Showing 3001 words to 6000 words out of 46304 words
Chapter 2 - MARYAM YAR KUNAMA COMPLETE- BY MRS BASAKKWACE .txt
tace,"tou ai gaskiya ta faɗa miki,zaki ɗaurata hanyar bin bokaye,lallai Khadija batasan waye keba,duk da tare kuka taso,ahh makashin ka na gindin ka inji masu iya magana mutum mugune ko ya mutu sai an ɗaure shi mutum mugun ice,wallahi Maryam kinci ka ~ƳAR KUNAMA~,kiji tsoron Allah ki bar mata mijinta ko zataji daɗin aure,Allah sarki baiwar Allah wata uku da aure ta fara fuskantan ƙalubalen rayuwa,ta ƙare maganan da sigar damuwa.
Mtsewww kefa Zainab ba mutunci ne dake ba,ba dama mutum ya gaya miki magana kita faɗa masa baƙaƙe,mtseww tou gobe Kamal zai tura gidan mu".
Ƙwalalo ido tayi tana kallon Maryam tana girgiza kai.
"Miye kike girgiza kai kamar ƙadangaruwa?.
"Wallahi Maryam ke ba ƴar halak bane,tashi kibar mana gida ko in lakaɗa miki bugun tsiya daga yau bani bake,don bazaa haɗa baki dani aci amanar baiwar Allah na,haƙƙinta bazai barmu ba".
Zainab jikinta harrawa yake idonta na juyawa tana kalle-kalle.
Maryam tasan halin Zainab zata iya yi mata komi,Maryam jida ƙarfi take,saɓan jakar ta tayi tafice,bata iske Mama a falo ba tafita saɗaf-saɗaf jikinta na rawa.
Tana fita ko tai saan samun napep tace mai sultan road ko ciniki babu ta shige gudun kar Zainab ta fito ta kamata ta naɗa mata na jaki.
**********
Zainab ko tagumi ta buga cike da tausayin Khadija,inde zainab ta shiga gidan Khadija sunan Khadija *BAZAWARA*,wani zazzafan hawaye ya zubo mata akan kumatu.
************
MORE COMMENT
MORE TYPING
SHARED
~Assalamu alaikum MRS BASAKKWACE book lovers you are the backbone of her success, now she has the opportunity to show me how much you love me, short stories that I will release soon *WATA KISHIYA*, so I need to vote Hope you will join me in this competition as usual, this is a different story from the rest of you from hearing its name.~
~As you may have heard from the beginning, the story is different.🤤~
*MARYAM*
_(Ƴar Kunama)_
~ROMANTIC STORY~
*ƘIRƘIRARRAN LABARI,BANYI DON CIN MUTUNCIN WANI KO WATA,TRUST, FRAUD, REASON, COLLECTION AND KNOWLEDGE*
MALLAKIN:- *CAT LOVER*
*PAGE 5*
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
**********
Zainab ko tagumi ta buga cike da tausayin Khadija,inde zainab ta shiga gidan Khadija sunan Khadija *BAZAWARA*,wani zazzafan hawaye ya zubo mata akan kumatu.
Zainab kasa daurewa tayi tabar ma zuciyarta sai da ta gaya ma Mama,Mama tayi matuƙar mamaki batai tunanin haka daga Maryam ba,tace kuma karta ƙara ganin ta a gidan ta.
**********
Khadija sai after 05:00pm tafito daga ɗaki,yanda tabar dining ɗin haka tazo ta iske shi,wani ciwo taji a zuciyar ta,komawa ɗaki tayi ta ɗauko mayafin ta ta kwashe flacks ɗin ta fita dasu,ɓan garan mai gadi ta nufa,da sallama ta shiga gidan.
Da fara'anta matan Maigadi ta amsa mata,jiki na rawa ta shimfiɗa mata tabarma.
Khadija ko sai murmushi takeyi,zama tayi tana aje flacks ɗin hannun ta.
Gaisawa sukai a mutunce,suka ɗan taɓa hira kafin,tace ma ga abinci su juye.
Murna awajan Inna Adama ,ba'a cewa komi, ɗauko kwanika tayi ta juye,zata wanke flacks ɗin Khadija ta hanata,da ƙyar ta bari ta wanke mata flacks ɗin kafin sukai sallama ta wuce.
Tafito kenan ta hango shi a parcking space,yana sanye da yadi fari mai ratsin blue hulan kanshi blue yayi matuƙar kyau harda ga inda take tana jiyo ƙamshin turaren sa,kallo ɗaya tai masa ta kauda kai tabi hanyar ɓan garan su.
Shiko ko kallo bata ishe shi ba,byan ta aje flacks ɗin a kitchen ta fara tunanin mai zata girka.
*********
Wani mala-lacin mari yake ji a duk ɓan garan fuskan shi,sai da yayi namijin gaske ne bai ga taurari ba,balle har ya wuntsila.
"Kamal mai Khadija take maka da har kake shirin ƙara aure bayan auran ku da wata uku ko huɗu baku cuka ba?.
Ta ƙarashe maganan da sigar tambaya,wata dattijuwa ce ke zaune kan kujera ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya,sai huci take kallo ɗaya zakai mata ka tabbtar mahaifiyar Kamal ce don suna tsananin kama.
Ƙasa ya ƙarayi da kansa yace,"Hajiya kiyi haƙuri,ba abinda zai sani ban ƙara auran nan ba tunda b haramun bane".
Riƙe baki Hajiya tayi tana mamaki,Kamal da in ta ce masa kaza,bai iya canjawa yau shi kece mata sai yayi abu.
"Kamal inde kaci amanar ƴar mutune,kasata cikin baƙin ciki da damuwa,bataji daɗin aure ba zakai mata kishiya tou kaida ubangiji,ban hanaka ba jekayi".
Miƙewa tayi batare da tajira mai zaice ba tai shigewar ta bedroom ɗinta.
Ya jima zaune a wajan yana huci shi kaɗai kafin daga bisani ya tashi ya wuce.
Yasan tunda Hajiya bata ɗaure mai gindin a aure ba,a family gaba ɗaya ba wanda zai ɗaure mai gindi ya ƙara aure.
Dole yasamo iyayen haya.
**********
A washagari ko ,yatura iyayen ƙaryan da yasamo da temakon Sagir abokin shi,suka basu manyan kaya mayan hula takalmi da agogo,da wayoyi ga kuɗi a aljihu,driver suka ba rantsatstsan motor benz sukaje gidan su Maryam inda aka nema masa auranta,aka sa biki nan da sati biyu.
Aiko Maryam na tabbatar wa,takira mallamin ta ta ƙara masa kuɗi,sannan takira Zainab,da Zainab kamar bazata ɗaga ba ta ɗaga,Maryam ko cike da murna ta shaida mata,Zainab kasa magana tayi ta kashe wayar don jin baƙin ciki take kamar ita zaayi ma cin amanar ga,batai sanya ba ta shirya tace ma Mama tazata unguwa ,Mama tai mata fatan alkhairi.
***********
"Innalillahi wa'inna ilaihi raji'un",shi kaɗai take maimaitawa tana zubda ƙwalla masu ɗumi cikin tashin hankali mai tsanani.
Zainab ma hawayw take ziddawa don tana tsananin son Khadija bata so ko kaɗan taganta a damuwa,da tasan mawiyacin tashin hankalin nan zata shiga da bata kasance na farko wajan faɗa mata mummunan labarin nan ba,amma tayi haka ne don tasan takunta da Maryam.
Tsagaita kukan Khadija tayi bayan taji zuciyarta ya mata sanyi,tace,"Zainab ya zanyi banda iko sakin kaina da yau na rabu da Kamal,Allah bai san saki da yau na nemeshi dakai na,wannan baƙin aure,miyasa Maryam ta naimi ta ƙuntata ma rayuwata,ban san mai na tare mata ba,da duk abinda na samu sai ta ƙwace shi,miye laifina don na zaɓeta ƙawa aminiya,ita ko ashe ta zaɓeni maƙiyiyar ta".
Shiru tayi tana sauke ajiyar zuciya mai nauyi.
Zainab girgiza kai tayi tace,"Khadija haka ɗan adam yake wanda kake ƙauna bashi keson ka ba,don Allah kiyi haƙuri ki sa salama acikin zuciyarki,komai kika ga ya faru da ɗan adam ƙaddara ce rubutacce tun ran gini tu ran zane,ko wani bawa da ƙaddaran sa yake tafiya,taki ƙaddaran kenan ki daure ki cinye ta".
"InshaAllahu Zainab,kuma ko da wasa bazan taɓa nuna alama ko damuwa ba da har Kamal zai gani a fuskata,koda ko yazo yana faɗa min maganan auran shi,duk da banyi tinanin ina da mutuncin da zai faɗa min,saide ƙila kawai naji labari ko na gani an kawo amarya".
Cikin raunan murya take maganan kamar zata fashe da kuka.
Zainab lallashi da ban baki ta rinƙa mata harsai da taga ta saki rai kafin tai mata sallama ta wuce.
*********
Ɓangaran amarya da ango ko wuni sukai suna sheƙe ayar su a hotel,basu suka dawo ya ajeta a gida ba sai goma ya wuce na dare kafin ya wuce gidan sa.
Tana zaune tana karatun alƙura'ani da ya zamo mata jiki ta ji tsayuwar motor sa da shigowar sa sha ɗaya da minti shabiyar da ta kalle a gogon dake manne a bangon ɗakin,girgiza kai tayi taji wani abu ya zo ya tokare mata ƙirji,tai sauri ci gaba da karatunta don yana matuƙar rawa a zuciyar ta taji damuwar ta ta wuce.
***********
Haka rayuwa taci gaba da tafiya,Kamal bai taɓa buɗe baki yace Khadija zan ƙara aure ba,haka bata ji a bakin Hajiyar saba,kullum sai sunyi waya safe da yamma,amma bata gaya mata ba,saide tace Khadija aita haƙuri zaman aure haƙuri ne,muma haƙuri mukai har muka kai iyanzun a ɗakin mazajen mu.
Khadija saide tai murmushi tai mata godiya,tunani take ƙila Hajiya bata sani ba,in bata sani ba suwaye suka nema masa auran Maryam tou,tunani kala-kala bata da mai bata amsa,ko gidan su bata gaya masu Kamal zai ƙara aure ba.
Maryam ko duk da ansa mata ranan aure ba abinda ya canja,game da bin maza da takeyi,shima kamal yazo yasha daɗin sa ga tafi.
~NIKO NACE YA SUNAN AURAN DA BABU ISTIBURA'I,DUK DA NASAN IYAYEN BASU SAN KALAN ZAMAN DA SUKEYI BA KENAN DA BAZAUAMINCE BA SAI ANYI ISTIBURA'I~
Kwanci tashi ba wiya asaran mai rai,saura sati ɗaya miki Maryam da Kamal.
Iyayen Maryam sunzo sunga ɓangaran da zaa sa Maryam sukace sammmm bazai yuwu ba ɗaki ɗaya da falo da kitchen da bayi,saide ya kama mata wani hayan, ko a fasa
Shiko izuwa yanzun kuɗin shi duk yayi ƙasa,bani-banin Maryam,akwatin kawai daya haɗa set shidda ya kashi kuɗi,ko a auran Khadija bai kashe kuɗi haka ba,ga event kala bakwai ko wanne da wajan da zaayi
Haƙuri ya basu,yace zai san yanda za'ayi.
Bayan sun wuce yashigo falo yana ƙwala mata kira..........
*TOU FAAAAA WAI MAI KAMAL ZAICE MA KHADIJA DON BAIDA KUNYA????*
COMMENT
ND
SHARED
~Assalamu alaikum MRS BASAKKWACE book lovers you are the backbone of her success, now she has the opportunity to show me how much you love me, short stories that I will release soon *WATA KISHIYA*, so I need to vote Hope you will join me in this competition as usual, this is a different story from the rest of you from hearing its name.~
~As you may have heard from the beginning, the story is different.🤤~
*MARYAM*
_(Ƴar Kunama)_
~ROMANTIC STORY~
*ƘIRƘIRARRAN LABARI,BANYI DON CIN MUTUNCIN WANI KO WATA,TRUST, FRAUD, REASON, COLLECTION AND KNOWLEDGE*
MALLAKIN:- *CAT LOVER*
*PAGE 6*
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Bayan sun wuce ya nufi part ɗinsu tundaga waje yake ƙwala mata kira,ke Khadija cikin tsawa da karaji yake ƙwala mata kira.
Idar da sallah azahar kenan,ko azkar bata samu daman yiba tamiƙe da wuri,don tunda ta tashi gabanta ke faɗi,zuciyarta na ɓaci.
Tabuɗe ƙofa kenan tasa kai zata fita,shima zai shigo,sukai gware ta bugu da ƙirjinsa kanta yace ƙummmm yawani sara,baya-baya tayi ta koma ta bugu da kujeran bedroom ɗinta.
Tai saurin dafe kai cikin tsananin azaba ,tace,"inna lillahi wa inna ilaihi raji'un".
Bai ko damu ba ranann haɗe kamar namijin zaki ya biyota ya take ƙafafuwanta da ƙafan shi dake sanye da cover shoe,yana murza ƙafarta
Azaba ƙarin azaba taji ya nunkun mata,ta saki wani ƙara.
"Ke dan ubanki kina ji ina kiranki,amma kina banza dani?.
Afirgice ta ɗago kai tana kallon shi,cike da mamaki take kallon shi,take taji azabar datake ji ya wuce mata,azaba da raɗaɗin zagin mahaifinta yafi azaban ciwon da takeji.
Mtseww "ni va wata magana nazo yi dake ba ,mai tsawo,so nike ki tashi daga part ɗinnan,ki koma one bedroom plat,nan zan sa amaryata nan da rana ita yau".
Bin sa da kallo take kamar a mafarki take jin maganganun sa.
Bai damu da kallon da take masa ba,kuma bai damu da rashin maganan taba,yaci gaba da faɗin,"kinemo wa ƴanda zasu taya ki ki tattara komatsan ki kimo can,don kayan da za'akawo ma amaryata baza su ɗauki can ba,kuma banda kuɗin kama mata haya don komi yazo a ƙurarran lokaci,don haka nabaki kwana biyu dole ki tashi na gaya miki".
Bai jira mai zatace ba yasa kai ya fice yana ta hura hanci da huci,kamar kumurcin maciji.
Zama tayi a wajan kamar mutum-mutumi mafarki take ko da gaske,ta jima zaune tana tufka da war-wara kanta yayi murfi,duk saƙe-saƙen ta ta kasa gano mai ya kamata tai ma Kamal.
**********
Ɓan garan Maryam kuwa,ta wanicicciko tayi fresh kamar sabon agwalima,jikin ta duk ya canja kamar mai sabon ciki,ga yawan morning sickness ,ga kasala da yawan bacci,shiryawa tayi ta tafi garkuwa hospital wajan saurayin ta Dr Hadi.
Tana zuwa kai tsaye tashiga office ɗinsa,tai sa'a ko shi kaɗai ne,da gudu taje ta faɗa kan cikin sa ta sakar masa dip kiss a kan lips.
Lumshe idanuwa yayi tare da shafo bombom ɗin ta ya matsa su.
Gantsare masa ƙirji tayi tace,"My Dr ban son iskanci,aurena 6days yai saura,ɗan zaro ido yayi yace,"aure zaki kibarni yanzun Maryam".
Ɗan juya ido tayi kafin tace waya gayama zan barka,da auran ma zan rinƙa zuwa kana sosa min wajan".
Murmushi yayi ya shafo nonuwanta,yace,"good job my dear kin san kan harka wallahi,banda wani fargaba dake,yanzun ma ina fatan kinzo kibani,ya kamata muyi kwana biyu ina gurzan ki,in dawo in ɗinke miki wajan".
Yana maganan yana mata wani mugun kallo yana lashe baki kamar maya.
Shafo sajen shi tayi ta mai kiss a goshi,lumshe eyes yayi.
Nan suka fara ya mutsa junan su, suna aika ma junan su saƙƙwanni naban mamaki,akan table ɗin wajan yacita har so uku kafin ya barta.
Tare sukai wanka suka fito suka shirya,kallonta yayi yace,"Maryam waya miki ciki?.
Yai tambayar yana mai kafeta da ido.
Yamutsa fuska tayi tace,"ashe cikine dani,ni wallahi ban masan waya min ba".
Mtsewww gajeran tsaki yaja kafin yace,"Maryam maiyasa kowani tom and jerry kike ba ma kanki,mtseww gashi yanzun zaki jamin aiki,kina ba kowa da ya taya ki ɗaga ƙafa,baki ko tsoron ciwo".
"Sorry dear" ta faɗa a taƙaice.
Kiran Nurse yayi ya yasa ta haɗa masa kayan abortion ta kawo masa drugs ya fara ba maryam tasa rabia ƙasan halshe rabi a gabanta ya tura mata.
_DA BADIN BADIN BA DANA RUBUTA DOSE ƊIN DA AKE SHA CIKI YAFITA KO NA WATA NAWANE_
**********
Ɓangaran Khadija ko zuciyarta tayi mata matuƙar nauyi,kuka take sosai babu mai lallashinta ta rasa wanda zata faɗa ma matsalan ta,bata son ta gaya ma mahaifiyarta hawan jininta ya tashi ,ko Aisha ta faɗa mawa tasan dolle Ummah ta taji .
Kuka take sosai har muryantabya dashe,ga ciwon kai da kanta tsananin sarawa kawai yakeyi kamar zai faɗi ƙasa.
**********
Ɓangaran Maryam ko,da ciwo ya taso mata kamar zatayi hauka,ƙasa ta tashi tana murƙusu-suwa,bata san sanda tafara kiran Allah tana salati da hailala da istigfari ba.
*SHEGIYA WAYA GAYA MIKI BARNO GABAS TAKE,SANDA KIKE ZUWA KINA BUƊE MUSU SUNA CI KINA JIN DAƊI BAKISAN CIRE CIKI DA AZABA BANE HAR KIKA BARI KIKAI,ASHE ƘARAMAR ƳAR BARIKI KIKE MTSEWWWW*
Dr Hadi na kallonta,sai ma ƙara mata dose da yayi ,harda suma,ta kwashe awa huɗu tana abu ɗaya,kafin jini ya ɓalle mata,yana fita guda-guda sosai-sosai.
Nurse ɗin labour room yasa suka gyara masa wajan ,aka ɗauko gado aka sata ya aka kaita ɗakin don mata wankin ciki,wajan wankin ciki taji azaban dayafi na ɗazun,da ya gama kuma ya ɗinke mata gaban ta tasssa.
*TOU YARINYA MAI ZAKI ƊINKE DON YASAN KOMI HARDA SHI KUKE TAMBAƊEWAR AI,KUMA YASAN BUDURCI DON MATAR SA A BUDURWA YA AURETA ,KEKO TAXI NO GRAGE,KOWANI TOM AND JERRY YA SHIGA.*
***********
Kabeer hankalin shi ya tashi sai kiran wayar Maryam yake ba adadi baa ɗagawa,daga ƙarshe Hadi yamai mesaage .
_ASSALAMUALAIKUM,ANGONA FARIN CIKIN RAYUWATA,KARKA DAMU INA LAFIYA, MUNATA HIDIMAN BIKINE,GA JAMAA,KASAN NAFI SO INYI WAYA DAKAI BA HAYANIYA,DA MUTANE SUN TSAGAITA I CALL U,I LOVE YOU TAKE CARE OF UR SELF_
Ya tura mai,shine fa yadena kira.
2Hour tayi tana bacci,don bayan angama saida yamata alluran bacci kafin tatashi.
*********
Khadija ko rarrafawa tayi tana bin bango harta isa bakin get inda Baba maigadi yake ta jigina da bango tace,".........!
COMMENTS
VOTE
SHARE PLEASE
~Assalamu alaikum MRS BASAKKWACE book lovers you are the backbone of her success, now she has the opportunity to show me how much you love me, short stories that I will release soon *WATA KISHIYA*, so I need to vote Hope you will join me in this competition as usual, this is a different story from the rest of you from hearing its name.~
~As you may have heard from the beginning, the story is different.🤤~
*MARYAM*
_(Ƴar Kunama)_
~ROMANTIC STORY~
*ƘIRƘIRARRAN LABARI,BANYI DON CIN MUTUNCIN WANI KO WATA,TRUST, FRAUD, REASON, COLLECTION AND KNOWLEDGE*
MALLAKIN:- *CAT LOVER*
*PAGE 7*
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Khadija ko rarrafawa tayi tana bin bango harta isa bakin get inda Baba maigadi ke zaune da ƴar radio shi yana sauraran labarai ,jigina tayi da bango sabida jirin da take ji yana ɗiban ta.
Sauke radion Baba mai gadi yayi yana washe hauru yace,"barka da wuni Hajiya".
Cije lips tayi na ƙasa tace,"yauwa Baba,dan Allah ɗan taro min napep ban iya tuƙi,kaina jiri nakeji".
"Ashaaa Hajiya Allah ya sawaƙa".
Miƙewa yayi yafita yana ta jero mata sannu,ganin ya tashi yasa ta zauna a kujeran.
Hon ɗin da ake ba ƙaƙƙautawa a bakin get ya tabbatar mata mai gidan ne yadawo, gashi yasa kanta ya ƙara matsanan cin sarawa.
Miƙewa tayi taje ta tura get ɗin duk da jirin da yake ɗibanta.
Da gudu ya shigo da motor da badin tayi saurin matsawa ba daya take mata ƙafafuwa, tajima jingine da get ɗin gaban ta na faɗi ta lumshe ido,sai da taji gabanta ya rage bugu kafin ta tura ta rufe get ɗin lokacin shiko har ya shige ciki.
Takai kusan 30munites kafin Baba da ɗanpep ya dawo,godiya tayi masa tafita ta shiga ba tare da tayi ciniki ba.
Kai tsaye asbitin garkuwa yakai ta,ta fiddo da 1k guda ta bashi,bata jira canji ba tai shigewar ta,baya ta bada kati anfito mata da file ɗin su ,bata jima sosai ba ta shiga ganin Dr,tamai bayanin yanda takeji,ɗeban jinin ta yasa akayi,akai gwaji,gwajin farko aka tabbatar tana ɗauke da ciki wata ɗaya da kwanaki.
Kawo ma Dr akai ya miƙa mata yana mata congrat,Khadija dubawa tayi cike da mamakin murnan da yake tayata,ganin tana da ciki miƙewa tayi a firgice tana kallon Dr tana kallon result ɗin,shima ita yake kallo.
Komawa tayi lokaci ɗaya ta zauna da ta tina wani abu,tana murmushi har dimple ɗinta suna lotsawa.
Dr shawar-war yabata yanda zata kula da cikinta da lokacin da zata fara zuwa awo,rubuta mata maganin da zata karɓa a pharmacyn asbitin yayi ta amsa ta fita tana godiya.
Pharmacy kai tsaye ta nufa ta basu takaddan.
Da gudu wata nurse tazo tana cewa ,Sister Fati yanzun zaki ga ƴar iskan da Dr Hadi ya gama ci a office ya cire mata ciki yai mata ɗinki da nake faɗa miki ɗazun zata fito".
Ware ido wacce aka kira da Sister Fati tayi tace,"aiko Sis Aisha tayi asara,Hadi da ba inda bai tsomawa har attenders bi yake da ƴaƴa arna, ƙilama yana da ƙanjamau da infection,mutum kamar kare,ni ƙyama yake bani shiyasa ban sake masa fuska".
Duk maganan da suke Khadija na tsaye tana jinsu.
Dai-dai lokacin Maryam tazo wucewa,Sis Aisha cikin ƙasa-ƙasa da murya tace,"gatanan".
_NURSE BADAI ƊABI'AN GULMA BA😂IN KANA KASHI KAGA NURSE KOMA KA ZAUNE ABINKA IN SUN WUCE KA TASHI KA WANKE._
Khadija hakanan kawai taji tana son ganin yarinyar ɗaga kan da zatayi wazata gani in ba Maryam ba,gabanta yankewa yayi ya faɗi,cike da mamaki,amma ta ɓoye mamakin ta.
Ido cikin ido suke kallon juna tsawon daƙiƙa.
Maryam ganin Khadija saida ƙirjinta ya buga.
Khadija ko murmushi ta samu kanta da sakar mata tace,"aa amaryan mijina kece a asbiti waye ba lafiya".
Cikin halin ko'in kula Khadija tai maganan.
Maryam gabanta faɗi yayi ta daburce lokaci ɗaya jin maganan da batai zato ba,don tasan Kamal bazai