Showing 1 words to 3000 words out of 45490 words

Chapter 1 - ZAUJUN MAJNUN by AMEENA UMAR FARUQ-1.txt

07 Jul 2024

14057

🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍


🎍 *_ZAUJEE-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_


🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍




Page1⃣to2️⃣


WRITTEN
By


🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍


OR


🎍 *MEENAT*🎍




Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJEE-MAJNUN_*




Am back💃
*_MASOYANA_*




GABATARWA _*Bismilahirrahamaniraheem!, da sunan Allah mai Rahama mai jinkai tsirada amincin Allah su tabbata ga shugaban mu annabi Muhammadu (S.A.W) da iyalansa da sahabban sa ameen, ya Allah Ina rokon yanda kabani ikon fara littafin nan lafiya ina rokon kabani ikon gama shi lafiya ameen*_.




*TSOKACI*
_Wannan littafi na rubuta shi don DON FADAKARWA da NISHA D'ANTARWA
Tareda ILIMANTARWA don haka ban rubutashi don cin zarafin wani ko wata ba so duk wanda yaga hali irin nashi to arashi ne nagode.




SADAUKARWA GA


*_My lovely blood sisters 👩‍❤‍👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi ours last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love💋💋💋._*




*~_TUKUICI_~*


_*Littafin ZAUJEE-MAJNUN gaba dayan sa tukuicine ga daukacin KU MASOYANA, aduk inda kuke afadin duniya Ina fatan alkairin Allah yakai maku, kusani inayin Ku irin babu adadi nan fa ai kundai gane ko lovers? nagode sosai.*😍_


_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~




https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/




*_LITTAFIN NAN NA KUDI NE NAIRA 200_*


_FREE PAGE_




_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_




✍🏽






_*Kaduna state*_
misalin karfe 10:45am na ran monday, da gudu
wasu kyawawan bakak'en motoci ne guda uku suka shiga cikin babban filin jirgi saman nan dake garin kaduna north, ba tareda wani bata lokaci ba sukayi parking alokaci daya cike da kwarewa, wanda hakan yadauki hankali jama'ar dake harabar gurin, gaba daya lanbar motocin irin daya ne kamar yanda naga an rubutu da manya haruffa kamar haka *BLUE 1 BLUE 2 BLUE 3,*



Cikin nutsuwa
aka bud'e kofofin mota biyu alokaci daya wasu manyan mutane suka fito su shidda, kowace mota mutun uku kenan sanye suke da bakak'en suit da bakak'en glass wanda yaboye kwayar idon su, kallo daya zakai masu kagane sudin bodyguards ne wato masu tsaron lafiya mutun jeruwa sukayi tareda kamewa fuskokin nan nasu ba annuri,




Dasauri drive daya motar yafito tareda zagayowa ya bude kofa ahankali wani kyakkyawan farin Dattijo ne yafito Wanda akalla zayakai shekara 60 ko fiye da haka sanye yake da blue suit mai asalin kyau da tsada, hannun shi rikeda yar sandan nan da yawanci gogaggun yan boko da masu kudi ke rikewa,




sannan wani kyakkyawan bakin Dattijo yafito shima shekaran sa bai wuce na wannan ba, saidai fuskar shi dauke take da zanen bare-bare irin wacce tunda ga goshi har saman karan hancinsa sai guda bibbiyu masu tsawo akan kumatun sa, shima sanye yake da suit din saidai nashi ash color ne shima hannun shi rike da sandar
Kallo daya Zaki masu kagane sudin gogaggun yan Boko ne wa yanda kudi dajin dadi yaratsa jikinsu.




Ahankali suka kalli juna tareda sakin murmushi sannan cikin harshen turanci fari yace Barr mukarasa KO?..yace OK Dr gasu" can ma zasu sakko, yace OK sannan suka nufi gurin jirgi da fasinjoji suke fitowa wanda dama tuni yasauka yayinda escorts uku din suka shiga gaba uku suka rufa masu baya.




"Wasu kyawawan samari biyu na hango cikin jerin fasinjojin dake sakkowa, wayanda shekarun su zayakai 30 daya fari ne daya baki, farin wanda kyansa yakeda matukar daukan hankali sanye yakeda blue yadi me asalin kyau da tsada anyi masa irin dinkin nan da samarin yanzu sukeyi wanda ake ratsa farin yadi, dinki ya kama jikinshi kad'an inda yafito da asalin cikar zatinsa na cikakkun maza masu jini ajika,




kafarsa sanye da blue takalmi me kyau da tsada, shima bakin irin yadin ne ajikinsa harda irin dinki saida nashi yadin ash color ne sannan shima fuskarsa dauke take da zanan bare-bari, suma kallo daya zakai masu kagane Boko da kudi tareda jin dad'i yaratsa jikinsu,




sannan ga dukkan alama irin yaran nan yan *GATA* domin kuwa ko wannan su hannusa daure da agogon gwal da zobba masu asalin kyau yayinda suke ri'e da kyawawan wayoyi tsadaddu guda uku-uku, kunnan su mak'ale da yar Bluetooth din nan ta amsa waya gaskiya guy's din sun had'u sai kallon su ake cike da burgewa.




Fuskokin su dauke da annuri wacce takara bayyanar da kwarjinin su sosai cikin takun kasaita me cike da nutsuwa suke takowa yayinda escorts dinsu hudu ke biye dasu suna ri'e masu da akwatinan su da kuma laptops dinsu
suna gama sakkowa,




Sai cak! farin saurayin
ya tsaya tareda yin sauri yadafe kanshi yana yamutsa kyakkawar fuskar shi me cike da lallausan saje, sannan yasaki wayoyin hannu shi suka zube akasa sai yasake dafe kanshi da duka hannunsa biyu tareda lumshe shanyyayun idanun shi sai kuma,yasaki wani irin firgitaccen karan da sautin shi yadauki gaba daya filin jirgi, sannan yafadi kasa tamkar gawa.
*Tofa meke faruwa???*




Cikin wani irin tashin hankali bakin saurayin nan yayi kanshi tareda escorts din shi suka dagoshi yana fadin innalillahi! *BLUE* meyasa meka?, dai-dai lokacin wayan nan Dattijoji suka karaso gurinsu
cikin tashin hankali farin Dattijo yasaki sandar hannu shi tareda tallabo kyakkyawan saurayin nan, cikin tashin hankali yace Oh! my boy what is wrong with you?..




sannan yakalli bakin saurayin nan cikin firgici yace *BULAMA* dama yarona bayada lafiya?.. cike da tsoro yace no Dad wlhy lafiyan "shi qalau muka taho, da sauri bakin dattijon nan yace subhalallahi! to me yasa meshi haka? da sauri yace wlhy papa ban saniba amma nasan tabbas lafiyar sa lau, papa yace yanzu ba wannan ba Dr mu dauke shi zuwa asibiti, cikin sauri escorts din suka dauke shi sukasa amota yayinda Dad shima yashiga yazauna tareda daukan kan *Blue* yadora akafarsa yana girgiza shi taredaa tura hannun sa cikin lallauwasan suman kanshi yana fadin Oh! my darling boy open u eyes kaji?




.yayinda suma su *Bulama* suka shiga dasauri sannan suma escorts suka shishshiga suka tayar da motocin, cikin sauri suka bar harabar filin jirgin
asibintin shika suka nufa dake cikin garin zariya.




************
*Zariya*
yau garin na zaria antashi da hazo me dauke da matsananci iska irin me tsananin sanyi nan wacce take ratsa jikin dan adam sosai,




kasan cewar lokacin hunturu ne gashi kuma dama lokacin sanyi zariya badama, don haka "kowa kagani sanye yake da rigar sanyi don kare kanshi daga matsanancin sanyi da'ake tsulawa, wanda be hana "mutane fitowa harkokin gaban su yanda suka saba kullum ba,




musamman "yan kasuwa sai sauri suke su isa gurin kasuwancin su" yayinda suma masu sana'o'in hannu ba'abarsu abaya ba, suma tuni suka fito gurin harkokin su na yau da kullum kamar dai yanda aka saba,




"sukan ma'aikatan gwamnati dama tuni sun dade da tsufa acikin ofishoshin su suna gudanar da aikinsu" kamar yanda, "suma d'alibai tuni sun dade da tsufa acikin makaranta cikin ajujuwa suna daukar darasi.




Sabanin wasu" matasan yan'mata da samari dana hango daga d'an nisa kad'an da makaranta *Al'azahar academy school* dake gadar saye kusa da yellow, suna sanye ne da riga da wando wanda idan bagizo idona ke mun ba kamar kayan makarantar ne,




banga fuskokin su ba saidai nayi nasaran k'irgasu wato su biyar ne chif!, maza biyu mata uku, wa yanda suke sanye da farin hijab dogo sosai don har yakawo guiwar kafarsu matan suna ri'e da hannun juna,




suma mazan haka suna ri'e da hannun juna ga duk kan alama akwai kauna ta jini tareda shakuwa me tsanani atsakanin su, tafiya suke ahankali tamkar wa yanda kwai yafashe ma aciki.




Cike da mamaki na kallin agogon hannuna inda yanuna mun karfe 10:50am wato 11:00am saura minti goma, da sauri na mai da kallona gurin su araina kuwa fadi nake kamata yayi ace yanzu yaran nan suna cikin aji suna daukar darasi kamar sauran dalibai yan'uwan su,




amma kuma sai akasamu akasin hakan shin ko me ne dalilin?..


banida me bani amsar nan sai wayan nan yara, hakan yasa nadan kara sauri kadan ina cigaba da kallon su tabbas uniform din *al'azahar academy school* ne ajikinsu, yayinda suka cigaban da tafiya abinsu ahankali ga dukkan alama su basajin wannan sanyin da'ake zabgawa,




Nikam gaskiya sun birgeni matuka ganin yanda suke tafiya cikin nutsuwa ba hayaniya balle tada kura irin na sauran wasu dalibai, to dama duk wanda yake *al'azahar academy school* saika same shi da kamun Kai da nustuwa, domin makaranta ce dake cike da tsantsar tarbiyya kasan cewarta had'e da islamiyya,




abin gwanin sha'awa sun sa yar karamar kanwarsu atsakiya suna ta tafiya, sauran kadan nakarasa gurinsu sai naga yar karamar ta tsaya cak! hakan yasa suma duk suka tsaya suna kallon ta, nima tsayawa nayi tareda sakin baki da hanci ina kallon tsantsar kyau da Allah yayi masu gawani irin matsanancin kama dasukai da juna wanda hakan yana nufin sudin y'an *AHALI* daya ne,




Gaskiya "sudin kyawawa ne sosai gasu da tsawo me matukar tsari da sha'awa ba irin me munin nan ba, kallo daya zakai masu kagane cikin biyu sun hada, jini daya KO *FULANI* ko *BUZAYE* koma dukka biyun domin kyansu yakai, saidai su" ba farare bane haka zalika kuma su" ba bakake bane saidai fatar su kalace me matukar kyau da tsada, wato chocolate color irin me haske da shaini din nan.




Haka zalika kana ganin su zaka fahimci basuda wani tserayya ta haihuwa atsakanin su, domin kuwa wannan nabin wannan waccan nabin wannan haka suke "babbar cikin su wacce ke sanye da wando kore riga da hijab farare shekarun ta zayakai 16, sai me bimata namiji ne shi kuma zayakai shekara 14 shima wando Kore yasa riga fara sai me bimasa mace ce ita kuma shekarun ta zayakai 12,




itama riga da hijab farare da wando Kore wato yan sakandiri suke da wannan shirin, sai me bima macen namiji ne shekaran shi zayakai 10 shima wandon sa Kore riga kuma me gida-gida pink colon da ratsin fari wato chak kenan, sai yar karamar su itakam shekaran ta baifi 4 zuwa 5 ba itakam da'alama akwai d'an tazara tsakanin su da wanda takebi, itama wandon Kore ne amma rigarta irin na wanda take bine wato me gida-gida amma hijab dinta fari ne kal wato irin na yan'uwan ta mata sukuma yan primary ne.




Gani nayi 'yar karamar su tasaki hannun dayar takama duka hannuwan babbar tareda daga Kai ta kalle ta sannan ta kwab'e fuska, cike da yarinta tace Aunty *BEENA* yanju shi kenan ankole mu daga school baza mu qala zuwa ta ba kenan?..




shuru tayi tana kallon ta tsawon wani lokacin ba tareda ta bata amsa ba, hakan ne yasa ta turo baki tareda sakin hannuta taje gurin babban namijin ta kama hannun sa duk biyu tace yah *BAS* shikena daga yau mun daina zuwa school?..shima shuru yayi bai bata amsa ba sai kallon ta da yake,




don haka taje gurin dayar macen tace Aunty *BANA* ki fada mu baza mukara zuwa school ba?..itama shuru tayi tana kallon ta, cikin sanyi jiki ta kalli dayan namijin tareda turo baki tace yah *BASH* aikai ma nasan bazakai mun magana ba tunda su Aunty *Beena* basuyi mun ba, ai baruwana daku kuma aina gane saboda bamu biya kudi bane shine aka koremu to ai kafar "Abbun mu tana ciwo baya iya tafiya balle yasamo kudi yabamu, sannan shikuma "kawu Muda yaki ba "Ammun mu kudinta balle tabiya mana shine suka koremu,




ta nagama fadin haka sai ta fashe da kuka me ban tausayi, aikam dasauri su kayi kanta yayinda *Beena* ta tsugunna tayi tsawon dai-dai ita tareda rungume ta ahankali take girgiza mata Kai alamar tayi shuru, shuru tayi sannan tace Aunty *Beena* sbd bamu kai kudi bane akakore muko?..kai ta gyada mata alama "eh, fuska tasake kwab'ewa tace to ai "Abbu bayada lafiya to aunty *Beena* wane zaya bamu kudi mukai school?.. cikin tsananin tausayi Kansu tace....








_Muje zuwa yanzu za'afara_


So
More
Comments more
typing and pls share it
🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍


🎍 *_ZAUJEE-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_


🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍




Page3️⃣to4️⃣


WRITTEN
By


🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍


OR


🎍 *MEENAT*🎍




Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJEE-MAJNUN_*


SADAUKARWA GA


_My lovely blood sisters 👩‍❤‍👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi our last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin ba adadin fa irin so muchhhh lovo_💋💋💋.




*Littafin nan na kudi ne duk me bukata zaya iya turo katin mtn ko airtel na 200 a wannan layin 08161850024 idan kuma tresfa zakuyi duk zaku iya tuntuban layin sai abaku acc no nagode.*




_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~




https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/






_FREE PAGE_




✍🏼




_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_






Sai kuma tayi shuru na kusan tsawon mintin biyu da'alama magana tanayi mata wuya, sannan ta sauke ajiyar zuciya ahankali cikin zazzakar muryar ta me dad'i tace "ALLAH shine zaya bamu don haka karki damu domin yasan halin da muje ciki kinji ko? kai ta gyada alamar to,




tace yauwa my *Banu* to d'anyi mun dariya mana nagani, aikam dasauri tawashe d'an karamin bakinta me dauke da fararan hakora, tace yauwa kokefa to mutafi gida kinga "Abbu da "Ammu suna can sukad'ai ko?..tace to tareda juyawa ta kalli *Bass* cike da shagwab'a ta mika masa hannu tareda fadin yah *Bass* dauke ni kaji?,




cikin wasa yace nakiya ke da kikace baruwanki damu, so muma baruwan mudake ko my *Bash* yace eh d'iyar kawu "muda kawai yakarasa fadi tareda yimata gwalo, kafa tafara bugawa cikin shagwaba tace Aunty *Beena* kingan shi ko?..




murmushi tayi wanda kusan tare sukayi da yan'uwan sannan, tace kai yah *Bass* itakam d'iyar "Abbu da "Ammu ce bata kawu muda ba ko?.. tace eh kawu Muda yace wai haka? kai ta gyad'a almar eh yace to shikenan yar *Banu* *Banu* ta yakareshe fadi tareda daukanta yadora akafad'arta,




sannan suka cigaba da tafiya abinsu gwanin sha'awa sunayi suna fira me cike da kaunar juna ahaka har suka isa gidan su dake anguwan fadaman sarki alokaci tuni *Banuja* tayi barci, kasan cewar tsakani anguwar su da school din akwai nisa.




Wani gida suka shiga me bakin get wanda kallo daya zakaiwa harabar gidan ka fahimci masu shi suna cikin wani hali, domin kuwa filawoyin dake shuke a harabar gidan duk sun bushe saboda rashin ishenshen abincin su da basa samu,




Duk kansu bakinsu dauke da sallama suka shiga wani babban falo wanda yake dauke da wasu tsofaffun kushin din da duk yadinsu ya yayyage,




Daku na hudu ke acikin falon don haka direct suka nufi daya daga ciki still bakin su dauke da sallama wanda basu shigaba har saida aka amsa masu tareda basu izinin shiga tukun, sannan suka shiga.




Inda suka iske wata kyakkawan mace fara amma ba irin faudin ba tareda wani kyakkawan mutun wankan tarwad'a wanda kallo daya zakai masa kafahimci yanajin jiki matuka kasan cewar yanda yake fitar da numfashi, kwance yake akan wata lotsatsiyar katifa yayinda rabin jikinshi yake rufe da bargo, saidai banda kafafun sa domin kuwa suna saman ciyarta matar tana manmatsa mashi ahankali,




Lokaci daya su ka dago kai tareda tsura masu ido, kallo daya zakai masu ka gane su din ne iyayen su saboda tsananin kama, cike da ladabi suka zube agaban su tareda cewa Abbu sunnu da jiki Ammu sunnu da gida,




da kai Abbu ya amsa sabani Ammu da tace yauwa sannun ku, amma lafiya naga kun dawo ba lokacin tashi ba? cikin sanyi murya *Bana* tace Ammu ankoro mune saboda bamu biya kudin makaranta ba, kuma yan school din mu suna tayi mana dariya wai mu duk time sai ankore mu saboda Abbumu baya biya mana kudin school,




kuma yau har saida *Banu* tayi kuka, ko *Bash* yace eh saida Aunty *Beena* ta lallashe ta tayi shuru sannan yah *Bass* yagoya ta har tayi bacci.




Da sauri Ammu ta kalli Abbu wanda shi din ma ita yake kallo cikin b'acin rai tace kagani ko kagani ko? haka kakeso mu cigaba da rayuwa cikin kunci? yanzu haka abincin da zamuci yana neman yafi karfin mu ga ciwon ka kullun karuwa yake,




Sannan shima karatun so ake ya tsaya masu, gashi kullun nayi magana sai kace nayi hakuri na kyale shi" to kasani wannan karon bazan kyaleshi ba dole naje yaya Muda yabani hakkina kome zaya faru yau saidai yafaru Amma bazan yarda ba, eheee! sannan ta sauke kafafun shi daga saman cinyarta ahankali tamike.






Ahankali yabi bayanta da kallo har ta fice daga dakin sannan yamaida hankali kan yaranshi, wayan da tsabar ladabi tunda "Ammun su tafara magana kansu ke duke har tafita.






Cikin sanyi murya me dauke da murmushi Abbu yace to yan albarka kuje kucire uniform din bakomai Allah zaya rufamana aciri inshallah kunji ko?, ahankali suka ce to tareda mikewa har da *Bass* dake goye da *Banu* suka fita amma banda *Beena*, shuru yaratsa dakin na wani dan lokaci sannan Abbu yace ya akayi ne ta Abbu maman Ammu?...




ahankali tadago kai idanun ta cike da kwalla cikin sanyi murya tace Abbu maganar "Ammu yana nufin zataje abuja gurin kawu Muda kenan ko?... kai ya gyad'a mata alamar "eh ido ta lumshe aikam take hawayen suka zibo cikin muryar kuka tace Abbu meyasa zakabar ta taje?




yace saboda tana bukatar zuwa kin kuma sannan bazan hanata ba tunda alkawari na daukarma "lnna ta, duk abinda Ammun ku tabukata nayi mata muddun be sabawa shari'aba to nayi mata, tace amma Abbu kasan kotaje "kawu Muda bazaya bata hakkin taba tunda tunba yau take zuwa ba amma be bata ba,




yace haka ne tace to kagani hakan yana nufin baya daninyar bata don inda yanada niyya da yabata, tunda yau shekara hudu kenan tana tafama wahala akan abu daya, yace haka ne amma kinsa halin Ammu ku dakafiya tace to nidai tunda be da niyyar bata hakkin ta don Allah Abbu kace ta kyale "shi aigida biyu ne wanda idan ba duniya akwai lahira,




cikin sanyin jiki yace haka ne zan mata magana ki kwantar da hankalin ki kinfan banson kinasa damuwa

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login