Showing 33001 words to 36000 words out of 45490 words
rai yace to dana fadamki mekikace....cewa nayi anhaukata shi amaidashi tamkar karamin yaro tayanda bazaya iya moruwa ba, to anhaukata shi amaidashi yanda kikeso koba ayiba?...
cikin rawar muryar tace duk yanda nakeso anyi bako har raba mahaifina da shegiyar "matarsa kuma har yanzu bai dawo da itaba kuma baya tunanin kowace mace naji dadin aikin sosai boka, saidai nidai banasan ganinsa adoron kasa, to aljanuna bazasu iyakashe ba yakikeso ayi?...cike da bakin cikin jin haka tace to boka abarshi yadauwama cikin haukar har karshan rayuwarsa, karki damu wasu.
"Surutai yayi sai Kuma yai shuru can yace angama d'an gudurgu sannan yasa hannunsa cikin wata bakar tukunya datake daure da jan zare, yadauko wani kullin magani cikin bakin kyalle da'aka nannad'e da jan zare, yamika mata tare da cewa ga wannan inji aljani gudurgu yace abaki kiringa zuba masa aciki abincin yanaci har tsawon kwana ashirin da d'aya idan har akayi hakan batare da antsallake ranaba to bazaya taba warkewa ba har abada,
"Jikinta yana rawa tamika hannun takarba tana godiya sannan yasake cewa aljani gudurgu yace" ki kulada waccen ukunyar karki bari kowa yagani don idan wani yagani to, dasauri tace aibabu Wanda zaya gani to kikula sosai to boka dungu zan kula, yauwa sannan yace zaki bada jini da dubu hamcin zakuma kiba boka dungu kanki yahuta har natsawon kwana biyar,
wanda hakan shine mahad'in biyar bukatarki da sauri tace badamuwa boka dungu aihakan ba bakona bane, indai bukatata zata biya ko kwana nawane zan amince,
"Wata mahaukaciyar dariya yayi tare da mikewa ita kuma ta kwanta cikin wannan kazamin gurin, yayinda boka yake kokarin rabata wa'iyazubillah!, nikam ina ganin haka nayi waje.
*_Zariya_*
********
Misalin karfe 10:00am baban abdul ya'isa anguwar su *Blue* baisha wahalar gane gidan ba, bayan yasallami me mashin sannan yanufi get din ya kwankwasa megadi yaleka tare danufin ya tambaye sa wayake nema,, sai yaga baban abdul din kasan cewar jiya saida dad yakira dukka masu kula da gidan harda megadin da escorts dinsa yanuna masu su *Beena,*
murmushi megadin yayi tareda cewa au mlm mansur ne?... eh ni baba megani buɗe masa yayi yashigo sannan suka gaisa har yake tambayar ina *"Beenazar* mutumiyar megida *"Bilal*, tana gida wlh ayya atun safe mutuminta yake rigimar nemanta har nan bakin get yake wai sai nabude masa kofa yaje gurinta,
"dariya yayi tareda cewa allah sarki *Bilal* Allah yabashi lafiya cike da jimami yace ameen ameen kaidai, yauwa alh yana ciki Kuma?..eh yana nan to sannan yanufi cikin.
"Da sallama yashiga falon dad da *Bulama* suka amsa fuska dauke da fara'a dad yace mlm mansur ka'iso?..yace eh tare da zama akasan kafe, da sauri dad yace ah! mansur kahau kushin Mana, murmushi yayi yace a ah alh nanma ya'isa gaisawa sukayi har da *Bulama* sannan yatashi yashiga ciki yabar dad da baban abdul din,
gyara zama dad yayi sannan yace dafarko inasake Mika godiya ta gareka wanda tasanadin kane naga yarona saboda haka ga wannan check ne na dubu dari biyu, cike da tsananin farin ciki baban abdul yakarbi check din tare da cewa nagode sosai allah yakara budi yakuma ba *Bilal* lafiya,
"Cike da jin daɗi dad yace ameen sai abu na biyu "alh Usman mahaifinsu *Beenazar* yafada mun hatsari yayi amma bai fadamun abinda yasamu kafarba shin menene matsalar kafar nan tashi ance ne bazata gyaruba ko me?....dasauri yace a ah wlh zata gyaru matsalar kudi ne da babu shiyasa,
Dad yace Allah sarki to badamuwa yanzu jibi monday zansa azo adaukeshi" aikai shi asibitin mu sai muduba shi mugani, cike da farinciki yace to alh Allah yakaimu mun gode sosai yace bakomai sun dantaba fira kad'an akan rigimar da *Blue* yake saiyaje gurin *Beena*,
"sannan yace alh ni zantafi a ah tun yanzu?...eh wlh inaso naje kasuwa ne, to shikenan tare suka mike dai-dai lokacin da *Bulama* yafito *Blue* yana biye dashi abaya, sanye yake cikin riga t-shirt baka da wando fari yayi kyau sosai sai kamshi turare yake, yana ganin baban abdul yaturo Baki tare fadin ina my *Beena* friend?...dasauri dad yace tana nan zuwa ko mansur?..eh zatazo, dariya yayi sannan suka raka baban abdul yatafi.
*_Abuja_*
*******
Saida boka yagama fasikanci da aunty *Bebe* sannan tafito tasa kaya bayan ta cikashi da kudi sannan tanufi gida, diret bayi tashiga tayi wanka sannan tashirya cikin riga da zani na atamfa super holard,
"bayan tagama shiri tsaf tafito falo inda ta'iske yaranta matan zaune, Daya daga cikinsu wacce da alama itane babba kuma kyakkawa da'ita tana kama da *Blue* kallonta tayi cikin wani irin yanayi tace mom ina Kuma zaki ?...naga yanzu fa ki kadawo,
kallon diyar tayi cikin sanyi muryar kamar wata mutumiyar kirki tace ayya Jiddona Zariya zani kin manta ance anga *"Bil* boy, shine nakesan naje naganshi murmushi tayi tareda cewa Allah sarki my uncle *"Blue* mom gaskiya idan akai hutu zamuje muganshi ko?..tace eh yauwa mom to sai kindawo kigaida "shi,
Sannan kicewa Grandpa idan bai dawo da yar tsohuwar matarsa ba idan nazo dakaina zanje nadawo mashida "ita, wani irin harara tawatsa mata tareda cewa koyan zuma aida kinje kindawo mashida ita", dariya jiddo tayi tace Kai mom wai meyasa bakisan grandma tadawo?...dalla rufemun baki bansani ba idan "dad dinku yazo kuce natafi,
"Da sauri tace mom kaidai dad besan zakije Zariya ba?..cikin tsawa tace dalla gafara yasani nadai Kira wayarsa ne akashe to, mom adawo tafiya amma dai jirgi zaki hau nakuma sandai sai gobe ko?..tace eh tare tafara tafiya yayinda sauran suka bita da Allah yakiyaye hanya ta amsa da amin sannan tafita.
*_Zariya_*
*******
Koda aunty *Bebe* ta'iso Zariya ta'iske anata rikici da *Blue* wai sai yafita yaje gurin *Beena* kasan cewar batazo ba kamar yanda tace, wanda dama bazuwan zatayi ba tadaice Masa hakane don yaci abincin yakuma yi wanka,
"Don haka sai faman kuka yake kamar yanda yasaba ko abincin Rana yakici har karfe biyu da rabi rana cikin, tashin hankali *Bulama* yace dad akai shi gidan su *Beena* din kawai yaganta tunda batazo ba,
Cike da damuwa yace a ah son kar atakura "mata kabarshi aizayayi shuru, koda aunty *Bebe* ta tambaye me yasa meshi akafa mata jitayi wani irin tsoro yakamata yayinda taji tanasan ganin wacece wannan *Beena* din dakyarta lallashesa yayi shuru yadaina kukan,
amma sai faɗin my *Beena* friend yake sannan tashiga kicin da kanta tagirka Masa abinci, Bayan ta barbadesa damaganin da boka yabata sannan takawo masa, da lallashi da idan kaci zankaika gurin *Beena* friend dinka,
sannan yaci yana gamawa yafara wani irin ihu nafitar hankali tareda rike Kai gaba daya hankalin su, yatashi ita me fuska biyun harda kukan munafurci, yadauki tsawon lokaci yana ihun sannan can saiyai shuru sai kuma barci yadaukesa anan kan kafet.
***"*"**
Aban garen baban abdul Kam yanafita banki yaje yacire kudin inda yamayar cikin asusunsa, sannan yadebo wasu yaje kasuwa yasiyo buhu-buhun abinci kowa biyu sannan yayi chefane me raida lafiya sannan yanufi gida.
Su *Beena* Kam yini sukan ranan zuciyarsu cike da kewar *Blue*, musamman *Beena* din data tuno yanayin dasuke ciki da shirmen dayake mata sai tayi murmushi ko dariya idan ta tuna na tausayi Kuma sai kwalla yazubo mata,
Ko yanzu zaune take atsakar gida ita kai sai faman tunanin shi take sai kawai taga anatå shigowa da
buhu-buhun abinci sai kuma ga baban abdul yashigo hannunsa rikeda leda me shakeda chefane, bakisan kamar gonan auduga
dasauri taje takarba tare dayimasa sannan yace yauwa, bari Naga abbu nafito inasan magana dake cikin faduwar gaba tace to,
"zuwa yayi yafadawa abbu alkairi da dad yai masa cike da farinciki abbu yake tayasa murna, yace abbu na'ajiye maka dubu hamsi kaja jari dariya yayi yace Kai mansur akwaika da abin dariya, wanda bayada lafiya inashi ina wani janjari umuh?..allah kuwa,
Humm kaidai kakara cikin kasuwancin ka allah yasa masu albarka yace Ameen abbu aikwanan nan zakawarke, bari na koma kasuwa to Allah yabada sa'a ameen sannan yafita da sauri,
Tsaye ya iske *Beena* tana jiran fitowarsa, murmushi yayi cikin wata irin murya dabata taba saninshi da'ita ba, yace malama *Beenazar* kenan ya gida?..
cikin sanyin murya tace lafiya lau munga abinci mungode allah yakara budi, ah! bakomai nima dad" *"Bilal* yabani dubu dari biyu dasauri tace ayya ya yah *Bilal* my friend yayi shuru yadaina kukan yaci abincin yayi wankan?..duk alokaci daya tajero masa wayan nan tambayoyi,
murmushin karfin hali yayi sannan yace yana lafiya Kuma duk yayi abinda kika tambaya, ajiyar zuciya tayi yace kinaji ko *Beenazar*?..Kai ta gyaɗa, wato nadade inasonki kuma wlh aurenki nakesanyi ido tazaro cike da tsananin tsoro ta kalle shi bakinta na rawa tace.......
Muje zuwa
Tareda
✍🏼
*_LUFHAT CE_*
🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍
🎍 *_ZAUJUN-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_
🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍
Page2️⃣8️⃣
WRITTEN
By
🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍
OR
🎍 *MEENAT*🎍
Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJUN-MAJNUN_*
SADAUKARWA GA
*_My lovely blood sisters 👩❤👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi our last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love💋💋💋._*
Littafin nan na kudi ne duk me bukatar zaya iya turo katin MTN na 200 a wannan layin 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi zaku iya ta account no kamar haka 0047769671 Abdullahi Amina gt bank nagode.
_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/
✍🏼
_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_
"Baban abdul kasan abinda kake faɗi kuwa?...haba *Beenazar* nasa ni mana wlh duk abinda ki kaga ina maku inayi ne don allah da kuma sanki, na daɗe ina son nafaɗa maki dana tuna yanda kuke da "maman Abdul sai nafasa Amma daga baya danaga bata da matsala shine nace to bari nafaɗa maki,
"Da saurin tace kai ke ganin bata" da matsala amma bari kaji duk yanda muke da'ita dazaran taji kana so na da aure "Kai ko bada aure bane to kasani daga ranan matsaloli zasu tashi, saboda haka don Allah kayi hakuri baban abdul ni bazan iya auren ka ba,
domin ina ganin girman ka haka zalika in ganin mutunci "matar ka wacce, na dauke ta" tamkar yayata da muka fito ciki daya kaga idan ko haka ne to bazan iya auren mijin yayata ba don haka kayi hakuri,
da sauri yace don Allan *Beenazar* kar kice haka wlh ina son ki sosai nayi maki alkawarin baki farin ciki kai ta girgiza tare dacewa kayi hakuri baban abdul, sannan tashige falo da sauri yana kwala mata kira amma bata juyo ba Kai ya girgiza tare da ficewa daga gidan aranshi yana tunanin hanyar da zayabi don ya mallaki *Beenazar*.
yana fita yaga adaidai ta sahu yana sauke maman Abdul baki yabude ciki da mamakin ganinta, murmushi tayi tare dacewa ai inata karan wayarka baka dauka ba dariya yayi yace ayya tana silent ne tace shiyasa bakaji ba, abdu yaje ya rungumesa tare da cewa abba yace na'am abdalla kundawo lafiya?.. yace eh.
nan yaba me adaidaita kudinshi tare da daukan akwatin kayansu suka shiga gida yana yimata sannun da hanya tana amsawa tare da tambayar shi ya aiki lafiya taganshi yanzu?...nan yake faɗa mata abinda yadawoyi tace allah sarki ai mungode bayan ya'ajiye kayan sannan yafito yatafi kasuwa gurin sana'ar shi.
*Beena* Kam tana shiga falo tsayawa tayi tana maida numfashi tamkar wacce tayi uban gudu sai kuma tace
lallaima wannan baban abdul din Wai yana Sona,
harda wai zaya aure ni tab!, "Yana sanki Kuma?.. inji cewar *Bass* dake fitowa dakinsu dasauri ta kalle shi tare dacewa eh wai ba, lallai Kam sai wai shiya manta yanda kuke mutunci da matarsa ne?..Oho! mashi ke dalla kyaleta niban baki goyan bayan haka ba,
Oh! kila shiyasa yaketayi Mana hidima ko?..tace kila nidai mushiga gurin abbu kaji gaskiya Kam maganar babu dadin ji sannan suka shiga dakin abbun.
Ita Kuma maman Abdul bayan ta huta sannan tashiga gidan su *Beena* cike da murna *Beena* ta tare ta, bayan tagaida bab Sai suka fito falo suka zauna anan take bata labarin *"Blue* cike da tausayi maman Abdul tace allah sarki bansan "Shiba Amma na tausayawa halinda yake ciki sosai,
Wlh allah yabashi lafiya tace ameen ai baban abdul yafaɗa mun alkairin da mahaifinsa yayi mashi, tace eh wlh harda muma yasiyo Mana abinci tace ayya nan dai suketa fira inda *Beena* tasake cemata tayiwa baban abdul godiya tunda ta tafi yaketa ɗawaini dasu,
"murmushi tayi tace aishi haka "yake abinshi be rufe Masa ido ba ko kad'an bada dadeba tace da *Beena* tazo ta tayata gyaran gida, nan tafadawa abbu yace to suje harda *Bana* ta tayasu tace to sannan suka fito suka shiga gidan maman Abdul din.
********
"Aban garen su *Blue* kuwa tunda yafarka yacigaba da rigimar neman *"Beena* friend din shi,har yamma bai daina abu guda ba duk yafita hayyacin shi gwanin tausayi gashi dad yafita zuwa asibiti,
"Saboda ankawo emmegancy don haka aka kirashi tunda shike da duty shiyasa yatafi, don haka daga *Bulama* sai aunty *Bebe* da peter ke kwasan rikicin aunty *Bebe* duk haushe yakashe ta saboda tayi lallashi har tagaji shiyasa aranta takeji kamar takama shi tayi ta duka koma ta sheƙe masa wuya ya mutu kowa yahuta,
"agefe daya kuma tanajin tsanar *"Beenazar* din nan da bata gani ba tare da wani irin faduwar gaba wanda tarasa dalilin ta najin haka.
"Dad bai dawo ba sai bayan magrib sannan inda ya'iske *Blue* yayi zuru-zuru yaki cin abincin dare sai lallashi sa suke, cike da tausayi dad yace my son yadai?..
fadawa yayi jikin dad yafashe da kuka me cike da shagwaba yace dad I want go my *Beena* friend yace to kaci abinci sai mutafi dakyar yaci abinci, Kai atakaice dai haka suka kwana Basu runtsaba don haka gari na wayewa.
"Bayan sunyi breakfast da kyar sai dad yashirya *Blue* da kanshi inda yasa mashi wata tsadaddiyar shadda gold color, sannan yafeshe shi da turaruka masu matukar kamshi ya daura masa agogon glod sannan yasa mashi takalma tsadaddu farare masu asalin kyau yanata murna,
yace dad zamutafi gurin my *Beena* friend ko?...yace inshallah yau san nake *Beenazar* tazama taka da sauri aunty *Bebe* tace dad meka ke nufi?... murmushi yayi tare da fadin alkhairi kushirya zamu tafi gidan su *Beenazar* tace dad tunda sassafe Nan?...
"eh idan yaso in muka dawo sai kitafi shikuma son sai yatafi office hakan tashirya gabanta yanata faduwa aranta kuma tanajin ta tsani wannan *Beenazar* din tun Bata ganta ba,
misalin karfe 8:30am nasafe suka nufi anguwar su *Beena* bayan dad yasasun tsaya hanya sun siya goro da alawa wanda hakan yasake ba aunty *Bebe* tsoro, har aranta tana cewa to me Kuma dad zayayi da wayannan tarkacen?...
Da sallama suka shiga falon Wanda sallamar cé takatse wasu *Beena* karin kumallon, dasuke adakin abbun kasan cewar yanzu Nan sukeyi *Bass* ne yatashi yaleka yagansu sai yakoma yafadawa Abbu yace ah! kace su shigo Mana, yace to tareda komawa cikin sakin fuska yace Bismillah abbu yace kushigo sannan suka shiga,
*Blue* kam yana ganin *Beena* ya'isa gurinta da murna harda tsalle kamar zaya dauketa yagoya don jin daɗin ganinta, zama yayi dirshan kusada ita cikin farinciki yace my *Beena* friend inata ne manki, itama cike da murnan ganinsa tace da gaske my yah *Bilal* friend?...Kai ya gyaɗa mata alamar eh tace to gani me ka kawo mun?...
teddy hannun shi yamika mata karɓa tayi cike da murna tace wow! is so beauty wannan din ka kawo mun?...Kai yasake gyaɗa mata alamar eh yana dariya tace to nagode sosai,
kayi breakfast kuwa yau?...baki yatabe kamar zayayi kuka ido tazaro cike da tsoro me hade da kulawa tace bakayi bakenan kanajin yinwa?...yace yes tace oh! yah *Bilal* my friend meyasa?..
bakayi breakfast ba ko?... kilama shiyasa naga duk kafaɗa bari na zubo maka taliya zakaci ko?....yes mikewa tayi danufin taje tazubo masa sai Shima yamike zaya bita tace kazauna bari nadawo kaji?.. kafaɗa ya maƙe alamar a ah, to zomuje zujawar dazatayi taga dad tsaye fuskarsa cike da farin ciki da sauri ta tsugunna cike da jin kunya tace dad ina kwana?...
ita har ga Allah ta manta da mutane aguren cikinjin daɗi yace lfy lau *Beenazar* Kinga yayanki ya damemu da rigima sai yazo gurinki ko?..Kai ta gyaɗa tare da mikewa tafita yayinda mutuminta yabita yana my *Beena* friend wait for me.
"Abbu yace dr ku zauna mana *Beenazar* da *Bilal* sai allah idan suna tare mantawa sukai dakomai, dariya dad yayi yace gaskiya kam ainagani sannan suka zazzauna aunty *Bebe,*
"Kam Kamar ta kurma ihu don bakin cikin ganin yanda *Blue* yake farin cikin ganin *"Beena* aranta kuma tana tunani yanda zatayi ta takama wanna *Beenazar* din burki domin idan har tabarta tacigaba da shiga sha'anin *Blue* to tabbas zayata bata mata lamarinta,
"Bayan angaisa sai abbu yace akawo masu abinci dad yace sun koshi, sannan abbun yace Dr inafata dai lfy nagan ku dasassafe?...yace lafiyar kenan wannan aunty *Bilal* tana zaune da mijinta da yaranta a Abuja jiya tazo dataji anga *Bilal* shine nace tazo tasake yimaku godiya, abbu yace Allah sarki sannu yana ya megidan da yara?..
cike da bakin ciki tace duk suna lafiya _domin jitayi tsanar mutumi yaɗarsu azuciyatar Kamar yanda tsanar ɗiyarshi ya ɗarsu aranta,_ munfa gode a ah ha aibakomai da aina kowane, sannan dad ya kalleta ita da *Bulama* yace ku Dan bamu guri kad'an zamuyi magana sukace to tareda mikewa suka fita Wanda aunty *Bebe* bataso haka ba,
"A falon suka iske su *Beena* damasu tuni suna falon zazzaune, yayinda *Blue* yake tazubawa *Beena* shagwaba domin yaci abinci cewa yayi saidai tabashi abaki bayanda ta'iya dole take bashi saboda gudun rigimar shi,
yana ganin aunty *Bebe*