Showing 39001 words to 42000 words out of 46304 words
Chapter 14 - MARYAM YAR KUNAMA COMPLETE- BY MRS BASAKKWACE .txt
ɗaya Maryam ta wargaza kayan ta ta zazzage su tana neman control doll ɗinta bata gani ba ta nemeshi sama ko ƙasa yayi ɓatan dabo,hankalin ta yayi dubu ya tashi,miƙewa tayi lokaci ɗayabta zama kamar mahaukaciya tayo falo bata ga Momyn ta ba ta nufi bedroom ɗinta.
Tokarin ƙofar tayi ta buɗe da ƙafa ta shiga.
"Ke lafiya kike shigo min kamar mahaukaciya".
"Momy nafi mahaukaciya Mom million uku akamin doll ɗinan amma ya ɓace babu shi Momy duk sati sai nabashi jinin shanuwa Momy na manta sam banbashi ba,ƙilan shiyasa ya ɓace".
Tou faa waro ido Momy tayi tace," ke kina da hankali kuwa?.
"Momy nafi mahaukaciya".
"Kije ki ƙara dubawa".
"Momy nawatsa komi bayananan bayanan".
Tana magana tana zabure zabure kamar mahaukaciya.
***********
"Hajiya nasan na tafka kuskure yau dana je gidan su Khadija na tarar an ɗaura mata aure ƴan uwanta sun wulaƙanta ni,nasan ni na fara wulaƙanta kaina,Hajiya na tafka kuskure".
"Tabbas da lokacin da na hanaka auranta da kaji da duk haka bai faru ba,ni ban masan zatayi aure ba".
"Hajiya Allah yasa haka shine mafi alkhairi".
**********
Khalil ni bance ka sake matar kaba,......
!_typing🖌️_
*🔘MARYAM🔘*
_(Ƴar kunama_)
*DACE DA JUN YA FITO DA ƊUMIN ƊUMINSA A DARAN JIYA*
*KAR KU YI SANYA WAJEN KARANTA WANNAN GAWURTACCEN LITTAFIN WANDA YAZO MUKU DA ZALLAR SOYAYYA😘 UWA UBA GA FAƊAKARWA DA NOSHADAÑTAR GA MAI KARATU, YANA NAN YA FITO MASOYANA A DUK IN DA KUKE KU GARZAYO GA AUNTY NA HADIZA D/AUTA TAZO MUKU DA SABON LITTAFINA MAI SUNA ~DACE DA JUNA~ FREE BOOK NE KUƊINKU SU ZAUNA LAFIYA TAKU HAR KULLUM,DAGA IN GAN TACCE ALƘALAMIN TA🖌️ DA BAYA RUBUTA SHIRME,MASOYANA KU NUNA MA AUNTY NA SOYAYYA TA HANYAR ZUBA MATA SHARHIN DA KONI BAKUYI MIN IRIN SHIBA*
*HADIZA D AUTA (Princess Dija) FASIHIYAR MARUBUCIYA MAI CIKE DA HAZAƘA❤️🥰*
~MRS BASAKKWACE TAKU CE D/AUTA TAKUCE,BURINA BAI WUCE IN FARANTA MUKU MASOYANA BA KODA KO ACIKIN ƘASA KUKE INA ƘAUNAR KU ACIKIN BACCI KO A FARKE🥰❤️~
MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)*
*(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)*
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo
WHATSAPP NUMBER:- *08167151176*
WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE*
GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*
IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE*
TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE*
SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE*
*PAGE 39*
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
********
"Khalil ni bance ka sake matar kaba,amma kasani bazan taɓa sonta har abada ba,Allah bazai taɓa kawo randa zan sota ba,duk wani ɗa da zata haifa maka ba jika na bane,kunemi kakan shi,sannan ka rubuta ka aje in na isa dakai sai ka aure budurwa mai nono a tsaitsaye,ba bawara ba".
A magan ganun Mom na farko ne kaɗai ya mai daɗi amma sauran duk dummm yamai a ƙwa-ƙwalwa yai kamar sabon taɓaɓɓe uana binta da ido cikin rashin fahimtan maganganun mahaifiyar nashi masu ɗaci,bata damu da rashin maganan sa ba da kuma yanayin kallon da yake mata kamar baƙuwar halitta taci gaba da faɗin,"da badin zunubi da fushin ubangiji ba da ya halasta aure kuma kuma baisan saki,in akai saki al-arshin ubangiji na girgiza,sabida tsananin mumin kalman da nauyinta Allah na fushi da wanda yakeyi ni Karima bazan so Allah yayi fushi dani ba,ni Karima bazan so al-arshin ubangi ya girgiza sabida dalilin banzon auran ka da wancan bazawaran ba,amma kasani komi daran daɗewa inde ina raye sai ka ƙara aure".
Sauke sanyayyan ajiyar zuciya yayi yai ƙasa dakai yace.
*************
"Cabɗi amma Kamal baida kunya", faɗar Ummah da take girgiza Abul yanajin riga,ga Khadija naso taci abinci yaƙi barinta tabzauna.
"Umma wallahi ƙarfin halin shi yayi yawa da har zaizo ya wani ce abashi ɗanshi,da badin tarom jama'a ba wallahi sai na tattaka mai wiya".
"Wai kai Khalil yaushe zaka ɗau rigan haƙuri kasa ma wiyanka,yakamata ka koya halin dattako halin haƙuri".
Faɗan Abba da ke zaune gefen Khadija don yamzun jiki alhamdulillah,ba inda bai motsi ajikin sa sanadiyar wani ƙwararran likita Dr Sayyid ɗan garin bayalsa da aka dawo dashi 44 akai musu hanyar ganin shi yace ai gashin ƙashi za'ayi masa ,kuɗi mai yawa suka nema awajan su basu damu ba suka biya ake kai shi kullum ana gasa masa ƙashi,yanzun tafiya ne yake koya da ya daɗe baiyi ba yazamo masa baƙo.
"Abba haƙuri ya raina mu ya raina mana hankali ya saketa saki uku ya dawo yace ya maidata a garin gaɓa gaɓa ya taɓa ganin anyi haka?,auran zina ma yakeso sunyi".
"Khalil in shi bai san mai yakeyi ba ai mu munsan mai mukeyi,amma ka rage saurin hannu".
Umma ta faɗa tana kwantar da Abul a gadon shi na jarirai.
"Ni wallahi Umma in zan mutu sai dai in mutu na yarda in zauna da kowa komin talaucin sa,amma ba Kamal ba,ni kaɗai nasan baƙin ciki da wahalar dana ƙunsa a zaman gidan sa ,Allah yasa ƙarshen wahalar ne Ummah".
Khadija ta faɗa tana ƙara tanƙwashe ƙafa ta ɗebi abinci takai baki.
"Yaya ai ni zan bada labarin cin mutuncin dana iske anayi miki,kema wata sauna baki bige mata baki,nagode ma Allah halina halin Bross Khalil bamu bari sai ta kwana ballan tana tai tsami shiyasa na miƙe tsaye na ƙwato miki ƴancin ki,da yanzun kina cikin wahalan da sai mun kasa ganeki".
Faɗan Fatima da take kwance kan kujera tana danna waya.
"Kede auta kide bari kawai Allah ya sawaƙa ,Allah karka jarabce mu da abinda baida ƙarshe,amma naga aya,ƙaddara bata fuskan yanda bata zuwa ".
"Daku kuma rabo in ya rantse".
Faɗar Ummah da ta dawo ɗauke da tray ɗin abincin Abba.
Kamal gyara zaman shi yayi ya aje waya agefe da tun ɗazun sauraran su kawai yakeyi gyaran murya yayi yana kallon ɗaya bayan ɗaya.
"Wannan duk ba mafita bane,ko musu ko kar muso Kamal shine mahaifinsa bamu isa mu raba shi da shiba,akwai zuri'a babu amfanin rabuwar rashin mutunci,in yazo yanaso yaga ɗan shi aɗauka akai masa shikenan sannu bata yanka wiya".
"Tabbas kuwa faɗan Abba,ba a canja ma tuwo suna".
"Sosai kuwa hamdala zamuyi tunda ba'aje ko ina ba yadawo yayi nadaman maganaganun sa masu ɗaci" .
Sharwa da nusar dasu illa hana shi ɗan shi da suke niyar yi ya rinƙa basu hatsai da yaga sunyi gamsu kafin suka canja hira zuwa wata.
************
Momy ina so kisani ƙaddara tasa tun farko Khadija ba matata bane,tana da rabon ɗan wani ajikin ta,wanda inda mun matsa ƙila in iya mutuwa,Momy Allah kaɗai yasa yawan ƴaƴana da zasu fito daga jikin Khadija,ƙaddara ta raba mu,ƙaddara ta fito da ita ƙaddara ta ƙara haɗamu,Allah nai kaɗai yasan dalilin ƙara ƙadarta haɗuwar mu da Khadija Mom don Allah kice kawai Allah yayi albarka ki mana addu'a Mom sam ban taɓa ji a zuciyata zan zauna da mata fiye da ɗaya,amma in haka ne mafi soyuwa a zuciyar ki yazamomin wajibi tilas inbi umurnin ki don ganin dakyau a rayuwata".
Cikin sanyayyan murya yake magana cike da ladabi da biyayya.
Sauke nauyayyan ajiyar zuciya Mom tayi tasan in banda son zuciya irin nata da take ƙoƙarin sama kanta tsanan Khadija,ba gairi ba dalili,dalilinta ɗaya da taƙi auran ɗanta tun farko sai bayan ta dawo bazawara zata ce zata aure ɗanta,sannan za'a bashi.
Bai damu da shirun da tayi ba,don baiyi tinanin jin amsa daga gareta ba,yaci gaba da faɗin Mom inda Khadija ta bijire ma iyayenta taƙi auran zaɓin su daga farko ta aure ni,mai tayi kenann,wani kalan baƙinciki iyayen su zasuji a zuciyar su,ki auna kamar kece Amra tayi miki haka ta bijire ma umurnin ki ya zakiji a matsayinki na uwa,Mom ke uwa ce mai ƴaƴa mata,yanzun mijin Yaya Aisha yace zai ƙara mata kishiya ya zakiji,ko kuma azo neman Amrah a fasa ya zakiji,ko uwar mijin Amrah ta rinƙa nuna ma ƴarki ƙiyaya ya zakiji a zuciyar ki Mom dan Allah ki ɗau Khadija kamar ƴarki da kika haifa,kisota kamar yanda kikeson Amrah ,Yaya Aisha dani,in kai haka shine zai tabbatar min da soyayyar da ako da yaushe kike gwadamin,kiyi haƙuri Mom in maganganuna sun ɓata miki rai".
Cikin raunanniyar murya Khalil ke maganan,kamar zai fashe ma Mom da kuka.
Shiru tayi tana nazarin magan ganun sa bata gama nazarin wasu ba gashi ya ƙara zubo mata wasu,lallai Khalil aduk magan ganun shi yayi aiki da hankali da ilimi,gaskiya ne ashe kana haifan ɗa yafika tunani da hangen nesa,kamar yanda malami ke koyar da ɗalibi yazo yafishi iyawa.
Gyara zaman tayi ta harɗe ƙafa ɗaya kan ɗaya tana girgiza ƙafa tana taɓa baki,kafin tace,"tashi ka tafi zanyi shawara da tunani".
Murmushi yayi yace Mom baki buƙatar tunani ko shawara don duk wanda zaki nema shawara ba lallai yabaki kamat wacce zan baki ba,Mom kisa albaraka kawai".
"Yanda taga lokaci ɗaya ya dawo cikin farin cikin sa yasata tayi murmushi tace tashi naji Allah ya albarkaci auran ku".
Cikin kuwa da wani matsanan cin farin ciki kamar anbashi kyautar motor ya buga tsalle ya faɗa jikinta suka zube kan tattausan gadon ta yana dariya,itama dariyan take da kyar ta iya cewa" tou ɗaga ni kaje ka sallame baƙin ka dare yayi".
Peak kiss ya sake mata a kumatu da lips da ƙirji cike daso da ƙaunar ɗa da uwa ya miƙe ya fice yana dariya.
Murmushi tayi tana jin wani nishaɗi,bata san mai yasa da taga Khalil cikin nishaɗi ba,itama ta shiga kenan,sanda yashiga halin damuwa da aka hanashi auran Khadija tare suka shiga baci ba sha,da ƙyarvda addu'o'i suka dawo dai-dai.
Zuwa yayi ya sallame abokanan sa kafin ya koma part ɗin shi yayi wanka ya shafa'i da wutiri don yaga shaɗaya ta wuce ya hau gado ya danna number wayar masoyiyar shi matar shi kuma,da tun safe da sukai waya basu ƙara yi ba.
**************
Kamal yanda yaga rana haka yaga dare bacci ɓarawo bai sace shiba,yayin ya rinƙa tinanin soyayyar su da Khadija da zaman auran su da yanda ua dawo yana ƙuntata mata tana rama wani wani ta kauda kai,yaci kuka sosai kamar ƙaramin yaro koda asubah tayi idon shi sun kumbura kamar zasu faɗo ƙasa ,ahaka ya ɗaura alwala ya fita masallacin dake kallon gidan su na gidan maƙwaftan su.
***********
Khalil da Khadija acikin wannan daran ko sun raya shi cikin so da ƙauna da ƙyar Khalil yabarta badon yaso ba sukai sallama sukai bacci cike da nishaɗi da ƙara so da ƙaunan juna.
**********
Maryam duk duban duniya sunyi ba gunkinan ya ɓace ɓat,ance in raƙumin ka ya ɓace ko cikin tandu ne kaduba,haka ko sukai suka haƙura da niyar washa gari zasu tafi niger wajan wani banufe aikin sa kamar yanka wuƙa ne,aiko cikin bacci aka rinƙa firgitata da tsoratata,ana faɗin za'a sha jinin ta halittu kala-kala,rikitattan ƙara ta saki da yaja hankalin tashin duk wani mai rai dake cikin faɗin gidan su sukayo part ɗin su suna bugawa,Mom ɗinta hankali tashe ta nufi ɗakin ƴar tata da idon ta ke runtse inta buɗe halittu marasa kyau keyowa kanta suna ya ƙushin jikinta suna faɗin kibamu jini,buga part ɗin da akeyi yasa Mom juyawa taje ta buɗe su Hajiya Rabi ne da ƴarta ɗaya da tayi saura batai aure ba Sumayya,suka shigo suna lafiya?.
Mom tace Maryam ce ban san mai ya faruba,ihu kawai take tana Mom zasu kashe ni Mom kitemaka min suna tsotse min jini Mom nashiga uku".
Da gudu sukayi ɗakin jiyo kalan manta da ƙarfi don ba zasu cire tsamani har maƙwafta ta tada ba halin da suka iske ta sun firgita tayi tsirara ido a kulle ga jini na zuba a jikinta kota ina kamar an tsagata da reza tana ihu.
Sallati Mama Rabi ta fara tana tafa hannuwa,kallon Sumayya tayi tace maza ɗauko min wayata in kunna mata karatu,ƙila aljanu ne dare yayi bare akira malam,juyawa sumayya tayi da gudu a zuciyarta tana faɗin Allah ya ƙara ƙila asiri uwarta taje yima wata ya dawo mata.".
Mom ko ja baya tayi duk ta tsorata,Mama Rabi ta matsa kusa da ita ta roƙ hannayan ta wani mugun ihu Maryam ta sake da gidan sai da ya ƙara ɗauka ta zube a ƙasa sumamma.
Bata ji tsoro ba ta riƙo goshinta dake fidda wani jini baƙiƙirinta kama tofa mata addu'o'i babban tashin hankalin maigidan bai nan yayi tafiya.
Kusan awa biyu kafin a hankali Maryam ta soma sauke ajiyar zuciya tana miƙa take yanke jinin yafara tsotsewa ya ƙame ko ina ya haɗe kamar ba ita ba.
Sumayya da take tsaye riƙe da wayar Mama bako tausayin Maryam ko ɗigo a zuciyarta fatan ta ta mutu awan nan halin miƙa ma Mama,amsa tayi ta sa mata fatiha a kunne ƙira'an shureim.
Mom tsoro ya kamata da nadama,ji ko ita bata je wajan ƴarta ba,bata taɓa tunanin akwai temakon da Rabi zatayi mata ba don basa ko sannu in Rabi zata kwana mata sannu ko kallo bata isheta ba.
Wani kunya taji ya kamata kamarbta nitse a ƙasa.
Sumayya aika mata da harara takeyi ƙasa-ƙasa.
"Wajan asubah Mama tace Hajiya jeki kwanta,kema Sumayya zan kwana da ita".
Sumayya da kamar jira takeyi tasa kai ta fice tana galla ma Mom harara,da caraf a idonta tsaki tayi ƙasa ƙasa ta fice.
Dariyan yaƙe Mom tayi tace aa maman yara kije ki kwanta in kula da ita".
"Aa ba za ayi haka ba".
Mom cike da nauyi da kunya yauce ranan farko da taɓa nadaman abinda take ma Mama rabi ta fita tatafi ɗakin ta amma bacci ya gagareta mai ke shirin faruwa da ƴarta.
Tun daga wannan ranan da safe Maryam zata warware da dare ko bata isa tasa haƙarƙarinta a katifa ba,kuma kullum Mama rabi ke kwana da ita,tana ƙoƙari amso mata temako a wajan malamin islamiyan su na addu'o'i do da temakon addu'o'in ta ke zaune har yanzun a ɗakin auran ta.
Mom ko ta bazama gidan bokaye tana ta cusa masu kuɗi,suka haɗa ta faɗa da Nawal babban aminiyarta a bariki cewa ita tai ma ƴarta asiri don taga ta fara arziki,take Mom taje taci mutuncin Mawal sukai uwaka ubanka aka rabu baram baram da gorace gorace,amma har yanzun babu sauƙi sai awajan ubangiji,ana haka Alhaji Bala ya dawo yace ko ba ruwan shi duk wanda ya ɗebo da zafi bakin sa,ko sisin shi bazai bada ba wajan memo ma Maryam magani,ai ba shi yace ta biye uwarta ba ta kashe auran sa ya cire hannun sa akan ta,da ƙayr Mama rabi ta lalalsheshi ta nuna masa hannun ka bai ruɓewa ka yanke ka yar,yace mata wallahi biyar bai badawa haka ta haƙura ta barshi tasan shi da kafiya in ya kafe ba mai laƙwasa shi.
**********
Khadija da Khalil ko soyayya da shaƙuwa ta dawo sabuwa fil a leda basa minti talatin basu nema ɗayan su a waya ba,gefe guda kuwa Abul na samun kulawa yayi ɓul-ɓul dashi ,ga gyaran da take sha,an ɗaga tarewata da Khalil za'a haɗa da bikin Khalid da Zainab ,Khalil da Saudat ƙanwar Zainab Fatima kuma da abokin Khalil Fu'ad nan da wata biyu,su Khalil sun hana ƴan gidan su Zainab ko siyan tsintsiya su zasuyi komi a faɗar su ko sun zama ɗaya.
**********
Hajiya tazo tabasu haƙuri kuma tayi ma Khadija fatan zaman lafiya a gidan miji,Umma ta gwada mata ba komi da Abba,kuma har yanzun Kamal ɗan su ne,taji daɗi sosai jin kalaman su ga ɗanta
**********
Kamal in yanaso yaga Abul saide ya taso Hajiyar shi gaba suzo tare ya tsaya a waje duk yanda Abba ya nuna mai komi ya wuce har yanzun yana matsayin shi na ɗan shi ya rinƙa shigowa amma ina kinya ta hana shi shiga,saide a ɗauko yaro akawo mai shi,duk zuwan shi ko daga nesa bai taɓa ganin Khadija ba,da ƙyar Hajiya ke raba shi da yaron su tafi bai ƙi su wuni ba,duk ranan da sukazo gidan su Khadija Kamal da kuka yake tafiya ƙarshen ta ma ya kwana da zazzaɓi Hajiya tai ta faɗa,da ƙyar ya cire abin a ransa sam baison ɓacin ranta,daga ƙarshe daya ga ba sarki sai Allah ya gaji da zaman gida da yawo wajan abokai ya tattara kuɗin shi ya koma kasuwam cin shinkafa,amma har yanzun yana da muradin yaga Khadija ko so ɗaya kafin nufashin shi ya ɗauke a duniya.
Maryam fa abu yaci tura ta rame tayi baƙi komin su yayi ƙasa,duk bokaye sun cinye amma ba sauƙi,in ka matsa sai kace zaka dawo baka isketa da raiba.
Ɓangare guda kuwa shirye shiryen bikin akeye ɓangare uku........!
TOHHHH FAAAA
_typing🖌️_
*🔘MARYAM🔘*
_(Ƴar kunama_)
*I WILL NEVER HATE ANY ONE, BUT I WILL DISTANCE MY SELF FROM PEOPLE WHO DO NOT VALUE ME🤷♀️🤸♀️*
NA MARUBUCIYAR:-👇
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
AWANI GARI
JIDDATOU
ND NOW
MARYAM ~ƳARKUNAMA~
MALLAKIN:- *Khadeejour Muhammadou(THE CAT LOVER😸😹)*
*(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)*
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo
WHATSAPP NUMBER:- *08167151176*
WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE*
GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*
IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE*
TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE*
SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE*
*PAGE 40*
*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*
Ɓangare guda kuwa shirye shiryen bikin akeye ɓangare uku.
Khadija da su Zainaba tare sukeyin komi nasu da ya shafe amare saloon lalle gyaran jiki,wacce tayi musu makeup ɗin events ɗin da ma mutum ɗaya ce.
*********
"Khalil kaje airport ka ɗauko Aunty Murja driver na aike shi karta ƙaraso tai ta jira".
"Ok Momy bari in tafi yanzun wallahi jikina duk yayi sanyi Mom wani kala nakeji kamar wani abu zai faru dani".
Acikin raunan niyar murya yai maganan yana kwantar da Munif akan kujera yaron Aunty Aisha.
"Subhanallah gajiyan biki ne kawai kadawo kasha magani ka ɗan kwanta".
"Tou Momy bari inje indawo inshaAllahu".
"Allah ya tsare ".
"Ameen Momy".
Miƙewa yayi yafita har yaje bakin motor shi yasa key zai buɗe komai ya tina ya ƙara komawa falo.
"Aa mai kamanta kadawo kanan kallo na".
"Babu komi Mom wallahi jinake kawai inzo in ƙara kallon fuskan ki bana gajiya da ganin ki".
Yana magana yana shafa sumar kansa yana murmushi.
"Kaide akwai wautan ƴan fari, kadawo kaje a aske gashinan haka za'a kaima mata haka za akawo ma ita kai kamar an kwaɗa rama niban san mai kukeyi da tara gashi ba".
Har yanzun akwai murmushi kan fuskan yace,"Momy zanyi missing ɗinki kamar yanda zaki nawa na tafi sai nadawo kimin addu'a".
"Nidai ka isheni da surutu kamar mai barin wasiya".
Murmushi kawai yayi ya ƙarasa inda Munif ke kwance yaro ɗan wata biyar ya lakuce kumatun sa.
Ya miƙe yace,"Mom bye bye i miss you".
"Miss u too tunda yarinta ya motsa".
"Keko Hajiya Karima Tankon kine fa".
Inji ƙawarta Hajiya Sa'ah.
Murmushi yayi ya fita ya kasa tafiya ya laɓe jikin ƙofa ya samu kansa da leƙe yana hango Momyn shi cikin so da ƙauna tsawan minti talatin kafin ya