Showing 114001 words to 117000 words out of 288773 words
Chapter 39 - JARUMAR UWA Complete Book by Merhreeyaertou.txt
matuk'ar sanyaye ta samu gefen gurin ta zauna had'e da zabga uban tagumi,,,, duk yadda take b'oyewa Ayman wannan rashin fahimtar da suka samu da sameera saida yaji??? Toh taya kenan?? Lallai ta yarda baki shege nee... Shiyasa bata tab'a aminta da wani kunne yaji sirrinta ba don baki bazai iya hak'uri ba saiya fad'a.....
Ayman kam bai sake ce da ita komai ba ya fuce daga d'akin da mugun sauri don ya isa ga bedroom d'inshi koya samu damar yin kukan shi yadda ranshi yake so....
Ita kanta auntien kuka take irin wanda takan jima batayi shiba,,,,, maganar Suraj gaskiya ne,,,, tabbas ya fad'i gaskiya da yace babu yadda zata rayu koda bata tare dashi ta iya mantawa dashi, ya riga ya gama yi mata tabo da illar da ko bata koma gare shi da yaran shiba ba zata iya rayuwa cikin sa'ida da salama ba.
Sai ta sake fashewa da wani kukan kamar k'aramar yarinya,,,, Saida tayi me isarta sannan ta d'auki wayarta ta kira no malam. Bayan ya d'aga sun gaisa take sanar dashi abinda ake ciki maganar da khaleefa yazo mata dashi, shi kanshi malam abun ya d'aure mishi kai, a tunanin shi Ayman ne zaice Yana sonta har ma ya aureta,,,, sai gashi khaleefa.... Ganin magana ba zata yiwu a daren ba sai yace ta bari da safe zai zo gidan.
★★★★ Ko bayan sunyi sallama shirin kwanciya bacci tayi, ta tofe duk kusurwowin d'akin da addu'a sannan ta kwanta.
Ayman kuwa da khaleefa ya fara cin karo a parlour, ya d'auke kanshi zai huce khaleefa ya rik'e gefen rigar shi ta baya, sai ya tsaya ba tare daya juyo ba yace, "bacci nake ji ka rabu dani na tafi khaleefa...".
Tattaki yayi zuwa gaban shi ya tsaya ya kalleshi da kyau yace, "babu baccin da kakeji kada ma ka fara yimun k'arya.... Abu d'aya kawai zan tambayeka...".
Sai baice komai ba ya tsaya yana sauraron shi. Khaleefa yace, "shin kasan wannan yarinyar da nace zan aura ne dama??... Koda yake dole ma zaka santa. Amma meye dalilin da yasa ka fara maganar da kayi da farko? Ayman kada ka b'oye mun komai....".
Da ido kawai Ayman ya dinga kallon shi har saida yaji kallon ya isa yace, "why are u staring at me just like dat". Sai ya samu gefen table ya zauna ya had'a kai da gwiwa. Shima khaleefa zama yayi kusa dashi ya dogare hannunshi duka biyu.
"Ka daina tunani ko kokwanto akan maganata khaleefa,,,, Ni damuwata bata da alak'a da auren ka sai tsoron kada kaima irin abinda ya faru dani akan Nur ya same ka..... Shin ko kasan auntie da Mamie yanzu haka basa tare?".
Duk da abun yaba khaleefa mamaki amma bai nuna ba ko a fuskarshi yace, "hakane! Nasan dole watarana zasu rabu,,, saboda mutane ba mahaukata bane... Shin Kai bakaji a jikin ka akwai wani abu dangane damu na rashin gaskiya ba ko k'ank'ani??? Ayman bance auntie batayi k'ok'ari ko wahala damu ba, sannan bamu nemi komai mun rasa ba a rayuwar mu, amma ita kad'ai ba zata wadatar wajen zaman mu cikakkun mutane ba har sai da taimakon uba ko dangin shi.... Sannan maganar raihanatu ina ji a jikina ba zasu hana ni aurenta ba.... saboda dalilai da yawa masu alak'a da wani sirri nasu daban..... Da wannan nake baka shawarar ka ajiye komai a gefe, insha Allah komai ya kusa zuwa k'arshe...". Khaleefa yana gama yin maganar shi ya mik'e tsam ya barshi a gurin ya shige d'akin shi.
Shima Ayman k'afafun shi yaja ya tafi nashi d'akin ya kwanta, sai a lokacin ya samu damar futar da hawayen daya cika idanun shi fal!
A wannan dare Ayman yayi kuka yayi kuka har ya godewa Allah, daga k'arshe da bacci ya gagara sai ya k'arasa daren da tasbihi da tahmidi.
******Raihanatu kuwa ko da ummie ta cire yatsunta a fuskarta dafe kuncin tayi tare da duk'ar da kanta k'asa. "Fad'a mun daga gidan ubanwa kike cikin daren nan?". Kasa cewa komai tayi sai idanunta da suka tara ruwan hawaye. "ba zaki fad'a mun ba raihana?" Ummie ta sake tambaya cikin d'aga murya yanzu.
Sai a lokacin Abba ya k'araso kusa ya taka mata burki ta hanyar d'aga mata hannu, "kinga don Allah ki bita a hankali kada ki sauke mata fushin da ba ita ta sabbaba miki shi ba a kanta". Sai ya k'ara fuskantar raihana da kulawa yace, "Ina kika tafi duk tsawon wannan lokacin raihana.... Kinsan kuwa yadda kika so ki d'aga mana hankali?". Raihana data fara kuka cikin muryar kukan tace, "kayi hak'uri Abba ban futa da niyyar zama ba,, mota ce ta buge mun k'afa saida muka je asibiti sannan". Sai a lokacin hankalin su ya kai kan k'afarta da take nad'e da bandage. Ummie shigewarta tayi ciki sai Abba ne yace, "ayyah ta yaya?" Ganin ta kasa ce mishi komai sai kuka, sai yace "Shiga ciki ki daina tsayuwa a nan kinji....". A hankali ta ci gaba da tafiya har ta isa k'ofar parlon su ta shige, bata tsaya anan parlon ba duk da yadda su jidderh suka damu da ganinta cikin wani yanayi har suna yi mata sannu.
*****A daren ranar mahaifin raihana yana zaune saboda sab'anin da suka samu da ummie d'azu da yamma, wayar shi dake daura da ita tayi ringing, batayi k'asa a gwiwa ba wajen mik'a mishi wayar har yanzu fuskarta a d'aure. Ganin wanda yake kira a wannan dare saida gaban Abba ya fad'i, a fili ya furta "hasbunallahu wani'imal wakeel". Addu'ar data janyo hankalin ummie kanshi tana kallon shi, a handsfree ya saka wayar don suji komai shida ita, bayan sun gaisa da alhaji abubukar cikin girmamawa kamar koda yaushe, shiru duk sukayi, shi Abba yana jiran yaji da wadda alhaji abubukar d'in yazo, shi kuma alhaji abubukar yana jin nauyi da girman abinda zai fad'a har cikin zuciyarshi, baisan meya samu Imran d'in ba, baisan dalilin daya sa yazo mishi afuja'atan a yammacin ranar da magiya gami da rok'on ya gaggauta soke maganar auren su shida raihana ba tunda sauran lokaci basai anzo gab da biki ba.
Kakkarfar ajiyar zuciya ya sauke kafun ya fara magana da dukkan nutsuwar shi, "bansan me zance muku da zan iya wanke kaina har ku fahimce ni cikin sauk'i ba alhaji,,,,, saboda yaron nan......." Nan ya labarta mishi duk yadda sukayi da Imran a yammacin ranar. Shiru Abba ya sake yi kafun yace, "innalillahi wa'inna ilaihi raji'un" ummie da take gefe ta furta k'asa k'asa sai kuma hawaye ya soma bin kuncinta a nutse yana gangarowa k'asa. Abinda bata tab'a yiba duk tsawon lokacin da aka d'auka ana saka da fasa auren raihanar. Dama tunda taji wayar cikin daren nan tasan akwai matsala.
"Kada wannan ya dame ka,,,, bashi ya ganta yace yana sonta har suka daidaita kansu? Kuma yanzu yace ya faasa? Toh duk kai meye naka a ciki yallabai..... Don Allah kada ma wannan ya dame ka,,, haba ai mun zama d'aya babu wani banbanci,,, Allah yasa hakan shi yafi alkhairy".
Duk yadda yaso nuna b'acin ranshi akan abun Abba ya hana shi koda furta mummunar kalma akan abun har Allah yasa suka gama maganar su sukayi sallama, duk da lefe kad'ai suka buk'ata Amma Abba yace sam dole a had'a musu har kud'in auren su a tattara a mayar musu duka.
Cikin k'arfin hali da dauriya ya tashi ya tafi gidan malam. Bayan yasa an mishi sallama da malam ya futo, kwashe duk yadda sukayi da alhaji abubukar yayi ya fad'awa malam d'in, shi kanshi malam ya jinina girman al'amarin a ranshi da zuciyarshi, sosai tausayin yarinyar ya kama shi, gata dai k'aramar yarinya amma tana fuskantar k'addara me girma. Malam ya jajanta mishi kwarai a k'arshe ya bashi shawarar a rufe maganar ga kowa kada a fad'a, sannan kamar yadda yayi niyyah kada ya fasa mayar musu da komai nasu har dukiyar auren su.
Ba musu Abba yayi na'am da shawarar malam, don shi kanshi baya buk'atar kwayayato da yamad'id'in mutanen gari a kanshi dama iyalan shi gaba d'aya.
A wannan dare ne kuma auntie tayi waya da malam bayan tafiyar Abban raihanah.
_ci gaba_
Washe gari kamar yadda malam ya fad'a sassafe ya zo gidan, a parlon k'asa ya zauna suna magana da auntie, bayan ta gama warware mishi yadda sukayi da khaleefa dallah dallah, shiru yayi yana jinjina abun kafun can ya nisa yace, "tabbas an fasa auren yarinyar nan da wannan yaro d'an gidan alhaji abubukar tun a daren jiya mukayi magana dashi mahaifinta, yanzu anjima kad'an zasu zo su karb'i dukiyar auren su da kayan lefe".
Shiru auntie tayi kafun zuwa can tace, "kwana nawa ya rage bikin". Malam yace har yau kwana hud'u kenan cif". Sake yin shiru tayi kafun ta sake cewa, "kana ganin zasu ba da auren y'ar su ga khaleefa? Khaleefan da bashi da wani cikakken asali uwarshi tazo da cikin shi gari har gobe ba wanda zaice ga uban shi....". Malam baisan lokacin daya d'ago ya kalleta ba jin irin furucinta. Ga mamakin sa hawaye ya gani bisa kyakkyawar fuskarta had'e da wani rauni daya mamaye ta lokaci guda. "Da bakin ki yau kike aibata y'ay'an ki irin yadda sauran mutanen gari kan aibatasu surayyah". Da gefen hannunta ta share hawayen fuskarta tace, "toh ai gaskiyane malam, akace ranar wanka ba'a b'oyon cibi,,, sai dai duk wuya duk rintsi nayi alk'awarin khaleefa ba zasu tab'a jin komai daya faru tsakanina da Suraj shekaru talatin har da d'oriya daga bakina ba". Sai taja gwauron numfashi, "bansan dalilin khaleefa na auren wannan yarinyar ba, bayan na tabbata baici ace sun fad'a soyayyar juna a d'an tak'aitaccen lokacin had'uwar suba,,,, kai ko da ace daga dawowar shine ma, bare jiya jiya.... toh amma duk da haka ba zamuyi k'asa a gwiwa wajen nema mishi aurenta ba...Ni da kaina zanje na warware musu zare da abawa,, idan har sun amince dashi a haka sai ayi maganar aure....". Sai ta mik'e tsaye tana girgiza kai kafun taci gaba da fad'in, "Amma fa nayi alk'awari malam,,, indai khaleefa da wata manufa zai auri yarinyar nan... Saina shayar dashi ruwan mamakin da bai tab'a zato ba, sai ya raina kanshi a hannun raihana sannan auren su mutu ka raba". Tana gama maganar ta ta haura stairs a gurguje.
Ko data sauko cikin shiri take nad'e da lafaya da jaka had'e da mukullin motarta.
"Muje malam ai yanzu baiyi sassafe ba ko?".
Malam yace,,, "eh amma me kike shirin aikatawa haka". Sai datayi murmushin gefen baki sannan ta bashi amsa da, "abinda babu wata suruka ta hausa data tab'a aikatawa". Daga nan malam bai sake cewa komai ba yabi bayanta suka futa.
*****A dai dai k'ofar gidan su raihana tayi parking, ta futo ita da malam suka tsaya suna nazarin abinda ya kamata suyi a lokacin, shin zasu shiga babu iso ne ko kuma zasu fara neman yaro ya musu sallama da me gidan? Ganin zata k'ara b'atawa kanta lokaci sai kawai tace da malam tana zuwa. Ta cusa kanta cikin gidan bakinta d'auke da sallama. A lokacin su hibba ne kawai suke budurin su a cikin gidan. Daga ummie har raihana ba'a samu wanda ya iya futowa don gabatar da ayyukan gidan kamar kullum ba, ba wai don basu tashi daga bacci ba, a'a sai don dukan da maganar jiya tayi musu, musamman ma ummie,,, data kwana da wannan tashin hankali a ranta, har tsoro take gari ya waye su Abba abubakar su mayar da kayan auren nan matar shi ta samu abun yad'awa cikin dangin salees,,, barin ma Inna taji labari ta kwaso jiki ta taho da tulin tijararta gidan. Ita kuwa raihana da tunanin wannan bahagon al'amari daya tinkarota ta kwana,,,, ta auna ta duba ta birkita amma har yanzu bata ga aibun abinda take shirin aikatawa ba, duk ta inda ta b'ulla sai taga auren khaleefa shine babbar maslaharta, koba komai zasu samu nutsuwar ruhi ita da mahaifiyar ta,,, ta d'ora da karatunta kamar yadda take mafarki a shekarun baya kafun ta fahimci tarin k'alubalen daya ke tattare da rayuwarta gaba d'aya. Da wannan tulin tunani da kuma k'afarta data kwana tana zugi ta kwana, ko da asuba da kyar ta iya mik'ewa ta d'aura alwala ko daba sallah zatayi ba,,,, ta koma ta sake kwanciya.
Al'ameen ne ya d'an fi hankali duk cikin su muhibba, don haka shiya yiwa auntie iso har cikin parlon ummie da yake tashin k'amshin room freshener kamar ba safiya ba. Ko data zauna idonta akan k'aton hoton raihanan ya fad'a, ta k'urawa hoton ido tana kallon yarinyar duk da ba wai yaune karon farko data fara ganinta ba.
"Tace tana zuwa" shine abinda ya shiga kunnenta, kuma ya sabbaba dawowar ta daga d'an k'aramin tunanin data fara tafiya....
Da sakakkiyar fuska ta shafa kan jidderh data kawo mata wannan sak'o tare dashi mata albarka. Mintuna k'alilan da zamanta a parlon ummie ta futo cikin dogon hijab,, ba k'aramin mamakin ganin auntien tayi da wannan uban safiya ba. Haka dai ta saki fuskarta sosai ta k'arasa har kujerar dake kusa da tata ta zauna. Suka fara gaisawa.
Bayan duk sun gama jin lafiyar juna, auntie ta fara gabatar mata da abinda ya kawota,,, "Da farko dai nasan zakiyi mamakin ganina a gidan ki da wannan safiyar ko,,, to sai dai ba abun mamaki bane in kika ji abinda nazo dashi, amma kafun nan tare da malam muke, sannan in ba damuwa ko zan iya ganin mahaifin raihana da ita kanta raihanar?". Tunda auntie ta fara magana ummie ke kallonta tana nazarinta sosai har takai Aya.
Ajiyar zuciya ta sauƙe a boye kafun ta mik'e tace, "Babu damuwa bari nayi mishi magana, ita kuma tana ciki ko bacci take ma...." Saita kwalawa al'ameen kira, yazo da sauri tace ya kira mata raihana a d'aki. Yaron ya tafi da gudu don isar da sak'on da aka bashi,, ita Kuma ta futa don tayi magana da salees.
Shima ya tashi already yana zaune gefen gadon shi yau ko sukunin lazumi bai samu ba sai tunani daya cika kwanyarshi fal.
Ko da ummie tayi sallama bai iya motsa bakin shiba sai a zuci ya amsa.
Daga jikin k'ofar ta sanar dashi akwai bak'uwa da take son ganin shi a parlour.
Kusan tare suka futo shida ita har inda aka ajiye surayyah,,, kamar had'in baki itama raihana a dai dai lokacin ta futo sanye da dogon hijab har k'asa tana d'ingisa k'afarta.
Daga jikin k'ofa ta tsugunna ta gaishe da auntien, ta amsa tana k'ara yabawa nutsuwa da kamalar yarinyar.
****Saida ta gaisa da mahaifin raihana sannan ta fad'a mishi malam yana waje tare suke. Sai ya tashi da hanzari ya futa zuwa wajen su kuma ya barsu nan zaune cirko cirko da fad'uwar gaba da take had'e da tunanin abinda ya kawota a wannan safiyar.
Ko da Abba ya tarar da malam a waje, har k'asa ya durk'usa suka gaisa saboda matsayin uba daya ke ba malam d'in. Da kanshi yayi mishi jagora har cikin parlon inda duk suke, saboda a gurin su malam ya huce matsayin bak'o da zai tsayar a k'ofar gida.
*****Bayan sun tattaru a guri d'aya cikin nutsuwa da tausasan lafuzza surayyah ta fara koro bayaninta kamar haka........
*Ina masu buk'atar ayi musu invitation card, logo, player, video invitation, carton, advert, sticker da sauran abinda ya shafi harkar graphics, toh maza ku garzayo ga fad'uwar ku tazo dai dai da zama, Maryam sulaiman (maman almustapha), tazo muku da duk abinda kuke so cikin kwarewa, gwanancewa da iyawa, ga duk mai buk'ata sai ya tuntub'eta ta lambar wayarta kamar haka👉🏻 08028175615*
_Comment anda share_.
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page thirty three3️⃣3️⃣
"Kamar yadda kuka sanni, surayyah Adam nake, tsintacciyar y'a ga iya da malam, saboda a zahirin gaskiya bamu had'a komai dasu ba....." Cikin rashin fahimtar abinda take son aiwatarwa malam ya kalleta, sai ta gyad'a mishi kai, "kamar yadda na fad'a maka malam ranar wanka ba'a boyon cibi".
Sai ta maida hankalinta gasu ummie da Abba taci gaba da fad'in, "duk da kasancewata ba cikakkiyar bahaushiya ba, amma na rayu cikin k'asar hausa tare da hausawa babu wani banbanci tsakanina dasu ni a gurina..... Ba zan kira kaina da mara cikakken asali ko tushe ba, saboda na futo ta tsatso mai kyau, da asalin gata da tarbiyyah, sai dai wani abu mai girma da k'arfi ya futo dani daga rufaffen muhallin da nake rayuwa cikin tsaro da mutumcin da a duniya ba wanda ya Isa ya Samar dashi sai iyaye ko wakilan su na kwarae, k'addara ta raba ni da d'an uwana da bani da kowa sai shi a duniya, wato sauban,,, k'addarar kuma bata komai bace face ta haihuwar y'an biyuna khaleefa da Ayman, tabbas wad'annan yaran a yanzu su kad'ai suka rage mun kuma sune rayuwata, zan iya sadaukar da komai dana mallaka a duniya indai zasu tsira....suyi rayuwa cikin aminci da mutumci".
Ajiyar zuciya mai tsayi ta sauke kafun taci gaba da bayaninta, "duka Ina baku wannan labarin ne ba don komai ba, sai don neman auren y'ar ku da d'ana khaleefa