Showing 33001 words to 36000 words out of 46304 words

Chapter 12 - MARYAM YAR KUNAMA COMPLETE- BY MRS BASAKKWACE .txt

Advertisement

23 Jun 2024

7116

yaro sun sha kyau ga ƴan uwa da abokanan arziki,take yaji kanshi ya sara aje wayar yayi gefe tare da dafe kai ya jingina bayan sa da jikin kujera,innalillahi wa inna ilaihi raji'un kawai yake mai-maitawa a ƙasan zuciyar shi idon shi na masa gizo yana son ya tuna wani abu amma sammm ya kasa a haka ya sulale ya kwanta kan kujeran kan shi na tsanan ta sarawa kamar zai sauka ƙasa.








Alhaji Labaran ya ma Maryam shatara ta arziki,da zumar nan da sati ɗaya shima yana nan tafe,sai da suka gama iskanci a filin jirgi kafin afara kiran facinja ya rakata har bakin jirgi sai da yaga ta shiga ,kafin ya bita da wani shu'umin murmushi ,mai cike da ma'anoni da yawa da shi kaɗai zai iya faɗan mai murmushin nan ke nufi,kafin ya juya ya cire waya ya kira wata number yace," ya gama da wannan ishun ,banji mai na wancan ɓangaran ya faɗa ba,saide naga ya sheƙe da dariya ya cire wayan akunne ya jefa a aljihu ya nufi inda aka tanada don aje motoci ya shiga motor shi ya fice a air port ɗin bai maga tashin su ba.






Itako harda ɗan guntun hawayen ta ta shiga ta zauna a mazaunin ta lumshe idanuwanta tayi ta lula duniyar tunanin rayuwar ta a paris chaina germany,london ,makkah,american.






Yau iyayen Khalil sukazo suka samu Khalid da Khalil da Bappah su Alhaji Wada,da Abban su bayan sun gaisa,suka basu waje suka taɓa kayan motsa baki,kafin suka dawo suka zauna suka ƙara gaiswa ,kafin suka gaya masu abinda suke tafe dashi,Khalil yace yanzun Khadija ba budurwa bane dole sai sun tun-tuɓeta sunji ra'ayinta komai kenan zasu kirasu su sanar dasu, daga bisani sukai musu sallama suka tafi.






Bayan tafiyar su ne suka saka Khadija agaba suka tun-tuɓeta don jin ra'ayinta,cemusu kawai tayi sunfita hangen nesa sanin ya kamata ,sunfita sanin abinda zai dace da ita,tabar musu zaɓi,zaɓin su shine zaɓinta Allah yasa Khalil yazama alkhairi




Abin yayi ma Yayyunta daɗi sosai da har yanzun zaɓin su take nema ba nata ba,addu'an fatan alkhairi sukai mata.




Kafin Khalid ya kira Dadyn Khalil ya shaida masa,lokacin suna tare da Khalil bayan sun gama wayab ya gaya ma Khalil,Khalil murna da tsalle kamar wani ƙaramin yaro da gudu yafita falon ya nufi side ɗin shi ya faɗa bedroom ya nufi bathroom ɗinshi.








Alhaji Safwan girgiza kai kawai yayi yana murmushi ,yana jin wani nishaɗi na ratsa jikin sa,ganin ɗanshi ɗaya tilo na miji ya dawo cikin wal-walar sa, tunda yaji zai samu abinda zuciya ke buƙata.






"Kai yanzun Alhaji bazawaran nan zaka aura ma yaron nan?.






Faɗan Hajiya Karima da take zaune kan ɗaya daga cikin lumtsatsun kujerun da suka ƙayata falon,tana zaune tana jin maganan da Dad ɗin Khalil ke faɗa masa game zuwan sa gidan su Khadija,jikin Khalil duk yayi sanyi ,itako a zuciyar ta addu'a take Allah yasa kar iyayen Khadija su amince,da can ba'a bashi ba sai da ta zama bazawara,sai taji Allah bai amsa addu'an ta an amince.






Wani kallo Dad ya watsa mata,da saida ƴan hanjinta suka kaɗa tai ƙasa dakai tsawan mintina yana kallonta yana ƙare mata kallo kafin yace,"Karima wai yaushe kika raina ni?,da har zanyi magana ki tsalleke shi wato kina biye maganan Aisha ko,tou wallahi in har Khalil bai aure ƴar nan ba,tou bazai aure zaɓin ku ba".






Ɗagowa tayi ta zuba masa idanuwanta da suka kawo hawaye tace,"Alhaji ba rainaka nayi ba, yarinyar nan bazawara ce,budurwa ɗanya sharaf yakamata ya aura yaji daɗin budurci ba bazawara ba,sam da Amira Khalil wallahi ya dace".






Da ido yake kallonta yana watsa mata kallon sama da ƙasa harta dasa aya sam baiyi yunƙurin katseta ba,saunke nauyayyan ajiyar zuciya yayi kafin yace ,"naji batunki amma ban ɗauka ba,basu samun wajan zama ba azuciyata,wannan banzan tunanin kune kawai namata masu ƙwaƙwalwan kifi,manzon Allah SAW da yafi Khalil girma da ɗaukaka da baida zunubi sai Khalil mai cike da nauyin manyan zunubai ne zaki ce yafi ƙarfin auran bazawara Karima tou wallahi zanyi mummunan saɓa miki akan maganan in bazaki sa albarka ba ki shiru".






"Alhaji nima fa ina da haƙƙi akan Khalil don ni na tsuguna na haife shi kuma ban amince ba,ai manzon SAW daban Khalil daban".




"Sannu mai haƙƙi kuma karki aminta wallahi Karima zanyi mummunan saɓa miki,daga yanzun inna ƙara jin maganan nan na rufeta ".






Yana gama maganan,bai jira mai zata ce ba ya miƙe yana saɓa malum-malum ɗinsa ya haura saman steps.




Da harara tabi bayan shi tana jan ƙwafa.








Can na hango Khalil aci wanka da farar shadda,baƙin hula baƙin takalmi,tun kafin ya ƙaraso ƙamshin turare sa ke ma maraba.






"Momy ina Dad?.






Abinda ya fara faɗa kenan da yashigo falon ya tadda Hajiya Karima nata girgije-girgije kamar bishiya.






Harara ta dalla masa kafin tace.




*********
Maryam ta abuja suka sauka,bayan fasinjoji sun fito aciki harda ita ta samu mai texi sukai ciniki zuwa kaduna ta shiga bayan ya loda mata kayanta a bayan motor suka ɗau hanyar kaduna ,sunkai jere sai kawai.










MORE COMMENT
MORE TYPING




_typing🖌️_



*🔘MARYAM🔘*
_(Ƴar kunama_)






NA MARUBUCIYAR:-👇
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
AWANI GARI
JIDDATOU
ND NOW
MARYAM ~ƳARKUNAMA~


MALLAKIN:- *MRS BASAKKWACE*






*(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)*
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo




WHATSAPP NUMBER:- *08167151176*
WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE*
GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*
IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE*
TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE*
SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE*








*PAGE 34*


*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*


Maryam ta abuja suka sauka,bayan fasinjoji sun fito aciki harda ita ta samu mai texi sukai ciniki zuwa kaduna ta shiga bayan ya loda mata kayanta a bayan motor suka ɗau hanyar kaduna ,sunkai jere sai kawai,ƴan fashi suka tare su,bata san sanda ta saki fitsari a wando ba,don bata taɓa gamo da ƴan fashi ba,ko ɓarayi basu taɓa shigowa gidan su sata ba,sai yau gata gasu,ga manyan bindigogi,ɗaga bindigogi sukai suna harbin sama ba ƙaƙƙautawa,addu'an ta Allah yasa ba fulani bane masu sace mutane.




Tsawan mintina biyar suka tsagaita da harbe-harben.




Sa hannu ɗayan su yayi yabuɗe murfin motor yace ,"shegiya ƴar iska fito",aiko jiki na rawa ta fito ta zuƙunna a ƙasa,sa ƙafa yayi ya tokareta ta faɗi ƙasa yace,"dan uwarki haka aka koya miki ladabin manya,kwanciya zakiyi muduba kason mu in babu mu lakaɗa miki duka mutafi",aiko har karkarwa take takwanta flat a ƙasa,jiki na rawa,ɗaya daga cikin ɓarayin ya ƙaraso yasa ƙafa ya taka mata ɗuwawu da wani ƙaton takalmin sa,yanayi yana busan sigari,abinda Maryam ta tsana warin sigari,ƙoƙarin toshe hanci take tana kakarin amai,ɗaya daga cikin su yace,"ke dan ubanki zakizo har wajan sana'an mu kina toshe mana hanci,Allah kaɗai yasan mai ubanki yayi arayuwar shi ko ki cire hannu ko in gyara miki zama ƴar banza mai kama da ruwan aski".






Yau Maryam taga tasko taga ruwan rashin mutunci ga kakanin kakanta, zaginta kawai suke,ɗayan na murje ɗuwawunta da takalmin sa.




Mai duba motor acikin akwatinan da alhaji labaran ya bata harda akwatin kuɗin,da in an canja su su Maryam suda talauci sunyi hannun riga,duk sun watsa mata kaya,wusur kawaibya hura saura ɓarayin suka ƙaraso ya jefa musu akwatin suka caɓe.




Duban ɗaya yayi yace," mutafi haka nawajena".




Juyawa sukai suka shiga motocin su sukai cikin daji.


Saida suka wuce da tsawon minti talatin Driver texi ya iya motsi da tunda akace su fito ya fito ya kwanta a ƙasa ƙwaƙw-ƙwaran motsi yakasa,Maryam tunda taga sun wuce take shashsheƙar kuka da ƙyar ta miƙe ta zauna a cikin motor,driver ya tattara kayanta yamaida motor yashiga yai mata key suka ci gaba da tafiya ,alokacin da driver ke kwashe mata kaya bai kula dawata ƴar gunki ba na ƙasa ya take ta ta fashe,dai-dai lokacin wani abu hayaƙi baƙi ya rinƙa fita daga jikin Kamal yana ficewa ta window ga shegen wari,kan Kamal ƙara tsanan ta ciwo yayi jin wani mugun ɗoyi dake shigowa ɗakin da bai san ko daga ina bane,laluban rigar sa yayi ya toshe hanci amma duk da haka bai daina jiba har tsawon minti shabiyar kafin yadena ji,lokacin ɗaya wani mugun bacci ya rufe mai ido kamar yasha ƙwaya,Maryam ko sai riskan kuka takeyi,driver sam ya kasa bata haƙuri,don shi Allah-Allah yake ya shigo inda mutane,tunda suka taho har aka gama masu fashi kamar haɗin baki inba tsuntsaye dake shawagi a wajan ba,babu wani ɗan adam ko motor ko mashin da ya gifta balle wasu hukuma,sosai yake ba motor wuta,bashi ya tsaya ba sai da ya ganshi a nasarawa,kafin ya sauke ajiyar zuciya yafara tuƙi a hankali,zuwa lokacin Maryam harta gaji da kuka ta haƙura,idanuwa sun kumbura suntum,gashi sai kiran number Alhajinta takeyi baya shiga balle ya ɗauka ta gaya masa mai ke faruwa.




Alhaji Labaran ko yana gama aikin shi da Maryam ya cire sims ɗin da tasan shi dasu ya karya,yace na tabbata zaki gama jin daɗin duniya da kuɗin da na baki kafin kidawo ki raina kanki kiyi kukan da kin sanin shiga bariki a rayuwar ki,a hankali komai zai wakana",yana maganan shi kaɗai yana dariya kamar taɓaɓɓe.






Driver a hankali ya rinƙa bin kwatance da Maryam take mai har jabbi easte ,numbobin gidaje yake dubawa har yazo number 26 yai parking ya juya yace," Hajiya mun iso".




Ahankali ta buɗe bakinta da yaringa yai mata nauyi,zuciyarta cunkushe yake da damuwa ga rashin samun sugar Dad ɗinta ga sace maƙudan kuɗin da ta samu a wajan shi,tace.




**********
Harara ta galla masa kafin tace,"Khalil ina zaka kake ta rawan ƙafa?.




Ƙasa yayi da kansa cike da kunya,cike da ladabi yace,"Momy gidan su Khad.......!




"Yimin shiru sakarai da baisan inda ke masa ciwo ba,akan bazawaran kake rawan gindi Khalil,tou wallahi kafita gidanan da sunan ka tafi wajan wata bazarawa wallahi bada miyau naba".






Cikin tsawa da ɗaga murya takatse shi cike da masifa.




Sulalewa yayi ya zube kan ƙafafuwan shi a ƙasa ya ƙara ƙasa dakai ya marairaice yace,"Momy kima Allah kiyi haƙuri kibar ni inje in ganta,wallahi ina da muradin ganin ta ,in ba haka ba mutuwa zanyi Mom".






Taɓa baki tayi ta ɗaura ƙafa ɗaya kan ɗaya tace," Khalil ka jima baka mutu ba,da can ubanwa ya hanaka mutuwa da taje ta aure wani bata aure ka ba,ɗana ɗaya tilo namiji ya rasa wanda zai ɗauko min suruka sai bazawara,bazawara ce fa Khalil sam bakamin adalci ba,da zuri'an mu,inko kagabka aureta tou bayan raina ne".






"Aiko Karima da ranki sai Khalil ya aure Khadija in har ina da rayuwa,bakin rainani ba kin fara take maganata kina sa ƙafa kina shureta,zamuga nida ke wake zaman wani".






"Dad don girman Allah kayi haƙuri tunda bata so na haƙura nima".




"Wallahi sai ka aureta tunda ka nuna kanaso naje na tambayo aka bamu baku isa ku maidani dattijon banza ba,mai magana biyu,duk abinda na yanke saibya zartu,zamana kuke ƙarƙashin ikona kuke kaida Karima ba zaman ku nake ba".




Yana gama magana yasa hannu ya kwashe key ɗin motor shi dake kan kujera da wayoyin shi ya fice fuuuuuuu,ba tare da ya tsaya ya ji mai zasu ƙara faɗa ba.






Shiru kowannen su yayi da abinda yake saƙawa a ƙasar zuciyar shi.






*************
"Zainabu Abu wani shawara zaki bani,nidai nace komai suka yanke dai-dai ne".




Sauke sanyayyan ajiyar zuciya Zainab tayi tana shafa hannun Abul-bait tba tare da ta ɗago ta dube Khadija dake zaune kan dirowan madubi ba tace," hakan da kikayi dai-dai ne ,abinda babba ya hango yaro ko rimi ya hau bazai hango ba,ko Kamal na gari ne sharrin Maryam ya sauya shi,wanda ina da yaƙinin mugun asiri tai masa babu Allah a zuciyar ta".




Sauke ajiyar zuciya tayi tare da lumshe idanuwa kafin tace," Allah yasa haka yafi zama alkhairi".




Ameen suka amsa a tare.




********
Hon driver texi yayi saida mai gadi ya fito yaga waye kafin ya buɗe get ɗin yanda yaga idon Maryam addu'a yayi Allah yasa ba sako sheɗaniyar nan akayi ba?.




MORE COMMENT
MORE TYPING
_typing🖌️_







Kada damuwa guda ta sanya ka rikice, har ka cire tsammanin Rahamar ALLAH (SW).


ALLAH (SW) yasan zaka iya, ba zai jarabceka da abinda ba zaka iya ba. Kuma Kasani cewa, akwai kyauta mai-tsoka, ga soja da yake bakin-da'ga, fiye da wanda yake gida.






*🔘MARYAM🔘*
_(Ƴar kunama_)






NA MARUBUCIYAR:-👇
SAMHA
ƳAR MACE
KISHIYACE
SURUKAR ZAMANI
GIDAN SADIƘ
MATAR BAHAUSHE
TAHEER
LAILAH
A GIDAN MU SUKE
NOOR JAHAN
JAHAN KHATOON
AWANI GARI
JIDDATOU
ND NOW
MARYAM ~ƳARKUNAMA~


MALLAKIN:- *MRS BASAKKWACE*






*(🌲S•°W•°A Is a for eNliGhtEniNg pEoPle tO lEaRn tHiNgS tHaT rElAtE mArRiAgE🌲)*
https://www.facebook.com/107753568169994/posts/107758194836198/?sfnsn=mo




WHATSAPP NUMBER:- *08167151176*
WHATPADD:- *MRS BASAKKWACE*
GMAIL:- *MUHAMMADKHADIJA748@GMAIL.COM*
IG ACCOUNT:- *KHADDEJATOU BASAKKWACE*
TWITTER:- *@MRSBASAKKWACE*
SNAPCHART:- *KHADEEJATOU BASAKKWACE*








*PAGE 35*


*BISSIMILLAHI RAHMANI RAHEEM*




********
Hon driver texi yayi saida mai gadi ya fito yaga waye kafin ya buɗe get ɗin yanda yaga idon Maryam addu'a yayi Allah yasa ba sako sheɗaniyar nan akayi ba?.






Fita tayi tai cikin gidan su a guje ɓangaran Momynta ta nufa,bayan ta wurga ma mai texi dala ɗari,da murna ya dafe abin sa ,suka fara sauke kaya da Maigadi.






Kaman an wurgota ta faɗo falon,Momynta miƙewa tayi tana salati tana faɗin" lafiya Maryam daga ina haka wurijam-jam kamar ankoro ki,yaushe kuka dawo ƙasan ina Kamal ɗin?.




Lokaci ɗaya ta wurgo mata wa ƴannan tarin tambayoyin,faɗawa tayi kan kujera sai sauke numfashi take kamar tayi gufun fam falaƙi,gudun ceton rai.




"Tambayan ki nake kina min banza".




Ahasale Momynta ke magana.




"Momy ni kaɗai nadawo saukana kenan nayo gida,mun haɗu da ƴan fashi daga hanyar abuja zuwa kaduna da zaman ƙasan nan mundena shi".




Sama-sama take magana kamar numfashin ta zai ɗauke.




Nan Momy tafara faɗa tana zagi da ashar,don ita yanzun kusan dole take zaman gidan su Maryam,don ko tace Alhaji Bala ya saketa bata da inda zata.






Momy tayi mugun ɗaga hankalinta tace," jakar kuɗi ne Kamal ya baki ko yaya ya akai bai tura miki ta bank ba?.






"Ya mutsa fuska tayi ta gyara zama tace Mom sa a haɗa min ruwan wanka a bani abinci kafin kiji koma mai nene wai ke ance miki tare da Kamal nake?.






Gwalalo ido Momy tayi cike da mamaki kafin tace," tou da ubanwa kike inbada Kamal ba?.




"Momy tou ɗaga murya kishiyoyi suji su sama abin goranta miki ,bari in shiga toilet ɗinki inyi wanka,kisa ashigo min da kayana".






Bata jira mai mahaifiyar ta zata faɗa ba,ta miƙe ta wucewar ta ɗakin mahaifiyarta.






Momy ko zama tayi ta rafka tagumi cike da mamaki,tou yawan ƙasashen nan da Maryam tayi da uban wa tayi inba da Kamal ba, tambayar da bata da mai bata amsa sai Maryam shiyasa ta gimtse bakinta tayi shiru tana jiran ta ta fito taji kanun labarai.






Mahaifiya Maryam Hajiya talatu,tun daga zamanin ƙuruciya ta kasan ce ƴar barikibta bugawa a jarida,bata kunyar ta gwada ma ko waye ita ƴar bariki ce,gidan su gidan talakawa ne futuk,ita kuma ta taso da son abin duniya da ƙwaɗayi,sam bata godiya Allah akan abinda mahaifinta Mallam Idiris ke sana'an saida kayan miya abakin kasuwa,mahaifiyarta ko sai tayi dakau suke samu suci,ta sama ma rayuwarta rayuwar ƙarya da kai kai matsayin da Allah bai kai suba, tun tana zuwa tallan kayan miya idonta ya buɗe ya goge da ba maza haɗin kai suyi mata juye ta koma gida,duk faɗan da iyayen ke mata na ta riƙe kimarta na ƴa mace da mutucinta,tayi fatali dasu ta watsar,don tana samu riba mai kyau tana sayan kaya masu tsada tana sawa,inde ta ubanta ne sai sallah-sallah zata sabunta ɗinki,itako bata ƙi ba kullum tasa sababin kaya,tana da shekara goma sha biyar ta ƙara fanɗarewa ,tasamu ƙawaye gogaggu wa ƴanda suka fita sanin harkan bariki suka ƙara dimiyar da ita,itace wannan motor ya aje wannan ya ɗauka,duk unguwan su ko wacce ƴa ba a barinta yawo da Talatu da asalin sunan ta Hauwa'u gudun karta ɓata musu tarbiyan ƴaƴa,shiyasa bata shiga harkan kowa a ɗage take kallon shi,iyayenta sunyi duka haka yayyunta maza amma abanza har suka koma mata nasiha.




Kwatsam sai ga Talatu da cikin,mahaifiyarta nan take ta yanke jiki ta faɗi sa gawarta,sabida tsananin baƙin ciki,abinda ƴar su ɗaya tilo mace ta aikata,haka mahaifinta,tare akai musu zana'ida aka kaisu gidan su na gaskiya.




Bayan bakwai aka raba gado ta saida nata ma yayanta Habu,ta tattara nata tabar gidan ta koma can gidan wata ƙawarta Nawal mai zaman kanta suka dasa da ga inda suka tsaya,bayan Nawal takaita inda ake zubar da ciki sun kai shi rariya.




Tana yawan shiga maƙwafta gidan su,tunda ta ƙyalla ido taga mijin Hajiya Rabi taji duk duniya,Hajiya Rabi tun farkon ganin Talatu taga tayi mata tana sonta da ƙawance ta rinƙa hanta ajiki,ba abinda take ɓoye ma Talatu game da sirrinta dana mijinta,Rabi nada ƴaƴa huɗu Zulaihat ce babba ,sai Bilal,sai husna sai ƙaraminsu Faruƙ.




Talatu ko takamu da tsananin son Alhaji Bala,inda tagayama Nawal take suka kai sunan shi gidan malami suka zuba kuɗi,ko sati ba'ayi ba sai ga Alhaji Bala yazo ya nema Talatu da kanshi kuma yace aure yakeso iyayenta yakeson yaje yagani,ta faɗa masa sun rasu ya tausaya mata yace bata da ƴan uwa tace akwai yayyunta a unguwan kanawa, da Habu da Sa'idu mai wanki da guga,ɗaukan ta yayi suka je har gidan su,lokacin Habu ashe har yayi aure matar da ciki ita bama ta sani ba,don rabonta da gidan tunda ta barshi,ba laifi sun ɗan gyara gidan harda fenti.




Gaisawa sukai a mutunce ya gaya musu mai yake tafe da shi,sunyi farin ciki da murna ya faɗa musu randa zai turo maga batan shi,kafin suka tafi bayan ya musu shatara ta arziki.






Bayan ya ajeta ya shiga gida,yayi wanka yaci abinci kafin ya dube mai ɗakin shi yace," Rabi aure fa zan ƙara".




Murmushi tayi tace," yau kuma da zolayar da kazo kenan Honey?.






"Wallahi ba wasa ba ba zolaya ba,ina yarinyar nan da take shigowa wajanki ta nan gida Talatu,har naje naga iyayenta munyi magana".






Cikin halin ko in kula yayi maganan kan shi tsaye bako ɗar a zuciyart shi.






Cike da mamaki tace," wacce Talatu Honey in wasa kake min don Allah kadena banso,kaje ka auro duk matan duniyar nan amma banda Talatu".






"Wallahi Rabi ba wasa a magana ta ".




"Tohhh fa kasan wazaka aura ka kawo min gida ka haɗa ta da ƴaƴana".






"Tou ai kinsanta tasanki shiyasa na zaɓeta da ta zamo abokiyar zaman ki".






"Kana cikin hayyacin ka kuwa Baban Bilal?.






"Tsafff kuwa".






Murmushi tayi da yafi kuka ciwo tace..........!






MORE COMMENT
MORE TYPING


_typing🖌️_



*🔘MARYAM🔘*
_(Ƴar kunama_)




TALLA!TALLA!!TALLA!!!
*🌺🌺DACE DA JUNA🌺🌺*






*MALLAKIN HADIZA D AUTA*






*SADAUKARWA GA

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login