Showing 42001 words to 45000 words out of 46304 words
Chapter 15 - MARYAM YAR KUNAMA COMPLETE- BY MRS BASAKKWACE .txt
tafi a saluɓe ya shiga motor ya nufi gidan su Khadija kiran ta yayi awaya yace ta fito waje ta fito masa da Abul.
Bata jima ba sai gata ta fito saɓe da Abul a kafaɗan ta,gidan gaba ta buɗe ta shiga,bayan sun gaisa ƙura mata ido kawai yake bako ƙyaftawa.
"Yadai zan mutu ne wannan irin kallo haka Aynul-hayat?.
Murmushi yayi yace,"a'a kawai naga kinyi kyau ne sannan zanyi missing ɗinki".
Wane missing nida gobe za'a kawo maka ni My Happiness".
Murmushi yayi ya ɗau Abul dake kan cinyarta ya fara shilla shi sama yana masa wasa,yana ta ɓangale baki yana dariya.
"Aynul-hayat kaga yanda kayi kyau kana ƙyalli kana sheƙi,hancin ka ya ƙara tsayi".
Murmushi kawai yayi ba tare da yace mata komi ba yaci gaba da ma Abul wasa,sai da yaji hannun sa yayi sanyi ya miƙa mata shi ya zuba mata ido itama shi take kallo.
Tsawon minti biyar ba wanda ya kauda idon shi,shine yai kauda shirun da cewa Nisful-hayat airport zanje Aunty Murja zan ɗauko,sai mun dawo i miss you in Allah yaso zan zo da yamma".
Sauke ajiyar zuciya sanyayya tayi yaude kawai ta tashi gabanta na faɗi bugun zuciya take fama dashi tace,"Allah ya tsare miji na".
"Amin baki ce ba".
Murmushi tayi tace," i love you.
"I love you nd I miss you my life".
Murmushi tayi tana fita ta saɓa Abul a kafaɗa ta hanyar shiga gidan su.
Yana tsaye ya ƙura mata ido har sai da ya ga shigan ta cikin gida ya sauke ajiyar zuciya ya ja motor shi ya wuce airport.
Ya shiga kenan kiran Aunty Murja na shigowa tace mai sun sauka kusan minti biyar ina ya tsaya kuma Karima tace ya taho tun ɗazun,murmushi yayi yace ina ganin ki yanzun,gani nan inda ake parking motor.
Aje wayar sukai ya gyara parking ya kashe motor ya fito don taimaka mata da ɗaukan kaya,yana gafda ita yaci tuntuɓe ya yanke jiki ya faɗi.
Subhanallah mutane sukayo kanshi koda akazo aka juya shi ko motsi baya yi,ihu Hajiya Murja ta kurma tana faɗin na shiga uku karde ya mutu,da ƙyar wata mata tajata gefe shi kuma aka ɗauke shi sai asbiti suka bi bayan shi.
Ga Hajiya Karima nata kiranta ta kira Khalil amma duk ba wanda Hajiya Murja ta iya ɗauka,kasancewar wayar shi a hannun shi ya fito da ita,wanda yafara zuwa ya ɗauka ya bata.
Hankalinta sam ba ajikinta yake ba fatanta dai Khalil Allah yasa ba mutuwa yayi ba.
Dubawan farko likita yace musu ai Allah ya amshe abinshi.
*INNALILLAHI WA INNALAIHI RAJI'UN DUK WANI MAI RAI SAI YA ƊANƊANI ƊACIN MUTUWA YANA SO KO BAISO,DUK ƘAUNAR KA DA DUNIYA KANA TSAKA DA JIN DAƊIN TA ALLAH KE KASHEKA YAGA ABINDA ZAI FARU,YANZUN MUTUWAR FUJU'A AKEYI DA CIWO BA CIWO,MUTUWA ISHARA CE GAMAI HANKALI,ALLAH KASA ƘARSHEN MU TAFI FARKON MU KYAU,ALLAH KAJIƘAN IYAYEN MU ƘANNAN MU DA YAYYUN MU DA ƳAƳAN MUSULMAI DA SUKA RIGA MU GIDA GASKIYA HAR ZUWA YAU,MUTUWA GASKIYA CE TSAYUN ALƘIYAMA GASKIYA NE,MUYI ƘOƘARI RAGE NEMAN DUNIYA MU NEMI LAHIRAN MU DON SHINE RAYUWA MAFI JIN DAƊI DA ZAMIYI BAYAN WASU SHEKARU IN MUTU,BABU ABINDA YAFI JIN DAƊI KA JE GABAN UBANGIJI KA ANSA SAKAMAKO DA HANNUN DAMA KA SHIGA ALJANNA MAFI ƊAUKAKA WATOU ALJANNA FIRDAUSI,ALLAH KA SA MUSHIGA ALJANNA GABAKI ƊAYAN MU.*
Timmmm Aunty Murja ta zube a ƙasa sumamma.
Nan akayo kanta lokacin kira ya ƙara shigowa wayar Khalil.
Wani ya ɗaga da sallama,Momy sai da gabanta yayanke ya faɗi kasa amsa sallaman tayi tace," ina Khalil ɗin waye kai".
"Uhm ɗan matsala ce kaɗan amma gasunan asbitin airport,kizo da maza".
"Miya faru sunyi hatsari ne?.
A kiɗime Momy ke maganan.
"Hajiya kwantar da hankalin ki babu komi".
Cikin kwantar da hankali yake mata maganan.
Katse wayarta tayi ta kira Alhaji Safwan yana ɗagawa ta faɗa mai maike faruwa,take yaji hankalin shi ya tashi yana kusa da wajan yace mata karta zo zaije shi da su Alhaji Muftahu suna tare komai kenan zata ji,katse wayar yayi ya gaya ma abokanan sa maike faruwa,take hankali tashe kowa ya faɗa motor shi suka ɗau hanyar airport.
Kai tsaye asbitin suka nufa da kwatan ce wanda wayar Khalil ke hannun shi suka isa.
Suna zuwa yace musu suje A/E room.
Gaban Alhaji Safwan faɗi kawai yake yi nufe ɗakin karde hatsari sukayi.
Suna shiga Hajiya Murja na farkawa tana faɗin nashaiga uku mutuwa ya zakiyi mana haka ango ne fa na shiga uku ni Murjanatu".
Dummmmm Dad ɗinshi yaji akunan sa kamar an ɗauke jin sa.
_INA GODIYA DA ADDU'O'IN KU FANS,ALLAH YABAR ZUMUNCI DA ƘAUNA_
_typing🖌️_
*🔘MARYAM🔘*
_(Ƴar kunama_)
NA MARUBUCIYAR:-👇
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
AWANI GARI
JIDDATOU
ND NOW
MARYAM ~ƳARKUNAMA~
MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)*
*(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)*
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo
WHATSAPP NUMBER:- *08167151176*
WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE*
GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*
IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE*
TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE*
SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE*
*LAST PAGE*
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
*SADAUKARWA GA DUKKAN MASOYANA WANDA NASANI DA WANDA BANSANI BA ALLAH YABAR ƘAUNA A DUK INDA KUKE*
~TUNI~
*AJIYA NA DUBA COMMENT ƊINKU WAJE GROUP DABAN DABAN,KUNA TA ƘORAFIN MIYASA NA KASHE KHALIL,MUTUWA BA RUWANTA DA KHALIL ANGONE IN LOKACIN KA YAYI SAI KA TAFI,SANNAN KO KHALIL BAI MUTU BA BABU AURE TSAKANIN SA DA KHADIJA,SABIDA KAMAL BA A HAYACIN SA YA SAKETA BA,SANNAN WASU NACEWA KARTA YA SA MA KHADIJA ƘANJAMAU,SAM MARYAM BATA DA ƘANJAMAU ,BA ƘANJAMAU YA KASHE TA,SHAN JININ TA ALHAJI LABARAN YAYI YABA MA DODON TSAFI,SANNAN KUMA YANA SADUWA DA ITA TA BAYA BATA GABAN TABA,KAMAL SO ƊAYA YA TAƁA AMFANI DA MARYAM A ZAMAN A AURAN SU,SABIDA LALURAN DA YASAMU NA DUKAN DA KHADIJA TAYI MAZA A JOYSTICK ƊINSA,DON HAKA KAMAL BAIDA ƘANJAMAU KO KAƊAN.*
Dummmmm Dad ɗinshi yaji akunan sa kamar an ɗauke jin sa da ganin sa tafiya yayi luuuuuu zai faɗi ƙasa Alhaji Mukhtar ya tare shi ya faɗa jikin sa,yana faɗin subhanallah Alhaji,zaunar dashi yayi kan kujera.
Hajiya Murja tasowa tayi ta yaye zanin da aka lulluɓe Khalil dashi,yana kwance fuskan shi sai wani ƙayataccen annuri ke futa tana ƙara haskaka ta,kamar amai magana ya amsa,rungume shi tayi tana jijjigashi tana faɗin Khalil nasan ƙarya ne baka mutu ba,katashi mutafi gida gobe ne auran ka ka tashi,sambatu kawai take tana kuka,da ƙyar aka fiddata aka sata a cikin motor,yayinda Alhaji Safwan ko ɗan yatsan shi ya kasa motsawa,Alhaji Muftahu da Alhaji Mukhtar su sukai cike-ciken files aka basu gawan Khalil.
Hajiya Karima hankalinta yayi dubu ya tashi ,sai kiran number Khalil dana Dad dana Murja bawanda ake ɗagawa.
Ɓangaran Khadija jikinta taji ya ƙara sanyi gabanta na tsanan ta faɗu,ga Abul sai rigima yake yaƙi hannun kowa sai ita,shima yaƙi yin shiru sai tsandara ihu yakeyi,aje shi tayi ta sa shi a gaba tana kallon shi kamar ta fashe da kuka,sanin illan zubar ma yaro da hawaye yasa ta kasa.
Hajiya na ƙoƙarin fita Alhaji Muftahu suna shigowa yasa ta dakata bata gama tsinkewa da alamarin ba sai ga motor asbiti a bayan su,sandarewa tayi tana bin motor da kallo tana kallon su,Hajiya Murja ɓalle murfin motor tayi ta fito tana rusa ihu da kururuwan da yaja hankalin duk wani mahaluƙin dake gidan da maƙwafta tayi kan Hajiya Karima,tana faɗin ya mutu Khalil ya tafi ya barmu.
Baya kawai Mom tayi ta tafi zata faɗi Aisha ta tarota,kankuce mai gida ya kacame da ihu da koke koke,lokacin da aka fito da gawar Khalil zuwa babban falon gidan sai a lokacin kuka mai ciwo ya kufce ma Hajiya Karima,da ƙƴar aka jata side ɗinta.
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai Khalid ke maimaitawa,bayan ya aje kiran da aka yi masa yanzun
"Lafiya mai ya faru kake dogon salati haka?.
Faɗar Ummah.
Ƙasa yayi da kansa tsawan mintina kafin ya ɗaga da jajayen idanuwan shi yace,"Umma ina Khadija?.
"Tana ɗaki yau ɗanku yasata gaba da kuka".
Shiru yayi na ɗan wani lokaci kafin yace,"Ummah Khalil ne ya".
"Ya fasa auren ta?.
Umma ta tambaya a razane tana ƙwalo ido.
Girgiza kai yayi yana ƙoƙarin haɗiye hawayen dake niyar zubo masa yacw,"Ummah sai haƙuri Khalil lokaci yayi ya rasu",cikin wata irin sanyayyar murya yai maganan.
"Innalillahi wa inna ilaihi raji'un,kai Bross yanzun fa yabar nan ƙarya ne".
Duk a razane suke kallon ta.
Zama Khadija tayi ta ɗaura Abul kan cinyarta da yanzun ta samu yayi shiru.
"Ummah ni yau gaba ɗaya na rasa mai kemun daɗ....!
Ƙaran wayarta yasa ta kasa ƙarasa maganan da takeyi,ganin Zee yasa tai murmushi ta ɗauka ta kara a kune.
"Ke banson shashanci haka naji yaya Khalid na faɗa ƙaryace yanzun yazo nan yace min zaije filin jirgi bai mutu ba kudena faɗan ya mutu".
A tsawace tai maganan tare da kashe wayar tai wurgi da ita.
"Ke tashi ki ɗauko mayafinki".
Khalil da shigowar sa kenan jiki a sanyaye idanuwan shi sun kaɗa sunyi jaaaa.
"Kaima sun kira kane?.
"Eh wallahi mutuwar fuji'a tuntuɓe kawai yaci shikenan rai ya fita".
What Khadija ta faɗa a tsawace.
"Khadija kiyi haƙuri haka Allah ya ƙaddara,Allah da ya halicce Khalil yafiki son shi shiyasa ya amsa abinsa sanda bakuyi zato ba".
Sulalewa kawai tayi ta koma kan kujera tai shiru kalaman sa na dawo mata cikin ƙwaƙwalwa,kawai ta tsinta kanta da murmushi ko kaɗan bata yarda Khalil ya mutu ba,miƙewa tayi ta shiga ɗaki ta sawo hijjab ɗinta ta fito lokacin har Umma tasa hijjab tana riƙe da Abul,a tare suka fita a motor Khalid.
Tafiya suke ba ma mai kowa magana kowa da abinda yake saƙawa a zuciyar shi,har suka isa unguwar su Khalil da ya cika da mutane kowa yayi jigum-jigum ana jimamin wannan mutuwa ta Khalil mai cike da izina ga mai hankali,ganin cincirindon mutane a ƙofar gidan su Khalil sai alokacin zuciyar Khadija ya karye,gefe Khalid ya samu ya parking suka firfito Ummah ta ɗau Abul Khadija ko jan ƙafa kawai takeyi suka ratsa ta cikin taron maza kanta a ƙasa suka shiga cikin gidan da koke ya cika shi mata duk sunyi jugum jugum,duk da zuciyartavya karye kuka na ƙoƙarin kufce mata,amma ta danne.
*(INNALILLAHI WA INNA ILAIHIRAJI'UN,ALLAHUMMA AJIRNI FI MUSIBATI,WA AJILHI KHAIRAN MINHA,INNALILLAHI MA AKHAZA,WALAHU MA AƊAHA,WA KULLAH SHAI'IN IN DAHU AJALAN MUSAMMA,FALNASBIR WALNAHTASIB)*,kawai take nanatawa a ƙasan zuciyarta,falon Mom suka kutsa suka shiga inda Mom ke zaune tayi shiru ga ƙawayen ta na kuka amma ta kasa ko zudda hawaye ɗaya balle taji sauƙin raɗaɗin zuciyar da takeji na rashin ɗanta na miji ɗaya,shigowar su Ummah yasa ta ɗaugo ta kalle Khadija da kanta ke ƙasa yasa Mom ta fashe da kuka,ta miƙe ta jawo Khadija ta rungume ta,Khadija sauke ajiyar zuciya tayi ta fara bubbuga bayan Mom cikin raunan niyar murya tace,"Momy kiyi shiru dan Allah addu'a zami ma Khalil in har da gaske ya rasu,shine babban soyayyar da zamu gwada masa Momy,Momy har yanzun a zuciyata banji Khalil ya rasu ba",a hankali Mom ta rage kukan ta tana shashsheƙa tace,"Khadija dagaske Khalil ya rasu ya tafi ya barmu,mutuwar Khalil aya ce ga duk wani mai hankali",shigowa da akayi akace suzo ne angama shirya shi yasa Khadija bata ƙara cema Momy komi ba,suka bi bayan Alhaji Muftahu.
Khalil na kwance cikin farin lakafani a makara Dad na zaune kan kujera ya zuba ma gawan ido,gefe aunty Aisha,Khairat,Ummah,sai Khadija,da sauran ƴan uwan shi,fashewa sukai da kuka banda Khadija da Ummah da zubar hawaye kawai sukeyi, cikin ɗaga murya khadija tafara kwraro ma gawar Khalil addu'a tana zubar hawaye mai ɗumi a fuskanta,yasa dole su Mom sukai shiru suka fara amsawa da Amin,kusan minti shabiyar tana zuba addu'a kafin akazo a ka ɗauke shi aka fidda shi,Mom durƙushewa tayi a wajan tana kuka da ƙyar Dady ya iya miƙewa ya fita don ai ma ɗan shi sallah dashi,Khadija alwala ta je ta ɗaura haka Ummah suka fita waje don gabatar da jana'izan Khalil,yayi jama'a maza da mata suka sallace shi inda aka ɗauke shi a hannu ba a motor ba zuwa maƙabarta.
Momy ko take zazzaɓi mai zafi ya rufeta,Hajiya Murja ko tayi suma yafi biyar, sai da yamma Umma ta tafi gida tabar Khadija da Abul da niyar zata aiko mata da kaya,Ummah na tafiya Zainab da Saudat da Mama sukazo,mutane na ta zuwa daga ɓangaran dangin su Khadija kowa yana jimamin mutuwar Khalil,Hajiya Khalil ma tazo gaisuwa tana ta jimami.
Washagari aka ɗaura auran Zainab da Khalid,Saudat da Khalil,ba ai wani shagali ba,kasancewar anyi musu babban rashi ɗaura aure kawai akai da yamma aka kai amare gidan mazajen su.
Khadija ko tana gidan su Khalil tana amsan gaisuwa,Momy hawan jini mai tsanani ya shige ta lokaci ɗaya,yayinda Hajiya Murja kamar zata zauce,Khadija ko abinci bata iya ci ga shayarwa lokaci ɗaya ta faɗa ta rame,sai da aka share zaman makoki kafin ta koma gida,tunda ta koma take zazzaɓi itama,saida aka kaita asbiti ta amshe magunguna da alluarai.
Dady da Momy gaba ɗaya sai da aka rinƙa haɗa musu da addu'o'i kafin suka fara warwarewa ,mutuwar Khalil ya taɓa su sosai.
Khadija duk ta faɗa ta rame sabida tunanin yanzun kuma wazata aura,wa zai sota kamar Khalil,ita tama fasa auran zata girma da ɗanta ta raine shi,tunda bata da wani idda akanta sabida bata tare ba.
"Aa Kamal ne yau a gidan namu?.
"Eh wallahi Ummah" ya faɗa yana shigowa shida wani malami.
"Bissimillah ku kuzauna".
Faɗan Ummah da take sama Abul riga.
Zama sukai suka gaisa a mutunce,tasa aka kawo musu ruwa suka sha,tabashi Abul.
Ya amsa yana masa wasa yaron sai dariya yake mai.
"Yasu Hajiya Kamal?
Yace,"Ummah tana lafiya,nazo akan wata magana ce game da Khadija".
Tou ina jinka,cike da mamaki Ummah tayi maganan don bata taɓa jin yayi maganan Khadija ba tunda aka ja masa layi.
"Ummah har yanzun Khadija matata ce bata saku ba sabida ba acikin hayacina na saketa ba,kuma nai mata duk abinda da na mata ba,Ummah dan Allah kisa baki ta dawo gareni duk abinda ya faru bazai ƙara faruwa ba",Cikin maraicewar murya yai maganan.
"Da bada hayyacin ka bane yanzun ko ai kadawo hayyacin ka Kamal wallahi tallahi sai ka sake ni in kaine autan maza na barka,har abada kamar yanda nabar nonon uwata".
Faɗan Khadija da take dianing table tana zaune tana danna waya ko da suka shigo basu kula da ita ba.
Da mamaki Kamal yake kallonta,itama shi take kallo tana watsa masa mugun kallo.
"Bata damu da kallon mamakin da yake mata ba taci gaba dacewa na tsane ka Kamal dakai gwamma baƙin kare ya zama dole ka rabu dani tunda ba tare aka haife muba".
"Ke Khadija lafiya kike masifa haka?,turus yayi da ya haɗa ido da Kamal.
Faɗan Khalil da shigowan sa kenan yana gyara karin hulan dake riƙe a hannun sa.
Taɓa baki tayi tace," wannan marakunyar banzan ne Khalil,yazo wai da auren shi haryanzun akaina shida wani ustaz mai gemun bunsuru,wallahi ka faɗa mai sai ya sakeni".
"Ke Khadija miye kike yi haka ban san ki da haka ba abi komi a hankali,kar in ƙara jin bakin ki anan".
Faɗan Umma da sai yanzun ta samu daman yin magana.
Shiru tayi tana turo baki,da niyar komai zai faru yau Kamal bai barin gidanan sai ya bata takaddan ta.
"Ummah wallahi ba mai mata dole,in kuma ɗan shi yake bibiye ku haɗo mai kayan shi ya tafi mun bar mai abinshi".
"Kai mai yasa Khalil in kana magana baka lissafi ne zafin zuciya yayi maka yawa kai ma Allah ka bar zafin zuciya abinda hankali bai bada ba rashin sa bazai bada ba".
Faɗan Khalil da shima shigowar su kenan a Zainab a bayan shi.
"Wallahi Brother ka faɗa masa ya sakeni banso bazanyi ba dashi gwamma baƙin jaki".
"Wai ke bazaki ma mutane shiru bane?.
Kamal tunda suka fara magana yayi shiru yana sauraran kalaman Khadija da suka fi garwashi zafi a zuciyar shi.
Miƙewa yayi a kwantar da Abul ya juya yace ma wanda suke tare su tafi,shima miƙewa yayi yabi bayan Kamal.
Miƙewa Khadija tayi ta rufe mai baya tace,"kai wani irin maye ne kasake ni ban ƙaunar ka".
Ko sauraranta baiyi ba ya fice.
Khalil ma goyan bayan Khadija yayi ta inda yake shiga batanan yake fita ba Umma da Khalid shiru sukayi musu.
Kamal kai tsaye gidan su ya nufa yasamu Hajiya yace mata tazo suje unguwa,batai tunanin komi ba tasa maya fi ta bishi,kai tsaye taga sunzo gidan su Khadija ,da mamaki take kallon shi,bade tayi masa magana ba,har suka shiga,duk suna zaune a falo suna kallo suka shiga.
Cike da murna Khadija ta miƙe ta rungume Hajiya ,bayan ta zauna Khadija ta shiga kitchen ta kawo mata ruwa da snaks kafin tazo suka gaisa,bayan Khalil da Khalid da Zainab sun gaisheta.
Kamal na rakuɓe daga jikin ƙofa ,ko kallo bai ishe Khadija ba.
"Hajiya dan Allah ki roƙeta tayi haƙuri".
"In roƙeta mai wa zan roƙa?.
Hajiya ta tambaya cike da mamaki.
Khadija jitayi gabanta ya faɗi,sam bazata iya musunta ma Hajiya ba,bazata iya cewa bata son ɗanta a gabanta ba.
"Hajiya Khadija", yai maganan a taƙaice.
"Wai kai Kamal bance ka saketa ba,kabar maganan nan ,dama shiyasa ka ɗauko ni kakawo ni,wallahi ranka zai ɓaci",faɗan Hajiya da ranta lokaci ɗaya ya ɓaci.
Murmushi Ummah tayi tace," Hajiya baza ayi haka ba da Kamal da Khadija duk ɗaya ne awajan mu ,kubamu lokaci zamuyi shawara".
Hajiya taji daɗi maganan a zuciyar ta a zahiri ko ta nuna sam baza ayi haka ba,Ummah ta gwada mata in aure bai ƙare ba fa ya zasuyi,sun jima suna hira daga baya suka tafi.
Bayan fitan su Khalil da Khadija sukai tsalle suka dire suka wallahi sai Kamal ya saki Khadija,Ummah tace suje suyi tunani,Khalil yace tunanin kenan.
Tundaga ranan kusan kullum Kamal sai yazo,Khadija ko tana ganin zuwa shi take zuwa ta tasa shi gaba da baƙaƙen magana,wani lokaci yai kuka wani lokaci ya daure ma zuciyar shi ya tafi,Ummah tayi juyin duniya taƙiya ta bi zugan Khalil,duk abinda sukeyi Abba bai san maganan ba.,Hajiya tazo harta gaji tana roƙon Khadija don Kamal yabi ya fita hayyacin sa.
Fatima da haushin Kamal takeji amma yanzun tausayi yake bata sabida mugun wulaƙancin da yake gani wajan Khadija.
Ta sameta tayi mata magana,ta nemi dukanta yasa ta je ta samu Abba,take Abba ya kira Kamal ya kirata yace ta shirya ayau tabar masa gidan sa bazata kwana ba,aiko Khadija harda suma Khalil kamar ya haɗiye zuciya don baƙin ciki,Ummah dai cewa tayi Allah yasa haka shine alkhairi,Abba ko cewa yayi ko gawanta ne sai an maida shi gidab Kamal.
Da ƙyar Kamal ya roƙi Abba yabari nan da sati ɗaya yai gyare gyare Abba ya yarda,Kamal da farin ciki da murna ya koma gida ya sanar da Hajiya.
Khadija ko yanda