Showing 105001 words to 108000 words out of 288773 words

Chapter 36 - JARUMAR UWA Complete Book by Merhreeyaertou.txt

13 Oct 2025

4758

Gidan iya ta nufa bayan ta tsaya a store d'in kusa da anguwar ta sai musu duk abubuwan amfanin su na yau da kullum, don tasan ko k'arewa yayi ba zasu tab'a bud'e baki su fad'a mata ba.
A k'ofar gida ta tsaya ta samu yara suka dinga shiga da kayan ciki ta sallame su sannan ta shiga ciki itama.
Dasu harira ta fara karo a tsakar gidan iya suna gyaran kayan miya, bata tab'a ganin suba amma kallo d'aya ta musu tasan y'an uwan iya ne wad'annan duk inda suka futo, sai taji gabanta ya yanke ya fad'i, kenan y'an uwan su sun neme su! lallai watan tonuwar asirinta ya kama.....



_Comment and share_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page thirty3️⃣0️⃣


Iya da take aikin shiga da lufdin kayan abincin cikin store tana ganinta ta fad'ad'a fara'ar fuskarta tace, "sannu da zuwa doctor surayyah d'iyar albarka". Itama tana murmushin yak'e tace, "sannun ki dai iya". A nan tsakar gida kan tabarma ta zauna suka gaisa dasu harira, iya ma Suka gaisa bayan ta zauna. Malam da yake sitting room yana rubutu futowa yayi yazo suka gaisa dashi shima, sukaita mata godiyar kayan abinci dashi albarka, ita dai batace musu komai ba sai murmushi da tayi, don inda sabo ta saba da jin irin wannan godiyar daga gurin iya da malam d'in a duk lokacin data aiwatar da nauyin data dad'e da d'orawa kanta shi, duk sunyi shiru tsakanin su, ta b'angaren su iya so suke su fahimci halin da take ciki duk tazo musu yau jiki a sanyaye haka ba yadda suka saba ganinta ba, ita kuwa ganin harira ne ya k'arasa sage mata gwiwa gaba d'aya, tsoronta d'aya kada su iya suce zasu bita k'auye su barta ita kad'ai a duniyar da bata da kowa sai su.
Malam ne ya katse shirun su da cewa, "ina Adam da Abdallah". Surayyah ta gyara zamanta tace, "lafiyar su qalou, nima zuwa nayi don na fad'a muku gobe zan koma aiki saboda hutuna ya k'are tun wancen satin...". Malam yace, "Allah sarki Allah yasa a koma a sa'a, Allah yayi jagora". Ta amsa da ameen.
Ba ita tabar gidan ba ranar sai bayan sallar isha'i. Tayi sallama dasu iya dake cikin gida ta tadda malam shi kad'ai a d'akin bak'i shima tayi mishi sallama, shi kuwa wata sabuwar godiyar ya k'ara yi mata hadda share hawaye, itama kamar zatayi kukan tace, "don Allah ka daina kukan nan malam...". Malam yace, "Dole nayi kuka surayyah, kin gama mana komai a rayuwa, cin mu, shan mu, tufafin mu duk kece, kin share mana hawayen rashin haihuwar daba mu tab'a yiba, ba abinda zamu ce miki sai fatan Allah ya saka miki da gidan aljannah firdaus....". A sanyaye ta amsa da "ameen" sannan ta d'ora da fad'in, "nima ba abinda zance muku malam, kun share mun hawayen abubuwa da yawa, Ni dai fatana kayi mun alk'awarin zaku ci gaba da kasancewa kakkani ga yarana, yayinda ni zan ci gaba da amsa sunan y'ar ku duk wuya duk rintsi kada wani cikin yaran nan yasan akwai wata a k'asa".
Malam yace, "insha Allah nayi miki wannan alk'awarin doctor surayyah". Sai tayi murmushi ta k'arasa sallama dashi ta futa.


@@@@@@@


A washe gari Monday ta shirya da wurwuri ta tafi aiki ko break bata iya tsayawa had'awa ba, don a yanzu ba abinda tafi so kamar taga ta fatattaki sabon raunin da yake son shigarta ya kawo nak'asu da tawaya ga jarumtar ta.
Koda khaleefa suka futo yin breakfast shida Ahmad, a parlour suka samu Ayman yana safa da marwa hannayen shi duka goye a baya hannun shi rik'e da wayar shi, sun gaisa dashi sama sama khaleefa na karantar sabon sauyin dake tattare da k'anin nashi, bai zurfafa ba ya tafi da kanshi ya karb'i kayan Karin da mama haleema yau ta had'a.
A nan k'asan carpet duk suka zauna don suci abincin, kusan Ahmad ne ya tallafe su don a cikin su kowa tura abincin yake more especially khaleefa da girkin auntie kad'ai yafi so a duk cikin girke girke.
Bayan sun gama Ahmad yayi musu tayin futa suga gari, Ayman ya bashi uzurin akwai d'an aikin da zai kammala, khaleefa ma zai bada nashi uzurin Ahmad yace wallahi be Isa ba dole shi ya shirya suje.
Haka khaleefa ya shirya ba don yaso ba yabi Ahmad d'in suka futa, shi kuma dabarar Ahmad ta sasu yawo ba don komai bane sai don ya d'ebe musu kewar rashin walwalar da suke ciki su duka biyun.
Alhamdulillah kuma yayi nasara don tuni ya korewa khaleefa zaman tunani da jigum.

Kwana biyu Ahmad yaso yi amma sai gashi ya tasamma had'a kwana biyar a gidan, sosai yake iya yinshi wajen ganin ya fahimci matsalar su duka mutum biyun nan had'e da solving d'inta kafun lokacin da zai huce, auntie kullum zata futa aiki shi kuma baya tab'a barin su shiru musamman khaleefa don Ayman ya saki kad'an, sai dai har yau ya rasa ta hanyar d zai tunkari auntie da zancen da sukayi da mammie, gashi ita d'in ma bata samun wadataccen lokacin zama dasu kamar da farko yanzun.
A ranar da Ahmad ya cika sati ya shirya barin garin Kano, khaleefa da Ayman kamar suyi kuka har auntie ma saida taji ba dad'i saboda an saba dashi a gidan sosai, har mama haleema don itama ba kyale ta yayi ba, inya sameta a kitchen tana aiki ya dinga tambaye tambaye da mata karambani kenan. Toh shi mutum ne dabai saba zama shiru kamar su Khaleefa ba ko a gida. Kyautar turarukan maza masu tsada auntie tayi mishi, ta bashi su khumra ya kaiwa maman shi, ta bashi wani again ya kaiwa mahaifin shi, ya karb'a yana godiya sukayi sallama a daren.
Washe gari sassafe khaleefa da Ayman suka rakashi airport saboda mugun gargadi da jan kunnen da mahaifin shi ya mishi kan cewa lallai kar ya sake yace zai biyo mota zuwa Abuja. Soo motar shima anan gidan su Khaleefa ya barta za'a turo kwararren driver ya d'auka daga can.

Har ya tafi suna d'aga mishi hannu yana d'aga musu.
Ko a mota suna tafe ne kawai cike da kewar shi da zasuyi har suka k'arasa gida, ko karyawa khaleefa beyi ba yabi lafiyar gadon shi ya kwanta sai bacci, bashi ya farka ba sai raana, wayar Ahmad ya fara nema yaji ko ya isa gida lafiya, sai dai bai tafi ba.
Haka ya shiga bathroom d'inshi ya sake wani wankan ya futo cikin shirin white shirt and blue trouser, duk inda ya gilma ba abinda ke tashi sai lafiyayyen k'amshin turaren shi. Yayi sallar zuhur anan d'akin shi ya d'auki makullin motar shi ya futo ba tare da yasan inda ya nufa ba, tsit gidan nasu kamar babu kowa sai shi kad'ai, a hanyar sauka k'asa yaci karo da mama haleema zata hawo, sai ya bata hanya ta fara hucewa tukun, sai dai harta gilma shi ta dawo da baya, "kaci abincin ka kuwa khaleefa?". (Da yake yanzun ta sake banbance su musamman da halayya). "ai mama bar abincin nan kawai in na futa zan nemi wani abun naci". Mama haleema tace, "ooh to ba damuwa, d'an barkwanci ashe kuma ya tafi". Sai yayi y'ar dariya yace, "ehh Ahmad ba". Mama haleema tace, "Allah sarki sai yaushe zai dawo kuma?". Khaleefa yace, "Anya zai dawo ma... Toh maybe ko in zamu huce Germany ya taho ta nan". "Ayyah Allah sarki". Ta fad'a tana yin gaba don taga kamar ya k'osa da amsa tambayoyinta, shima waje yayi yana tunanin Ahmad da sauk'in kanshi, ya iya zama da mutane shiyasa duk inda yaje mutane son shi suke.
Tafiya yake ba don yasan Inda ya nufa ba, ga cikin shi dake aikin kiran chiroma ba k'auk'autawa.


_Flash back_


Raihanatu kuwa sun ci gaba da shirin bikin su hankali kwance ba tare da sunsan wainar da ake toyawa a gidan su Imran ba.
Ta can d'in mahaifiyar shi tana zaune da raana sai ga d'aya daga masu aikinta sun zo sun shaida mata tana da bak'uwa. Kamar tace a fad'a musu bata nan sai kuma ta fasa don batasan ko su waye ba, "kice musu Ina zuwa..." Hajiya tafeeda ta fad'a cikin ginshera. Ko bayan futar me aikin ma saida ta gama shan k'amshin ta sannan ta tashi ta futo.
Umma salaha da take zaune tana ta k'arewa gidan kallo a ranta tana jinjina girman daular da raihanan zata shiga ta huta bayan su y'ay'an su gasu can a wahala, sai kuwa cewa tayi hu'umm ai wallahi ko zanyi yawo tsirara ba'a Isa ayi auren nan ba, wannan babban family haka....tab.
Tana ganin hajiya tafeeda ta saita kanta. Ta zauna suka gaisa har tana tambayarta ya shirye shirye, bata amsa mata ba don a duk lokacin da akayi maganar auren Imrana ji take kamar ta kashe kanta don takaici, "wacece ke kuma" ta tambaya da gatsali. Sai ta k'are washe hak'oran ta waje, "ai dama nasan ba lallai ki shaida niba, kuma har asibiti mukaje kwanaki muka duba jikin yaron ki, toh nidai sunana salaha matar wan surukin d'anki Imrana" sake gimtse fuska hajiya tafeeda tayi cikin daka tsawa tace, "dallah malama tashi ki bani wajee". Da sauri umma salaha tace, "haba hajiya ai kya tsaya kiji abinda yazo dani ko?" Wani kallon banza ta kuma yi mata, ita kuwa cikin ko'in kula ta fara maganarta don hassada ta gama rufe mata ido tuni, "Kin ganni nan ba ruwana da harkar yarinyar da uwarta, don ni raihana ko gaisuwa ban ishe taba tana ganin ba ubanda ya Isa ya fad'a Mata taji, haka uwarta, kinsan Allah ba k'aramin mamaki nayi da akace d'anki ne zai auri gantalalliyar yarinyar nan ba, ta gama yawonta a gari na shek'e aya da wani yaron mak'otan mu, sau ba adadi uwar tana d'aukarta aje a zubar da ciki, ke ba don kar kice k'arya nake ba sai ince har haihuwa tayi a b'oye ba wanda ya sani, kinganni nan ba k'aramin aminci nake da ruqayya ba ada, babu sirrinta da ban sani ba, haka ba irin gaskiyar da bana fad'a mata amma bata d'auka, shine nidai na kasa hak'uri nace bari na nemeki na warware miki zare da abawa har makasudin auren raihana da Imrana ma saina fad'a miki....". Nan ta baje kolin hajar munafunci da sharri gami da aibatawa ga raihana da uwarta, itama kuwa hajiya tafeeda ta baje kunnuwa tana saurare dama a wuya take da maganar auren yarinyar yanzu kuwa gashi ta k'ara jin tabbaci kan rashin ingancin ta, haka ta gama karyayyakinta ta tashi zata tafi, har kyautar dubu biyar hajiya tafeeda ta mata da godiya bisa ga labarin data kawo. Umma salaha kuwa ta futo tana dariya da fad'in, "ahh ga kyauta ga fahimta, maga ta tsiya ai ba sai ayi auren mu gani ba".
Ita kuwa hajiya tafeeda a washe garin ranar ta sake samun Imran da titsiyewar shin ya shirya rabuwa da raihana ko sai ita ta rabu dashi! Hankalin shi tashi yayi, da yana murna kwana biyu ta rabu dashi da zancen ashe ita tana nan akan bakanta bai sani ba. Sai ya fashe da kuka ya durk'usa a gabanta yana kuka yana mata magiya kan ta barshi ya auri raihana shi yana sonta duk yadda take. Aikuwa ba k'aramin tashin hankali ya gani ba saida yayi da kace akan furucin shi, haka ta gama maseefa ta bashi wa'adin cikin nan da kwanaki uku ya yanke hukunci, ta barshi a gurin ba tausayi ba Imani kamar ba itace ta durk'usa ta haife shiba, haka Imran ya shiga mawuyacin hali a cikin y'an kwanakin, yana son zancen yaje kunnen mahaifin shi amma yana tsoron hukuncin da alhajin zai d'auka don dama ya dad'e da gargadin ta akan shiga shirgin maganar auren Imran d'in, a cikin datsin ko raihana bai samu sukunin kira yadda ya kamata ba, da zarar yaji lafiyarta data y'an gidan su yaji muryarta shikenan zai kashe wayar shi ya fad'a tunanin mafuta.
Kwana uku ya huce harda doriyar kwana biyu bai yarda sun had'u da ita ba suna ta wasan b'uya, a ranar da yamma ya taso kasuwa da k'udurin had'a kayanshi ya gudu gidan auntie rahama (matar babansu) ya rok'e ta kada ta fad'awa kowa yana gidanta har sai bayan an d'aura aure raihana ta zama tashi halak malak, a wannan lokacin yasan ya tserewa duk wani hargaginta kuma. Cikin rashin sa'a yana kulle d'akin shi yaci karo da ita tana tahowa gurin shi, gaban shine ya tsinke ya fad'i har ta kaiga ya saki jakar kayanshi bai sani ba, kamar yaga wata maseefa haka ya dinga ambaton sunan Allah a ranshi.
Ita kuwa fuska a d'aure ba annuri tace, "wato Kai shirin guduwa ma kakeyi?? Toh in kaso kabar duniyar ma gaba d'aya amma bayan ka warware wannan shegen auren na rashin albarka daga kanka". Duk jikinshi ba inda baya rawa, ganin kamar k'afarshi ba zata iya d'aukar shiba sai ya zauna dabas a gurin ya had'a kai da gwiwa. Cikin halin ko'in kula tace, "ka shirya aiwatar da abinda na umarceka ko sai na tsine maka albarka kamar yadda na tsinewa auren....".
Bakin shi yana rawa ya d'ago ya kalleta da fuskar tausayawa yace, "Ni bani da wani zab'i don bansan me zance da raihana ba amma duk yadda kika ce haka za'ayi". Cikin jin dad'i hajiya tafeeda tace, "good zakayi nadamar zab'in daka bani kuwa indai nice, kafun nan biyoni d'akina kada abban ku yazo ya ganka haka ka sani a uku kuma.....". Haka ta tisa shi a gaba har d'akinta ta murza key sannan ta karb'i wayar shi bayan ya cire mata a lock, tak'aitaccen rubutu tayi kamar haka, "raihanatu a yau ni Imrana ina farin cikin sanar dake cewa na fasa auren ki bisa kyakkyawar shaidar gani da ido ta gurb'acewar tarbiyya a tare dake, daga yau babu ni! babu ke!! Allah ya had'a kowa da rabon shi".
Sai data bashi ya karanta zuciyar shi kamar ta futo tasa shi yayi sending, cikin tsananin tashin hankali da muryar kuka ya durk'usa har k'asa yana mata magiya kan a sauya abinda za'a fad'a. Ta wani daka mishi tsawa tana fad'in, "ko mutuwa zakayi Imran saika rabu da yarinyar nan a yau, zakayi sending ko sai na tsine maka kabi duniyaaa".
Ba shiri yayi sending ya durk'usa kasan tiles yana kuka sosai, (ko marar Imani yaga Imran a wannan lokaci saiya tausaya mishi, Ni kaina na soma kwokwanto akan haihuwar shi, Anya hajiya tafeeda ta haife shi kuwa??).
Saida ta tabbatar sak'on yaje sannan tayi deleting, ta sake tsara mishi abinda take so ya fad'awa mahaifin shi a daren yau,,,,, haka yana ji yana gani ya amince sannan ya tashi jiki a sanyaye ya futa daga d'akinta, banda auntie rahama ta sake yi mishi mugun gargadi akan mahaifiya da shawarar binta sau da k'afa duk munin halin da zata zo dashi da tuni ya jima da yanke alak'a da ita ya tattara ya bar mata gidan, saboda ya jima da fahimtar bata k'aunar farin cikin shi a rayuwarta gaba d'aya. Saboda son kanta farin cikinta shine gaba da komai. .
Raihanatu kuwa a dai dai lokacin da ya tura mata wannan sak'o tana aikin ninke kayanta da wani almajiri yazo ya wanke mata. Koda taji shigowar sak'o da sauri ta d'auko wayarta da take kusa tana murmushi zata duba, sai dai me?? Wani mugun tashin hankali ne ya diro mata lokaci d'aya taji duk hankalinta ya tashi, sai ta kira no shi a lokacin ya zauna a d'akin shi kenan cikin yanke k'auna ya d'aga, da raunatacciyar murya gwanin tausayi ta fara tambayar shi, "da gaske ne sak'on dana gani daga gare kane Imran". Da kyar ya iya saita yanayin shi yace, "Eh raihana ki yafe ni, fatan Allah ya had'a fuskokin mu da alkhairy ya baki miji na gari wanda ya fini". Bai jira jin ta bakinta ba ya kashe wayar ma gaba d'aya yayi jifa da ita, don baiga amfaninta ba tunda gashi ta zamo silar rabuwarshi da masoyiyar shi.
Ita kuwa tsabar tashin hankali da rudu bata san lokacin da wayar ta zame a hannun taba ta daku da k'afarta. Saita rasa abinda zatayi a lokacin, kuka ko dariya ko duka biyu! Sai kawai ta zura hijab daga k'arshe cikin rashin sanin takamaiman abin yi ta fuce daga gidan su ba tare da tasan inda ta nufa ba rik'e da wayarta a hannunta, ko data kalli gabas! yamma! Kudu! Arewa! Bata ga wata madafa ba sai kawai ta rubutawa Ayman tak'aitaccen sak'o, "Ina cikin matuk'ar tashin hankali,,,, bansan me yake bibiyar rayuwata ba Imrana ya fasa aurena shima a karo na shida, Ina so kazo mu had'u yanzu....". Ko da tayi sending bata ci gaba da tsayuwa a k'ofar gidan ba tayi gaba. Tafiya take zuciyarta tana up and down tun tana gane inda take zura k'afarta har kanta ya kulle ta daina gane komai. Cikin rashin sani ta hau kan titi motoci suna ta horn bata sani ba sai ji tayi kamar an daki k'afarta da k'arfe me k'arfi,,, ta durk'ushe a gurin tare


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login