Showing 165001 words to 168000 words out of 288773 words
Chapter 56 - JARUMAR UWA Complete Book by Merhreeyaertou.txt
da khaleefa, sai dai kusa dana juna.
Lokacin da suka shiga raihana bin ko'ina na d'akin tayi da kallo, akwai k'aramin gurin hutawa kafun a shiga d'akin, me d'auke da k'aramin dressing mirrow da resting chair, Sai k'ofa guda d'aya.
Koda tabi bayan khaleefa ta shiga d'aki ne babba guda d'aya, me d'auke da k'aton gado da cupboard sai tivi a gefe da madaidaicin table me d'auke da kujeru biyu a gefe.
Khaleefa yana ajiye jakar kayan shi ya d'auki abinda zai d'auka ya fad'a bathroom.
Ita kam gefe guda ta zauna kan sopa a d'arare tana rarraba ido kamar wadda za'a sace a gurin. Kallon komai take daban a fuskarta, tana tunanin yadda zasu rayu a muhalli d'aya har na tsawon lokaci me tsayi tare haka, sai take ganin kamar akwai takura ai.
Tana zaune khaleefa ya futo da kayan daya cire ya ajiye cikin cupboard dake jikin bango, ya futa daga d'akin ba tare daya ce mata k'ala ba.
Saida ta d'auki lokaci har ta fara tunanin ko khaleefa ya tafi nema kenan sannan ta tashi ta shiga cikin d'akin wankan, tayi wanka ta shirya cikin riga mara nauyi ta futo ta samu kan sofa tayi kwanciyarta, duk da yunwar da take ji amma gajiya ta rinjayeta kafun wani lokaci tayi bacci.
Koda khaleefa ya dawo da abincin daya mata order tsayawa yayi yana tunanin yadda zai tashe ta daga wannan bacci me cike da azabar yunwa.
A gurguje please Ina cikin uzururruka🙏
_Comment and share✍️_
24/03/23, 2:05 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)
_(Under the pens of merhreeyeart lerhwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_
_Story and written by_
*Merhreeyaert lerwerl*
Page forty six4️⃣6️⃣
Ya dad'e a tsaye kanta yana kallonta, hallau sanye take da k'aton hijab ta nad'e har k'afarta, bacci take sadidan kamar wadda ta shekara bata runtsa ba, khaleefa kamar ya rabu da ita sai ya kasa, a k'arshe yayi k'undunbala ya fara duba saitin inda zai samu k'afarta, kamar me tsoron wani abu ya fara d'aga hijabin jikinta har chocolate k'afarta ta bayyana, wani irin jan lalle ne aka zana mata shi can k'asan k'afa irin na auntien shi, saboda kamawa har ya sauya colour daga ja zuwa maroon, wani takaici ne ya turnuke khaleefa lokaci d'aya da yaga lallen nan, ranshi yayi bak'ik'irin har yana takaicin kanshi daya tsaya tashin ta ma har yaje ya gani.
Fucewar shi yayi ya fasa abinda yayi niyyah.
Raihana kam ta jima tana bacci kafun ta tashi, ta shiga bathroom tayi uzurinta ta futo sannan ta ankara da abincin daya ajiye mata, yunwar da take ji tasa ba zata iya hak'ura ba sai taci koma na waye.
Lomar farko data kai bakinta saida ta rintse ido, wani kalar test da harshenta bai tab'a tasting ba, saboda yunwa dai haka ta rugungunta taci kad'an ta maida ragowar gefe inda ta ganta ta ajiye.
Har dare yayi ta sake komawa wani baccin khaleefa bai shigo ba.
Shi kuwa ta b'angaren shi yana tare da Ahmad suna meeting kan aikin da zasuyi da yadda zasuyi, sam basu rabu ba sai nisan dare.
Lokacin daya shigo raihana ta dad'e da yin bacci kan sofa, Saida ya duba abincin yaga kad'an taci, ya tab'e baki ya sauya kayan jikin shi zuwa na bacci ya kwanta kan gadon.
_asuba ta gari_
Washe garin ranar ma khaleefa tun da wuri ya sake futa ko breakfast bai tsaya yiba, haka ta yini ita kad'ai da jagwalgwalallen abincin Germany daya Sha banban da wanda ta saba ci a k'asar ta. Har dare bata iya cin komai ba, ga yunwa da take neman ganin bayanta.
Bai dawo da wuri ba ranar ma har dare, tana son yin bacci amma yunwa ta hanata.
A nutse ya turo k'ofar ya shigo bakin shi d'auke da sallama, da ita ya fara cin karo a zaune kan carpet ta hard'e k'afafunta ta zura kanta a tsakanin cinyoyinta.
Kallo ya bita dashi farom up to toe, yanzun ma sanye take da doguwar rigar bacci mai kauri, ta d'ora madaidaicin hijab daga kanta zuwa gwiwar k'afarta.
Motsin shi yasa ta d'ago kanta tana kallon shi da idanunta da suke nuna kamar tayi kuka.
Kamar ya tambayeta ko wani abu yana damunta? Sai kuma dai ya share, yana ganin in akwai abinda yake damunta zata fad'a mishi tunda ba jaririya bace ita d'in.
Tana nan zaune har yayi shirin kwanciya bacci, yayi addu'o'in shi ya kwanta, don tuntuni suka ci abincin su shida Ahmad a gidan cin abincin da suka saba ci.
Wani abun mamaki sai ya kasa baccin yana tunanin abinda yasa har war haka ba tayi bacci ba, tabbas daga yanayinta daya kalla kad'ai yasan ba lafiyarta ba, toh amma meya hanata fad'a mishi in ma bata da lafiyar?
Sai ya tashi zaune ya soma bin komai na d'akin da kallo, kafun ya sauko duka ya duba abincin yau da aka kawo mata, suna nan ta tare su kan table bata tab'a ko guda ciki ba.
Abinda ya d'aure kan khaleefa kenan? Sam tunanin shi bai bashi nau'in abincin ne bata saba dashi ba.
Gefen bed ya koma ya zaune ya tsura mata ido yana kallonta ta cikin dim light, kanta jingine da bango idanunta a lumshe, kamar ba zaice komai ba sai kuma yace, "Ina fatan dai kina lafiya".
Ba tare data kalle shi kota motsa daga yadda take ba tace, "umm!".
"Toh me yasa baki ci abincin kiba?". Ya sake tambayar ta.
Sai yanzu ta motsa ta hanyar yamutsa fuskarta tace, "bazan iya ciba".
"Me yasa?". Ya sake tambayarta still idon shi a kanta.
Tashi tayi zaune sosai ta kalle shi sau d'aya ta d'auke kanta, "wannan ba irin abincin dana saba ci bane". Ta fad'a da murya a sanyaye.
Sai yanzu ya gano bakin zaren.
Agogon wayar shi ya duba yaga lokaci, kafun ya mik'e ya futa.
Abincin da yasan zata iya ci ya tafi ya nemo mata, yasha wuya kafun ya samo mata, burger da maultaschen, yana ganin kamar zata iya cinsu, don gidan abincin da suke samun Nigerian dishes tuni sun kulle, ko kafun yazo tayi laga laga ta kusa mutuwa saboda yunwa data galabaitar da ita.
A k'asa ya zauna nesa da ita kad'an yace, "ga irin wanda zaki iya ci".
Da kyar ta tashi, khaleefa ya mik'o mata tea me zafi daya had'a mata, ta amsa da sauri ta shanye har jikinta yana rawa rawa.
Abincin ma hannu baka hannu kwarya ta ci wanda ya sauwak'a ta ajiye ragowar a gefe. Saida ta wanke bakinta ta d'auro alwala ta futo sannan khaleefa ya sauke ajiyar zuciya ya kwanta.
Itama ta samu guri ta kwanta.
@@@@@@@
Kwanaki biyu suka k'ara a hotel d'in suka samu masaukin su da zasu zauna, k'aramin plat ne me d'auke da parlour! Da 2 bedrooms sai kitchen da harabar gaban gida da aka cika ta da shuke shuke kamar garden.
Da taimakon Ahmad suka shirya gidan da duk wani abun buk'ata na amfanin yau da kullum, suka tattaro raihana daga d'akin hotel zuwa gidanta.
Raihana sai taji tafi sakewa akan wancen takurarren muhalli. Komai na parlon light ash ne, dinning kad'ai fari sol.
D'akunan gadon kuma kala biyu, wanda khaleefa ya d'auka white bedroom ne, ita kuma nata pitch.
Tana zaune a parlon tana hutawa Ahmad sai zolayarta yake wai har ta fara gajiya da Germany bayan ko sati bata rufa ba, ita dai murmushi tayi mishi ba tace komai ba, don in akwai abinda yafi gundara ma tayi da k'asar, yanzun ita inda khaleefa zai taimaketa daya had'a ta da auntie da y'an gidan su taji muryar kowa kota samu nutsuwa in taji lafiyar su.
Agogon bango dake mak'ale a wata kusurwa can ta parlon ta gani, saita tashi don sama musu abinda zasu ci don taga alamun basu da niyyar futa yanzu, aiki ma suka fara ta system d'in khaleefa.
Abinci mai sauk'in sarrafawa tayi don ta gaji burinta kawai da tayi sallah ta kwanta, tana gamawa ta jere musu a dinning ta shige d'akinta.
Tunda ta tafi hankalin Ahmad ya koma kan dinning inda ta jere abincin data gama girkawa yanzu, dama ga k'amshi ya cika musu hanci tuntuni.
Ganin khaleefa kamar baya jin yunwa sai ya magantu, "yae! Man nifa abincin can ya tafi dani, Ina ganin bari nayi sallah nazo na....". Bai k'arasa ba sai y'ar dariya da yayi.
"Ohhh! Sorry lokacin sallahn ma ya kusa hucewa", ya k'arasa fad'a a k'agauce yana rufe system d'in ya mik'e, shima Ahmad mik'ewar yayi.
Saida sukayi sallah sannan khaleefa ya mishi jagora zuwa dinning d'in. Ahmad da zumud'i yake ta k'ok'arin saving kanshi, duk wannan k'amshin ba wani abinci na daban bane, jallop rice and beans ce sai had'in ordabur da ta musu. Da basise.
Ko a ido yadda abincin ya had'u ya matuk'ar tafiya da hankalin khaleefa, amma abu guda daya tuna yaji abincin ya bashi haushi ranshi ya dawo bak'ik'irin, haka ya tashi daga gurin da sauri ya koma inda suke zaune da farko bayan ya tsiyaya ruwa a cup.
Ahmad da mamaki yake tambayarshi, "lafiya kuwa?".
Yamutsa fuska yayi yace, "normal am okay".
Shiru Ahmad yayi yana tunanin dalilin da yasa khaleefa ba zaici abincin ba duk yadda yayi dad'i ya samu gyara na musamman daga matar da suke da tabbacin tsantarta.
Shi dai kam saida yaci ya k'oshi sannan ya baro dinning yana magana da d'an k'arfi yadda raihana zata iya jiyowa.
"Madame munci abinci yayi dad'i Allah ya saka da jannatul firdaus....".
Tana kwance ma ita tayi nisa a duniyar bacci sam bata san wainar da suke toyawa a gidan ba.
Yana zama khaleefa ya tashi yace, "muje ko?". Ahmad baisan ko'ina yake nufi ba amma sai ya tashi ya mara mishi baya suka futa a gidan.
Gidan cin abincin Haveli suka nufa inda suka saba cin abinci lokaci zuwa lokaci yayi order, abun ba k'aramin mamaki yaba Ahmad ba har saida ya kasa hak'uri ya magantu, "Man nifa ban gane maka ba, ka bar abinci me kyau a gida kazo kana cin wannan".
Sake b'ata fuska yayi kamar ba zaice komai ba sai kuma da kyar dai yace, "baka ga hannu da k'afar raihana ba?".
Ahmad dafe kanshi yayi, bai gani ba kam tabbas, amma yasan indai jikinta da lalle bazai tab'a iya cin abincin taba.
Cike da tausayin yadda zai dinga missing abincin raihana masu dad'i yace, "Man lokaci fa yayi daya kamata ka danne zuciyarka akan rashin son lallin nan, indai ba har in kaci zai dawo bane....".
Shiru yayi ma Ahmad ba tare daya ce mishi kanzil ba, yana ganin Ahmad don baisan irin tsanar da ya yiwa lallin bane, ko auntie don ya gama tabbatar da ingancin tsabtar ta yake iya jurewa yaci duk rintsi, amma wannan raihana kam, bazai iya ba.
Har ya gama suka tafi basu sake ce da juna komai ba tsakanin su.
Basu koma anguwar ba sai bayan da suka gama duk wani uzurun su a gari, kasancewar gidan Ahmad yana kusa dana khaleefa sai gasu sun dawo kamar yadda suka tafi, sai dai wannan karon kowa nashi guri yayi.
A lokacin raihana ta sake gyara gidan ta dafa sabon abinci amma bada yawa ba don taga wancen basu ci na kirki ba.
Tana zaune kan kujera ta kanannad'e jikinta kamar me jin sanyi, wayarta ce rik'e a hannunta ko me take dubawa oho shi dai daya shigo yanzu bai sani ba.
Raihana sam bata ji sallamar shiba don baya yinta yadda zata ji d'in, rufe k'ofa da yayi yasa ta d'ago da sauri tana kallon k'ofar.
Takowa yake sannu zuwa cikin d'akin da tafiyar shi me bayyana zallar aji da nutsuwa.
"Sannu da zuwa". Ta fad'a k'asa k'asa tana d'auke kanta ga barin kallon shi.
Saida yasha k'amshin shi son rai ya gama k'arewa komai na gidan kallo da tunanin daga inda wannan k'amshi mai shegen dad'i yake futowa sannan yace, "yauwa".
Zama yayi cikin kujerar yayi relax yana sake shak'o nau'in k'amshin daya zarta wanda yasani tare da auntien shi dad'i da sanya nutsuwa a ruhi.
Raihana dama bacci ne fal idonta, zaman shi a gurin yasa ta takura don haka ba dogon sharhi ta d'auki wayarta tayi cikin d'akin gadonta. Bayan tayi addu'a me tsayi ta tofe duk kusurwowin d'akin tayi kwanciyarta.
Shi kam saida ya d'au tsawon lokaci yana tunani kafun ya mik'e ya shige d'akin shi shima ya rufo.
@@@@@@@@
Sosai khaleefa ya shiga busy cikin satin, a sati na gaba kuma suka fad'a bakin aiki.
Ranar farko da khaleefa ya ganshi zaune a office matsayin kwarrren likitan (physiotherapy) saida ya kai goshin shi k'asa yayi sujudushshukur yayi addu'o'i ya godewa Allah bisa wannan muhimmiyar rana daya nufe shi da gani.
Office d'inshi shida wasu mutum biyu cikin rukunin su bakwai yana k'ark'ashin doctor andal, su kuma Ahmad zasuyi aiki tare da wancen likitan.
Ranar ko daga yanayin yadda raihana taga ya shigo gidan ta tabbatar yana cikin tsananin farin ciki.
Ta jima tana son neman alfarmar ya had'a ta koda auntie ne taji lafiyarta tare data mutanen gidan su, amma ta rasa ta inda zata fara tunkarar shi, kullum sassafiyar Allah ya futa baya dawowa kuma sai ta kwanta bacci, bata san ina yake tafiya ba,,, me yake yi da har yake d'aukan lokaci me tsawo haka a waje, shiyasa ta fara ganin baiken Auntie da take tunanin zata iya kawo gyara wa rayuwar mutumin da mantawa yake yi da ita ma gaba d'aya cikin babin rayuwar shi.
Tun tana ajiye mishi abinci a dinning ta d'auka yadda ta barshi har ta gaji ta daina.
A yau ma bata tsammaci dawowar shiba, bayan ta gama komai da yammacin ranar gajiya tayi da zaman kad'aici ta lek'a ta wajen window tana kallon anguwar da take tsit ba alamun mutum ko guda, sai motoci da suke hucewa tsilli tsilli.
Kamar koda yaushe yauma sanye take da wadatattun kayan da suka suturta jikinta da kyau, duk da garin ba sanyi sosai amma ita har yanzu garkuwar jikinta bata gama sabawa da k'asar ba, shiyasa take jin sanyin da kyau.
Akan idonta suka zo a motar Ahmad, ya futo ya lek'a ta windown motar ya yima Ahmad magana ta sakanni ya nufo hanyar gidan, shi kuma Ahmad ya tsaya nan gida na kusa da nasu.
Zuba mishi ido raihana tayi tana kallon yadda yake takun shi har ya fara k'ok'arin bud'e k'ofar.
Saita kautar da idonta ga barin kallon side d'in da yake tana sauke ajiyar zuciya.
Shima yana shigowa idanun shi ita suka fara gani, ya bita da kallo kamar me karantar wani abu a tare da ita kafun ya k'arasa shigowa parlon ya zauna cikin d'aya daga kujerun da suka k'awata d'akin.
Kamar bata san dashi ba tace, "sannu da dawowa".
Shima ba tare daya d'ago ko ya sauya daga yadda yake ba yace, "fatan kina lafiya".
Tace, "lafiya lou".
Shiru ya sake biyo baya na wasu mintuna kafun ta kawo mishi ruwa me sanyi da marar sanyi da cup a tray.
Saida ya lumshe idonshi a lokacin da tazo gab dashi wani mayen k'amshi ya shiga hancin shi.
Ita kam neesa dashi ta zauna cikin d'ari d'ari kamar tana tsoron wani abu tace, "dama.... Dama Ina son don Allah nayi magana da Auntie idan babu damuwa".
Shiru yayi bayan ya had'iye makwarwar ruwan daya zuba a bakin shi yace, "Zan saita miki sim d'in Germany gobe sai ki kirata da kanki".
Da "toh" ta amsa shi ta tashi ta bar mishi parlon, khaleefa ya dafe kanshi yana tunanin yadda Auntie take son dagula mishi lissafi k'arfi da yaji. Fisabilillah yanzu wannan turaren, ga lallen k'afarta kamar ma bashi da niyyar bin ruwa koya daina zargadilar EVE ANO yana neman abincin k'asar Nigeria safe da rana da dare, kamar babu ita a gefen shi.
(Nikam nace kamar matar gaske🤔😜)
************
Yammaci ne misalin gab da sallar magrib.
Zaune take a