Showing 30001 words to 33000 words out of 46304 words
Chapter 11 - MARYAM YAR KUNAMA COMPLETE- BY MRS BASAKKWACE .txt
ɗa da halinsa kiyi haƙuri".
Sa hannu tayi ta ɗauke hawaye masu zafo da suke kwararowa daga idonta tace,"ba komi ɗan kuka ne mai ja ma uwarsa jifa,wata rana sai labari",cikin sanyin murya gwanin ban tausayi.
Khadija ko tunda taji kalaman Hajiya Bilki a akan surukarta ta juya ta runtsa ido cike da takaici da kunya,sam Hajiya Bilki bata da mutunci da da daraja na gaba da ita shiyasa ko kaɗan basa zama inuwa guda.
Duk wanda yake ɗakin sai da yaba Hajiya haƙuri don sam basuji daɗi abinda Hajiya Bilki tayi ba.
Ta ɗan jima kafin ta aje yaron tai musu sallama ta tafi,cike da dana sanin zuwa ganin yaron,duk da wani ɓangare na zuciyarta farin ciki yake da wannan haihuwar,Fatima tai mata rakiya har bakin motor tana mai ƙara bata haƙuri tana faɗin ba komi,harsai da taga driver yajata sun bar haraban asbitin kafin ta koma ciki.
Khadija najin tafiyarta amma ta kasa buɗe ido suyi sallama saboda kunya.
Ahankali suka rinƙa watsewa daga ita sai Fatima suka rage,lokacin goma na dare yayi Khalil ya dawo ya kawo musu abinci da drinks kafin yai musu sallama ya tafi gida.
Washagari bayan likita yashigo ya dubata ya duba baby basu da wani damuwa ya sallame su,koda suka koma gida cike yake kamar gidan biki,ƴan uwa da abokanan arziki duk sun hallaro ganin Babyn Khadija.
Abba tunda ya ɗauke yaron ya hana kowa duk wanda zai ganshi saide ya leƙeshi a hannun Abba yai masa addu'a.
Khadija kaɗai ya yarda ta amshi yaron taba ma Iya Lami tai mai wankan yama,ta shirya shi ,kafin tai ma uwar yaron wanka.
Hajiya tunda ta koma gida take neman layin Kamal,amma bata samu,ta cika da mamaki,gashi taje gidan shi ance sun tashi ai.
Kiran Khadija tayi ,bayan sun gaisa ,ta tambayi kwanan yaro tace mata yana lafiya,Khadija ta ƙara bata haƙuri akan abinda ya faru jiya tace mata ba komi kafin ta tambaye ta inane gidan su amaryan Kamal taje taji inda suka koma,Khadija tai mata kwatance,tai mata godiya ta kashe wayar.
Sa Driver tayi yakaita unguwan su Maryam ,bayan sun shiga yayi parking ta fito ta shiga gidan.
Part ɗin farko ta ƙwan-ƙwasa haɗi dayin sallama,ba'a jima ba akazo aka buɗe akai mata iso,ta shiga ta zauna a kan kujera.
Mai aikin tace bari ta kira mata Hajiyar gidan,shiga ciki tayi ta kira Momyn Maryam ta isketa tana waya da Maryam ɗin saida ta ƙare kafin take gaya mata tayi baƙuwa,da mamaki tace baƙuwa kuma,ina zuwa", Tani dawowa tayi ta sanarda Hajiya,kafin taje ta kawo mata ruwa da drinks.
Momy takai minti talatin kafin ta fito,ta hakince kan kujera tana kallon Hajiya tace,"sannu da zuwa".
"Hajiya tace yauwa,ya gida?
"Lafiya lau,saide ban shaidaki ba".
Murmushi Hajiya tayi tace,"Sunana Hajiya Aisha mahaifiyar Kamal".
Momy ta faɗaɗa murmushi tace," aa Allah sarki da yake bamu taɓa haɗuwa ba balle in shaida ki,ai Kamal yana da kirki,Allah ya masa albarka".
Murmushin yaƙe Hajiya tayi tace,"amin dama nazone kubani number Kamal daya canja kuma kimin kwatance gidan da suka koma".
Da mamaki Mom ke kallon ta,tama raina mata wayo tace ita mahaifiyar shi ne kuma ra rasa number shi yatsina face tayi kafin tace,"kin ce ke mahaifiyar shi ce kuma ki rasa number shi da sanin inda yake,kina nufin baki san Kamal yana dubai da matan sa duka ba".
Murmushin da yafi kuka ciwo Hajiya tayi tace,"Hajiya kenan Kamal tunda ya aure ƴarki na kasa gane gaban shi ko bayan shi sannan ai matar sa ɗaya don ya saki ɗaya,ɗiyar ubangidan shi da yaci amanar sa,yanzun ba wannan ba nazo ne kibani number sa don nasan bazaki rasa ba tunda ɗana na tare da ƴarki,in faɗa masa Khadija ta haihu,ɗako yafito sakkkkkkk shi,ya aiko da kayan barka".
Momy daskarewa tayi a wajan,daga ganin yanayin mahaifiyar Kamal da yanda take magana ta karanci duniya ta iya yaɓa magana.
"Mai kike nufi Hajiya kina nufin ƴata ce ta rabaki da ɗanki ko yaya,duk ɗan da kika ga ya guji uwarsa tou ba ɗan......!
"Dakata Hajiya bashi ya kawo ni ba,ki haƙuri na katse numfashin ki,ashe rashin mutunci da rashin kunya a nono wancan mara kunyar tasha,ni dama ban ɗauke ku a surukai ba,don auran ban taɓa sa masa albarka ba,nayi takaici rasa surukar arziki ƴar gidan girma ƴar dattawa Khadija Basheer wanda ƴarki taci amanar ta ta aurar mata miji".
Mom batakai ga ƙarashe maganan taba Hajiya ta katseta ta hanyar ɗaga mata hannu.
Jin kalaman Hajiya yasa Mom saurin ɗagowa tana kallon ta mai take nufi dama mijin Khadija Maryam ta aura,bakinta har kakkarwa yake tace,".............!
_typing🖌️_
*🔘MARYAM🔘*
_(Ƴar kunama_)
NA MARUBUCIYAR:-👇
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
AWANI GARI
JIDDATOU
ND NOW
MARYAM ~ƳARKUNAMA~
MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)*
*(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)*
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo
WHATSAPP NUMBER:- *08167151176*
WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE*
GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*
IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE*
TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE*
SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE*
*PAGE 31*
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Jin kalaman Hajiya yasa Mom saurin ɗagowa tana kallon ta mai take nufi dama mijin Khadija Maryam ta aura,bakinta har kakkarwa yake tace,"kina nufin Kamal mijin Khadija Maryam ke aure?, bakinta na kakkarwa,taɓa baki tayi taci gaba da faɗin "sai mai inta aure mijin Khadija in ba'a aure za'a aure uwar ta balle harta haife ta,ai ba haramun bane don ta aura mijinta,tamin dai-dai bata yar a ƙasa ba hakan ya tabbatar min dacewa tabbas Maryam ƴata ce ta sha nono na Allah yai mata albarka".
Murmushi Hajiya tayi ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tana kallon Mom a ɗage tace tabbas kuwa ba haramun bane ,Allah ya halarta ,amma ai ana barin halas kodan kunya,ko bayan ran Khadija in Maryam ƴar halas ce bazata iya auran mijin Khadija ba,sabida amana,amma hakan da tayi ya tabbatar mana da shegiya ce ƴar satan kwana,ai wallahi kamar maza tana ga binsuraye,mtsewww".
Hajiya cikin kakkausar murya take maganan ta ƙare shi tana mai jan dogon tsaki.
"Ke Hajiya tun muna shaida juna tashi kibar min gidana,ehe,ɗan naki da ya samu tarbiya ai bazai gujeki ba,amma da yake baki iya masa tarbiya ba ,ai ya juya maki baya".
Murmushin da ke ƙarama fuskan Hajiya kyau ta ƙara saki tare da cewa,"in ana maganan tarbiya ke har zakiyi magana,ba bin boka da ƴan tsubbun da ta tsotsa a nono bane yasa ta rabani da ɗana ɗaya tilo,Allah ya isa bazan taɓa yafe maku ba wallahi,in shaAllahu rabbi sai ƴarki ta ƙarashe rayuwar ta kare sai yafita mutunci a idon duniya".
"Wallahi ba amin ba ,li'ilafi ƙafa dubu,ɗanki dai da yaƙi maki biyayya ,ƴata ko ita zatai rayuwa mai kyawu tunda tana faranta min".
Miƙewa Hajiya tayi tana gyara hijjab ɗinta,tace,"in kin gadama ki kira shi ki faɗa masa inko baki gadama ba karki faɗa masa duk tsiya dai ba zai haifi yayan wannan ɗan ba,duk wanda za'a haifa ƙanin shine,balle daga ganin tambaɗaɗɗan ƴar nan taki ta tsiyayayar a titi tuni ba'abinda zata ɗauka".
Tana maganan murmushi fallllll akan fuskanta tana ƙarewa tasa kai bata jira mai Mom zata kuma cewa ba ta fice.
Ƙwafa Mom tayi ta cije ɗan yatsa tayi kamat zatabi Hajiya sai kuma ko mai ta tina ta fasa.
Hajiya motor ta faɗa Driver ya ja suka fice a gidan ,sai da ya halba motor kan titi kafin ya tambaye ta inda zasu tafi ta gaya masa.
Gidan wani mallami sukaje a hayi bakin ruwa,nan tasa aka bincika mata wani hali yaronta yake,nan mallamin ya faɗa mata halin da yake ciki bai ɓoye mata komi ba,tashiga ruɗu da tashi hankali,kuɗi ta zuba masa don akarya asirin Maryam,bayan tabar gidan wani gidan mallamin ta ƙara zuwa abinda wancan ya faɗa mata shi shima ya faɗa mata nan ma ta ƙara bada kuɗi kafin ta wuce taje taga baby da Maman shi bata jima ba ta wuce gida ta kira kawun shi ta faɗa mai abinda ke faruwa,yayi takaici da baƙin ciki sai faɗa yakeyi kamar Kamal ɗin na gabanshi.
Shima baiyi ƙasa a guywa ba,yabada addu'o'i a masallatai da makarantun islamiya.
Washagari ya turo da kayan barka aka kai gidan su Khadija.
Ranan ƙauri rago aka yanka ,gida ya cika maƙil kamar ranan suna,Hajiya tace musu suyi ma yaron huɗuba da duk sunan da suke so,dama Khalid yamai huɗuba da sunan Abban su.
Ɓangaran Maryam ko tunda Mom ɗinta ta kirata ta faɗa mata yanda sukai da Hajiyar Kamal ta kuma faɗa mata Khadija ta haihu ta samu na miji hankalinta ya tashi,bin mallaman ƙasar india ta rinƙa yi sua amfani da ita da zumar zasu kashe yaro,tabasu ɗan lokaci,don sam bata so Kamal ya zama yana da ɗa ko ɗaya,so take da yayi ritaya yabar aiki ta aika shi lahira ita kaɗai zataci gadon shi,dama mace Khadija ta haifa,amma namiji yafita gado akan maine wallahi saita kashe shi haka ta ƙudira ma kanta aniya.
Ɓangare guda Dr Hadi yasata a gaba da kira sai ta dawo ko ya biyota ƙasar duk wacce za'ayi ayi kawai,hankalinta duk baya waje ɗaya ,ƙarya take so tayi ma Alhaji Labaran taje nijeriya.
Kamal ko yana can yana aikin shi hankalin shi yana wajan mahaifiyar sa amma ya ɗaga waya ya kirata sam bai iyawa,Maryam kaɗai yake iya kira,itama sai yata kira da wiya take ɗagawa so ɗaya,abin nacin zuciyar shi sosai da damun shi,amma ya kasa furta ma kowa
Hajiya tasa addu'a akan ɗanta kota ina yayinda Mom da Maryam suke ƙara ɗaura aiki.
Wani lokaci Kamal ji yake jikin sa kamarbya kama da wuta gaba ɗaya rayuwar sa bata masa daɗi,bai ganin ko wacce mace a matsayim mace inba Maryam ba.
A satin Maryam tayi visa zuwa nijeriya inda Alhaji labaran yai mata shatara ta arziki tsaraba kamar za'a buɗe shop rite.
Tunda Khadija ta haihu Zainab ta tattaro ta dawo gidan su Khadija,Maman Zainab ma tazo barka,kullum Zainab sai tasa pics ɗin jariri a facebook anan Khalil yagani yake tambayanta yaron waye ta faɗa masa.
Aiko take yaje ya tada ɓalli a gida sai anje an nemo masa auran Khadija,mahaifiyar shi da tabi zugan Aisha tace sam bata yarda ba sai dai ya aure Amira yana saurayi mainzaiyi da bazawara da aka hanashi auran ta tun tana budurwa,sai yanzun da taje tasha wahala aka sako ta kafin za'a bashi.
Dayake Dad ɗinshi akwai tsare gida sam bai ɗaukan maganan mata take yaja musu layi ,yace in ya ƙara jin maganan wallahi sai ya ɓata ma kowa rai,haka ko akayi sun san bai magana biyu bai ɗaukan raini yasa kowa yasa ma bakin shi linzami badon sun so ba.
Dady Khalil tare da abokanan sa sukaje gidan su Khadija,suka shiga sukai barka harda bada tukuyci Khadija sai jin kunya take,cewa sukai suna so suga mahaifinta Khadija.............!
_typing🖌️_
*🔘MARYAM🔘*
_(Ƴar kunama_)
NA MARUBUCIYAR:-👇
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
AWANI GARI
JIDDATOU
ND NOW
MARYAM ~ƳARKUNAMA~
MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)*
*(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)*
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo
WHATSAPP NUMBER:- *08167151176*
WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE*
GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*
IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE*
TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE*
SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE*
*PAGE 32*
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Dady Khalil tare da abokanan sa sukaje gidan su Khadija,suka shiga sukai barka harda bada tukuyci Khadija sai jin kunya take,cewa sukai suna so suga mahaifinta Khadija a karo na biyu.
Khadija tunda taga Dad ɗin Khalil gabanta ke faɗi bata san mai yasa ba,waya faɗa musu ta haihu dama Khalil ya ji maganan da Saudat tai mata yai biris ko burabisko kamar bai jiba.
Ummah tace mai yana bacci sai dai su dawo suga Khalil ko Khalid,haka suka tafi batare da sunga wani babba nata ba.
Ana gobe suna,kayan rabon suna kamar ba'aso daga ɓan garan Khalil da mahaifin shi, haɗe da raguna biyu a yanka ma yaro,baki kawai Khadija ta sake tana kallon kaya,Umma sai murna take haɗi da godiya,haka ɓangaran iyayen Kamal suma sun ɗan taka rawan gani ba kaman ɓangaran Khalil da kamar su akai ma haihuwar.
Hajiya rago ɗaya ta aiko,Khalil da yace a maida musu kayan su,Umma tace baza,ayi haka ba,komai suka kawo su amsa.
Uwar ƙarni tasha gyara da ƙumshi kamar wata amarya.
Gida yacika falllll da ƴan uwa da abokanan arziki kowa ka gani fuskan shi cike yake da fara'a da annashuwa tsan-tsan farin ciki ba'a cewa komi.
Koda Khadija na tare da Kamal sai haka.
Yau ta kama suna gida ya cika maƙil sai girke-girke ake ana sauke wannan tunkunyar a ɗaura wannan,manyan mata ne kawai ke shige da fice da manya lesuka da shaddodi da ,atamfa,duk sun sha gwala-gwalai,biki yayi biki ba ƙarya da dangi suke kuri,uwar biki taci ado Hajiya Khadija uwar Basheer (ABUL-BAIT),sai fara'a da murna take,ga ƙawayen su na makaranta duk sun iso ,kowacce tayi wankan kece raini ba ƙarya,Zainab itace gaba-gaba,uhm amara ƙirjin biki duk wani abu na ɓangaran ƙawayen su itace gaba,hotina kawai sukeyi suna watsa shi media.
Ƙarfe biyu dai-dai ƴan tawaga *ƳAR KUNAMA FANS* suka shigo kowa kanta a sama sunci ado kamar ba'a mutu ba,can na hango @EISHERH anci supper wax da gwala-gwalai a hannu da kunne da yatsu,kannan a sama,an ratayo jaka ba'a ko ganin gaba,daga can nesa na hango Mom Farisa anci leshi sai washe baki ake haƙoranta suka bayyana da suka sha ado da haƙoran zinari na makka,har zan wuce ,na hango ƙawata Jikar Hajiya sakan baki da hanci nayi irin wannan kyau ƙawata,leshin jikin ki zaki ba,wannan ɗauri ko ture kaga tsiya sunan wani ɗauri,gefenta kuma Zee Cute sai zuba take kamar kurna,daga gefenta Hadiza Yola ce,su Fulani Girl ko ana zuwa plate aka ɗauka Mom Dad ɓangaran da kiɗi ke tashi ta nufa,Humaira Abdullahi,wajevta samu ta zauna ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya taci glass baƙi sai taunan cigam take kowa a ɗage take kallon sa,daga gefen ta Aishat El,musa ce kanta nakan wata,daga can na hango Dido,Mamee sai rawan kai take duk inda taga ana hoto sai ta faɗa,Sakina irin wannan rawa haka,Nawwara nadaga gefe tana kallon ƙasan zanin kowa,can na hango Zee Yero ta tasa plate shaƙe da naman kaji,duk da nana karere gayyar soɗi bai hanata buɗe ciki tana yagan nama ba ,gefenta Ni'imatu Badamasi ce ba abinda take sai cire selfie , kai masha Allah dana hango Khadija Ummu Sayada,kunsan khadijoji akwai iya wanka,sai danayi da gaske nima na ganeta , sai ga Maman Hussaini nasa shinkafa a jaka,ɗayan ma Khadija Umar Ahmad ta haɗu ta haɗe, su Aunty Jmaila an hakimce kan kujera sai tashin ƙamshi take,daga gefe can walida sama ne,na hango Deejo itama sun haɗa kai da Sayyada sai ƙus-ƙus suke,gaba ɗaya fans ɗin ƴarkunama idona ne kaɗai zai iya hangen ku amma alƙalami bazai iya rubuta kuba,kun mana kara wajan sunan Basheer Allah yabar zumunci,daga ɗayan ɓangaran *FULANIN TASHI* *FANS* ,suma tawagar su ta iso irinsu
Maryam Muhammad sunci ado mashaAllah @❤️❤️❤️❤️ ,Mummy daga gidan *KIBIYAR SO FANS* na hangi Zeenatu halliru ,daga gidan *UWAR MIJI FANS* mamman mohammad ma tazo bikin sunan Basheer daga *LE QUEL JE VEUX FAN*
, Mom yusura,Zainab Muhammad duk sun hallaro *AISHA FULANI GAL FANS*
, Safiya Aliyu safiya89, *MAIRO ƳAR ƘAUYE FANS*,Mami😘 *WAYE SANADI COMMENT GROUP*, *KHAUSAR NOVELISTE*, *AƘIDA TA NOVEL FANS*, *MOONLIGHT WRITERS FANS*, *AK SARAKI PALACE GROUP*
, *MUTUNCIN ƳA MACE FANS*, *MARYAM DILLALIYA FANS* *HOME OF QUALITIES WRITERS FANS* duk sun hallaro gida yacika fammm ba masaka tsinke,kowa yazo taya murnan suna Basheer (ABUL-BAIT),kowa ci yake yasha ya goge wiya,masu takeaway nayi masu ci subar shi anan sunayi,anata hotina kota ina amaryan ƙarni nata sawa tana sauyawa kaya kala-kala.
Dangin Kamal ma sunzo da tawagar su,sunci ado kamar baza'a mutu ba,sun samu tarba awajan Ummah da sai da suka koma suka ba Hajiya labarin kalan bikin da akayi sai sambarka sukeyi,wa ƴanda sukai vedio da waya suna ta nuna ma Hajiya,nan sukai ta zagin Kamal yayi sake na dafe ai wannan ba dangin yar wa bane sun san mutunci al-umma,anyi bikin da basuyi tsammani ba,sunji kunyar bada kayan goyon da suka kawo,da suka ga himili kayan da mutane keta shigowa dashi ,ƴan kallo kawai suka zama,ashe ƙaryan arzuki suke ga inda arziki yake nan,inda ake biki ana facaka da kuɗi kamar ba'aso.
Ba mutane suka rage a gidan ba sai magariba,kuma kowa ya wuce da sobeniyas ɗinshi gida,wannan suna saidai muce mashaAllah yayi albarka anyi shi cikin farin ciki a gama cikin farin ciki,Allah ya maida kowa gidan sa lafiya.
Sai bayan ishaa'i mutane sun tafi kusan ba kowa sai su isu-isu da ƴan uwansu na kusa,nan suka fara tarin kayan da ta samu ita da jinjiri da zun-zurutun kuɗi da tasamu daga ƙawaye ƴan-uwan Umma da Abba,matan abokanan yayyunta,cousines sam Zainab ta kasa irga kuɗi zuba shi tayi a leda ta kulle ta jefa mata shi cikin jaka.
lKamar kullum yana kwance kan kujera bayan yadawo aiki yayi wanka ya ci abinci ɗaukan wayar shi yayi ya kira Maryam bata ɗauka ba,kunna data yayi ya shiga whatsApp da yayi wata bai duba ba,bayan message sun gama shigowa,yawan message ɗin da yagani a family group ɗinsu yasa shi fara buɗewa,bi yake daki-daki yama karantawa har yazo kan hoton wani yaro mai tsananin kyau a ƙasan hoton yaga an rubuta...........!
_typing🖌️_
*🔘ƳAR KUNAMA🔘*
*Da Ace ɗan'adam Ya San ƙimar Haƙuri,Da Girman Ladansa,Da Bai Yi Fatan Gaggautuwar Yayewaba,...Duk Sanda Ka Gane Cewa Allah Bai Dora Maka Damuwaba,Sai Dan Ya ɗaukakaka,Hakan Zai Sa Ka Gane Cewa Duk Abubuwan Da Suke Faruwa Gareka Marasa Dadi,Alkhairi Ne*
_RIƘON AMANA SAI ƊAN HALALI BUTULU KO BAZAI IYA BA🤗👌_
MALLAKIN:- *MRS BASAKKWACE*
*~PAGE 33~*
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
shiga whatsApp da yayi wata bai duba ba,bayan message sun gama shigowa,yawan message ɗin da yagani a family group ɗinsu yasa shi fara buɗewa,bi yake daki-daki yama karantawa har yazo kan hoton wani yaro mai tsananin kyau a ƙasan hoton yaga an rubuta *MASHA ALLAH WELL COME TO THE WORLD UR NEW BORN BABY*, tasayawa yayi ya tsura ma hoton ido son yaron da ƙaunar shi nabin zuciyar shi da ratsa jinin jikin sa ,sawan lokaci ya ƙura ma hoton ido,kafin ya fara bin message ɗin daki-daki yana ga anyi tagged ɗin sunan shi anayi masa barka da Allah shi raya,gaban shi take ya yanke ya faɗi,sai yanzun Khadija ta faɗo masa a rai,watou harta haihu kenan,a hankali har yazo kan hotinan ranan suna ,ga hotina nan birjit na suna Khadija da