Showing 21001 words to 24000 words out of 46304 words
Chapter 8 - MARYAM YAR KUNAMA COMPLETE- BY MRS BASAKKWACE .txt
Khalil,ta sace number aa awayan Khadija tana kiransa tana kushe Khadija yaci mata mutunci na ban mamaki,dalilin tsanar shi kenan ko sunan shi Khadija takira ta rinƙa tsaki kenan kamar wata tsaka.
Take tabi shawaran ƙawarta ta rungume zaɓin mahaifinta,tafara sakewa da Kamal.
Acikin lokaci ƙanƙani,ya mantar da ita wani Kalil da kalaman soyayyan shi masu sace zuciya.
Suna gama school da one month aka ɗaura auranta da Kamal taga gata,kuka da hawayen da damuwar da Abban ta yasa aransa na rabuwa da mafi soyuwar ƴarsa shiya kawo masa faɗuwa har ya samu mutuwan shashi guda.
Daƙyar aka raba Khadija da Abban ta tana kuka yana kuka akatafi da ita gidan mijjnta Kamal dake Yahya road unguwan rimi .
Maryam bata taɓa ganin Kamal ba sai randa aka kawo ango,ta ɗauka zata ganshi kalan ƴan cirani sai taga duk ya wuce tinanin ta,tunda ga lokacin ta kasa kwance da tsaye saida ta sace number shi awayar Khadija,tun tana kiranshi yana ƙi ɗauka har yafara ɗauka,ta ɓullo mai da ƙudirinta yaci mata mutunci naban mamaki,aiko tasha alwashi saita aure shi kota halin yaya.
Haka ko akayi ta faɗa fafutukan neman malamai,watarana tana ɗaki taji Momyta suna waya da wani malami aiko ta ƙudiri aniyar satan number shi ta gwada saar ta akanshi,aiko ta fake idon uwar ta ɗau number shi.
Sukai magana taje ta same shi,yanemi sai yabiya buƙatar shi da ita babu wani dogon nazari ta bashi haɗinkai,aiko taga aiki.
Ruwa a jallo Kamal yafara bibiyarta ta kafar sadarwa har suka haɗu suka fara masha'a.
Alokacin ne Khadija taga sauyi daga wajan mijinta,yadena bata kulawa da tattali,baima da lokacinta ada ko ko kitchen zata inde yana gida tare suke zuwa,yanzun ko baida lokacin zaman gida balle yama ci abincinta,ta kira Maryam in abu ya dameta tabata shawara na banza tai ta dukan cikinta.
Wannan shine taƙaitaccen tarihin su Khadija har yakai Kamal da auran Maryam,acikin rashin hayyacin sa.
Ƙaran wayarta ya fargar da ita ya dawo daga duniyar tinanin da ta lula,jawo wayar tayi da hannu ɗaya ta juyo ta taga Zainab ce,ɗagawa tayi tana murmushi tasa akunne baki ɗauke da sallama,gaisawa sukai kwana biyu,ta tambayi Zainab yaushe zata shigo tace mata da week end,sun ɗan taɓa hira,kafin suka aje wayar.
Miƙewa tayi jin ana kiran la'asar yasa ta miƙe tana tunanin mainzata dafa,ban ɗaki ta shiga tai alwala tafito tai sallah,bayan ta idar ne ta fita zuwa kitchen bayan ta sa ɗan ƙaramin hijjab ɗinta da ya zamo mata abin shiga kitchen ko zaman falo,gashi gobe zataje awo,da wuri zata tashi ta gama aiki tafita abinta.
Tuwon shinkafa tayi da miyan kuɓewa bayan ta sauke ta haɗa musu juice ɗin kokumba,ta ɗebi nasu takai musu,kafin ta kwaso wa ƴanda suka ɓata ɗazun takai kitchen ta wanke tass ta kwashe plates ɗinsu takai dianing ɗinsu,kafin ta kwashe duk abinda zatai amfani dashi ta kai bedroom ɗinfa,don inta shiga da magrib bata fitowa sai washagari.
Tafito kenan ita kuma tana shigowa,kallon juna sukai a ɗage,Khadija ko mamaki take ashe matar gidan bata nan ,ji yanda ta fita bako mayafin kirki kamar ba matan aure ba.
Itako harara ta galla ma Khadija ta wuce tana kaɗa body soso da take sawa a ɗauka nata ne.
Taɓa baki Khadija tayi ta shige ɗakin ta.
Haka rayuwa taci gaba da tafiya ma Khadija duk wani bauta ita keyi ma Maryam,dafarko Kamal na hanawa,yanzun ko bashi iyawa yana kallo Maryam kecin mutuncin Khadija,Khadija ko tayi alƙawarin bazasu taɓa ganin gazawar ta ba,ga cikin ta ya ƙara tsufa sosai don takai wata takwas,ahakan har wankin unders take ma Maryam da guga,tai ta zaginta wai suna cidata tana ta ƙatuwa tai ƙaton kashi ko kuɗin cizo ta kasa haifa,saide tayi murmushi,ta gode ma Allah da cikin nan ɗan sirri ne,ba falasashe ba,har wannan lokacin Maryam na kawo gardawa gidan ko ta fita ta same su,ko Kamal na nan sai de tace ƙanan tane.
"Kewace iriyar ƴar iska ce jaka jahila insaki wanki tun safe zan saka kaya amma ki kasa wanke min su".
Cikin tsawa da hargagi take cima Khadija mutunci dake tsaye tayi ƙasa dakai ,zuciyarta na mata matuƙar zafi da turƙiƙi.
Ba zato ba tsammani duk sukaji muryanda da dukkan su saida suka waiga a razane tun balle Khadija.
"Wanake gani kamar Maryam ,mai yakawo Maryam gidannan da har take ci miki mutunci?.
Tana maganan tana ƙara shigowa cikin falon.
Maryam tayi matuƙar razana tana komawa bay.
*INA GODIYA SOSAI DAJIN DAƊI YANDA KUKE WATSO MIN COMMENT MAI SHARHI,MUSAMMAN FANS ƊINA NA GROUP ƊIN ƳAR KUNAMA FANS,ALLAH YABAR ZUMUNCI DA ƘAUNA,HAR A ALJANNA FIRDAUSI,INA ƘAUNARKU KAMAR YANDA KUKE NUNA MIN SO,GASKIYA KUNA ƘOƘARI DA ƁATA LOKACI WAJAN FARANTA MIN RAI TA HANYAR SHARHIN KU😍😘😍*
_typing🖌️_
*🔘MARYAM🔘*
_(Ƴar kunama_)
NA MARUBUCIYAR:-👇
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
AWANI GARI
JIDDATOU
ND NOW
MARYAM ~ƳARKUNAMA~
MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)*
*(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)*
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo
WHATSAPP NUMBER:- *08167151176*
WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE*
GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*
IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE*
TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE*
SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE*
*PAGE 22*
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Maryam tayi matuƙar razana tana komawa baya,ta jingina da bango,tasan halin Fatima,sam bata ɗaukan raini.
"Yayah Khady maike faruwa ne?.
Ta kuma tambaya akaro na biyu.
Harara Khadija ta galla mata tace,"idon ma tambaya,yaushe kuka dawo?.
Khadija tai saurin canja akalan ansan tambayan da wani tambaya,gudun kar Fatima taima Maryam ɓarin makauniya.
Yaya nibashi nake tambaya ba,mai yakawo Maryam gidan ki da safe acikin wannan shigar Brother bai nan ne?.
"Kishiyata ce",tafaɗa cikin tsawa a taƙaice,tare da zama kan kujera tana zuba ma ƴar'uwanta ido,da lokaci ɗaya kamanin ta ya sauya,tana kallon Khadija tana kallon Maryam da tai tsuru-tsuru kamar kaza a ruwan zafi.
Takawa tayi tana rangaji ta nufi inda Maryam ke tsaye ta tsaya a gaban ta tana binta da kallo daga baya ta saki wani murmushin da ita kaɗai tasan nufin shi tace,"da gaske Kamal kike aure Maryam mijin aminiyar ki ,wallahi inde haka ne kin cika asararra butulu,wai mai yasa baki ramin kanki saide ta rinƙayi kina shiga?.
Cikin kakkausar murya take maganan ,ranta haɗe kamar hadari.
"Fatima kima Allah kibar maganan nan kizo mu shiga ciki".
"Wallahi Yaya bani bari,tun ina ƙarama ban taɓa son Maryam ba don ruwa munafukai gareta,bantaɓa ƙaunar zaman ku da Maryam ba,kawai don naga kina sonta yasa ban gwada miki ba".
Cikin muryan kukan da ta kasa danne shi saida ya suɓuce mata take magana.
Jikin Khadija yayi matuƙar sanyi zuciyarta sai wani bugawa yake fat-fat kamar zai fito waje.
Mtsewww ba'a aure aka aure ta,da zak......!
Maryam ta fara magana cike da tsan-tsan rashin kunya,bata kai ƙarshe ba taji saukan wani wawan mari a bakinta.
Dafewa tayi ta sulale ƙasa ta saki ƙara.
Fatima binta tayi ta danƙo wiyar riganta ta miƙar da ita,ta ɗaga hannu zata ƙara kashe Maryam da mari da duk ta gama firgita yanda taga gaba ɗaya kamanin Fatima ya sauya tun ba yau ba,tasan Fatima fitinan na ce bata ɗaukan raini musamman abinda zai taɓa ƴar uwarta sai inda ƙarfinta ya ƙare.
Hankaɗa ta akayi ta faɗi ƙasa timmm ta buga ƙugu ,azaban zafi ya ziyarce ta,amma ba wannan bane damuwar ta,ta maza tayi ta miƙe tana kallon wanda ya ture Kamal ne ke tsaye yana binta da mugun kallo.
Khadija sakan baki tayi ta kasa ko motsi ƙarfin hali irin na Fatima,ko ita da akai mawa ta haƙura,balle ita da yanzun ta san da zancen.
Murmushin da yafi kuka ciwo Fatima tayi kafin tace,"wallahi Kamal kayi asara,butulu kawai,ɗan tsako kaci ka goge bakin ka,anya kai ɗan halak ne ba shege ba,ka rama alkhairi da sharri,wallahi kaban mamaki, saƙo ka bada aje a gaya ma iyayen gidan ka,da suka maida ka ɗa,da har wata ƳAR KUNAMA taganka ta aura,amma sam dakai da Maryam Khadija bata cancanci haka daga gareku ba".
Cikin dakewar zuciya take maganan,batare da shayi ko shakka komi ba.
Dubanta yake a wulaƙance yace," ke mara kunyar banza,da arzikin ubanku da babu shi,da temakon ubanku da babu shi,dama can Allah ya hukunta sai nayi kuɗi nakai wannan matsayin,balle akan ɗan dukiyar da bai taka kara ya karya ba zakuzo kuna min gori don haka daga ke har ita Khadijan...........!
MORE COMMENT
MORE TYPING
_typing🖌️_
*🔘MARYAM🔘*
_(Ƴar kunama_)
NA MARUBUCIYAR:-👇
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
AWANI GARI
JIDDATOU
ND NOW
MARYAM ~ƳARKUNAMA~
MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)*
*(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)*
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo
WHATSAPP NUMBER:- *08167151176*
WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE*
GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*
IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE*
TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE*
SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE*
*PAGE 23*
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Dubanta yake a wulaƙance yace," ke mara kunyar banza,da arzikin ubanku da babu shi,da temakon ubanku da babu shi,dama can Allah ya hukunta sai nayi kuɗi nakai wannan matsayin,balle akan ɗan dukiyar da bai taka kara ya karya ba zakuzo kuna min gori,kuɗin uban naku da bai wuce cefanan wani gida ba,tou dake da Khadijan ba abakin komi na ɗauke kaiba,kai harda ma iyayen naku,don haka Khadijan ma bana buƙatar ta,nasake saki uku".
Dukkan su da tsan-tsan mamaki suke kallon shi,ya rufe ido yana zuba rashin mutunci,jikin Fatima yai sanyi Allah sarki,Abba yana ganin yaba ma wanda zai riƙe mai Khadija amana,ashe abin ba haka bane,koran maciji ne acikin koron ciyawa,macijin sara ka noƙe,daga ƙarshe harda mata sakin wulaƙanci baccin cin amanar ta da sukayi da ƙawarta.
Khadeeja ko wani shock taji tunda ga ɗan yatsarta na ƙafa har zuwa ƙwa-ƙwalwar jikin ta,jin kalaman shi na saki,ko amafarki bata taɓa tunanin duk cin mutuncin Kamal ba zai taɓa sakin ta,gashi yau don cin fuska yaci mutuncin ta agaban ƙanwar ta da kishiyar ta,saki,danne zuciyarta tayi ta miƙe take taji wani ƙarfi ya zo mata wanda ɗazun bata samu ba,ta tako tazo inda Kamal ke tsaye yana ta zare ido,don yasan yayi suɓul da baka,saida ya furta tsoro ya kama shi ,lokaci ɗaya zuciyar shi ta cika da tarin dana sani.
Murmushin da yafi kuka ciwo ta sake masa tace,"alhamdulillah,in rabuwa dakai alkhairi ne Allah ya tabbatar min,Allah kar ya haɗa ni dakai ko amafarki, Allah yasa in haifa wannan cikin babu rai don de da inrinƙa ganin shi ina tunawa da butulun ubanshi,ajawo shi inuwa ya maida mu rana.
Tunda ta gaya kalman ciki yake binta da kallo yaƙara tsorata ya koma baya yana kallonta.
Maryam a tsorace tace,"ciki Kamal wallahi banaka ban........!
Kan ta ƙarasa taji saukan mari a bakinta,tai saurin haɗiye maganan ta tana ƙanƙame jiki.
A zuciye Khadija ke nuna ta,tace,"ance miki ban kawo budurci gidan miji bane,a asbiti bayan Dr yagama anfani dani yacire min ciki kafin ya ɗinka ko yaya,wallahi kibini a hankali,ga mijinki nan ki tambaye shi yanda ya sameni.
A tsorace mai cike da tarin firgici Maryam ke kallon Khadija,ya akayi tasan mai ta aikata ranan da suka haɗu da Dr Hadi a aabiti.
Murmushi Khadija ta ƙara sake mata,mai cike da ma'anoni da yawa,kafin ta dubi Fatima tace muje kitayani haɗa kayana masu mahimanci".
Kamal jiki na rawa yayo kan Khadija yawani rungumeta yana faɗi "wallahi babu inda zakije,ni ban sake ki ko ɗaya ba".
Tattara ƙarfinta tayi ta hankaɗa shi,saura kaɗan ya faɗi ƙasa yai ta maza ya miƙe,binshi tayi ,tana nuna shi da ɗan yatsa rai ɓace tace,"wallahi Kamal inkai jahili ne niba jahila bace,a gaban shedu matarka da ƙanwata kabani saki uku,kuma ko ba agaban su bane wallahi na saku,don bazan yi auran zina ba,kalan na mai ɗaki da soso,in zaka mutu wallahi sai nabar gidanan in koma inda akasan mutuncina".
Zuba guywowinsa yayi a ƙasa ya haɗa hannuwa alaman lallalshi yace,"kima Allah ki rufa min asiri,Fatima don Allah kisa baki,amaida shi saki ɗaya tunda ta nace ta saku".
"Wallahi karka ƙara kiran sunana dawannan ruɓaɓɓan bakin naka,tsintaccen mage dama ance baya mage".
Ba tare da ta saurare mai zai faɗi ba ta tura ƙofar ɗakin Khadija ta shiga.
"Khadija don darajan Allah dagaske kina da ciki,shine kika ɓoye min".
"Ba cikin kabane a kwararo tayi shi,in ba munafintata kake yi ba kace min baka da lafiya kana binta cikin dare kana cinta, ban sani ba,bayan kamin alƙawarin bazaka taɓa kusantan taba".
Maryam ke maganan cike da tashi hankali.
Khadija sa tsan-tsan takaici take kallon Maryam,kafin ta juya tana ɗaga ƙafa a hankali sabida cikin yayi matuƙar nauyi ya tsufa tana gafda haihuwa,da ido Kamal ke binta sam bai taɓa lura da yanayin mu'amalan Khadija kalan na masu ciki bane sai yau,shiga ɗaki tayi ta iske Fatima ta kusa haɗa mata kayan drawer ta buɗe ta ɗauko ta kaddun asbitin ta ta fito yanda ta barsu haka ta iske su ko wannen su yayi tsuru da abinda yake saƙawa a zuciya.
Wurga ma Kamal result ɗin asbitin tayi kafin tace,"wallahi matarka ta ƙara sheganta min ɗa sai na kusa kasheta da bugu,sannan muje kotu ta gayamin yaushe taganni da gardi suna shigo gidana in mijina ya fita,miye bamu sani ba,wallahi Kamal ko ba kasake ni bazan taɓa bari ka kusance niba,sai kayi gwajin ƙanjamau".
Tana gama faɗa ta juya ta shigewar ta ɗaki,gabanta na dukan uku-uku.
Dukawa yayi ya kwashe result ɗin ya fara dubawa,in zai iya tunawa last sex ɗin da yayi da ita ,ita dakanta ta nemeshi ta takura shi ya biya mata buƙata,wata biyu kafin auran Maryam tabbas wannan cikin nashi ne don yanzun yakai kimanin wata takwas harda kwanaki,dudduba sauran yayi yaga Edd ta 7may,sauke nauyayyan ajiyar zuciya yayi.
Mtsewww "ka yarda da takaddun bogi a raina maka wayo,kai da ba namiji ba,baka aiki".
Maryam ke magana a ƙufule.
Kallonta kawai yayi da shanyayyun idanuwan sa da suka canja launi zuwa ja,yace,"in ma shege ne nawa ne ina so,ke wata mu nawa ko ɗan shegen kin kasa ɗauka".
"Ta gidan ubanwa zan ɗauka,baccin lagwani yafika amfani mtsewwww".
"Ni kike zagi Maryam?.
"Na zaga ɗin".
Tamaida mai martani a taƙaice.
Ƙwafa yayi batare da yace mata komi ba,ya ya juya yaje jikin babban ƙofar falon ua kulle ya sa key ɗin a aljihu,yasan haka kawai zaiyi yahana Khadija fita tunda bata da key.
Dai-dai lokacin suka fito da akwatina a hannun su cike da kaya,tana sanye da doguwar rigan atamfa ta yafa gyale,batare da sun kalle kowa na falon ba suka kama hanyar waje.
Murmushin mugunta yayi yace............!
MORE COMMENT
MORE TYPING.
_typing🖌️_
*🔘MARYAM🔘*
_(Ƴar kunama_)
NA MARUBUCIYAR:-👇
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
AWANI GARI
JIDDATOU
ND NOW
MARYAM ~ƳARKUNAMA~
MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)*
*(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)*
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo
WHATSAPP NUMBER:- *08167151176*
WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE*
GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*
IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE*
TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE*
SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE*
*PAGE 24*
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Murmushin mugunta yayi yace,"basai ku fitan ba na gani".
Batare da sun kula shi Fatima ta murɗa ƙofar taji akulle,ta gir-giza tabbas a kulle.
Khadija cewa tayi ,"barshi ,kwaso kayan mukoma ɗaki,duk abinda zan kulashi yake nema kuma wallahi bazanyi ba".
Komawa ɗakinta sukai batare da sun kalle ko ɗayan su ba,balle su kula su,abin ya ɓata ran Kamal ba kaɗan ba,yaso suyita musayar miyau.
"Kira big Bross ki faɗa masa,wallahi jin gidanan nakeyi kamar wuta".
Khadija ta faɗa tana ƙoƙarin zare mayafinta.
Fatima ɗaga wayarta tayi ta kira yayansu ,amma bai ɗaga ba,kiran Khalil tayi ringing biyu ya ɗaga,bayan sun gaisa take faɗa masa mai yake faruwa,ya kiɗimu sosai ba kaɗan ba,jin halin takura da matsin da ta fuskanta ahannun wanda sukai ma gata suka maida mutum,ranshi ɓace yace gashinan zuwa.
After 30munites yanayin yanda ake bugun ƙofar falon kaɗai ya tabbatar masu Khadija Khalil yazo,Khalil bai iya fushi ba ko yaya,tun yana ƙarami bai da haƙuri,duk wanda ya nuna masa ɗan yatsa sai ya karya ƴar banza.
Kamal dake kwance kan kujeran Khadija har bacci ya soma ɗiban sa,yaji ana tokarin ƙofa kamar za'a karya,a sukwane ya miƙe yana faɗin waye,wani mahaukaci ne?.
"Ubanka ne,Uban matambayi".
Khalil yabashi amsa a ƙufule.
Jin muryan Khalil saura kaɗan ya saki fitsarin da yake ta matsewa a wando.
"Zaka buɗe min ƙofarnan ko sai na kira masu cire ƙofa sun karya min shegiyar ƙofar?,tunda bata gidan ubanka bane".
A tsorace yake,gaban shi faɗuwa yake,buɗe ƙofar yayi ya koma gefe,Khalil naji anbuɗe yasa ƙafa ya banko ta ta buɗe,yasa hannu ya kwashe labulayan ya watsa su kan ƙofa,cike da takun ƙasaita ya shigo falon yana ƙare ma Kamal kallo yana kallon falon.
Murmushin da shi kaɗai yasan ma'anar sa kafin ya busa iska daga cikin bakinsa yace,"Khadijaaaaa".
Cikin ɗaga murya.
Duk da suna jiyo abubuwan da ke wakana a falon,amma basuyi yunƙurin fitowa ba,don kar Khalil ya haɗa dasu,yafa mayafinta tayi ta fito.
Kallon ta Khalil yayi,duk tayi baƙi kuma idanuwanta sun faɗa girgiza kai yayi ya sa ɗan yatsa ya ɗauke hawayen dake ƙoƙarin zubowa kan kumatun shi yace,ku fito da kayan kuzo mu wuce".
"Kai ma Allah Bros Khal.......!
Hankalin shi tashe yayo kan Khalil yana masa magana,bai ƙarashe ba Khalil ya dakatar dashi ta hanyar ɗaga masa hannu,maida baƙin glass ɗin dake hannun shi yayi kan fuskan shi ya yamutsa fuska yace,"Kamal nabaka nan da 5hours ka tattara kabar mana gidan uba tunda ba gidan ubanka bane,da har kake da zarra da ƙwanjin cin mutuncin ƴar masu gida a gidan ubanta,ka wulaƙanta ɗiyar da iyayenta suka ɗauke ka suka maidaka mutum da kowa ke sha'awar ka,in ka manta in tina maka,wannan gidan gidan Muhammad Basheer ne Ba gidan Kamal Musa ba".
Kalil na magana yana murza ƴan yatsu suna fidda ƙara,cike da kakkausar murya yake ma Kamal magana,da duk ya gama tsurewa,yanayin da yaga Khalil ɗin sam ba wasa a fuskan shi balle ya kawo mai raini.
Dai-dai lokacin su Fatima suka gama fita da kayan su,juyawa yayi yabi bayan ƙannan shi,har yakai bakin ƙofa,ya juyo yai murmushi yace,"Kamal da ka rubuta barin aiki da karka rubuta yazama dole kabar aiki a ƙarƙashin kamfanin mu,don gaba bamusan gadar zaren da zaka ƙulla ba ƙila kasa a kashemu ka cinye komi namu,don bamu kake so ba dukiyar mu kakeso".
A tsure yake kallon Khalil,zufa kawai take keto masa duk sanyin Ac dake ratsa falon bai hana Kamal zufa ba,wannan wane irin jarabawa ce ta same shi lokaci ɗaya,ya rasa komi a lokacin da baiyi zato ba,ya manta sam ba'a basa takaddun gidannan ba,ya zauna yana feleƙe da rashin mutunci,zama yayi kan kujera daɓas yana faɗin innalillahi,wa inna ilaihi raji'un.
*😱😱😱😱😱😱WAI DAMA GIDAN BADA GUMIN KA KA GINA BA,NA ABBAN KHADIJA NE,OFFICE ƊIN MA DA KAKE TAƘAMA DASHI SU SUKA ƊAURAKA,LALLAI KAM GATA YAYI MAKA YAWA*
Khalil sa kai yayi yabi bayan ƙannan