Showing 162001 words to 165000 words out of 288773 words

Chapter 55 - JARUMAR UWA Complete Book by Merhreeyaertou.txt

13 Oct 2025

4788

A ranta tace toh sabon salo
Ta d'auke kanta kamar bata gani ba ta nufi waje.
A k'aton tsakar gidan ta d'auki buta dake can k'asan bishiya ta tarar mishi ruwan. Kafun ya gama alwalar ta shimfid'a mishi k'atuwar darduma a gefe d'aya.
Yana tada kabbarar sallah tayi cikin d'akin ummah ta sake kwanciyar ta, duk yadda take son daurewa ciwon cikinta ta kasa, hak'urin ta yana neman gazawa.
Khaleefa koda ya idar da sallar zaman shi yayi dirshan yana ta hira da ummaah hadda cin abinci, haka kurum yaji matar ta kwanta mishi a rai, da nutsuwarta da tsabtar ta da addininta sai yake ganin kamar iya tasu.
Shida kanshi ya yiwa ummah bayanin tafiyar su Germany, ta yita musu addu'o'i da fatan samun nasara.
Lokacin daya tashi tafiya ummaah ta dinga kwalawa raihana kira bata jiba saboda bacci daya fara fizgarta.
Har saida ta shiga d'akin da kanta ta tasota tana mata fad'an baccin la'asar, hadda fad'awa khaleefa duk lokacin da yaga ta kwanta da la'asar kada ya saurara mata.
Khaleefa yayi murmushi yana sake yaba nagartar baiwar Allahn.
Itama saida ya ajiye mata kud'i masu yawa sannan ya tafi, raihana ma sukayi sallama ta tafi.
Bata iya zuwa gidan kowa ba daga nan saboda yadda ta gaji ga ciwo da cikinta yake sai gida.
Suna zuwa yana parking dama ta futa gudu gudu sauri sauri ta shige d'akin gadonta, ta fad'a kan bed ta kwanta tana jin yadda ciwon yake sake nuk'urk'usarta.
Khaleefa kamar ya bita yaji abinda ke damunta sai kuma dai ya share, yana rufe murfin motar shi Ahmad yana futowa daga saman part d'in Ayman.
"Man wai ina ka shiga ne, nazo tun safe ina neman layinka baka picking".
Murmushi yayi a lokacin da Ahmad ya k'araso sukayi side hug yace, "Kaine kake kirana ko Muhammad? Don ni kiran Muhammad nake ta gani".
Ahmad yace, "Muhammad d'in ma yana neman ka, nima kuma ta number Muhammad d'in na kira ka". .
"Amma lafiya kuwa?". Khaleefa ya tambayi Ahmad yana kallon shi.
Ahmad yana y'ar dariya yace, "lafiya lou kawai ka basu shawara ne kyauta.....".

Happie juma'at Mubarak mah fans, fatan kuyi hutun k'arshen mako lpy. Kwana biyu sai nake ga kamar JARUMAR UWA ya fara futa a kanku shiyasa bakwa comment yadda ya kamata🤦‍♀️ Ina so dai a kullum ku sani, comment d'inku shine kwarin gwiwar mu marubuta


_Comment and share_✍️
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Merhreeyaert lerwerl*


Page forty five4️⃣5️⃣


Cikin rashin fahimtar inda zancen Ahmad ya nufa khaleefa yace, "kayi mun bayani yadda zan gane Ahmad''.
"Toh aure zai d'aura gobe".
"Ah haba! Amma ya mamaye mu, dama anyi engaged ne?".
Ahmad yace, "a'a duka baifi one week dayin maganar auren ba, wai ya koya daga gare ka, akwai abinda ka hango idan ka koma Germany ba aure, kasan shi dama kullum me kwaikwayon kane".
Murmushi yayi suka jera zuwa cikin parlon, bai expecting ganin taba shiyasa suka shiga ba tare da sun nemi izini ba.
Turus! Khaleefa ya tsaya daga bakin k'ofa, karo na farko da yaji bari ya taimaka mata wajen kare mata mutumcinta kamar yadda take takatsantsan a koda yaushe, mukullin hannun shi ya kad'a mata. Ta tashi zaune da sauri tana kallon direction d'in da yake tsaye.
Ganin kamar akwai mutum a bayan shi sai taja jikinta tayi cikin bedroom d'inta da sauri.

Koda suka shiga khaleefa saida ya d'aukowa Ahmad ruwa me sanyi da copi sannan ya zauna suka gaisa, ya tambayi lafiyar y'an gidan su dashi kanshi Ahmad d'in.
Shiru ya biyo baya tsakanin su kafun Ahmad yasha ruwa ya tambayi khaleefa, "Man kasan tun waccen ranar a duhu ka ajiye ni fa".
Kallon sakanni uku zuwa hud'u ya mishi yace, "game dame fa".
"Auren ka ba shiri da yarinyar dana tabbatar babu b'urb'ushin sonta a zuciyar ka, tunda ni dakai duka munsan Saleema kake so, kake son aure...".
Khaleefa Koda ya gama sauraron shi murmushi yayi ya gyara zaman shi da kyau kafun yace, "maganar ka tana hanya Ahmad, duk da a halin yanzu bazan iya ce maka komai ba in banda na jaddada maka abun nan dai daka sani, Ina son Saleema kuma bana mafarkin rayuwa da ko wacce mace bayanta,,,, amma aurena da raihana na baka wuk'a da nama ka fassara shi ta kowacce fuska da tayi maka.....".
Da matuk'ar mamaki Ahmad yake kallon shi, sama da shekaru ashirin suna tare tun lokacin k'uruciya amma har yanzu ya kasa fahimtar wane kalar mutum ne shi, Koda yake shi zuwa yanzu ma ya kamata ya daina mamakin al'amuran khaleefa gaba d'aya, ya taya shi da addu'a kurum.
Sai ya wanzar da murmushi take a fuskarshi yace, "Tom Allah ya zab'a maka abinda yafi alkhairy a rayuwar ka".
Khaleefa ya amsa da "ameen" ba don addu'ar ta gamsar dashi a zuciyarshi ba.

*****A daren ranar raihana kasa bacci tayi saboda tsananta da ciwon cikinta yayi, dama saida auntie ta lura da yanayinta tun farkon dare ta tambayi ko akwai abinda yake damunta, tace ita fa lafiyarta lou, a lokacin bata d'auka ciwon zaici gaba bane sai kuma gashi, haka ta gama murk'ususunta ta tashi ta d'aura alwala ta dinga karanto duk addu'ar da tazo bakinta, a haka ciwon ya gama sharafin shi ya lafa.

Da safe ta tashi kamar batayi ciwon komai ba, sai dai duk jikinta ba kuzari, ta shirya cikin shigarta mai kyau ta d'ora hijab d'inta ta futo parlour tana kallo.
Tana nan khaleefa ya futo cikin riga da wandon shadda, kanshi babu hula sai gashin kan da aka saisaye aka rage mishi yawa. Kallo d'aya raihana ta mishi ta d'auke kanta ta mayar kan tivin dake magana a parlon.
Saida yazo dab da inda take zaune sannan ta gaishe shi, bai amsa ba sai zuba mata ido da yayi yana kallonta kamar me karantar wani abu.
Cikin murya mara amo kuma yace, "ko zan iya samun abinda zansa a cikina kafun na futa".
A nutse ta mik'e ta isa gurin da mama haleema takan ajiye musu abincin karin su duk safiya.
Plate biyu tayo saboda itama bata ci komai ba, ta mik'a mishi nashi, itama tayi gefe da nata.
Har ya gama ci ya ajiye mata plate d'in ya fuce bata fara cin nata ba, sai tsakura da take kad'an kad'an.

****An d'aura auren Muhammad a anguwar su dake...... Bayan d'aurin aure sun gudanar da reception da ango ya shirya don abokan shi kad'ai. Da zasu tafi Ahmad da khaleefa suka ajiye mishi kud'i masu yawa gudunmawa. Ya karb'a da kyar bayan sun takura mishi yana godiya.

Lokacin da suka dawo a saman part d'in Ayman suka sauka, saboda raihana ta samu bak'uncin su al'ameen, Abba da kanshi ya kawo mata su da safe, yace in yamma tayi ko al'ameen zai iya dawo dasu gida in aka sasu a napep.
Farin ciki a gurin raihana ba'a magana, ranar wuni tayi suna budurin su ita da yaran, da yamma da auntie ta dawo ta kai mata su suka gaisheta, sai a lokacin khaleefa ya ga ashe sune bak'inta da yaji hayaniyar su tun rana. Ya kuwa dinga jansu da hira har abun yaba auntie da raihana mammaki, suma yadda suka sake dashi kamar sun shekara da sanin shi.
Da suka tashi tafiya Auntie ta had'a su da tsaraba me yawa, khaleefa kuma da kanshi ya kaisu har k'ofar gida, bayan ya tsaya dasu a supermarket ya k'ara musu da nashi kason.

A daren ba suyi bacci da wuri ba, auntie da kanta ta dinga taya raihana had'a duk abinda tasan zata buk'ata, saida ta tabbatar ta had'a komai yadda ya kamata sannan ta tafi ita kuma ta samu ta d'an rintsa.

Safiyar ranar da zasu tafi ta futo wanka da safe d'aure da guntun towel, tana tsaye gaban mirrow tana sharce gashin kanta da cumb, aka mata knocking, saita jawo hijab da sauri ta zura sannan taje ta bud'e k'ofar, khaleefa ne tsaye kamar kullum yau ma cikin shigar k'ananan kaya da suka dace da zubin halittar shi, fuskarshi ba wannan d'aurewar yau kafun tace wani abu ya riga ta da cewa, "barka da safiya". Raihana saida ta d'an diririce sannan ta amsa da, "barka fatan kana lafiya".
"Lafiya Lou, amm yauwa takardun nan zaki bani, saboda zamu tafi dasu za'a kaiwa k'anin dad d'in Ahmad".
Ba musu ta juya ta d'auko mishi a inda ta ajiye su ta sake dawowa ta mik'a mishi bayan ta russuna.
Har ya juya zai tafi ya sake waigowa ya kalleta, tana nan tsaye rik'e da k'ofa, "ki shirya flight d'in k'arfe goma zamu bi".
Ta gyad'a mishi kai sannan ta juya don k'arasa abinda takeyi a ciki.
Misalin k'arfe takwas na safe ta gama shirinta tsab tana zaune a parlon auntie tana tuttura abincin data tsare su suci gudun tafiya da cikin yunwa, yau bata saka wannan uban hijabin ba, sai kwalliyarta da tayi me kyau cikin doguwar riga abaya golden, rigar daga sama ta d'an kamata kad'an, sannan daga ciki tayi shape me kyau, daga k'asa kuma ta bud'e sosai.
Ta tubke gashin kanta ma'abocin tsawo da yawa a k'eyarta, tayi rolling da madaidaicin gyalen rigar, fuskarta powder ce kawai sai wet lips, sai kwalli data zirara a idonta, a tak'aice dai kwalliyar ta mata kyau ta kuma dace da ita, a yau kam khaleefa tunda ya ganta ya kasa d'auke idon shi a kanta, so yake yaga abinda yake fusgar hankalin shi akan kwalliyarta ta yau, yaga abinda yake k'ara mata kyau bayan bata kasance fara ko mai irin zokalelen hancin nan da manyan idanu ba, ko kuma a'a don bata zurma wannan uban hijabin nata bane? Raihana kuwa tana zaune duk jikinta a sanyaye.
Daga ita sai shi a parlon Ayman ya shigo bakin shi d'auke da sallama, duk suka amsa mishi suna kallon inda yake tsaye, ya mik'awa khaleefa hannu suka gaisa, raihana ma ta gaishe shi, ya amsa mata sama sama saboda kiyaye hak'k'in auren yayan shi dake kanta.
Anan yayi musu sallama had'e da bada uzurin general meeting da zasuyi da duka ma'aikata, duk wanda bai kasance a gurin ba kuma zai shiga matsala.
Da kyau khaleefa ya amshi uzurin shi, suka rungume juna suna sake yin sallama da juna.
Yana futa raihana ya turowa raihana sak'o kamar haka.
"Zuciyata ta aminta dake, shiyasa har ciwona ya warke lokaci guda dana ji irin alk'awarin da kika d'aukar mun, raihana son da nake miki wani lokacin har tsoro yake bani, a yanzu dana ganki kusa da khaleefa sai naji tsorona ya sake ninkuwa, bansan wacce irin rayuwa zakuyi keda twin bro na a wata k'asa ba duk da nasan waye khaleefa, ba wai ina nufin na shiga tsakanin ki keda mijin ki ko mu shiga hak'k'in shi saboda ni ba,,,, don Allah ki kula da rayuwar khaleefa, in kikayi haka shine zaki tabbatar mun da soyayyah ta,,,,, kema ki kula da kanki.....".
Raihana ta karanta sak'on Ayman yafi sau hud'u amma ta kasa fahimtar takamaiman abinda yake son fad'a a dunk'ule, tana tunanin kamar ko baya hayyacin shi ya rubuta sak'on shiyasa ya kakkamo zantukan ya had'a.
Daga ita har khaleefa sunyi zurfi shiyasa har Ahmad yayi sallama ya shigo cikin shiri basu ji shiba, saida ya tab'a kafad'ar khaleefa sannan, ita kuwa raihana bata ji nata gani ga uban tagumi data rabka da wayarta a hannu. Ahmad har gaisheta yayi bata jiba, haka khaleefa ya kira sunanta sau biyu bata jishi ba. Duk sunyi mamakin abinda ya d'auki hankalinta haka har tayi nisa cikin wata duniyar daban.
Futowar Auntie ce ta dawo da ita hayyacinta tayi firgigit tare da sauke b'oyayyar ajiyar zuciya. Khaleefa ta saci kallo sai gashi idon su ya fad'a cikin na juna a sa'a.
D'auke kanta tayi, shima ya d'auke nashi yana tunanin abinda ya faru ta zama haka lokaci d'aya.
Saida auntie ta k'araso suka gaisa da Ahmad, sannan itama ta gaishe shi, ya amsa yana ta zolayarta wai ya shigo tana can tunanin zata bar k'asa da familyn ta. Ita dai murmushi kawai tayi.

Kamar yadda suka tafi wancen ranar haka yauma zasu k'ara tafiya a karo na biyu, sai dai da tarin sauye sauye, a wannan karon sunfi girma akan wancen lokacin, sannan an samu k'arin raihana, babu kuma Ayman.
Daga gefe d'aya na hango raihana da auntie tsaye a gefe guda, idonta ya ciko taf da hawaye, ita kanta auntien idonta ruwan hawaye ya tara, ba don kada ta sake karyawa raihana zuciya ba da itama kukan zatayi, masu iya magana suka ce sabo turken wawa, yau auntie da raihana suka sake tabbatar da hakan, don kuwa a d'an zaman da sukayi tare wata irin soyayyah da shak'uwa ce ta shiga tsakanin su marar iyaka, da gaske suke jin kewar juna kamar su cancelling tafiyar su zauna tare.
Saida auntie tayi gyaran murya sannan ta fara yiwa raihana magana da sanyin murya, "Toh raihanatu, yau dai gaki zaki kasance a k'asar da baki da kowa baki da komai sai khaleefa, wani bahagon mutum da Allah ya baki a matsayin miji, Ina son kiyi mun alk'awari zaki kasance garkuwa a tare dashi, ki kasa ki tsare ki yak'i duk wani abu marar kyau da zai shigo cikin rayuwarshi kamar yadda kowacce uwa take yi a rayuwar d'anta, ki saki ranki kiji a jikin ki kamar muna tare, kada kiji shayi ko tsoron yi mishi magana akan komai daya sab'awa shari'a da k'a'idar aure da iddinin islama, Ina fatan ranar dazan kawo ziyarar farko Germany na tarar da wani khaleefan daban ba wanda kuka tafi tare ba....". Raihana sunkuyar da kanta k'asa tayi cikin taushi da laushin murya tace, "ki gafarceni auntie, insha Allah zanyi kamar yadda kika ce". Ta k'arasa fad'a tana share hawayen da suka taru a idonta.
Auntie rungume ta tayi a jikinta tana share mata hawayen, ji take kamar kada ta bawa khaleefa raihana saboda ta fahimci bai gama sanin ciwon taba, sai dai tafiyarshi ba ita kamar ta bashi wani lasisi ne nayin yadda yaso a k'asar da babu wanda yasan shi, ba wani babba da zai kwab'e shi, baya ga haka ma suna buk'atar kusanci na kusa don suyi karatun juna yadda ya kamata suga abinda mutane suke gani a rayuwar su dasu basa gani har yanzu.
Duk yadda auntie taso kasa daurewa tayi har saida ta zubar da hawaye.
Tabbas iyayen raihana sun kasance masu yakana da matuk'ar d'auke kai, ita kenan da ba ita ta haife taba take jin kewarta Ina ga uwa da uban da suka kawota duniya. Tasan Allah kad'ai yasan abinda yake ransu a yau a halin yanzu ma.
Tattaki kad'an Auntie tayi bayan raba raihana da jikinta, ta kaita inda khaleefa da Ahmad suke tsaye, ga jakunkunan kayan su a kusa da k'afar su, hannun khaleefa ta kama ta had'a dana raihana sannan tace, "khaleefa ga amanar raihana nan, ka tabbatar ka kular mun da ita fiye da yanda zaka kula da kanka..... Ina fatan Allah ya baku nasara akan abinda zai mai daku".
Duk kallonta sukeyi har Ahmad a lokacin data fara juyawa da nufin barin gurin, saida tayi tafiya mai nisa sannan ta waiwayo ta kalle su ta sakar musu murmushi, ta sake ci gaba da tafiyar ta.
Raihana ta zabura zata bi bayanta, khaleefa ya hana mata damar haka ta hanyar sake rintse hannunta da yake cikin nashi hannun, saita juyo ta kalleshi, ya sakar mata lallausan murmushi, yana jin laushi da d'umin hannun har ta cikin jinin shi.
Bai sake hannunta ba suka fara takawa a haka, hannunta d'aya janye da trolleynta, shima rik'e da jakar kayan shi.
Suna gaba Ahmad na bin bayan su har suka k'arasa inda za'ayi musu screening.

K'arfe hud'u da minti ashirin da shida jirgin su ya sauka a Berlin Brandenburg international airport dake Germany.
Tafe suke su biyu a gaba, ita kuma tana bin gefen da mijin ta yake a baya a baya daf dashi a d'arare har zuwa wajen filin jirgin.

Dole ranar a hotel suka sauka saboda sun sake apartment d'insu tuni.
Raihana tana zaune a harabar Sorat hotel Brandenburg ..... har suka shiga sukayi booking d'aki khaleefa yazo ya mata magana suka tafi tare.
Suna tafe Ahmad na zolayarta, Wai duk tayi laushi da wuri daga y'ar wannan tafiyar, ita dai murmushi kawai ta mishi ba tare da tace komai ba.
D'aki daban daban suka kama Ahmad


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login