, sai dai yafi k'arfin ka, sannan ku jira yadda hak'k'in surayyah zai muku". daga nan tayi wani irin miskilin murmushi wanda bai hana b'acin randa take ciki futowa ba.
Taci gaba da tafiyarta tana sake sake a zuciyarta har daga k'arshe ta yanke hukuncin taje gidan Auntie Sarah, kamar yadda zuciyarta ta umarceta haka ta d'auki hanyarta sai dai kash! Tana zuwa k'ofar gidan wani abu yayi Mata dabaibayi ya tsaida ita, duk yadda take yak'i da Suraj da K'arfafa jikinta ma'abocin rauni da zuciyarta abin yaci tura, har ta d'ora hannu da nufin danna door bell sai kuma ta janye hannunta, kalaman sauban suka soma amsakuwwa a cikin zuciyarta kamar lokacin yake fad'a mata su, salin aalin ta soma barin k'ofar gidan looseless, she hope to be dat daughter, she also want dat courage but she don't know how and where to find the confidence, daga k'arshe zuciyarta ta bata shawarar ta inda aka hau tanan ake sauka, a garin da bata da kowa, a k'asar da batasan kowa ba sai shi wato ta koma ga mafarin Suraj ko ba komai zata rayu cikin salama ita da abinda zata haifa, dede da second bata so ta k'ara a garin Abuja balle harta kwana, ta yiwa ranta alk'awarin dole ta bar garin a daren yau.
Abinda bata tab'a yiba tsawon rayuwarta, inda bata sani ba bata tab'a sanin inda haryarshi take ba ta nufa wato neman motar haya, tayi sa'a tana tsayarda wata mota ta tsaya, abinka da bata sani ba, Sam bata iya banbance motar data tare tafi kama da private car ba ta hayar da take nema ba, don haka ba b'ata lokaci tace, "malam inda zan hau motar Kano zaka kaini".
Mutumin ya d'anyi shiru yana nazarin tazarar da take tsakanin tasha da inda zashi a lokacin, kuma dai yaga batayi kama da masu hawa lift ba amma ta tareshi, ko kuma dai tana da lalurar kwakwalwa ne? Ganin yadda take share hawaye sai tausayinta ya kama shi bai ce mata komai ba ya bud'e mata gaban mitar ta shiga rungume da jakar kayanta
Sunyi tafiya mai d'an tsayi Kanta a k'asa har Suka k'arasa, sai daya ce mata, "munzo fa".
Sannan ta d'ago ta d'auko abinda ya rage mata na kud'i a hand bag da take sakale a jikin trolley ta, "kayi hak'uri wannan ne kad'ai abinda yake hannuna".
Kallonta mutumin yayi da mugun mamaki kuma ya kalli kud'in hannunta, US dollers. Wacece ita d'in?
Ganin ya tafi tunani ita kuma tana sauri ne gashi har rana ta d'aga sai ta sake mik'a mishi, "bani da canjin naira ne kayi hak'uri".
Girgiza Mata kanshi yayi yace, "ki barshi kawai".
Sake kallon shi tayi tace, "shukran jazeelan laka".
"Ba komai" ya fad'a yaja motarshi ya yi gaba zuciyarshi fal da al'ajabin wannan baiwar Allah.

Ta soma tafiya cikin tashar jiki a sanyaye a salub'e, kafun wasu mutane suzo suna tambayar ta inda ta nufa, ba b'ata lokaci ta fad'a musu inda zata, nan suka yi mata jagora har mazaunin da sukayi mata a cikin motar. Ranar surayyah ta d'and'ana kud'arta ba kad'an ba, yadda ta tsani shirgin mutane da shiga ciki sai gata dumu dumu tana gwara numfashi dasu a motar haya, haka ana soma tafiya warin fetur ya soma damalmala mata lissafi, tashin zuciya kamar ta mutu, dole daga k'arshe sai toshe hancinta tayi, ta hak'ura da numfashi yadda ya kamata.

Lokacin da akazo maganar kud'in motarta sai ta basu wannan dollers d'in da driver farko yak'i karb'a, suma k'in karb'a sukayi saboda tsoron ko fake ne, dole a k'arshe sai d'aya daga zoben hannunta na gold ta basu donta fanshi kanta a gurin marassa mutumcin drivers d'in, d'aya cikin sune yace, "haba baiwar Allah tun hawanki motar nan muke d'aga maki k'afa, nan da kika gammu bama yadda mu d'auki passenger bai bada kud'i cash an bashi resit ba sai ke, kuma don rainin hankali anyi miki alfarma kin wani d'auko jabun doller kin bamu, sannan mun ki karb'a kin sake d'auko wani zobe wai gold don tsabar kin maida mutane shashashu, to gaskiya hajiya ina ganin gwara mu saukeki a hanya kawai ki Sami wanda zai karb'i wannan zoben ya kaiki".
Wannan mutumi da yake zaune gefen driver ya k'arasa fad'a fuska ba fara'a, kuka ta somayi wiwi tana bashi hak'uri da rantsuwar duk abinda ta basu babu jabu, batayi haka da gayya ba wallahi ko 1naira babu a hannunta sai abinda ta basu d'in.
Wata mata da tunda suka soma tak'addama take kallonsu, sai lokacin tasa musu baki bayan ta karb'i zoben a hannun surayyah ta k'are mishi kallo, zobe ne mai tsada mai daraja k'irar wani babban company na k'asar Dubai, akalla kud'in shi zasu iya kai 70k a kud'in Nigeria.
Jakarta ta duba ta lalubi kud'i ta tambayi masu motar nawa ne kud'in su suka fad'a ta basu, sannan ta kirgo wasu masu yawa ta mik'awa surayyah, "Ni na karb'i zoben ga cikon kud'in da yayi mun saura Ina fatan kin hak'ura da abinda nayi miki, nayi miki haka ne saboda kada in kinyi gaba kici gaba da rigima da wasu mutanen".
Karb'a surayyah tayi kawai don alokacin she have no choice.

@@@@@@@@@

K'arfe 6:36 dai dai Suka k'araso garin kano anguwa uku motor park, duk passenger Suka futo itama ta futo tana tunanin inda zata nufa, ga yunwa ga har lokacin k'afarta ba takalmi, ga kishirwa, ga gajiya, sannan ga wani irin yanayi da yake hajijiya da ita abinda bata tab'a jiba tunda ta samu cikin jikinta, a sanyaye jikinta ta dinga bin inda taga mutane sunayi neman napep, dai dai inda matar data siya zobenta a mota ta tsaya, sai dai ko kafun surayyah ta kaiga tambayar matar abinda ta zo da nufin tambaya wani mugun amai ya taso mata, haka ta durk'usa a gurin ta shiga kyelaya shi kamar zata amayar da y'ay'an hanjinta.
Matar ce ta taimaka mata da pure water bayan ta gama ta d'an wanke bakinta da fuskarta. Matar da son neman maganarta tace, "dama baki da lafiya? Ina kikayi ne da sai in taimaka in nemo miki napep".
Zuciyarta sosai ta karye a lokacin tuno da rayuwar data zab'a ma kanta yanzun kamar wata marar galihu ko y'ar kanta, bayan tana da kyakkyawan asali da dukkan gata.
"Ni anguwa........ Zani ko kema can zaki".
Matar ta sake fad'a tana kallon surayyah da take ta yak'in b'oye hawayenda suka cika idonta.
Gyad'a Mata Kai kawai tayi, in few seconds matar ta samo musu napep Suka shiga bayan ta fad'a mishi inda zai kaisu ya fad'i kud'inshi.
Tafiyar minti 20 zuwa da y'an mintuna suka isa anguwar ta masu k'aramin k'arfi.
Ko kafun surayyah tayi wani abu matar ta biya kud'in har nata, sai tayi Mata godiya kawai ta saita hanya kamar wadda tasan gari don kauce ma bin diddigi irin na matar.
Tana jinta tana fad'in ki huta gajiya "Allah ya raba lafiya".
Lumshe fararen kwayar idanunta da a yanzun suka sauya colour tayi taja doguwar ajiyar zuciya, yanzu a d'an zaman da sukayi matar nan harta karanci tana da ciki?
Surayyah taci gaba da Jan k'afafunta da jakar kayanta tana kewaya anguwar har daga k'arshe Allah yasa ta samu dakalin wani masallaci ta jingina tana sauke lodi lodin ajiyar zuciya, zunbur tayi ta mik'e a lokacin da limamin masallacin ya tada sallar isha'i maza Suka soma yink'urin zuwa su shiga don bin jam'i, sai a lokacin ta tuna rabonta da sallah tun ta asubahi.
Sake rintse idanunta tayi ta kifa kanta da gwiwowinta tana jin yadda duniyarta take jujjuya mata.
Bayan an idar da sallah duk wanda yazo hucewa sai ya kalleta har kowa ya watse mallam liman ya gama zaman lazumi shima ya futo.
Yana Shirin kulle masjid d'in surayyah ta d'ago kanta da idanunta da take gani dishi dishi da kyar tace, "don Allah ka taimakeni........".
Iya abinda ta iya fad'a kenan ta zube a gurin babu numfashi, malam hankali a tashe yayi kanta yana salati da sallallami ga dare ya Soma nisa bare ya kira wani ko wasu.
Kusan mintuna biyar sun huce babu inda yake motsi ko guda a jikinta, ganin haka sai ya nufi gidanshi wanda yake daura da masallacin, tun daga zaure ya soma kwalawa iya salaha kira, "salaha! Salaha!! Salaha futo mana kina Ina ne?".

Da sauri iya data Soma gyangyad'in bacci ta nufo zauren tana amsa Kiran mijin nata, "malam lafiya wannan kira haka kamar sabon makaho". Da sauri ya dakatar da ita "d'auko gyalenki ki biyo ni kiga wani abu".
Ba musu ta koma ta yafo gyale tazo ta sameshi.
Har inda surayyah take ya kaita ya fad'a mata abinda ya sani game da zuwanta gurin da abinda ta fad'a kafun ta yanke jiki ta fad'i, d'an Jim iya tayi kafun ta nisa sosai tace, "toh yanzu dai duniya ta zama abin tsoro, yanzun nan taimako sai ya jawo maka hau, sannan wannan yarinya ce budurwa, duk inda ta futo ba daga wahala take ba dole akwai wani abu da yake faruwa da ita".
Malam yace, "Shiyasa na kira ki ai yanzu ya kike ganin za'ayi salaha?".
Ehhh to Ni Ina ganin mu taimaketa da zuciya d'aya tunda macece ta samu mafaka zuwa gobe da safe in ta dawo hayyacinta muji abinda ya rabo ta da gida, inda hali muyi mata naseeha albarkacin mu sai kaga ta shiryu ta koma".
"Shikenan hakan ma yayi". Malam ya fad'a iya kuma ta soma kici kicin d'ago ta da kiran ta, da kyar suka samu da yayyafe yayyafen ruwa ta farfad'o malam ya jawo trolley ita kuma iya ta d'an rik'o ta sukayi gidanta.

Tana zama ruwa shine abu na farko data soma tambaya, iya ta deb'o mata me sanyi a randa ta had'o mata har da dambun tsakin masarar da tayi a daren ranar.
Ruwan kawai ta iya sha ta d'auko ledar magungunan ta a jaka tasha, su dai kallonta kawai sukeyi suna son suji ta bakinta amma bata da niyyar ce dasu komai banda godiya da tayi musu gashi ma kamar bata hayyacinta.
Ta jima a jingine kafun magungunan da tasha su soma tasiri a jikinta wani nannauyan bacci ya soma fizgarta, iya ta kawo mata pillow nan ta b'ingire.
"Tirk'ashi malam yarinyar nan kamar tana d'auke da juna biyu sannan wannan kwayoyi data afa Allah yasa ba y'ar kwaya bace?".
Shiru ne ya biyo baya saboda shi malam harga Allah baya yi mata kallon gurb'ataccen tarbiyyah yafi son ta tashi suji komai daga bakinta.


@@@@@@@@


Washe garin ranar kiran sallar farko ta tashi sai dai da wata matsananciyar yunwa, iya tana alwala itama ta futo bayan ta d'auki buta ta tambayi iya bayi ta nuna mata, bayan ta futo kuma ta durk'usa kusa da iya ta soma d'aura alwalar ta itama.
Ko kafun ta shiga iya ta shimfuda mata darduma ko zatayi nafila kafun a tada sallah, Zama tayi ta had'a kanta da gwiwa kafun can ta tambayi iya da take ta faman jan carbi bayan ta idar da sallah, "don Allah zan samu abinci?".
"Laaa zaki samu y'ar nan bari na kawo miki, iya da k'ok'ari har wutar icce ta hura ta dumama mata sannan.
Ko lokacinda surayyah ta kai lomar dambu bakinta Saida ta rintse ido saboda bak'on test da taji ya ziyarci kan harshenta, wato karo na farko data tab'a cin dambu irin wannan a cimar hausawa. Ba laifi taci abincin da yawa kuwa, sai dai fa tashin zuciyar amai yana barazanar tunkud'o mata shi waje ya zama asara, da sauri ta d'auki maganin amanta tasha, sannan bayan wasu mintunan ta tashi ta shiga jero duk sallolinda suka huceta.
Akan sallayar wani baccin ya sake awon gaba da ita wanda ya kaita har k'arfe goma da rabi na safe.

Lokacin data tashi jiki a sanyaye ta futo tsakar gidan ta samu iya tana aikin d'aura gyad'a mai gishiri a leda, malam kuma yana kishingid'e kan buzunshi yana jan carbi, har k'asa ta durk'usa ta gaishe su cikin mutuntawa, iya tace ga ruwa can idan zakiyi wanka na aiki y'ay'an mak'ota yanzu su sayo miki sabulu da soso, tace ba komai da kin barshi ma Ina da sabulu a jakar kayana da soson.
Daga haka ta d'auko soso da sabulun ta shiga wanka, bayan ta futo ta shafa mai ta sauya kayan jikinta zuwa wata doguwar rigar ta atamfa super Holland futowa ta sakeyi tsakar gidan ta zauna a inda iya ta nuna mata.
"Kuyi hak'uri tun jiya Ina cikin wani yanayi ban iya tsayawa munyi magana yadda ya kamata daku ba, toh nidai bayin Allah sunana surayyah Adam Kuma ni haifaffiyar k'asar Sudan ce garin Khartoum dake arewacin Sudan. Mahaifina Adam da mahaifiyata mai sunana, mu biyu suka haifa a duniya daga yayana sauban sai ni, dukkannin su Allah yayi musu rasuwa ta silar accident da sukayi a jirgin ruwa, lokacin Ina da shekaru goma a duniya, kusan zan iya cewa a Nigeria nayi rabin rayuwata a gidan yayana dake garin Abuja wanda yake aiki da wani company...... Yayi aure da y'ar can asalin k'asar mu yanzu haka suna da yara uku, abubuwa da yawa sun faru dani a shekarar dana shiga jami'a Ina level 2h babba a ciki shine had'uwa ta da k'addarar rayuwata Suraj, labarina daga nan sirri ne da bazan iya tattauna shi da kowa ba, sai dai ince kuyi hak'uri watarana idan lokacin kuji yayi zakuji komai".
Ta Kai k'arshen zancenta tana girgiza kai kawai da share hawayenta da gefen d'an kwalinta.
Iya ce tace, "Allah ya magance mana abinda yafi k'arfin mu surayyah sai dai mu d'in da kike gani masu k'aramin k'arfi ne, muna da cin yau muna neman na gobe a gurin Allah, ba lallai ne ma ki iya cin cimar muba? Bare irin rayuwarmu ta wahala da talauci".
"Baki da matsala dani akan komai, ni y'ar kasuwa ce, kuma Ina tafe da takardun makaranta na in Allah yasa na haihu lafiya zan nemi aikine a garin nan kuma naci gaba da business d'ina, alfarma d'aya kawai nake son kuyi mun".
"Wace alfarma ce fad'i muji yarinya".
Ta sake gyara zamanta cikin k'arfi da dakiyar zuciyarta take yin komai a yanzun tace, "so nake ku d'auke ni kamar y'ar ku a gidan nan, y'ay'an da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login