Showing 3001 words to 6000 words out of 288773 words

Chapter 2 - JARUMAR UWA Complete Book by Merhreeyaertou.txt

13 Oct 2025

225

zan haifa su zama jikokinku, labarin da zasu kallah kullum game da kansu ya zama, mahaifin su ya rasu malam shine mahaifina ke kuma mahaifiyata, bana son su samu damar da zasuyi d'igon tunanin akwai wani abu da ake b'oye musu.....".
Sai lokacin malam ya mik'e zaune sosai yace kiyi bayani yadda zamu gane yarinya, kina nufin kinbar gidanku kenan har abada? y'ay'a har guda nawa kuma kike nufi? Sannan ki dubi girman Allah ki fad'a mana shin suna da cikakken asali mai kyau ko kuwa ta wata hanyar daban kika samar dasu? Ko iya wannan kad'ai ne ki sanar damu don Allah mu futa daga rud'ani da kwokwanton da kika jefa mu ciki"

Mik'ewa tayi tsam ta shiga ta futo musu da takardu har guda uku, tace, "ko akwai wanda ya iya karatu a cikinku?".
Iya tace, "malam ya iya karatu don a k'auyenmu kafun mu baro garin har headmaster yayi a wata makarantar firamare".
Tashi ta sakeyi ta kaiwa malam takardun ya dudduba, bayan ya gama cikin farin ciki yace, "d'an Damm malam yayi kafun ya dubeta cike da tausayawa, shi kanshi idanun shi Saida Suka tara ruwan hawaye, Allah kenan mai yin yadda yaso a lokacin da yaso, sama da shekara ashirin suna neman haihuwa basu samu ba amma yau ga wata ta samu ta wata hanya daban. Sai yayi murmushi mai kama da dariyar yak'e yace, "Masha Allah yarinya! Allah ya futo mana da twins cikin qoshin lafiya ya hore mana abinda zamu ciyar dasu".
Iya kam cikin rashin fahimtar komai tace, "au ni da yake ban iya karatu ba shine ba za'ayi mun bayani ba malam".

Murmushi har lokacin akan fuskar malam yace, "zanyi miki bayani anjima insha Allah kuma muna maraba da samun d'iya irinki surayyah, munyi miki alk'awarin sirrinki zai tsira irin yadda kike so a gurin mu har abada".
Surayyah tana kuka tace, "nagode malam".
Tun daga wannan rana surayyah taci gaba da Zama tare dasu babu raini bare raina matsayin su, komai sukayi zata ci in aka d'auke fura da nono da gyad'a, yayinda take fama da matsanancin laulaulayi daya hanata sak'at, tana son taje hospital amma tana tunanin ta inda zata fara, so take ta siyar da duka gwala gwalanta sai ta samu wataccen kud'in da zatayi komai, ga magungunan tama duk sun k'are shiyasa yanzu komai taci saiya dawo, ita kanta iya ta fahimci magungunan sune suke taimaka mata ashe take d'an zama da kwari.
Bayan wata guda, kud'in da suke hannun surayyah da matar nan ta bata a mota duk sun k'are sakamakon taimakawa su malam da takeyi.
Gidan ciki da parlor parlor ne guda biyu sai fallen d'aki da sitting room da ba'a gama ba suke kiwon kaji a ciki, fallen d'akin suka bata duk da babu komai a ciki sai labulen net saboda sauro da k'atuwar tabarmar da take kwana a kai in ta shimfud'a bargo, mutanen anguwa y'an tsirko sunyi ta zaryar zuwa ganinta har sun gaji sun daina, wasu sun ganta wasu kuma harsu tafi tana d'akinta don ba wani son shiga mutane take ba sosai.
Most of the times she enjoy been alone, tun ba yanzu ba dama haka rayuwarta take.
Yau tun data karya da kunun tsamiya da iya tayi da k'osai bata koma bacci ba ta fad'a wanka ta shirya cikin d'aya daga abayoyinta da tazo dasu a akwati.
K'aramar jaka ta d'auka ta had'a duka golds d'inta a ciki da kud'ad'en k'ashashen k'etare, tayi kyau saboda har yanzu bata sauya ba kamar ba'a k'aramin muhalli take rayuwa ba, cikinta ya futo d'as ta cikin rigar, idan tana lissafe wannan wata na shida ne ya kama, shiyasa take son ta samu enough kud'i a hannunta kota samu ganin consultant doctor da yasan aikinshi don ya duba ta yadda ya kamata.
Lokacin data futo iya tana ta aikin d'auraye kayan ta dana su data wanke, "surayyah badai kin futo ba?".
"Eh iya na d'auka ma kin shirya? Wankin Dana ce ki hak'ura iya idan na dawo a kira yarinyar nan data wanke mun kwanaki ta yi mana shine kikayi?".
"Uhum! Babu komai surayyah ni wanki baya d'aga mun hankali nama gama bari na d'auko gyale na in muka dawo saina k'arasa shanyawa"
"Ai da kin shanya kawai iya saina jiraki".
"A'a idan rana tayi ba zamu samu yadda kike so ba, hayaniyar mutane a kasuwa kan iya sa miki ciwon kai ma ki dawo gida ba lafiya".

Kusan tare suka futo suka iske malam a zaure yana ta lazumi, sukayi mishi sallama suka huce.
Tunda suka futo ake binsu da kallo har surayyah ta gaji ta b'oye rabin fuskarta da gyale, bata San meye abin kallo a shigarta da ita kanta ma in banda abu na mutane.

Gurin Gold d'in suka soma zuwa, sark'a guda uku (mai hawa uku) sai zobe da abin hannu, sark'ar k'afa da d'an kunnaye, suka siya da daraja kuwa yadda ya kamata a take suka bata kud'in ta.
Daga nan sukayi banki inda aka sauya mata kud'in zuwa naira, basu dawo gidan ba har saida Suka siyi duk abin buk'ata na yau da kullum wanda zasu d'an jima musu iya cikinsu dai ita da iya da malam bai k'are ba.


Kwana biyu a tsakani iya ta rakata wani Private hospital taga likita, wanda bata dawo ba har saida akayi mata scanning aka tabbatar da k'oshin lafiyar abinda ke cikinta.



@@@@@@@@@



Daga nan surayyah taci gaba da rayuwarta cikin kiyayewa da bin dokokin likita, zuwa lokacin kuma komai yana tafiyar musu dai dai ita da sababbin tsintattun iyayenta da basu tab'a haihuwa ba Suka sameta a sama batare da ko sisin suba take d'awainiya kullum dasu.
Tana son yi musu abubuwa da yawa a gidan amma cikin jikinta yasa ta dakata, lokacinda ta shiga watan haihuwarta likitan da take gani yasa ranar da za'ayi mata CS saboda girman da yaran sukayi idan akace zata haifesu da kanta zata sha wahala sosai.
Malam da kanshi ya rakasu ita da iya har asibitin, tana kuka ta rik'e hannun iya tace, "su yafe mata duk abinda tayi musu na d'an zaman da sukayi tare, za'a shiga dani theatre ko na mutu ko na rayu iya Allah shi kad'ai yasan wanda zai faru a ciki amma don Allah idan har banyi tsawon rai ba akwai golds da Master card d'ina kiyi amfani dashi ku inganta rayuwar y'ay'a na bana son su tashi cikin wahalalliyar rayuwa, ba wai kuma don na raina matsayinku Kona abinda kuke dashi ba, a'a naci buri naci alwashi indai da raina ina numfashi yarana zasu samu kyakkyawar kulawa da tarbiyyah, toh ko bana raye ina son na cika wannan alk'awarin".

Iya tana kuka sosai ta sake rik'e hannun surayyah a nata tace, "ki daina irin wannan maganar surayyah, insha Allah zaki rayu tare da y'ay'an ki, ki basu irin tarbiyyar da kike so, ki kula dasu da kanki".

Tana kuka iya na kuka sukayi sallama, aka huce da ita tana d'agowa iya hannu.



Somun tab'i kenan, more comment more typing.




_Comment and share_
24/03/23, 1:58 pm - Merhreeyaertou ✍🏻✍🏻: *JARUMAR UWA*🧕
(Romantic luv storie)


_(Under the pens of merhreeyeart lerwerl and doctor Ferhyeez m usmern as in-identical twins)_


_Story and written by_



*Mareeyeart lawal*


Page two 2️⃣


An yiwa surayyah aiki cikin nasara inda aka ciro mata yara biyu maza kyawawa. Bayan nurses sun gyara su suka futo da yaran aka mik'awa iya da malam d'ai d'ai ita kuma me jego akayi d'akin hutu da ita, iya ma ita sam bata yaran take ba tafi damuwa da uwarsu, basu san ya zasu yi da yaran nan ba muddin ya zamana surayyah ta mutu, basu san daga takamaiman inda take ba bare dangin uwarta kona ubanta, hannun iya har rawa suke a yake a lokacin da ta karb'i yaran, "yarinya Ina fatan mahaifiyar su tana raye cikin k'oshin lafiya ko?". Iya ta tambayi wata nurse
"Eh yanzu haka tana bacci ne zaku iya zuwa ku ganta ma".
Ajiyar zuciya suka sauke kusan a tare suna hamdala ga Allah subhanahu wata'ala kafun subi bayan nurse d'in har zuwa d'akin da ta kama wato aminity, tana kwance tana bacci magashiyan tamkar mataciyyah hannunta d'auke da ledar ruwa drip yana shiga da kad'an da kad'an.
Sai a lokacin suka kalli yaran da kyau, kyawawa dasu Masha Allah, sai dai basu d'auki kamar uwarsu ba ko kad'an har hasken fatar, to ko kamar waye wannan suka biyo? Allahu a'alamu.
Surayyah ta d'auki wasu hours masu yawa tana bacci kafun ta dawo hayyacinta, da iya ta soma tozali tana aikin bama jariri guda madarar da nurse ta had'a ta koya mata yadda ake yi, yayinda d'aya yake ta aikin callara kuka, zaune ta mik'e da kyar idonta akan yaran babu ko k'iftawa tana kallonsu, "sannu surayyah" iya ta fad'a tana k'ok'arin matsowa kusa da ita don ta nuna mata abinda ta haifa.
Alhassan ta soma karb'a bayan ta rintse idonta tace, "wannan shine abdallah Suraj abdallah (Khaleefa)".
Na biyun ma ta d'auke shi tace, "Adam Suraj abdallah kai kuma (Ayman)".
Tambayar ta iya tayi bayan ta karb'e su, "sunan wa kenan kika sa musu surayyah".
Fuskarta da Murmushi mai ciwo, yayinda kwayar idonta ta tara ruwan hawaye tace, "iya Adam sunan marigayi mahaifina kenan, Abdallah kuma wani kwayar mutum ne guda d'aya tilo daya yi mun abubuwa da yawa, tarin alkhairan da bazan tab'a mantawa dashi da suba har abada a lokacin da yake raye".
"Allah sarki Allah ya gafarta musu". Iya ta fad'a tana sake kallon fuskar yaran, tana son tambayar ta dawa suke kama amma tana tsoron kada ta sake d'aga mata hankali duba da a yanzu hakan ma kuka takeyi daga fad'ar sunan yaran, toh amma ya kamata ko yaya ne taji wani abu ko guda a tare dasu, sai ta bari bayan ta nutsu kad'an sannan ta jefa mata tambayar "toh dawa suke kama kenan yaran? Naga dai basu d'auki komai naki ba surayyah".
Dam! Dam! Gaban surayyah ya fad'i, zuciyarta ta tsinke idonta ya sake tara ruwa, "wad'annan yara ba kammanin kowa suka d'auko ba iya saina azzalumin mutum! macuci! Mayaudari maha'inci kuma k'addarar rayuwata Suraj abdallah tofa, hak'ik'a iya ban tab'a shiga tashin hankali ba a rayuwa irin wanda suraj ya jefa ni, ya ruguza ni, ya ruguza mun rayuwata, ya raba ni da duk wanda zan rab'a naji sanyi a rayuwa, sai dai kuma nayi nadama nayi alk'awari zan kasance, *JARUMAR UWA🧕* Uwar da y'ay'an ta ba zasu tab'a kukan yin rashin wani abu ba a rayuwa, zanyi aiki tuk'uru na tabbatar da gaskiyar maganar nan da bature yace, "any thing man do, woman can do better" (amma fa idan ya had'u da me k'arfin zuciyar da wutar d'aukar fansa ke turuwa kullum a cikinta), zanyi istigfari iya, in nemi kusanci da mahaliccina, in mik'a mishi dukkan ragamar rayuwata sai yadda yaso yayi dani......"
Ita kanta iya ta tausaya mata, kuma taji dad'in furucinta na yanzu da yake nuni da nadamarta a fili k'arara, lallai yaran mu na wannan zamani sun tafi da yawa, in banda lalacewar zamani yaushe mace zata amince da namiji har wani abu na auratayya ya shiga tsakanin su, namijin daba mijin taba! Kae Allah ka tsare mana zuri'a kawai, gashi yanzu abinda ya haifar.
Abinda iya ke fad'i a ranta kenan tana kallon kyakkyawar fuskar yaron dake hannunta.
Toh tun daga wannan rana surayyah ta sawa ranta jarumta da k'arfin gwiwa na dole akan sabuwar rayuwar da take tunkararta, she promise to be the best mother ever to her children, k'arfin da yake zuciyarta ya kori duk wani rauni na jiki fata fata, satin ta guda a hospital d'in suka sallamota gida da dokar likitoci lifdi lifdi irin wanda duk wata mace da akayiwa CS bata Isa ta tsallake ba. A daren ranar kuma mallam yayi musu hud'uba da sunayen data zab'a musu.
Ko sau d'aya surayyah bata tab'a sawa ranta wani abu makamancin lanjere da kwanciya ba, komai da take yi kafun ta haihu bata fasa ba, washe garin ranar bakwai ta ba mallam kud'i ya siyo raguna uku manya aka yanka a matsayin hakika, tasa iya ta nemo mata wata mata anan saman anguwar su da zata tayata kula da yaran da kuma ayyukan gidan da suka yiwa iya yawa, ba don iya taso ba haka dai ta hak'ura ta kyale ta cox ta nuna tausayawa gare ta, duk da ita bata ga yawan aikin ba ta saba yin ninkin ba ninkin d'insu ma.
Halima wata macece da miji ya mutu ya barta da y'ay'a har biyar maza da mata take k'ak'anik'ayi da neman yadda zata rufa musu asiri, ta kanyi sirfau, wankau har ma da nanny a makarantun yara koda iya ta tuntub'e ta da batun yiwa surayyah aiki ba musu ta amince saboda duk rintsi aikinta a gida zaifi mutumci akan na makarantun yaran musamman da taji za'ayi mata kyakkyawan biya da d'an abinda surayyan take dashi.
Ta fara zuwa aiki tun a washe garin ranar da akayi maganar aikin da ita.

***********

Toh watan surayyah biyu da haihuwa ta karkab'e takardunta da 🏧 card d'inta ta futar da kud'i masu yawa aka soma gyaran gidan. Aiki akayi tuk'uru na rushe rushe da gyaran each and every part na gidan aka like shi da tiles da kayan gini na zamani, parlour ne dogo akayi mai d'auke da 3 bedrooms sai kitchen a gefe da fallen d'akin da take rayuwa akayi mishi bathroom sai toilet biyu da sitting room inda malam zai iya harkar malumtar shi.
Kud'in data narkar har saida su iya suka ji tsoro don basu san ta inda ta samo su ba, kuma kasancewar har yanzu basu ga wani abun zargi a gareta ba sai suka tafi a yadda tayi musu bayani kurum. (Abinda basu sani ba shine irin wannan kud'ad'en tana da shidan su a account d'inta banda kadarorinta)
Surayyah bata tsaya iya nan ba saida ta k'ara da siyo kayan abinci masu yawa da duk wani abun buk'ata da zasu jima suna amfani dasu basu k'are ba. Godiyar da malam ya dinga yi mata har saida ya had'a da kuka, ita kanta kukan ta dinga yi duk suka had'u suka narkar da zuciyar iya itama ta soma kukan.

Y'ay'an ta Masha Allah sun sake mul mul dasu kyansu ya sake futowa saboda tsabar kulawar da suke samu, a yanzun watansu uku amma inka gansu saika d'auka sun kai kusan wata biyar saboda girman da sukayi da wayo.
A ranar wata litinin da safe surayyah ta shirya ita da yaranta cikin shiga ta mutumci da kamala, takardun makarantarta ta d'auko tun daga primary har jami'a ta zura a cikin envelope ta d'auki jaka ta zuba duk abinda take tunanin yaran zasu buk'ata.
Ta d'auki khaleefa (alhassan kenan me sunan abdallah) halima ta d'aukar mata Ayman (alhussain kenan me sunan Adam). Tare suka futo suka tarar da iya na faman aikin suyar gyad'a me gishiri da yake bata rabo da k'ulle k'ulle.
Da fara'ar ta ta dube su tace, "y'ar daraja har kun futo".
"Eh iya ai munso muyi late ma".
"Toh Allah ya tabbatar da alkhairy ya bada abinda akaje nema".
Da ameen ta amsa ta nufi d'akin malam, shima addu'ar ya mata tayi musu sallama suka futa ita da halima.
Asibitin doctor fatahi ta nufa direct saboda shine kad'ai ta sani har take tunanin zata iya yi mishi bayanin abinda take buk'ata yayi mata.
Taci sa'a ranar a nan zaiyi aiki sai dai ance zai kai ten to eleven kafun yazo, guri suka samu suka zauna zaman jiranshi.
Koda yazo ita ta fara shiga ganin shi bayan ya daidaita zaman shi a office, bayani tayi mishi na aikin da take nema ga kuma shaidar kammala karatu tare da ita.
Sab'anin tunanin ta ashe ba mutumin kirki bane a gurin ba b'ata lokaci ya nemi had'in kanta, aikuwa tayi mishi tatas! Ta zage shi cikin fusata ta tattaro kan yaranta sukayi gida.
Daga iya har halima babu wanda ya tambayeta ba'asin sauyawarta ko yadda tayi dashi, ita ma kuma bata fad'a ba.
Bayan wata d'aya bata hak'ura ba ta sake futa duk da aikin ma ya fara futa a ranta duka, to amma saboda wasu abubuwa da yawa da suke faruwa da kuma tana buk'atar aikin don kud'ad'en asusunta su tsira shine ta sauya hanya.
Amma wannan karon govement hospital taje kamar za taga likita, luckly likitan ya karb'i takardunta da alk'awarin zai nema mata gurbi taje ta saurare shi kawai, ya karb'i phone no ta ta dawo gida amma wannan karon da fara'a sosai kan fuskarta.
Tayi jiran a k'alla kwanaki ashirin kafun ta samu kiran shi yana buk'atar ganinta urgent.
Ita kad'ai ma ta tafi ta bar yaran a


Related Ebooks

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login