Showing 15001 words to 18000 words out of 288773 words

Chapter 6 - JARUMAR UWA Complete Book by Merhreeyaertou.txt

13 Oct 2025

227

inda yake saida atamfofi da materials yana samun rufin asirin, shi ya gina gidan shi k'arami a sharad'a inda aka Kai ruqayyah da farko.
A farkon aurensu ruqayyah Sam bata samu matsala da dangin miji ba, amma tafiya tana dad'a nisa matsaloli na b'arkowa ta hanyar k'ulle k'ullen makircin salaha matar yayanshi abubakar, su uku kacal mahaifiyar su ta haifa a duniya, amma kishiyarta nada y'ay'a ba laifi. A d'akin su daga Abubakar sai salees, sannan ta ukun su mace mai suna ziyada. Da bala'i da maseefa Inna mahaifiyar salees ta rabo su da anguwar sharad'a Suka dawo kusa da gidan yayan shi suke zaune opposite, a cewarta wai ruqayyah ta jashi wata duniya mai nisa donta raba zumunci, wayyoh Allah ai tunda suka dawo ruqayyah bata huta ba daga wannan maseefa sai wannan sharri, zaman lafiya dai yayi qaura sai zaman hak'uri da shiga d'aka Kai kuka, amma duk da haka ruqayyah tana iya k'ok'arin ta wajen ganin ta kyautata musu ba tare da la'akari da abubuwan da suke mata ba, ta fara haihuwar yaranta, raihanatu ce babbah sai Salma tana binta irin tazarar kwanikar nan, sannan khausar wadda itama tazarar ta da Salma irin ta raihana da Salma ne, daga nan ta jima bata haihu ba kafun ta haifo d'anta namiji mai suna al'ameen, da muhibba nabi masa sai auta jidderh. Su shida kenan ta haifa cip a duniya.
Toh Raihanatu itace ta kwashe tsanar da ake yima uwarta tsab saboda itace ta fari kuma a yaran kusan ita tafi d'aukar yanayin ruqayyah hatta da jiki da kuma yanayin magana da tafiyar su iri d'aya ce, abu na biyu daya k'ara zafafa gabar su shine yadda mutane suke son yarinyar wato ta taso da farin jinin mutane, Sam ita ba'a son nata haka, kuma ba komai yasa haka ba sai rashin tarbiyyar yaran nata.
Toh haka sukaita wannan rayuwa cikin takura da maseefar umma salaha, abun har yakai yaran suma sun shiga ciki tsakanin su da yaran gidan sai hantara da kyara tamkar basu had'a komai ba, ta b'angaren ci gaban rayuwa kuwa salees mahaifin raihana kullum k'ara ci gaba yake yi, yanzun haka ya k'ara gyara gidan da suke ciki ya zama ginin tsakiya na zamani. Babban parlour (main parlour kenan) me d'auke da bedrooms uku kowanne da bathroom a ciki. Ya sauyawa ruqayyah kujeru na zamani da kayan gado masu kyau, komai dai ya wadata kamar gidan amaryar da za'a kai yau ko gobe. Da farko har Gen ya sauya babbah, kafun daga baya yayi wearing solar, ya siya motar hawa mai kyau duk a shekarar, ya kuma tafi umrah tare da matarshi da mahaifiyar shi da kuma yayan shi, da suke matuk'ar girmama juna da zama lafiya.
Nan fa abu ya sake cin tura a gurin salaha, hassadarta da bak'in ciki muraran take nuna su. Duk da irin taimakon da salees yake musu kama daga abinci da suttura hadda solar suma yasa musu.
Tuntuni umma salaha taci mugun alwashi akan raihanatu da tafi tsole musu ido duk cikin yaran ruqayyah, sai dai bata samu isar da mummunar k'udurinta ba har saida wata rigima ta had'a suda ruqayyah (ummiey) a wani lokaci da hak'urin ta ya gaza, ta kasa jurewa cin kashin data zo yi mata har gida, a nan fa ita kuma ta samu damar futar da abinda yake cikin ranta, umma salaha taci alwashin indai tana numfashi sai taga uban da ya isa ya auri, ta rantse raihanatu bata da miji a duniya indai tana numfashi, (kuji sab'o fa🤔) wannan maganar ta dad'e a ran salaha kuma bata samu damar furtawa ba sai a lokacin, wannan case da tension da yake bin rayuwar raihanatu da mahaifiyar ta shiya haddasa har yau take rayuwa cikin k'unci, ba dama ayi sabga a familyn dangin ubanta in bata jeba magana, in taje kuma habaici da fad'ar magana, a tsaka mai wuyar da take rayuwa kenan, ga gori da cin mutumcin innah in ta tashi yi take tamkar ba jinin tace ita d'in ba, a yanzu haka anyiwa da yawa daga y'an matan family aure (da yake su ana gama secondary suke aurar da yaransu, babu wadda ta tab'a darawa higher institution sai raihanatu da har yanzu aure yak'i yiwuwa)
Sau biyar ana sa ranar aurenta ana fasawa, shiyasa malam salees mahaifinta yaga gara ta tafi makarantar a kan zaman jiran tsammanin warabukka.
An yiwa Salma k'anwarta aure yanzu harta haihu ma, khausar ma anyi engaged nan da 2 months za'a yi biki, da farko akwai wani guy da yake son raihanatu ilyas har yayi magana manya sun shiga, da za'a had'a bikin nata ne dana khausar d'in, to shima tana nan makaranta ya fasa suka karb'i dukiyar aurensu, ummien su ta kirata take kwantar mata da hankali kafun ta shaida mata suma sun fasa, bata bata labarin tijarar da Inna tazo tayi ba Cox bata son sake d'aga mata hankali, amma daga yanayin yadda muryar ummien take a sanyaye ta fahimci Inna taji labari tazo tayi tijarar data saba kenan.
Tashin hankali da kukan daya taso mata shiya haddasa ta futo daga hostel d'insu tayi bayan gari ta samu kan dutsen da takan zauna a duk lokacin da Ayman ya kawo mata ziyarar k'arshen mako, don b'oyewa su raheela k'awayen hostel d'inta komai,
Sai dai luckly tayi gudun gara ta fad'a gidan.... Tana Zama ba jimawa Ayman ya kawo mata ziyarar duk k'arshen mako, ya risketa a haka. Sai ya zamana sun raba damuwar tare, haka ya zauna ya shiga kwantar mata da hankali, duk da bata yarda tace mishi komai ba.

Raihanatu ba wai ta d'auki son duniya ta d'ora a kan duk samarin da take yi bane, a'a tashin hankalinta na kasa fahimtar k'addarar da take bibiyar rayuwarta ne, bata San ya zatayi da dangin mahaifinta ba idan ta koma gida hutu, bata manta yadda sukayi da hajiya innah last akan wannan saurayin ba,

"takanas dama nazo gurinki y'ar iya gadon bak'in hali da mugun abu, naji ance wani ya kawo kud'in auren ki za'a had'a ayi bikin ki dana khausar, toh saura shima ki kore shi da bak'in jinin ki da mugun abu, don a wannan karon idan har ya fasa auren ki k'auye zanje can garin su baban ku na nemo wani k'aton da yak'i aure in had'a ku kije can dama k'auyen shi yafi dacewa dake, mai bak'in mugun abu, ai wallahi yarinya kin had'u da wulak'anci tunda kika gado mugun halin uwarki tass ga tanan tana jina kamar wata ta Allah".
K'asa tayi da kanta tare da kife kan jikin gadon da take kwance had'e da dafe kanta da hannuwanta biyu, "wayyoh Allah ummie na wai me yasa hakan yake ta faruwa da ne? Shin me na rasa da duk wanda yazo zai aureni yake guduna? why! why!! whyyyy!!!". Sai ta k'ara fashewa da kuka mai ban tausayi, "Ashe ya fasa aurena shiyasa tun safe nayita kiranshi baya d'agawa" ta k'ara fad'a cikin damuwa da muryar kuka......
Ringing d'in wayar tane ya dawo da ita hayyacinta, ta mik'e zaune tana duba k'awayenta na d'akin d'aya bayan d'aya, Allah ya taimake ta duk bacci sukeyi data tonawa kanta asiri. Agogo ta fara dubawa, 1:30 am. Wayar ta d'aga ganin Ayman ne yake kiranta cikin wannan uban dare, abinda bai fiya faruwa ba sai da kwakkwaran dalili. "Hello raihanatu" shiru tayi mishi, "kina jina ko raihana nasan ba bacci kike yi ba"
Gyaran murya tayi cikin son b'oye damuwarta tace, "yaya Ayman ya kaje gida?".
"Lafiya ba lafiya ba raihana gani a gida amma har yanzu na kasa samun nutsuwa, hankalina yak'i kwanciya, sai tunani nake akan halin dana barki, don Allah raihana ki k'ara hak'uri bayan na dawo banje gida ba saida na tsaya gurin iya, ita take bani labarin abinda ya faru wanda in zaki mutu ba zaki tab'a bud'e baki ki fad'a ba, anan na fahimci duk abinda ya haddasa miki shiga wannan yanayin, tabbas ko waye dole ya shiga irin halin da kika shiga ace ana kawo kud'in auren ka ana karb'a har sau biyar! Ya Allah!" Numfashi ya ja mai tsayi taci gaba da fad'in, "sai dai kanshi ya yiwa raihanatu, asarar shine daya bari nagartacciyar mace kamar ki ta subuce mishi, kiyi hak'uri insha Allah mijin ki yana tafe nan bada jimawa ba, dama wad'an can duk cikin su babu mijinki shiyasa.... I'm sorry please raihana".
Share hawayenta tayi da tafin hannunta cikin cool voice tace, "na gode da kulawa yaya Ayman insha Allah zan ajiye komai a gefe na fuskanci karatuna, ni dama komai ya fuce a raina tuni".
Cikin jin dad'i yace, "Yauwa ko ke fa raihanatu, ki kalli kanki a mirror gobe from up to toe, zaki fahimci irin baiwar da Allah yayi miki wadda ba duk mata ba, kuma saboda su ba mijin ki bane shiyasa suka kasa fahimta har suke iya barin ki, baki rasa komai ba raihana hasalima irin ki a cikin mata k'alilan ne"
Murmushi tayi tare da rufe fuskarta kamar yana gabanta tace, "Kae Yaya Ayman Kai dai kake ganin haka tunda muna tare".
"Koda wasa dear ni kinsan a har kullum Ina fad'ar abinda yake gaskiya ne, yanzu dai ya kamata ki huta nima tunda naji muryarki komai dai dai zanyi sallah raka'a biyu sai na kwanta"
"Au zakayi sallar amma ni kace mun na kwanta? Toh nima sai nayi sallar kuwa zan kwanta".
Y'ar dariya yayi yace, "toh ai komai saida nutsuwa ake yinshi, ke a halin yanzu kina buk'atar kiyi bacci kwakwalwarki ta samu nutsuwa sannan ko".
"A'a fa kaga ma ni sai anjima dama wannan kira cikin dare kamar wani korarre". Raihana ta k'arasa fad'a k'asa k'asa.
"Iyyeh wato kin dawo dai dai har zaki fara ko? Toh shikenan ai zamu had'u ne Zan rama tuwo kika ci......"
Hararar wayar tayi tace, "Ina zaka ganni ma? Hun un ai kafun mu had'u ma nasan ka manta".
Dariya yayi yace, "toh shikenan zamu gani, dear sai anjima lokaci yana tafiya".
"Okay byee have a nice day".
"Aha".
Daga haka sukayi sallama, alwala ta d'auro tayi nafula raka'a biyu tayi addu'o'inta ta kwanta.
Shima Ayman dama akan sallayar yake raka'a hud'u ya k'ara kawowa yayi addu'o'in shi yasa pillow a kan sallayar ma nan k'asa ya kwanta.

_Toh sai muce Sweet dreams besties_.


*Germany*

Tun daga ranar da khaleefa ya ganta a restaurant bai k'ara sake rasa ta ba, yanzu wani lokacin ma tare suke shigowa gidan ko ya riga ta da mintuna, har yanzu basa yin magana amma sukan yiwa juna murmushi.
Yau khaleefa tun daya tashi baya jin dad'in jikinshi, hakan ya hana mishi futa ko ina yana kwance a gida, saida yamma ne da yayi sallah ya lallab'a ya futo ya zauna kan barendar gaban d'akin shi yana duba magazine.
"Assalam" akayi mishi sallama da siririyar murya. D'ago kanshi yayi ya kalleta, itace dai tsaye gabanshi sanye da farar doguwar riga tayi rolling kanta da k'aramin gyale. Sai ya ajiye jaridar hannun shi yace, "Assalamu alaikum ko hajiya ba wai assalam ba, as a Muslim ya kamata ki gyara". Murmushi tayi mishi cikin sakin fuska tace, "ayi hak'uri toh assalamu alaikum".
Shima fuskar shi da Murmushin yace, "waalaikissalam better ai ko".
"Uhm gaskiya ne nagode, am dama wani taimako nake nema a gurin ka, mukullin d'akina ne yak'i bud'ewa ko kuma nice na kasa ka taimaka mun dai don Allah".
Mik'ewa yayi yabi bayanta har suka isa wajen k'ofar, sai dai yana sawa ya bud'e, "ohh kaga abun mamaki tun d'azu nake wahala yak'i yi amma kai kana gwadawa". Murmushi kawai yayi yanzun ma, ta karb'i keyn ta a hannunshi tace, "nagode sosae".
Har ya juya zai tafi tace baka fad'a mun sunan kaba, a nutse ya juyo ya kalleta, "abdallah Suraj Abdallah amma zaki iya kirana da (khaleefa)".
"Woww nice name, Ni kuma sameera sulaiman, nice to meet you Mr Abdallah".
"Nice to meet you too" ya fad'a yana mamakin sauk'in kanta, tuntuni yake son mata magana amma baisan ko ta yaya ba, a fuska she look Soo classy shiyasa yake tsoron mata magana. Ita ma ta b'angaren ta tunanin da take yi kenan, he's wise ga kirki kuma ba girman kai, tana mamakin kanta da shiga hurumin shi ko Ina jin kanta da aji? Itace fa mace guda da kusan kowanne namiji keda burin k'ulla alaka da ita amma duk basuyi mata ba, da gayya take gwara kan maza, Sam bata d'auka za'a samu namijin da zai sauke mata duk wannan ajin a kusa ba.

Da sannu da sannu tafiyar khaleefa da Saleema ta fara zurfi har ta kaiga ya samu damar amayar mata da abinda yake ranta da wani yammaci, babu musu ta amince da soyayyar shi don dama yayi mata dai dai da ra'ayin ta.

************

Tsaye take gaban k'awarta Amna da take ta mata fad'a kan amincewa da soyayyar khaleefa bayan ga ra'ees nan yana ta bin kanta tak'i sauraron shi....."
Da sauri Saleema ta katse mata hanzari ta hanyar d'aga mata hannu, "kinga Amna ni dana san abinda zaki fad'a kenan duk da bazan fara ma baki labari ba, kinsan waye Abdallah khaleefa kuwa? Ya zarce tunanin ki Amna he's unique gashi very talent and intelligent ke ya zarce duk yadda kike zato, toh inba ganganci da wauta ba taya zan samu handsome guy kamar shi in wani tsaya kula ra'ees, toh bari in fad'a miki abinda baki sani ba ni ra'ees bai gama fucewa daga raina bama saida na had'u da Abdallah, na raina kaina, na raina ajina dana k'are da kula wani wai ra'ees".
Cike da d'unbin mamaki Amna take kallonta kafun tace, "kina cikin hankalin ki kuwa Anya".
Wani mugun harara ta balla mata, "zaki iya futa Amna banyi miki dole ki zauna dani ba, in ma hauka nake ina da wanda zai iya d'auka a yanzu, Soo babu laifi don kin kirani mahaukaciya".
Cikin hasala yanzu Amna ta mik'e tace, "Ni kike kora yau Saleema akan wani d'a namiji".
Saleema ta mata wani irin kallon raini tace, "Ko baki ji bane saina maimaita miki amna nace ki futa!!!".
Amna bata sake ce mata komai ba ta d'auki Jakarta ta fuce.
Tana futa Saleema ta kulle d'akinta tana jan tsaki, wayarta ta d'auko ta dannawa no khaleefa kira, bai d'aga ba ya katse ya kirata. "hello hubbie yau gaba d'aya ka manta dani". Saleema ce meyin wannan maganar cikin shagwob'a.
I'm sorry please kaina ne ya d'au zafi yanzun nan na shigo gidan ma".
"Ayyah ama sorrie hubbie yanzun kaci abinci ka huta anjima sai muyi magana"
"Nopp ba magana zamuyi ba Ina son mu had'u, kwana biyu nayi kewar kallon wannan kyakkyawar fuskar taki"
"Ayyah kasan nima nayi kewarka toh amma naga ai muna yin video call fa!!!".
"Video calk kad'ai bai wadatar ba Ina son na ganki zahiri bata waya ba".
Murmushi tayi mai k'ayatarwa hadda lumshe ido cikin salo tace, "okay yanzu dai kaci abinci plzz hubbie! see you later".
"Thanks lovely see you too".
Yana ajiye wayar ya soma cire takalmin k'afarshi, Ahmad da yake gefenshi yana danna waya yace, "yea! Saleema ce hala". Murmushi kawai ya mishi.
"Alhamdulillah abokina fa hala an tsinci dami a kala, abun mamaki wai kaine da soyayyah dumu dumu khaleefa, har yanzu Ina mamaki Allah".
"Hum meye abun mamaki Ahmad, daman can ban samu wadda tayi dai dai da ra'ayina bane".
Dariya Ahmad yayi sosai yace, "kasan Allah kada ka zurfafa don soyayyah daka gani kamar gwari ne ko riba ko fad'uwa......"
"Kaga! Kaga da Allah malam kuffa alaika haza..... kasan me bakin ka zai fad'a, kar ka soma had'a mun soyayyah ta da gwari, sannan ka daina yayatani, ga can su Mahmood sai damuna suke ba dama na bud'e wattsapp d'ina sai kaga jama'a sunyi mun caaaa haba Ina dalili soyayyah kamar kaina farau".
Dafa kafad'ar shi Ahmad yayi yace, "kayi hak'uri abokina yadda kake so haka za'ayi, Allah ya huci zuciyarka soyayyar taka ce tazo da salo na daban".
Bai kula shiba ya mik'e don Samar musu abinda zasu ci.

########

Kwanan Ayman biyar da zuwa gurin raihana k'anwarta Salma ta haifo d'anta namiji sankacece, dole ta tattara yanata yanata washe gari tayi sallama da y'an hostel d'insu tayo gida.
Da iya ta soma cin karo a farkon layi ta futo k'ofar gida tana raba yara fad'a.
Da fara'a sosai saman fuskarta ta k'arasa suka gaisa da iya, har iya na zolayarta, "kin tafi kin manta damu bulunbuk'ui amma daga jin kun samu baby shine kika wani tattaro kika taho da wata jakar kayan ki hargitsae hargitsae".
Dariya raihana tayi tace, "koma dai me zakice iya yau bazan kula kiba, ki lallab'ani in shige miki gaba gurin sabon angon da


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login