Showing 45001 words to 45490 words out of 45490 words
da misalin karfe 10:30am nasafe su ammu suka iso garin zariya kasan cewar sun taso dawuri, *Beena* tana ɗaki tana barci kasar cewar yanzu batasamun yin barci da dare sai gari yawaye sai tayita ramuwar barcin,
yayinda su *Bassam* suna tsakar gida suna wanki tunda yau lahadi abbu kuma yana gefe yana kallon su sai sugajin sallamar ammu,
Cak! suka tsaya dukkan su suka zubawa ƙofa ido aikam saigata tashigo fuskarta ɗauke da fara'a, aikam suka saki kayan hannun su harda *Bassam* suka nufeta dagudu suka rungume ta suna wani irin ihun murnad dafaɗin ammun mu ayoyo, yayinda abbu yamike zumbur yazuba mata ido itama kallon shi da matsananciyar mamakin ganinshi ahaka,
"Ahankalin yakarasa gurinta cikin tsananin murna yace fatimata kece?...kaita gyaɗa dama sauda yawan lokuta jikina yana bani kina raye ashe hakan ne?...kai tasake gyaɗa mashi yayinda hawaye yake kokarin bin ƙuncinta,
Hannun yaɗaga sama yana me godiya ga Allah daya dawo mashi da matarsa uwar yayan shi sannan yakalli *Bassam* cike da farinciki yace *Bassam* karku kayar mun da Fatima ta mana, dariya sukayi dukan su cike da murna suka saketa sai alokaci abbu yaga su Abba dake tsaye suna kallon su cike da tausayin su,
yace a ah fatima ta ashe tare kike da Baki?..tace eh zuciyar ta cike da tambayoyi abbu yace sannun ku sannu dazuwa ku kushigo mana yafaɗi yana meyi masu jagora zuwa falo, yayinda suka bishi su *Banu* suna rikeda hannun ammu wacce keta kallon abbu dake tafiya lafiya mamaki take ya'akayi?...
Shigar su falo yayi dai-dai da fitowar *Beena* ɗaki tana yamutse fuska domin barcin bai isheta ba gashi hayaniyar su ta tasheta, ganin ammu ne yasata murza ido sai Kuma tabuɗe aikam ammu tagani hakan yasata saki ihun murna tare zuwa ta rungume ta sai kuma tasaki kuka, tana faɗin ammu dama kina raye shine kika barmu?...
"Ɗagota tayi daga jikinta ta ƙura mata ido inda nan take tagano tana ɗauke da ciki gaban tane yai mugun faɗuwa, cikin dariyar karfin hali tace eh to mine kuma na kuka bagashi Allah yadawo Dani gareku ba, sannan ta kalli abba tare dacewa yaya kuzauna mana kasan cewar haka take kiransa,
"Bayan sun zauna sai *Bana* takawo masu ruwa suna cikin sha sai ammu tamike wacce hankalin ta gaba ɗaya atashe yake da ganin yanayin da *Beena* take ciki, kallon ta tayi tare da kiranta ɗaki suna shiga ta kalli *Beenan* kirjinta yana bugawa tace *Beenazar* menake gani ajikin ki?...,
"Cike da rashin fahimta tace ammu mekika gani?... hararan ta tayi cike da bacin rai tace keee! banasan shashancin banza ina tambayar kina tambaya ta?...cikin faɗuwar gaba tace kiyi hakuri ammu ban fahimci kibane,
"Cikin fargaba tace ciki nagani ajikin ki ko?....kai ta gyaɗa kirjinta nacigaba da bugawa ido ammu tazaro cike da tsananin bacin rai tashaƙo wuyan ta tare da cewa....
Muje zuwa
*LUFHAT CE*