Showing 3001 words to 6000 words out of 45490 words
aranki ko? kaita gyada sannan ta tashi tafita jiki bakwari.
Dakin Ammu tashiga bakinta dauke da sallama, tsaye ta isketa hanun rikeda wayar nokia gefe kuma jakace ga kaya zube akasa, tsugunawa tayi tareda daukan kayan tana ninkewa tanasawa cikin jakar bayan tagama tarufe jakar,
sannan ta dukar da kai cikin sanyi murya tace don Allah Ammu idan kinje "kawu Muda be baki hakkin ki ba kiyi hakuri ki kyale shi yabaki inda bayada shi kinji? ba tareda ta kalle taba tace to sannan tadauki hijab dinta me ruwankasa dake rataye jiki kofa tasa alamar shirin tafiyar take,
Sannan tace to nizan tafi sannan tadauki pos dake ajiye saman gado tareda budewa taciro kudi naira dari biyar ta mikawa *Beena,* tareda cewa gashi kirike ko zaku siya wani abun ai akwai sauran garin dawa da na rogo ko?
kai ta gyada alamar eh tace to don Allah kikula da kanki tareda kannanki wanda nasan kinayi amma kikara, sannan banda yawon banza duk danasan ke bama'a bociyar sa bace, amman ki kula kinji ko?
Cikin sanyi murya tace to, Sannan tace yauwa yauwa yau ma zakije gidan "maman "Abdul din
ne gurin sakar?..tace eh to Allah yabada sa'a amaida hankali, sannan adawo dawuri atafi islamiya, sannan ki matsawa babana yaje gurin aikin sutafi tareda *Bash* idan *''Banu* na ta tashi ki kulamun da'ita sosai kinji?
tace to Allah tsare hanya tace to Amin Allah yayi maku albarka tashi ki kiramun babana yarakani bakin titi na hau mota zuwa tasha, ahankali ta mike tareda cewa to tafita batare da dadewa ba sai gasu tareda *Bass* har yacire uniform yana riga da wando nawani fari yadi, ba tareda yace komai ba yadauki jakar suka fita saida tashiga dakin Abbu sannan tafito yatafi raka ta,
Yayinda *Beena* tashiga dakin su cikin sanyi jiki tacire uniform tarage daga ita sai vest iya guiwa batada kiba saidai tanada shave me kyau, gata da dukiyar fulani dasuka cika mata kirji tanada matukar yalwar kashin kai wanda yakeda yawa da tsamo gashi baki sidik tanada ido me matukar kyau infact dai *Beena* kyakkyawace sosai,
ahankali ta zauna akan dan karamin gadon su me dauke da wata lotsatsiyar katifa ahankali ta lumshe ido, tafara tunanin rayuwar su ta baya.
*_ASALIN SU_*
Alh Usaman Dan Sudan shi ne asalin sunan Abbu, karatu ne yakawo shi garin zaria inda yahadu da wani shahararran me kudi me suna Alh sule me dabino wanda yazama ubangida ga Abbun Alh sule me dabino asalin shi mutumin barno ne kuma maraya ne bashida kowa Allah ya azurta shi da dukiya me tarin yawa kasuwanci ne yakawo shi zariya,
yanada mata
biyu kuma duk garinsu daya, Haj hajara da Haj Balkisu itama marainiya ce Haj Haraja tanada d'a daya me suna Mudansir, Haj Balkisu tanada y'a daya me suna fatima, gidan Alh sule kullum babu zaman lafiya saboda Haj Haraja masifaffiyar macece gatada kyashi da hassada,
wanda har ta koyawa danta Mudassir itakam Haj Balkisu macece me hakuri batada kyashi da hassada kamar mijinta, haka ake rayuwa gida kwasam sai ciwon ajali yakama Haj "Balkisu ba tadade dafara jinya ba tace ga garin nan,
Alh sule da Fatima sunyi kuka sosai na rashin Haj Balkisu salihar mace.
Bayan rasuwar Haj Balkisu Fatima ta fuskanci matsala sosai agurin Haj Hajara da d'a Alh Muda har da matar sa Safara'u, da Alh sule ya fahimci haka tana gama sakandiri sai ya aurar da ita ga Usman wato Abbu, inda Alh su yaikomai sannan yabashi dankareren gida afadaman sarki Fatima batason Usman ko kad'an,
amma batada zabi dole tayi hakurin biyayya ga mahaifinta domin ta fuskanci yanason Usman kasan cewar sa mutumin kirki me amana, bayan auran sai Usman yaje Sudan yadauko mahaifiyar shi domin Fatima taki sauraran shi beyi yin kurin fadawa Alh sule ba domin yana matukar kaunar Fatima bayason facin ranta ko kad'an.
Wani abun mamaki Fatima tana ganin Iya mahaifiyar Usman taji duniya babu wacce take kauna irin iya, don haka take bata kulawa sosai tamkar ita ce ta haifeta, wanda hakan bakarin samun kima tayi agurin Usman ba, ahankali Iya ta fahimci Fatima bata kula d'anta don haka sai tafara yimata nasiha cikin hikima don tabi mijinta su zauna lafiya, domin aljannar ta yana karkashin kafar mijinta, kasan cewar Fatima me fahimta ce sai tadauka.
Aure da albarka sai ga ciki ranan data haihu tahaifi y'a mace sankowa kin wanda yarasa, ranan zokuga murna gurin Usman da Iya yayinda murnan Alh sule yafi nasu, shiyayi komai ranan suna y'a taci sunan Haj Balkisu wanda ashe Iyama sunanta kenan,
don haka sai suna kiranta *Beenazeer,* bayan *Beenazeer* ta haifi namiji shine akasa masu sunan Alh sule wato Sulemain shine suke kiran shi *Bassam,* bayan *Bassam* ta haifi *Banafsha* sannan *Bashir* sannan auta *Banuja* haka suka taso cikin tarbiyya iyayen su tareda kulawar Alh sule, alokacin lya tadad'e da rasuwa yayinda Alh sule yadauki son duniya yadora masu,
komai sukeso yimasu yake musamman *Beenazeer,* wanda yasa Alh Muda yakeji kamar yakashe Fatima da yayanta kasan cewar shi Allah be ba matarsa haihuwa ba, don haka komai Alh sule yi masu yake da dukiyar sa suna rayuwarsu gwanin dad'i kwatsam ranan wata laraba Alh sule yakira Abbu don yakaishi Abuja kasan cewar dama shike tukashi duk inda zashi,
Don haka suna kan haryasu tazuwa abuja sukayi mummuna hatsari
aka kwashesu zuwa asibiti kwanan su biyu acikin asibiti Alh sule yace ga garinku nan, yayinda gaba daya rabin jikin Abbu yadaina aiki Fatima wato Ammu tashiga mummunan tashin hankali itada y'ay'an ta.
Ranan sadakan bakwai sai akayi maganar rabon gado inda aka nemi Alh Muda daya fadi abubuwan da Alh sule yabari, budar bakinsa keda wuya sai yace.....
_Muje zuwa yanzu za'afara_
So
More
Comments more
typing and pls share it
๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
๐ *_ZAUJUN -MAJNUN_*๐
_(miji mahaukaci)_
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
Page5๏ธโฃto6๏ธโฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *MEENAT*๐
Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now๐๐ฝ
*_ZAUJEE-MAJNUN_*
SADAUKARWA GA
*_My lovely blood sisters ๐ฉโโคโ๐ฉHadiza (aunty)and Nana Firdausi out last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love๐๐๐._*
Littafin nan na kudi ne duk me bukata zaya iya turo katin mtn ko airtel na 200 a wannan layin 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi duk zaku iya tuntuban layin sai abaku acc no nagode.
_____________________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/
_FREE PAGE_
โ๐ผ
_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_
"Ai babu abinda Baba yabari ko kudin dayake kasuwanci dasu duk na mutane ne, kuma tuni yabashi ya mayar masu da abinsu,
Cikin tsananin tsoro! Ammu ta kalle shi! haka malaman gurin mamaki yarufe su dajin wannan magana me kamada almara, domin dai ansan "Alh Sule yanada dukiya me tarin yawa,
Wanda kuma tabbas tashi ce bata wani ba amma taya d'an sa zayace wai batasa bace to me yake nufi?....yayinda Haj Hajara ta goyi bayan shi domin kuwa da daya daga ciki malaman dazasu raba gadon ya tambaye ta, meye gaskiyar lamarin?..
Sai tace ai gaskiyar kenan domin itama kusan kodaya yaushe yanafad'a mata ba dukiyar shi bace, abu kamar wasa yazama gaskiya don haka malaman da suka tsaya akan rabon gadon suka bar gidan,
Bayan sun tabbatar ma Alh Muda da mahaifiyar sa cewa muddun sukaci kwayar zarra na hakkin wannan baiwar Allah zasu biyata gobe kiyama, sannan suka fita.
Yayinda akabar shi daga shi sai Ammu da Haj Haraja cikin mutuwar jiki Ammu tace yaya Muda kaji tsoron Allah, taya zakace duk dukiyar nan bata "Baba bace?.
Dariyar mugunta yayi yace ah! dukiya kam ta duk ta "Baba ce kece dai bazan bawa ko sisin kobo aciki ba, wanda kukaci keda mijinki da y'ay'aki ya'isa haka wannan tawace nida y'ay'ana da zan haifa,
tace to don Allah kabada kudin ayiwa Abbun su aiki cikin masifa yace wlh ko sisi bazaya bayar ba aiba kudin ubansa bane, kai su tashi ma subar masa gidan shi,
Wasa-wasa Alh Muda yamursashe idonsa yahana ma Ammu gadon ta, kusan kullun taje don yabata tabiya wa yara kudin school, akuma yiwa Abbu aikin kafar sa wanda akace naira miliyan biyar za'ayi Amma Dan talikin nan har yau kusan shekara uku kenan,
Amma yaki bata ba tun yana garin kaduna har yakoma Abuja dazama cikin daya daga gidajen Alh sule, kasan cewar dama yanada gidaje a Abuja, aduk lokacin dataje saidai yaimata walakanci idan kuma tacinma yan arzikin yace mata tazo yawan maularta ko?...
To shine sai kaga wata rana yabata wasu yan kudi shine zata hau mota sauran suci abinci, idan kuma yanaji tsiya kosisin baya bata saidai Safara'u matarsa tabata kudin motar dawowa, shiyasa komai duk yacab'e masu rayuwa tayi masu zafi hatta da abinci dazasuci yana kokarin yafi karfinsu,
School kuwa tun sunayi masu hakuri har sungaji yanzu kusan kullun sai ankoresu, Abbu yasha ce" Ammu tayi hakuri ta kyale "shi tunda yaki bata Amma takiya kasan cewar Ammu akwai kafiya.
Ahankali ta sauke ajiyar zuciya sannan tamike cikin nutsuwa tashiga toilet din cikin dakin, *Beenazeer* kenan tanada matukar nutsuwa da kunya ga ladabi da biyayya musamman ga iyayenta tanada ilimin addini sosai,
Domin kuwa ta sauke alqur'an da hadda takuma an wasu littafai addini sosai, yanzu haka tana koyarwa a islamiyar su idan wata yayi abiyata wanda dashi ne suke dan samun abinda sukeci, amakarantar boko kuma tana S S 3 sune ma zasu rubuta jarabawa wannan time din, batada yawan magana domin kuwa miskilace tabugawa ajarida saidai tanada hakuri sosai amma kuma akwai matukar zuciya duk haka kuma tana da tsoro uwa uba ga kafiya wanda da alama Ammu su tabiyo,๐
Sannan tana matukar kaunar iyaye ta da yan'uwanta fiye da yadda take kaunar rayuwarta zata iyayin komai domin sama masu farin ciki, wanda hakan yasa iyayen ta suke kaunarta fiye da tunanin me karatu wanda suka dayai suka san adadisa aransu,
Ko bakomai itadin me shiga raice ga duk wanda ya zauna da'ita sai yaji tashiga ransa yaji yana Sonta, hakan nan suma yan'uwan nata suke kaunar ta ko dayake hakan yanada nasaba da yadda iyayen nasu suka koya masu kaunar junan su.
Bata dad'e atoile din ba tafito daure da tawul dai-dai lokacin da *Banafsha* tashigo dakin da sallama, tace Aunty *Beena* "Ammu ta tafi Abuja gidan "kawu Muda ne?..kai ta gyad'a mata cikin sanyi murya tace Aunty *Beena* Allah yasa kawu "Muda yaba Ammun mu kudin ta,
Ahankali tace ameen my *Banaf* kicire uniform kisa wasu kayan mutafi gidan maman Abdul tare kinji?..cike da murna tace to.
Cikin kankani lokaci *Bana* tashirya wanda kusan tare suka gama da *Beena,* sanye suke cikin riga da zani na wata blue atamfa bayan ta murza man kwalacca sai tafeshe jikinta da turaren humra da maman Abdul ta bata sannan su kasa hijab fari sannan suka fita,
Dai-dai lokacin da *Bassam* da *Bash* suka dawo raka Ammu, *Beena* tace su shirya su tafi gurin inda suke zuwa koyon dinki sukace to, dinki mata *Bassam* yakeyi yayinda *Bashir* yake koyan na maza *Bassam* tuni ya'iya dinki wanda har dashi suke samun kudin sayen abincin,
Sannan su *Beena* suka shiga dakin Abbu suka sallame shi sannan suka fito suka tafi gidan maman Abdul.
Maman Abdul makociyarsu ce, tana zaune da mijinta da yaran su biyu Abdullah da Anisa tanada kekunan saka Wanda take koyawa yammata aciki har da *Beena* da *Banaf*, maman Abdul tana matukar kaunar *Beena* saboda tanada basira sosai gata dasaurin dauka abu wannan kenan.
*Cigaba*
*ASIBITIN SHIKA*
****""""*****
Koda suka isa cikin sauri aka tarbe su kasan cewar Dad babban Dr ne acikin asibitin don haka akazo da gadon daukar marasa lafiya aka dauki *Blue,* wanda yaketa faman ihu tareda fisge fisge direct emagency room aka nufa dashi,
likitoci sunfi biyar akasa aciki
har da Dad sosai suka dukufa akansa yayinda yaketa fisge fisge tareda wani irin ihu,
Likitoci sunyi iya kokarisu akan *Blue* amma abun yaci tura domin kuwa be daina fisge fisgen da ihun dayake ba, tareda ture duk wanda yai yin kurin rikeshi,
Don haka dole suka taru kusan mutum goma aka danne shi sukayi masa alluran barci me matukar karfi, sannan suka fito kowa sai sharan gumi yake yayinda zuciyoyin suke cike da mamakin abinda yasa meshi haka...?
Musamman Dad.
Direct wani babban daki suka shiga inda suke tattaunawa especially idan irin haka tafaru, sosai ake tattaunawa akan wannan lalura da tasamu Dan abokin aikinsu, nan Dad yake fadama su yanda abun yafaru, sai daya daga cikin likitoci yace niko sai nake gani kamar aljanu ne suka shafe s....
Zumbur Dad yamike cikin bacin rai yace haba Dr lbrahim wannan wace irin magana ce....? D'an nawa ne aljanu suka shafa?...to kasani ni 'Dana ba buwasu aljanu dasuka shafe "sa, asalima ni mabansan akwai wasu aljanu aduniya ba,
Sannan yafita rai bace daga dakin daya daga cikin likitoci yace humm! Dr I b kenan kaima kasan cewa "Dr L U be yarda da duk wani abu daya shafi gargajiya ba,
Amma tabbas ciwon "yaron sa yayi kama da shafar aljanu, Dr I b yace "uhumm kaima kafad'a yanzu dai mubari yatashi musake ganin yanayin sa tukun ko?..suka amsa da eh haka za'ayi sannan suka fito kowa yanufi office dinsa zuciyar sa cike da tunani halinda *Blue* yake ciki.
Dad ma koda yafita direct office dinsa yanufa da sauri *Barrister* tareda *Bulama* suka bishi, alokaci daya suka zazzauna cikin tashin hankali *Bulama* yace Dad meye samu my *Blue?...* *Barr* ma irin tmbyr yayiwa Dad,
Shuru Dad yayi kafin cikin bacin rai yace kai kaji "Dr I b wai aljanu suka shafi my "boy da sauri cikin harshen turanci *Bulama* yace Dad
meye kuma haka..?wai evil, tsaki yayi yace karya ne Dad me I don't believe this wooo! Dr yace me to my boy,
Shikam *Barr* shuru yayi yana nazari lamarin can sai yace Dr lamarin fa akwai kamshi gaskiya, da sauri Dad yace haba *Barr* kamar ya fa?...
yace naga yanda yake irin yadda aljan...dasauri Dr yace enough! enough!! enough!!! *Barr* banaso kana alakanta "boy da wayan nan shirmen da ni kwata-kwata banyi believe dasu ba, yace sorry bawai nace sudin bane amh! to yanzu dai ya jikin nasa"?...
Cikin had'e buska Dad yace him in bad condition, yanzu ma saida mukayi masa alluran barci me karfi wanda zata iya kaiwa gobe so idan har yafarka banga wani cigaba ba zanfitar dashi waje, *Barr* yace to Allah yabashi lfy,
Dad yamike tare da cewa Amin mujen ku gida inason nad'anyi wani bincike akan ciwon boy, *Barr* yace ok *Bulama* yace Dad ni zan tsaya gurin my *Blue* murmurshi yayi tare da dafa kafad'ar shi yace karka damu my boy akwai masu kulashi so muje ka huta kaji..?
Yace yes Dad, Sannan Dad yafara fita sai *Bulama* da sauri *Barr* yakama kunnan shi aikam yasaki yar kara kadan cikin shagwaba yace ahhh! papa akwai zafi fa,
Kasa-kasa yayi da murya yanda Dad bazaya jiba, yace l know meyasa bakaji ina rabaka da wannan akida kana ko karin yiko?..yace papa me nayi?..yace gidan ku, cewa fa kayi bakayi believe da aljanu ba, yace gaskiya papa ni ban yarda da wasu aljanu ba, yace to dan ubanka ko ka yarda kokar ka yarda akwai aljanu,
Yace to papa ni ban taba ganin su bafa taya zan yarda akwai su?..,da sauri yace Dan ubanka karkayi fatan ganinsu domin ganinsu arayuwa ba alkhairi ba ne,
Kai! tsaya ma tukun kanayin addu'a kuwa?..yace papa inayi shimafa my *"Blue* yanayi sosai har yafini yifa, yace kaidai shashasha ne to wlh gara kadage dayin azkhar domin suna tsare mutum daga bad evil kaji ko?..
Yace to dai-dai lokacin da suka karasa gurin mota escorts suka bude masu, suka shiga
kasan cewar tuni Dad yashiga don haka sukaja suka tafi......
*WAI WANENE BLUE*?........
_Muje zuwa yanzu za'afara_
So
More
Comments more
typing pls share
it
*_LUFHAT CE_*
โ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธ
*ยฎ _PEN: WRITER'S ASSOCIATION_*
*~_Only the exquisite_~* *~__and whizkid_ _writers_~* ~*_are_* *_opportune to_* *_be__*~
*~_pen writers_~*
โ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธโ๏ธ
__________________
https://www.facebook.com/groups/1533639276725285/
๐๐๐๐
๐๐๐
๐๐
๐
๐ *_ZAUJUN MAJNUN_*๐
( _Miji mahaukaci_)
๐
๐๐
๐๐๐
๐๐๐๐
Page7๏ธโฃto8๏ธโฃ
WRITTEN
By
๐ *AMEENA UMAR FARUQ*๐
OR
๐ *Meenat*๐
Marubuciyar
*DA SANNU*
*ZUCIYATA CE*
*AFSANA*
*KYAUTAR ALLAH CE*๐๐ผ
and now
*ZAUJUN MAJNUN*
SADAUKARWA GA
*_My lovely blood sisters๐ฉโโค๏ธโ๐ฉHadiza (Aunty) and Nana firdausi our Last born do u know what...? sisters humm l really love love love yours irin babu adadin nan fa irin so muchhh love_*.๐๐๐
Littafin nan na kudi ne duk me bukata zaya iya turo katin mtn k airtel 200 a wannan 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi duk zaku iya tuntuban layin sai abaku acc no ba nagode.
*_FREE PAGE_*
โ๐ผ
*_Bismillahirrahamanirraheem!!!_*
*BILAL LAWAL USMAN* shine cikakken sunan sa sai abokan sa suna kiransa" *BLUE*, yakasan ce d'a ne ga Alh Lawal Usman kona ce Dr wato Dad asalin sa mutumin kano ne aiki ne yakawo shi zaria, gaba daya zuri'ar su Dad yan'boko ne na bugawa ajarida irin masu komai dabi'ar su ta bature ce
Kuma asalinsu fulani ne mahaifin Dad prof Lawal Bilai yarike mukamai sosai akasa najeriya yana daya daga cikin mutanen dasuke fad'a aji kasar nan, don haka zuri'ar su manyan mutane ne kuma masu kudi ne sosai Dad su uku ne kawai agurin iyayen su kuma duk kansu manyan ne acikin gwamnati, Kabeer shine babba wanda yake zaune a Lagos da iyalan sa matarsa daya da yaran sa biyu duk maza kuma shi din babban Lawyer ne,
Sai me bimasa macece me suna Sadeeya itama babbar Dr ce tana zaune abuja da mijinta da yaranta uku maza biyu mace daya, sai Dad Wanda shima babban Dr ne acikin asibitin shika da kuma Abuja Dad yaran sa biyu Aunty Aseeya itace babba wacce suke kira da Bebe kasan cewar sunan mahaifiyar Dad taci,
yanzu haka tana abuja tana auran wani babban Lawyer gwanati tanada yaranta hudu duk mata tana aiki ababban asibitin Abuja,
Sai *Bilal* amma ba maman su