Showing 27001 words to 30000 words out of 46304 words

Chapter 10 - MARYAM YAR KUNAMA COMPLETE- BY MRS BASAKKWACE .txt

Advertisement

23 Jun 2024

7119

da Zainab ba ƙaramin daɗi yai ma Khadija ,tasan komin banza zasu ƙara kusanci sosai da Zainab inta aura Yayan ta tazama familie su.








"Ummah zan tafi awo in nagama zanje in duba Hajiya wallahi Ummah tausayi Hajiya take bani bata da kowa sai Kamal gashi ya juya mata baya,wallahi Ummah duk abinda yake ba acikin hankalin sa bane,wata rana in abun ya sake shi zaki gans......!




Khadija ce kema Ummah magana yayinda take yafa mayafinta akai,Umma da take zaune falo tana kallon sunnah tv tawani katseta rai ɓace ta fara magana.




"Yimin shiru wawiya sauna in son shi kike kwashe kayanki ki koma gidan shi kinji,mara zuciya kamar ba bakatsiniya ba,anya kin sha nono na kuwa tantama nakeyi".






Murmushi tayi tace,"Ummah kenan Allah ua huci zuciyar ki na tafi sai na dawo".




Harara Umma ta wurga mata kafin tace,"tou adawo lafiya,zaki iya tuƙi kuwa?.




"Eh Ummah zan iya inshaAllahu".




"Allah ya tsare".




"Ameen Ummah".




Kafin tasa kai ta fita.




Tafiya ƙaɗan yakai ta asbitin bayan tayi parking motor ta ta fito da ƙaton tirtsetsen cikinta da haihuwa ko yau ko gobe ta rufe motor juyowar da zatayi wa zata gani ,da tun fitowar ta ya kafa mata ido kallon ta yake Kamar Khadija.




Itama kallon shi take da tun rabuwar su ko a ƙanya basu ƙara haɗuwa ba sai yau,haka kawai ta tsinta kanta da sakin murmushi.




Da mamaki yake kallonta shima murmishin ya sakar mata duk da suna nesa da juna,a hankali take ɗagana ƙafa tana takawa harta isa inda yake tsaye kusa da ƙofar shiga risefshon ɗin asbitin.






Tace,"Khalil ashe rai kanga rai ya bayan rabuwa".




"Lafiya lau,ya mai gidan?.




Jimmm ta ɗanyi kamar bazatai magana ba sai kuma tace,"waye ba lafiya?.




Cikin basar da zancen.


Yace,"wallahi Dadyne ba lafiya".




"Allah sarki Allah ya bashi lafiya".




Cike da tausayawa tayi maganar ya amsa da amin.




"Tou bari in shige".




"Tou Allah ya raba lafiya".




Amin ta amsa a taƙaice,kafin ta shige.




Bin bayanta yayi da kallo yayinda wani abu yake taso masa daga can ƙasan zuciyar sa.






Bata jima ba layi yazo kanta ta shiga taga Dr ta fito.




Abakin risefshon ɗin ta ƙara iske shi yana tsaye ya zuba hannu a aljihu,tunda ya ganta hankalinsa ya kasa kwanciya da ƙyar ya cireta a zuciyar shi ,shima saida aka haɗa da roƙon Allah gashi lokaci ɗaya da yayi tozali da ita ta taso masa da gyambon da yayi wiyar warkewa a zuciyar shi,dahar yanzun ya kasa kallon wata ɗiya a matsayin mace balle har ya fara soyayya yayi aure itako ta manta dashi har da cikin ta haihuwa ko yau ko gobe,wasu hawaye masu ɗumi suka zubo mai a kan kumatu sa hannu yayi ya ɗebo su,a hankali ya furta "ya zama dole in cireki a raina Khadija".






Harta gitta shi ta wuce sai kuma ta tsaya ya juyo ta dube shi da shima ita ya zuba ɓa ma ido baiso ya cika shige mata sabida akwai auran wani akan ta.




Uhm "yauwa muje in gaishe da Dad ɗin kafin na wuce".






"Maman ƴan biyu ",taji amfaɗa ta bayanta.




Juyowa tayi taga Saudatu ƙanwar Zainab ce,murmushi tayi suka gaisa.




"Ashe abinda ya faru kenan,Allah ya zaɓa miki wanda ya fishi Maryam bata kyauta na,Allah yasa da kin haihu kisamu miji ki aure ki aura wanda yafishi".






Gaban Khadija yakewa yayi yace rasssss jin maganan Saudatu satan kallon Khalil tayi ta wutsiyar ido taga hankalin shi baya kansu don sam bata so Khalil yasan Kamal ya saketa balle yai mata dariya yace Allah ƙara a zuciyar shi ko a zahiri bai nuna mata ba.






A zahiri idon shi na kallon wani waje yayida hankalin shi da zuciyar shi ke gareta,bai son ya fiye kallon ta kar zuciyar shi ta watgaje, yanajin abinda Saudat ta faɗa saida gaban shi ya faɗi amma wannan mijin nata baida mutunci da ciki ya sake ta,lallai kam in har ko bazawara ce tana haihuwa bazai bari wani ya riga shi ba zai nema a ɗaura musu aure inde ta amince.




Murmushi tayi kafin tace.........!








MORE COMMENT
MORE TYPING


_typing🖌️_



*🔘MARYAM🔘*
_(Ƴar kunama_)






NA MARUBUCIYAR:-👇
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
AWANI GARI
JIDDATOU
ND NOW
MARYAM ~ƳARKUNAMA~


MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)*






*(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)*
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo




WHATSAPP NUMBER:- *08167151176*
WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE*
GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*
IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE*
TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE*
SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE*








*PAGE 28*


*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
.
Murmushi tayi tana sauke sanyayyar ajiyar zuciya tana addu'an Alhamdulillah Khalil baiji ba hankalin shi bai wajan su kafin tace,"ameen ya su Mamah da Zee?.




"Wallahi suna lafiya,nazo gaishe da Maman ƙawata ne bata da lafiya".




"Allah sarki Allah yabata lafiya ki gaishe su".




"Za suji ki gaida Ummah da Abba da Fatima".




"Zasuji inshaAllahu".




Wucewa tayi ta shiga cikin asbitin.




Ɗan tsaki tayi Saudat ta cika surutun tsiya ko ina ruwanta da mata jaje oho.




"Muje ko",ya faɗa yana ɗan satan kallon ta.




Maganan sa ya katse mata tunanin da take.




Ƙaƙalo murmushi tayi kafin tace," tou".


Yana gaba tana bin bayan shi har ɗaki da aka kwantar da Dad ɗin shi.




Har ƙasa ta duƙa ta gaida mutanan ɗakin ta tambaye su yamai jiki suka amsa mata cike da sakin fuska,don duk sun santa a wajan Khalil ɗakin sa sai da aka mai da gaske aka rabashi da hotinan ta a waya da laptop aka gwada mai haramun ne matar wani ne,kowa da mamakin ganin ta dashi sukeyi.






Gaida Dad ɗin shi tayi ya amsa mata ba yabo ba fallasa ya tambaye ta ya mai gidan ya iyayeta tace lafiya lau ta ɗan jima duƙe kafin ta miƙe tai musu sallama ta wuce.






Khalil ya taka mata har gaban motor yana tason yai mata tambaya ashe bata aure yanzun amma rashin ganin fuska yasa shi haɗiye maganan sa.




Shiga motor ta tayi ta wuce.






Komawa ɗakin da mahaifinsa ke kwance yayi ya zauna.




Duban shi Dad ɗinsa yayi yace,"wannan ba yarinyar da kake neman kashe kan ka akanta bane,jibeta harda ciki ta manta da banzan soyayyar ka".




Daa mamakin su suka ga ya saki murmushi yana sosa ƙeya bawani damuwa a fuskan shi kamar ɗaun ko abin murmushi akayi bai yi saide ya taɓa baki yace," Dad ai yanzun bata da aure shima yaron da suka zaɓa fiye dani ya sakko masu ita,rabona ce dama ina ji a jikina zata dawo gareni wata ra.......!






"Dalla yi ma mutane shiru, sha-sha-sha,yanzun kana saurayi zaka aure bazawara",yayar shi aunty Aisha ta katse shi a hasale.




"Kai waya gayama ansaketa?.




Faɗar Dad.




Murmushi ya ƙara faɗaɗawa a fuskan shi yace," wallahi Dad ba ita ta gayamin ba jinayi suna magana da wata tana mata jaje,bama ta bani fuska miyi magana ba,koda na tambayeta ya mai gidanta kauda zance tayi da wata zance daban".




Tou mashaAllah in Allah yasa na tashi zan bincika inko haka ne sai na nema maka auranta aiba ita taƙi shi ba Aisha biyayya tayi ma iyayenta tana son shi aka raba su.




Aisha ba haka taso ba taso Dad ɗin su yace bai yarda ba,don akwai yarinyar ƴawarta da take mutuwar son Khalil amma ba ta ishe shi kallo ba,taso da Dad ɗin su ya samu sauƙi ta kawo masa batun Amira dole a cusa mai ita ya amsa,amma sai tasan yanda tayi ta cusa Amiran ta raba shi da wannan mai ruwan aljanun.




Fara'an Khalil ya ƙara faɗaɗa jin abinda Dadyn su yace.




Gajeran tsaki Hajiya Aisha tayi.






**********
"Lale marhaban ga ɗiyata ga ɗiyata ƴar albarka",cike da murna da farin ciki Hajiya ta tarbe Khadija.




Khadija faɗaɗa fara'a tayi tace,"Hajiyata barka da wuni".




Tana magana tana zama kan kujera.




"Sannu ya nauyi jiki,ya haƙuri Khalid yazo yana faɗa min abinda yaronan yayi nayi kukan takaici kunya yake hanani ɗaukan wayar ki wallahi".




Ƙasa tayi da kanta tana murmushi tace,"Hajiya bakomi nida shi ɗaya ne komi yima kaine".




"Hakane,Allah ya sauke ki lafiya".






"Ameen".




Sun jima suna hira sai wajan la'asar ta tafi gida,Hajiya sai hawaye take tana bata haƙuri.






***********
Maryamu ana ƙasar chaina ba abinda ta rasa Alhaji labaran ya luwaɗi da ita abokanan sa suyi satin su biyu suka tafi london anan ma bata canja zani ba tazama kamar texi no garej kowa ɗiba yake yi daga london suka wuce germany yawo kawai sukeyi a ƙasa she duniya tana ɗauka hot pics tana tura ma ƙawaye suna ƙara fasa mata kai suna zugata,ta ƙara haɗuwa da manya-manya gogaggun mata ƴan bariki da suka fita iyawa ƙara gogar da ita sukayi,can za mallamai masu mata aiki tayi tabar bokayen ta na nigeria.






************
Tunda ta tashi da ciwon mara tun cikin dare ta kasa bacci a daddafe tabari aka kira sallah asubah kafin ta rarrafa taje ta buga ma Fatima ɗaki,lokacin ta idar da sallah tana azkhar tace,"waye?,da ƙyar ta iya buɗe baki tace," sister buɗe kije ki buga ma bross Khalid yakai ni asbiti mara ta da baya na",a wahalshe take maganan.






Jin yanda take magana jikin Fatima rawa yakeyi ta taso ta buɗe ƙofar ta riƙeta tana mata sannu ta zaunar da ita akan kujeran dianing ,a sukwane ta buɗe ƙofar falon ta fita tai ɓangaran yayyun nata tana gudu.




"Ke lafiyar ki maike faruwa?.




Juyowa tayi taga yayan su Khalil ne ya shigo daga masallaci tace,"Yaya Khalil Yayace ba lafiya ƙila naƙuda ke damunta".




Kafin ta ƙarashe ya juya da sassarfa ua nufi part ɗin,bin bayan shi tayi ko kafin su shiga Khadija harta sakko ƙasa ta kwanta Allah kawai take ambato don ciwon ƙara tsanan ta yake yi.




Zage ƙwanjin sa yayi ya cin ciɓeta yace Fatima ta ɗauko key ɗin motor ta ,da sauri ta faɗa ɗakinta ta ɗauko key motor ta tafito yana manne da ita a ƙirjin shi yana hawaye tana ambaton Allah duk ya rikice,buɗe baya tayi yasa yace taje ta faɗa ma Umma su taho a motor shi ta duba part ɗinsu abuɗe yake ta ɗau key,hon yayi mai gadi ya buɗe masa yafita da gudu,da badin Khalid yayi saurin matsawa ba da ya take masa yatsu binsa yayi da ido yana mamaki lafiya shiga gidan yayi yana tambayan maigadi lafiya yace shima bai sani ba kamar dai Hajiya ƙarama ce ba lafiya da yake haka yake cema Khadija.






Part ɗinsu yanufa dai-dai lokacin Fatima tafito,kallon ta yayi yace "waye ba lafiya?




"Yayace ina tinanin haihuwa ce tace ciwon mara da baya".




"Ok jeki sa hijjab kizo muje asbiti ki ɗauko akwatin kayan haihuwar da ta shirya,amma karki faɗa ma Ummah don kar hankalinta ya tashi bata iya ruɗewa ba kin sani kuma kar Abba yaji shima kinsan yanda jikin sa yake".






Tou ta faɗa a taƙaice ta wuce part ɗinsu don cika umurnin yayanta,shima ya shiga ɓan garan su don canja kaya.






Khalil a mintina ƙalilan ya isa asbiti da yake asubah ce babu motoci kan titin ,yana zuwa ba'a tsaya neman file ba aka amsheta sai ɗakin haihuwa,Khalil sai hawaye yake kamar wani ƙaramin yaro,yanda yaga Khadija ta fita hayyacinta bai taɓa tunanin zasuzo asbiti tana da rayuwa ba,da ƙyar aka hana shi shiga ɗakin haihuwa.




Tsawan mintina kafin metro ta fito ta kira shi tace........!




_typing🖌️_



*🔘MARYAM🔘*
_(Ƴar kunama_)






NA MARUBUCIYAR:-👇
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
AWANI GARI
JIDDATOU
ND NOW
MARYAM ~ƳARKUNAMA~


MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)*






*(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)*
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo




WHATSAPP NUMBER:- *08167151176*
WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE*
GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*
IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE*
TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE*
SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE*








*PAGE 29*


*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*




Tsawan mintina kafin metro ta fito ta kira shi tace ,"ina kayan haihuwar da kuka zo dashi duk da akwai saura bata kai gaɓan haihuwa ba".






Dafe kan sa yayi da yake sara masa yace,"Hajiya za'a kawo yanzun".




Tou baida matsala ta faɗa tare da wucewa ta barshi a tsaye bata masa cikakken bayanin halin da ƙanwar sa take ciki ba,ɗan gajeran tsaki yaja kafin ya samu wata farar kujeran roba ya zauna ya rafka tagumi.




Bai jima sai gasu Khalid sun ƙaraso,suka tambaye shi ya take ya faɗa musu yanda sukai da metro,Khalid sauke sanyayyar ajiyar zuciya yayi yaja kujera ya zauna haka Fatimah.




Wasa-wasa saida Khadija takai magarib bata haihuba ta galabaita iya galabaita,ƙarfinta gabaki ɗaya ya ƙare duk tayi laushi,da ƙyar suka hana Ummah zuwa asbitin,suna ta kwantar mata da hankali,tai ta mata addu'a suma suna tayi.




Abban ta da ƙyar aka lallaɓa shi yaci abinci,don tunda ta dawo ita ke bashi abaki suna hira yanzun sauƙi Alhamdulillah amma da zazzaɓi yau ya wuni,wani lokaci har mamakin shi sukeyi kamar ita kaɗai ya haifa da ya ɗauke son duniya ya ɗaura mata,da badin mahaifiyar su ɗaya ba,da sunce bai son su,dalilin so da ƙaunar da Abban su ke gwada mata yasa suma suka ɗau soyayyar duniya suka ɗaura mata.






Daga ƙarshe akace aiki za'ai mata,saboda tasha wiya kuma ƙarfin ta duk ya ƙare,tsayuwa bata iyayi,Khalid yasa hannu a takaddan da za'a mata aiki,suka fita sallah magariba.




Fatima da dauriyan ta ya ƙare zuciyarta tayi rauni sosai,ba abinda takeyi face kukan tausayin Yayarta ita dai ƙaddarori kala-kala akan wannan auren da bai huce takai ciba,ga duk wa ƴanda aka kawo bayanta sun haihu sun tafi,itako har yanzun lokaci baiyi ba.




Nurse suna ƙoƙarin shiryata ,lokaci ɗaya taji wani ƙarfi yazo mata dawani nishi mai ƙarfi tana ko yunƙuri tanayi sai ga kan baby ya fito ,Nurse ɗin suka haɗa baki sukace Alhamdulillah,ɗaya ta temaka mata babyn ta ƙarasa fitowa ta miƙa ma wata ,ta fara ƙoƙarin goge baby.




Ɗaya ta gyara Khadija bayan ta ciro mahaifa,suka riƙeta suka kaita ɗakin hutu suka kwantar da ita akan gado aka ɗaura mata ruwa da allurai take baccin gajiya mai daɗi ya kwashe ta.




"Wata daga cikin nurse ɗin ta leƙo ta dube Fatima da take ta matsan hawaye,da fara'ar ta tace,"bar kuka ta sauka ansamu ɗa na miji azo abani goron albishir,babyn na cikin ƙoshin lafiya sosai,maman tana ɗakin hutu yanzun haka tana bacci".






Wani tsalle da kuwa da Fatima tayi tana faɗin "Alhamdulillah,zako ki samu goron albishir ba kaɗan ba".






Ɗaukan wayarta tayi ta kira Khalid an idar da sallah kenan zai fara azkhar yaga kiranta bai ɗauka ba harta katse ƙara kiran da tayi saida gaban shi ya ɓalle ya faɗi ya zaro ido yamiƙe jikin shi na rawa kardai Khadija ta mutu wannan kiran da Fatima ke mai.




Khalil ganin ya miƙe shima ya miƙe,rige-rigen fita sukayi suka nufi cikin a subitin da sasaarfa kowa da abinda yake saƙawa,dai-dai lokacin aka fito da baby acikin kayan sanyi yellow aka miƙa ma Fatima da take murmushi,kallon juna sukai Khalid da Khalil suka haɗa ido da mamaki suka ƙarasa wajan Fatima da take ɗaga Babyn tana faɗin "mashaAllah an samu Alhaji Basheer ko".




"Ta haihune ko har an gama aikin?,suka wurgo mata tambaya alokaci guda.




Murmushi ta faɗaɗa tana ƙanƙame babyn tace,"Allah ya taƙaita wahala tahaihu da kanta".




"Ina take" suka ƙara tambaya a tare.




"Tana ɗakin hutu tana barci,zamu iya shiga muganta dama ku na jira".






Ganin ba wanda yace abashi babyn yasa taci gaba da ƙanƙame shi.




Rige-rigen shiga ɗakin da take kwance da ƙarin ruwa sukayi suka taradda ita kwance ruwa na shiga jikinta tana bacci hankalinta kwance,fuskanta tayi fayau ta ƙara fari da kyau.




Shafa fuskanta Khalid yayi yace,"sannu da ƙoƙari Sister".




"Wallahi ko tayi ƙoƙari,ni anya nayi aure matata zata haihu ,inde haka ake haihuwa ba sauƙi".




Faɗan Khalil da yake zama gefen gado.




Murmushi Khalid yayi yace,"hakane wallahi haihuwa ba sauƙi mata na ƙoƙari Allah ya biya iyayen mu da gidan aljanna,kira Umma tabaka goron albishir mai aka samu?.




Ya ƙareshe tambayar da sigar tambaya,yana kallon Babyn hannun Fatima.




Murmurshi tayi tace,"Baby boy mai kama da ubansa,ya raba gardama".




Ɗan leƙa fuskan shi yayi ya yamutsa fuska yace,"Allah ya raya batare da yace zai ɗauka ba".




Khalil ya kira Umma ya sanar da ita ta sauka lafiya,Umma tai hamdala ta gaya ma Abba,sai murna yakeyi,dan danan suka fara kiran ƴan uwa na kusa dana nesa suna faɗan musu Khadija ta haihu,sai daga ƙarshe suka kira Hajiyan Kamal da kamar bazata ɗaga wayar ba sabida kunya sai kuma ta daure ta ɗaga ,bayan sun gaisa da Khalid ta mutunce yake faɗa mata Khadija ta sauka,tayi hamdala tayi murna ta tambaya wani asbiti ne ya faɗa mata aiko tace yanzun za'a kawo ta.




Ƴan uwa na kusa harsun fara zuwa asbitin kowa ya ɗau yaron mashaAllah suke faɗa Khalid ko da Khalil sunƙi ɗaukan yaron ƙememe gwamma Khalid ya leƙa fuskan yaron Khalil ko ko kallon banza bai isheshi ba.




Ana kiran sallah ishaa'i saiga Hajiya tazo ,Khalid ta kira ya fito ya ƙarasar da ita ɓangaran masu haihuwa,sai murna take yi gani jikanta jikinta har rawa yakeyi ta ɗauki yaron wani hawaye masu ɗumi suka zubo mata a fuska.




Jin ansa hannu a share mata hawaye yasata bin hannun da kallo Khadija ce da hayaniyan mutane yasata farkawa,fuskanta ɗauke da murmushi tace.........!








MORE COMMENT
MORE TYPING




_typing🖌️_



*🔘MARYAM🔘*
_(Ƴar kunama_)






NA MARUBUCIYAR:-👇
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
AWANI GARI
JIDDATOU
ND NOW
MARYAM ~ƳARKUNAMA~


MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)*






*(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)*
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo




WHATSAPP NUMBER:- *08167151176*
WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE*
GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*
IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE*
TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE*
SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE*








*PAGE 30*


*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*




Jin ansa hannu a share mata hawaye yasata bin hannun da kallo Khadija ce da hayaniyan mutane yasata farkawa,fuskanta ɗauke da murmushi tace,Hajiya dan Allah ki dena hawaye,nayi ma kaina alƙawari matuƙar ina raye bazan taɓa bari hawayen ki ya zuba a ƙasa ba,kona farin cikine".






"Mtsewww wawiya sauna zauna nan sun haɗa baki da ɗanta sunci amanar ku tazo tana hawayen gulma da munafurci kina wani share mata".




Faɗar Hajiya Bilki ɗiya yayan Ummah.




Kowa daskare wa yayi a ɗakin jin kalaman Hajiya Bilki ga dattijuwar tsohuwar nan.




Khadija kunya kamar ta nitse ƙasa jin kalaman yayar tata.






Hajiya ko ƙasa tayi da kanta zuciyarta na mata zafi ɗan kuka yaja mata jifa,da badin abinda Kamal ya aikata ba,har ƴar cikinta zata gaya mata magana.




Mtsewww "kunga tafiyata,don ba zan zauna inuwa ɗaya da maciya amana ba", ta ja tsaki a karo na biyu tare da saɓa jakan ta tayi waje.




Sai a lokacin Hajiya Sa'ah ta dafa kafaɗar Hajiya da kanta ke ƙasa tana ƙoƙarin tsaida hawayenta amma ta kasa tace,"Hajiya dan Allah kiyi haƙuri karki damu kanki akan kalaman Bilki,in ita tana miki wannan kallon muko bama miki,ba laifinki bane ,kana haifa ɗa kowa da halinsa,da halinsa kake ganin sa,don ba wanda yake haifa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login