Showing 6001 words to 9000 words out of 46304 words
Chapter 3 - MARYAM YAR KUNAMA COMPLETE- BY MRS BASAKKWACE .txt
gaya mata ba,a bakin wa taji,Zainab ɓan garan zuciyarta ya faɗa mata.
Waye baida lafiya Khadija ta ƙara mai-maitawa tana kafe Maryam da ido.
Uhm,amɓ....,dama...Momy ce ta aiko ni,bakijin daɗi ne?.
"Lafiya ƙalau nake nazo kawai genaral checkup,tunda mijina zai ƙara aure in gane lafiyata kinsa kana zaune ƙalau za' a ɗauko rigan da babu wiya asaka maka, a dan ƙara maka ƙamayaya".
Tana maganan tana murmushi,kamar ba abinda kecin zuciyarta,daga ƙasan zuciyarta kamar ta shaƙe Maryam don baƙin ciki,ta ɗanji sauƙi da raɗaɗi ta dalilin dan ƙara mata magana a dunƙule.
Murmushin yaƙe Maryam tayi duk da bata fahimci kalman rigan da bata da wiya da ƙamayaya ba,tace," kuma hakane fa".
Khadija murmushin da yaƙi barin fuskanta ta ƙara faɗaɗa shi tace,"ina miki fatan nasara,ki sani kuma wannan karon shine karo na ƙarshe da zaki ga abu a hannuna ki amshe shi,kuma ina mai ƙara tunasar dake ki rinƙa ramin kanki,karki zama macijin da baki ramin kanki saide wani yayi kizo ki shiga".
Khadija na magana tana ɗan dukan kafaɗar Maryam,tana gamawa ta ɗau ledan maganin ta ta wuce batare da ta jira mai Maryam zata kuma cewa ba.
Nurse ko sakin baki suke cike da mamaki suke sauraran kalaman Khadija da dukkan alamu tasan Maryam ciki da bai,don gashi tana mata jurwaye mai kaman wanka
Maryam ko tsayawa tayi sandaran-dan kamar mutum-mutumi ,kamar kazan da ƙwai ya fashe mata aciki.
Ɓangaran Khadija ko sai da ta samu kekenapep kafin hawaye masu ɗumi suka samu daman zubo mata a kuma,mamaki take yaushe Maryam ta lalace haka take bin maza kamar bunsura,uwa uba harda ciki ta zubar a satin da za'a mata aure,wanna wani irin aure ne ba istibura'i,lallai auran sunna ko auran zina sunan wannan ƙarin auran na Kamal ,ƙazan taccen aure kenan,wani ɓan gare na zuciyarta ya faɗa mata.
********
Maryam ƙafarta nauyi yai mata da ƙyar taja shi ta fita titi tahau napep duk da gidan su ba nisa daga wajan.
Aiko tana zuwa gida ta kira Kamal ta fashe dawani mugun kuka ,hankalin shi ya tashi,yana ta tambayanta lafiya,da ƙyar ya lallasheta jikinsa duk rawa yake.
Karkacewa tayi ta gyara zama tace.......!
*OHHHHHH NI MATAR BASAKKWACE,COMMENT ƊINKU NASANI FARIN CIKI DA NISHAƊI,INA GODIYA SOSAI DA ƘAUNAR DA KUKE NUNA MIN,ALLAH UBANGIJI YABAR ZUMUNCI🥰*
SHARED ND COMMENT
*MARYAM*
_(Ƴar Kunama)_
~ROMANTIC STORY~
~*BA SAI KA TAIMAKE NI BA,AMMA KAR KA CUTAR DANI🙌BA LALLAI SAI KA SAKANI JIN DAƊI BA🥰,BANDAMU DA MAƘIYI BA🤷♀️,AMMA KARKA NUNA MIN SOYAYYAN ƘARYA🤗BA LALLAI SAI KA SAKANI JINDAƊI BA🤗AMMA KARKA LALATA NAWA JIN DAƊI🥰🤗*~
*ƘIRƘIRARRAN LABARI,BANYI DON CIN MUTUNCIN WANI KO WATA,TRUST, FRAUD, REASON, COLLECTION AND KNOWLEDGE*
MALLAKIN:- *CAT LOVER*
*PAGE 8*
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
"Karkacewa tayi ta gyara zama tace,"Baby yanzun Khadija tabar gidanan,tamana zagin tatas ƴan gidan mu,harda buguna tayi ta rinƙa taka min ciki".
Tana magana tana sha-sh-sheƙar kuka.
"Kankutumar bala'i,yau ko sai taji ajikinta ita,kuma wallahi sai nakaita ƙara kotu".
Cikin ɗaga murya da tsawa yake magana.
Taci gaba da faɗin,"kuma tace in tanadi lakafani na shigowa gidan ta,amma dan Allah karka kaita ƙara kotu,ni da zuciya ɗaya nake sonta itace dai bata sona".
"Kafin ko ta kashe ki,zan gyara mata zama naga tashe rashin kunya takeji duk ta rainani".
Haƙuri yafara bata yana lallashin ta hartayi shiru.
*********
Da hannu ta ringa ma menapep kwatance har yakai ta ƙofar gida ta biya shi kuɗi,ta fita ta buɗe ƙaramin ƙofar ta shiga.
Baba mai gadi sai sannu yake mata,tana amsawa.
Tana shiga falon tai kiciɓus dashi ranshi haɗe,kamar an aiko ma da anyi masa mutuwa, yana ta kai da kawowa.
Harta gitta shi zata wuce bata kuma kallon shi ba,daga kallo ɗaya,sa hannu yayi ya danƙo hijjab ɗinta ya jawo ta ya wurgata ƙasan kafet,kanta yunƙara tai ƙarfin hali ta tashi kasancewa jikinta ba ƙarfi yafita ua take mata hannun ta.
Ƙara ta saki saboda a zaban da ya ziyarce ƙwa-ƙwalwan ta.
Bata gama jin azaban take hannun da ya take mata yace,"daga gidan ubanwa kike,da izinin ubanwa kika fita?.
Cikin halin ko in kula yake maganan.
Binshi tayi da ido tana ƙif-ƙifta su kamar tayi ƙarya,taɓa baki tayi tace,"asbiti naje,ga ledan maganina nan in har baka yarda ba".
Bin ledan da yafaɗi ƙasa yayi da kallo,magani suka watso,mtsewww daganan kuma fa?.
"Banje ko ina ba",ta faɗa a taƙaice.
Ni zaki maida yaro ki raina min wayo,kin ganni kamar sa'an ki,nazama warinki,zakije gidan matar da zan aura ki zage su tasssa,sabida kina baƙin ciki da ita ,ba'a aure aka aure uwar.....!
Kan ya ƙarashe tasa ƙafa ta haure shi tayi sa'an dai-dai kan joystick ɗinshi tabashi mugun tokari da harsai da ya baje a ƙasa,zabura tayi ta miƙe,yana murƙusu-suwa,kafin ya ankara tabishi ƙasan ta ƙara sa ƙafa ta-taka joystick ɗin.
Ihu mai ƙarfi ya saki,yana wuntsilawa.
Ranta ɓace tace,"wallahi Kamal duk iskancin ka karka ƙara sa sunan uwata ko ubana,ka tsaya iyakan kaina nice taka basu ba, nima baka auro ni don zagi da duka ba,in zakai aure ka auro duk mutan duniyar nan sam tunda ba akaina suke ba,bazai dameni ba".
Tana gama faɗa tajuya ta tai sauri ta buɗe ƙofar ɗakin ta tafaɗa ta kulle gabanta na tsanan ta faɗi.
Yajima kwance yana jin azaba fiye da two hours kafin ya ja jiki ya tafi bedroom ɗin sa,
daƙyar yakai wajan sidedrawer ya jawo wayar shi ya lalubo number Khalid yace masa yazo yakai asbiti bai lafiya.
Ɓangaran Khadija ko tana datse ƙofar tabar key ajiki gudun kar ya ɗauko extra key ya buɗe yasa,tajima jingine da ƙofa tana maida numfashi kafin ta cire hijjab ɗinta ta zauna kan kujera ta rafka tagumi,tana tunanin rayuwar su ta baya da Maryam,ta maida ta komin ta ƙawar ta,tana iya sadaukar da farincikin ta akan Maryam,ashe ita ko dariyan fatan baki take mata lallai kam dariya ba soba,firich ɗinta ta buɗe ta ɗauko fresh yo ta buɗe ta kwankwaɗa,sanyin ya ratsa jikinta da zuciyarta.
Ɓangaran Kamal ko zuwa yayi ya tarar da abokin nasa riƙe da sandar girman nashi ya damƙe gaban shi gabaki ɗaya yana ta ya musa fuska,a zuciyar shi yana addu'a Allah yasa bata kashe masa gaba bane.
*😂😂NIKO NACE ALLAH YASA BAZATA ƘARA MOTSI BA,BALLE HAR KA ƘARA CIN MARYAM,MUGA YANDA ZAAYI ZAMAN AUREN GABA GAƊI,LOL😜*
Tai maka masa yayi a hanzarce suka fita,yasa shi a motor bayan ya kwantar masa da kujera.
Khadija ko tana jin fitar shi ta fito ta ɗau ledan maganin ta,komawa ɗaki ta aje,kafin ta fito tayi alala irish da hanta,da source ta juye abinta a flacks ta koma ɗaki,dai-dai da ita tayi batayi dashi ba,ko tayi dashi baici saide taba su baba mai gadi.
*********
A asbiti ko bayan sunga Dr anyi gwaje-gwaje result ya fito, Dr ya tabbatar da cewa jijiyar joystick ɗinshi da take kawo maniyi tayi laushi da an ƙara bugun shi a wajan zata tsinke,bashi magun-guna yayi da allurai,da kuma bashi shawaran karyai sex har sai nan da 2months.
*NIKO NACE DANƘARI ƊAN GARIN ƘARAYE,A ƘAUYEN DAƊIN KOWA,GA KAMAL NA NIYAN ANGWANCEWA GA KHADIJA TA LALATA KAYAN AIKIN NASHI*.
Dr ya ɗaura shi akan magunguna masu kyau,Kamal yacika fammm Khadija in ya kamata sai ya illatata,uwa uba mai zaice ma Maryam da tasan yana aiki yanzun ko yazama hunkon ashana.
Zuciyarshi cike da saƙe-saƙe Khalid yazo ya ajeshi a gida ya wuce.
Koda ya shiga falon da harara yabi ƙofar ɗakin Khadija yana ƙwafa,kamar tana kallon sa.
😂😂😂AIKIN BANJA HALALA ADUHU😜.
Tundaga lokacin suke wasar ƴar ɓoyo da Khadija,bata fitowa sai bainan,gashi ɓan gare guda ya kasa gaya ma Maryam,Maryam ko rashin neman da bai mata ba yamata daɗi yanda zata gasa kanta yajita zammm a tsuke.
Aunty Maryam takira shi maganan gida da za'ai ma ƙanwar ta jere,hankalin Kamal ya tashi har yafita yadawo.
Tana zaune falo ta mimmiƙe ƙafa tayi farfesun kayan ciki yaji yafi tana haɗawa da bread tana ci tana korawa da shayi.
Batai aune ba taga mutum akanta ya haɗa giran sama dana ƙasa,duk da gabanta na faɗi tayi matuƙar tsorata,saura kaɗan fitsari ya kufce mata,danne tsoron tayi da firgita ta galla masa uban harara da manyan idanuwan ta..
Wani tuƙuƙun baƙin ciki yazo masa zuciya cike da mamaki yake kallonta sam bata tsoran shi yanzun da ko ko ɗaga ido batayi ta kalle shi ido cikin ido buɗe baki yayi yace,"keee ya mukayi dake,kin rainani ko,don kinga kinmin iskanci na ƙyaleki kincu bilis,ki tattara kayanki ki koma BQ".
Wani miƙewa tayi a zabure,tana aika masa da wani mugun kallo tace,"............!
*MRS BASAKKWACE*
_typing🖌️_
*🔘MARYAM🔘*
_(Ƴar kunama_)
NA MARUBUCIYAR:-👇
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
AWANI GARI
JIDDATOU
ND NOW
MARYAM ~ƳARKUNAMA~
MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)*
*(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)*
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo
WHATSAPP NUMBER:- *08167151176*
WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE*
GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*
IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE*
TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE*
SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE*
*PAGE 9*
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Wani miƙewa tayi a zabure,tana aika masa da wani mugun kallo tace,"wallah Kamal in duk duniya zasu taru wallahi ,suce in tashi in bar maka part ɗinan wallahi bazan tashi ba,saide in cewa kayi tafi gidan mu ka sakeni,zan kwashe kayana ko tasssss in barma gidan ka".
Duk da zuciyarta cike take da tsoro,amma a zahiri tsoron ya tafi dakewa tayi kamar bishiyar rimi.
Bata bashi daman yin magana ba taci gaba da faɗin,"kaga duk da four bedroom ne a part ɗinan wallahi baka isa ka shigo min da wata sheg.....!
Wani mugun mari ya saukar mata a lallausan kumatun ta da sai da ta haɗe maganan,ta dafe kumatu tana bin shi da mugun kallo yana ƙoƙarin ƙara mata ta wani cafke hannun sa da zafi nama,tana girgiza kai yayinda hawaye masu ɗumi suke bin kumatunta tace,"wallahi Kamal karka ƙara tafka kuskuren marina,mari nadaga cikin mafi mugun ƙasƙancin abu,tashine kasa a zuciyar ka bazan yiba".
Tana ƙare magana ta yarfar da hannun shi baki sake yake kallon ta,tana ta haƙiƙan cewa kamar gidan tane".
Koma tayi ta zauna taci gaba da cin abincin ta hankali kwance,kamar wani abu bai faru ba.
Ƙwafa yayi yace,"wallahi Khadija sai na gyara miki zama bata tashen rashin kunya kike ba,tunda kin ƙi tashi haka zan shigo da Maryam gidannan part ɗinnan kina gani wallahi,saide ciwon zuciya ya kama ki,mtsewww sakarya kawai".
Kamar da dutse yai magana,ko motsi batayi ba balle tasan da ita akeyi kai loma kawai takeyi tana kallon tv kamar ba wani mahaluƙi a ɗakin.
Ya ƙara wani mugun ƙuluwa,ganin tayi shiru kamar bata ji shiba.
Ƙwafa yayi ya ƙara fita fuuuuuuuuuu.
Da kallo tabishi tana mai mamakin mugun halin shi.
Shiko tafiya yayi gidan su Maryam ya basu haƙuri yace part ɗaya zasu zauna da Khadija,basai an kawo mata kaya ba,kafin ya gama ɗayan gini shi.
Da ƴan'uwanta sunƙi yarda da sukaji yace kafin ya gama ɗayan ginin shi haka suka yarda,company yaje yasai sababin funiture na gado ya tafi dasu gida suka cire wa ƴancan suka sa sababin,don Maryam tace bazata kwanta a gadon da Khadija ta kwanta ba,raba falon yayi ya maida kayan Khadija can gefe da dining ɗinta yasa akasa kujerun Maryam a ɗayan ɓangaran da dining ɗinta,store ɗin Khadija ya shiga ya kwashe kayan abinci ya maida mata kitchen ɗinta akasa kitchen cabinet,yace ma iyayenta sukawo kayan kitchen ɗinta.
Duk shige da ficen su Khadija na kallon su bata fito ba balle ace tayi.
**********
"Wallahi Maryam ko kibari in ciki koko in je in faɗa wa Kamal ɗin halinki".
"Dan Allah Khalil kayi haƙuri,saura kwana biyu bikina da ina hanaka ne da ban hanaka,kabari a ɗaura,zan rinƙa fitowa a duk inda kake ina samunka ba shine burin kaba".
"Ai wallahi tunda kika shigo ɗakinan baki fita sai kin buɗe min ƙafa naci,na ɗanɗani daɗin gyaran amarci".
Bai bata daman magana ba ya haɗe bakin su,yafara aika mata da wani mugun kiss mai kashe jiki da zautar da wanda ake aika mawa,take itama ta cafki harshen shi tana tsotsa,tana miƙa tana turo mai ƙirji tana goga masa breast ɗinta,suna sauke zazzafan ajiyan zuciya.
Kai hannuwan sa yayi yafara matsa nonon ta yana yamutsa su tana sauke ajiyar zuciya,yana rinƙo nipples ɗinta yana murza su,tura hannun ta tayi cikin wandon sa ta kamo joystick ɗin shi tana murzata bakin tana jijjiga ta ɗayan hannun ta yana cikin rigarshi tana shafa ƙirjinsa.
Ahankali ya zare mata kaya ya cire nashi,ya tura ta tsakiyan gado ya ware mata ƙafa ua danna mata joystick ɗin shi a ciki pussy ta,wata ƙara ta saki don shigan shi taji azaba,don ɗinkin da akai mata bai gama warkewa ba,caccakanta yai son ranshi saida yaji natsuwa ya ƙyaleta tai wanka ta tafi gida,bayan yabata dubu ɗari biyar gudun mawa,da ta koma gida ruwan zafi ta shiga tana ta gasa wajan don ta ciyu,don tana so tajita zam don,
da la'asar haka suka shirya suka tafi kamu.
"Wai ke Maryam kwata-kwata a sha'anin bikinan banga Khadija ba da zainab".
Taɓa baki Maryam tayi tace,"Aunty Sa'ah ,Momy ɗazun ta gama tambayata ,Khadija bata da lafiya,Zainab ko ƙanin babanta ya rasu ,kinji dalilin davya hanasu zuwa,kuma ma banda kirki bankai ma Ummah Khadija katin bikina ba,don tana mugun sona itama,kema shaida ce Aunty Sa'ah".
"Allah sarki,Allah yaba Khadija lafiya aiko zaki ban number ta inkirata,Khadija tana burgeni tana da kirki sosai,ina sonta duk cikin ƙawayen ki,ta biyo halin iyayen ta ,sanyin halin Ummah su yana birgeni bata ko magana sosai,Allah ya ba ma Ummah ta lafiya,don nasan tana da hawan jini".
"Wayyo,eh tana da hawan jini" Maryam tace a taƙaice.
Aunty Sa'ah tana ta kawo ma Maryam maganan Khadija ,Maryam na kaucewa
**********
Ana gobe biki akai wanki amarya,washa gari ko da misalin shaɗaya na safe dubban jamaa suka shaida ɗaura a MARYAM SA'ID da angon ta KAMAL MUKHTAR,murna wajan amarya da ango da sukaji an shafa fatiha babu kama hannun yaro.
Tana ji an ɗaura auran ta ɗau waya ta kira zainab ta shaida mata an ɗaura saide baƙin ciki ya kashe su,zama da Kamal har abada.
Murmushi Zainab tayi tace," Allah ya wargaza auranan inshaAllahu bazai je ko ina ba".
Tana gama maganan ta katse wayar zuciyarta na mata zafi da ƙunci.
Shiryawa tayi tace ma Mamanta zataje unguwa ta tafi gidan Khadija don zuciyarta ya koma wajan Khadija taje taga wani hali take ciki yanzun haka da mijinta ya auro mata aminiyarta.
Zainab bayan ta isa gidan kai tsaye ta shiga falon taga yanda aka sauya shi sai mamaki takeyi,ba kowa a falon sai ƙara tv.
Bedroom ɗin Khadija ta nufa ta buɗe ta shiga,tana kwance tsakiyan gadon ta tana bacci hankalin ta kwance kamar ba ita.........!
😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜😜 KAMAR BA MOM MUJAHID AKAI MA.......... BA YAU😂
*MARYAM*
_(Ƴar Kunama)_
~ROMANTIC STORY~
*ƘIRƘIRARRAN LABARI,BANYI DON CIN MUTUNCIN WANI KO WATA,TRUST, FRAUD, REASON, COLLECTION AND KNOWLEDGE*
MALLAKIN:- *CAT LOVER*
*PAGE 10*
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHIM*
Bedroom ɗin Khadija ta nufa ta buɗe ta shiga,tana kwance tsakiyan gadon ta tana bacci hankalin ta kwance kamar ba ita ake ma kishiya ba,zama tayi bakin gadon ta samu cinyar khadija dake waje ta aika mata da wani tsunguli,da yasa ta tashi a tsorace,tana warware ido,ganin Zainab na mata dariya yasa ta kai mata bugu tace,"muguwar banza har yanzun baki dena halin ki ba,wa yace ki shigo min gida har bedroom ba sallama?.
Haɗe rai tayi tana maganan tana hararan Zainab da sai dariya take, ta ƙare shi da sigar tambaya.
Tsagaitawa tayi da dariyan,tace,"wayace kibar gidan a buɗe,kina bacci ta ina kunnen ki zaiji sallama?.
Harara Khadija ta ƙara wurga mata kafin tace," ta kunnen ki,mutum na baccin sa mai daɗi zakizo ki tashe shi muguwa kawai".
"Yi haƙuri Khadija matar Kamal,uwar gida awajan Maryam kuma aminiyarta".
Da sigar zolaya tai maganan,tanayi tana kashe ido guda tana mata gwalo.
Mtsewwww ,"daga ita har Kamal ɗin na ɗaura ɗamaran ci musu a gidanan,Kamal bai san halina bane,ai ita Maryam ɗin zata bashi labari,wai kin san wani rainin wayo da Kamal yamin,wai saide in koma BQ yasa Maryam anan,ai tuni natashi tsaye na nuna masa bai isa ba,wallahi in yai wasa yau ɗinan Maryam bazata shigo gidanan ba".
"Cabɗi halin Kamal ya wuce tinani na,anya ba asiri tayi masa ba".
Taɓa baki Khadija tayi tace,"in ma asiri ne,ya tafi da hali,asiri ai yana tafiya da hali,waya sani ko kwance-kwance yayi ya ɓoye halin shi na banza ya bayyana na kirki,sam banso labarinan yaje kunan kowa a gidanan kar hawan jinin Ummah ta ya tashi".
"Nide Khadija kiyi haƙuri,duk daɗin zaman gidan iyaye,zaman gidan miji ya fishi".
"Wane gidan miji,tabɗi ba kalan wannan gidan mijin ba,gwamma inta zama gaban iyayena da kalan wannan aure wata uku da kwanaki an maka kishiya bakaji daɗin amarci ba,balle ka tabbatar ɗakin miji yafi na iyaye".
"Nide kiyi haƙuri ki kauda kai kiyi kamar bakiji ba,kamar baki gani ba Khadija,nasan ki da zuciya ba'ayi miki baki rama ba".
"Wallahi Zainab sai na tanka naga za'a shiga haƙƙina a cutar dani".
"Ohhh Khadija kin faye kafiya da taurin kai yanzun fa suna son suga duk abin da zakiyi ace kishine".
"Kishi,kishi fa naji kince,wa zanyi kishi da ita taɓarya da zani,saura maza,kowani tom nd jerry ya shiga,nagode ma Allah na kawo budurci gidan miji".
"Tou ke akace miki Maryam bazata kawo ba?.
Dariya Khadi ta kwashe dashi hartana wutsulawa ta faɗi ƙasa daga kan gado tace,"bari in gaya miki wani story",nan ta kwashe labarin abun da yafaru a asbiti,da labarin da taji nurse sunayi ta faɗa ma Zainab.
Zainab sakin baki tayi da ido tana sauraran Khadija.
Khadija bata damu da kallon da Zainab ke mata ba na mamaki taci gaba da faɗin,wallahi na gode ma Allah baya sex dani tun farkon auran mu da yakeyi sosai,daga baya sai yai sati bai yiba,banne man sa don kunya nakeji,daga ƙarshe ma ya dena,ina ganin last sex ɗin da mukayi ne nasamu ciki,amma wallahi in na ƙara buɗe ma Kamal ƙafa yacini sai in yaje anyi gwajin ƙanjamau an tabbatar min da bai dashi".
Innalillahi wa inna ilaihi raji'un Zainab ke mai-maitawa.
"Kidena mamakin ɗan adam Zainab,Maryam duk da suna da rufin asiri,amma tana da shegen son duniya,tana so arinƙa sata cikin manyan ƴaƴan masu kuɗi wa ƴanda ake damawa dasu,baccin baban ta tsohon edita ne na NTA kaduna,ba wani kuɗi bane dashi,face rufin asirin Allah da wadatan zuci,inde zata samu kuɗi ta biya ma kanta buƙata zatabi maza,ƴaƴan masu kuɗi ko masu kuɗin da kansu,su cita su bata kuɗi,ki duba shigarta yanayin shigarta koni da Abba na yafisu rufin asiri banayin shi".
Sauke nauyayyan ajiyar zuciya Zainab ta aje.
"Ban san mai nayi mata ba,mai na tsare mata ba,da har kullum ramina take shiga".
Sai yanzun Zainab ta iya buɗe baki tayi magana cikin sanyin murya tace kiyi haƙuri Khadija,kowa da yanda Allah ke jarabtar shi,ke Allah ya jarabce ki da mafi mugun