Showing 42001 words to 45000 words out of 45490 words

Chapter 15 - ZAUJUN MAJNUN by AMEENA UMAR FARUQ-1.txt

07 Jul 2024

14076

koɗaya asalima shikeda hakkinta Dan haka nema batare da ya wahalar da kanshin ba yakuma wahalar da lauyoyi,




"Da alkali yafaɗi gaskiyar iya adadin ƙadarorin da maƙudan kuɗaɗan da mahaifinsu yakari, Abba yace aika juya dukiyar ko?...yace eh ankuma samu riba ko?..



"yasake cewa eh to dole har dasu yakafadi aikam kawu muda yafaɗi, sannan abba yabashi sati biyu yahaɗo Kan komai ya amsa da to cike da wani irin tsoron Abba Daya kamashi, aidole abba kam akwai kwarjini da haiba ga kwarewa akan aikin shi.




*Bayan sati daya*
*********
"Aban garen *Beena* da *Blue* kuwa suna cikin rayuwar su me daɗi kwatsam saiga tauraruwa me wutsiya ganinki ba alkairi ba tazo masu, wato aunty *Bebe*,




"Ranan wata lahadi da misalin 11:30am nasafe ta'iso
dukkansu suna part din dad kasan cewar gurin firan su kenan koda yaushe, musamman ranan asabar da lahadin harda *Bulama* ake haɗuwa ayita fira,




*Blue* nan maƙale da *Beena* wacce yakeji kamar yagoyata, dad yana kan kushin zaune yayinda sukuma ke zazzaune akan kafe ita da *Blue* da *Bulama* kan *Blue* yana kan cinyarta, wai sai tayi masa kitse hakan ne yasa take tafaman jagula lallausan gashin da yake cukurkuɗe, sallamar tane nayan boko yakatse su wato excuse me...., *Bulama* he ya amsa da yes come in.




Zumbur *Blue* yamike cike da murna yana faɗin my aunty *Bebe* oyoyo rungumesa tayi tare da faɗin oyoyo my *Bil* boy, cike da murna dad yace *Bebe* kece ba waya dariya tayi tare fadin dad surprise nace zanyi maku *Bulama* yace gaskiya aunty kinyi mana zuwan bazata,




"Zama tayi kusa da dad tana gaida shi *Bulama* ya gaida ita sannan *Beena* tamatso kusa da'ita tana gaida ita, saidai me tana shaƙar kamshin turaren aunty *Bebe* taji zuciyar ta kamar zata fito take taji wani irin amai yazomata da gudu tamike tanufi toilet,




"Amai tadinga kwarawa ba ƙauƙautawa zumbur aunty *Bebe* ta yamike tabita kirjinta yana bugawa cike da tashin hankali, take faɗin meyasa meki?..



Bata iya bata amsaba domin Aman yaci karfinta, cike da fargaba tace sannun Kai ta gyaɗa mata *Blue* ma wanda tuni ya'isa toilet din sai sannun yake zubamata, tare da riƙeta yana sorry cikin ki yana ciwo ne shima Kai ta gyaɗa mashi bayan tagama aman sai ta wanke Baki da fuska sannan *Blue* yarikota suka tafito,




"Aunty *Bebe* na biye dasu zuciyar cike da tunanin meke faruwa dad da *Bulama* dake tsaye suka fasa xuba mata sannu, cike da damuwa dad ya kalleta yace sannun *Beenazar* dama bakida lafiya ne?...




kanta duke tace dad lafiya ta kalau kawai dai naji zuciya ta natashi sai Kuma naji kaita yana sarawa, yace ayya sorry yanzu yakikeji?...tace umh Ina ɗanjin kaina yana cigaba da sarawa Kuma har yanzu inajin tashin zuciyar,




cike da tsoro aunty *Bebe* tace umh! kamar yadaya kikace kinaji?...zatayi magana dad yace ko zaki dubata ne da sauri tace eh dad ok *Beenazar* kuje kiyi mata bayani tace to dad,




"Ɗaki suka shige cikin hikima aunty *Bebe* tayi tama *Beena* tambayoyi inda take tagano tana ɗauke da ciki, wani irin gume ne yakaryo mata cike da tashin hankali tafita inda *Beena* me biye da'ita kirjinta yana bugawa.




Cike da tashi hankali tace dad akwai matsala cikin tsoro yace meya faru?...tace dad ciki take dashi fa ajiyar zuciya yay tare da murmushi yace Kai *Bebe* to mine bin matsala aciki?...




dad cikin fa watan shi hudu da sati biyu Kuma kaga yau dayin bukin wata uku kenan cif kaga kenan bacikin *Bil* boy bane, yace tabbas haka domin jiya mukayi lissafi da *Bulama* ko?...




kai *Bulama* ya gyaɗa cike da fargaba cike da bacin rai yakalli *Beena* wacce gabadaya tagama rikicewa dajin wannan batu yace.....




Muje zuwa




*LUFHAT CE*


🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍


🎍 *_ZAUJUN-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_


🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍


Page3️⃣3️⃣


WRITTEN
By


🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍


OR


🎍 *MEENAT*🎍


Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJUN-MAJNUN_*


SADAUKARWA GA


*_My lovely blood sisters 👩‍❤‍👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi our last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love💋💋💋._*


Littafin nan na kudi ne duk me bukatar zaya iya turo katin MTN na 200 a wannan layin 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi zaku iya ta account no kamar haka 0047769671 Abdullahi Amina gt bank nagode.


_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~


https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/


✍🏼


_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_




"Au kina nufin kina dauke da cikin shege kika yarda aka ɗaurawa ɗana ke?...kai ta girgiza cike da tsananin tsoro...., Da sauri aunty *Bebe* tace karya kike dashi aka ɗaura aini tun farko banso auran nan ba Amma dad yakafe saida akayi aiga irinta nan....,




"cikin bacin rai yace ainayi tsammanin yarinyar kirkice kamilalliya ashe bansani ba shashashace marar kamun kai to kisani ni bazan ɗauki wannan shegen cikin wa ɗana ba....,




saboda haka yanzun nan basai anjima ba kitattara naki danake kibar mun gida kije can kinemi uban shegen cikin ki kinji ko?.... aunty *Bebe* tace dadai yafi kam wato da za'a likawa *Bil* boy tunda anga bashida hankali ko?...




"To Allah yakamaki saiki tashi kitafi can da tsiyarki kinji....,wani irin kuka *Beena* tasaki me cike da tsananin firgita da tsoro wannan bakon al'amari dayazo mata rana tsaka, Shikam *Bulama* wani irin gumi ne yake tsatsufo mashi tako'ina saboda tsananin tsoro gaba daya yashiga confused,




"Shikam *Blue* tunda akafara maganar yake rabon idanu yakalli wannan yakalli wannan domin dai baya fahimtar komai, sai dayaga *Beenan* shi tafashe da kuka sannan cikin damuwa yace sorry my *Beena* friend are sick?...




bata saurare shiba kuka kawai take cike da tashin hankali tace dad aunty *Bebe* me kuke faɗane ni kwata-kwata ban fahimce ku ba...., aunty *Bebe* ce ta harare ta tare da cewa ah! dad kaji y'ar raini hankalin yarinyar nan Waima bata fahimci abinda muke faɗaba?...




"Harara ya zubawa *Beena* cike da bacin rai yace rabu da mara kunya aizata gane,. tsaki mtsww! tayi tare cewa bari naganar da'ita kunnen *Beena* takama tare da cewa ciki! cikin!! dake jikin ki bana *Bil* boy bane kije can kinemi uban shegen cikin ki amma ba ɗan uwana ba kinji....?




Cikin tsananin kuka tace a ah aunty *Bebe* idan har ciki ke gareni to wlh na yah *Bilal* domin bantaba tarayyã dawani ɗa namiji ba idan bashib......,da sauri aunty *Beben* tace karya kikeyi taya za'ayi wanda bayada hankali ya'iya tarayyã aure dake?....




"Dad yace abinda nake tunani kenan...yau kaima kafaɗa, cikin rawar murya *Bulama* yace aunty *Bebe* aɗan sake bincike.... da sauri tace wani irin bincike bayan wanda nayi ko kana nufin bansan aikina bane?..da sauri yace a ah ba hakan bane....,




"To kuma na tambaye ta yaushe rabon dataga period ɗinta tafaɗa nayi lissafi inda yanuna mun da abunta tazo don haka ta tafi can tanemi uban shegen cikin ta, Kai kawai *Bulama* yake gyaɗawa kamar kadangare domin yarasa abuncewa ciki tsawa tace dalla gafa malama tashi kibar mana gida da wannan ƙazantar dake tare dake,




"Zumbur tamike cike da tsabar tsoro tana tsananin kuka tanufi ɗaki yayinda *Blue* yabita wanda tuni yafara kuka ganin yanda takeyi, shi duk atunanin shi batada lafiya ne shiyasa take kukan Dan haka yake cewa sorry my *Beena* friend Kisha magani....




"Akwatin kayanta taɗauko daga kan wedrof tabuɗe tashiga ciro kayanta tana sawa still sai kuka take kirjinta yana bugawa tsoro nasake kamata, yayinda shima *Blue* yake kuka sannan yakoma faɗin inazata pls karta tafi tabarshe batare data saurare shiba tacigaba da zuba kayanta cikin akwatin tana kuka me tsanani,




"Bayan tagama tarufe saita ɗauki hijab ɗinta tasa sannan ta ɗauki wayarta wacce dad yasiya mata tasa cikin jaka bayan tarataya jakar sai taja akwatin tafito yana biye da'ita kamar jela yana faɗin ina zata?...Bata tanka masaba domin kuka yaci karfinta,




Har takai bakin kofa zata fita yana biyeda ita da sauri aunty *Bebe* tarike shi, juyowa yayi cikin kuka me haɗe da shagwaba yace aunty *Bebe* I want to go my *Bebe* friend tace no don't follow her...why?...she is a bad person,




fisge hannun shi yayi tare da faɗin no is not my *Beena* zaya bita dad ya daka masa tsawa hakan yasashi tsayawa jikinshi yana rawa, cikin ɗaga murya come here! da sauri yaje still yana waiwayen *Beena* dake kokarin fita cikin kuka yace pls dad zanje *Beena*,




"Cikin tsawa yace sit down! da sauri ya zauna jikinsa sai karma yake hawaye sai zuba yake tamkar anbude fanfo yana fadin pls dad let me go my "*Beena* friend cike da tsawa yace shut up u mouth dasauri yasa hannu yarufe bakin, *Beena* kam tana tafiya tana garzan kuka har tasamu adai-dai tahau tafaɗa masa inda zaya kaita.




**********
"Kasan cewar akwai kuɗi ahannun ta wanda dad da *Bulama* suke bata wai kozata siya wani abu, shine taciro ajaka tabiya me adai-dai ta sannan taja akwatin tashiga gida still tana me cigada kuka, *Bassam* ne yafara cin karo da'ita ido yazaro cike da tsoro yakaraso gurinta jikinsa har yana rawa cikin rawar murya yace la..fi..ya?...




"Bata iyacewa komai ba saidai tasaki jakar tare da shigewa cikin falo da sauri, inda ta'iske abbu dasu *Bana* zaune zubewa tayi agaban abbun tana garzan kuka gabanshi ne yai mugun faduwa dai-dai lokacin da *Bassam* yashigo hannun shi ɗauke da akwatin,




kallon akwatin yashiga yi tare da *Bassam* din su *Bana* kam tsuru-tsuru sukayi suna kallon yar'uwar tasu datake gunji kuka me taɓa zuciyar me saurare,




"Ɗakin yakai jakar sannan yadawo kallon su *Bana* yayi yace mujen ku waje abbu zayayi magana da aunty *Beena* ahankali suka mike jikin asanyaye zusu feta dukkansu,




"Cikin wani irin murya abbu yace da *Bassam* barsu sufita Kai dawo fito sukayi shikuma yadawo yazauna kusa da *Beena* datake tasharɓan kuka, ta ɗauki tsawon lokaci tana kuka batare datace komai ba hakan yasa cikin sanyi murya *Bassam* yace aunty *Beena* kiyi shuru kifaɗi abinda ke faruwa?..,




Batace komai ba Kuma bata dana kukan ba gyaran murya abbu yayi shiyasa ta sassauta kukan sannan cike da fargaba yace *Beenazar* bari kukan nan haka faɗamun meke faruwa?...




Cikin kuka tace abbu sunce" ne nabar masu gidan, kamar yaya *Beenazar* to auren Kuma fa?...abbu nima bansani ba sun daice wai Cikin dake jikina bana yah *Bilal* bane?...




"Cike da bugawar zuciya yace *Beenazar* kinada cikin ne?...abbu haka sukace" ba hakan sukace ba faɗa mun yaushe rabon dakiga al'adarku ta mata?....kanta ɗuke tace tafaɗa masa,




"Tabbas kina da ciki *Beenazar* alissafi yau watan shi uku kenan har da yan kwanaki wanda yai dai-dai da watan nin auren ki kenan, amma menene dalilin su nacewa ba cikin Shiba ne?...cikin kuka tace nima bansani ba da sauri yace kinsani *Beenazar* wlh abbu bansani ba aunty *Bebe* ce" data dubani tace" haka kai ya girgiza cike da wani irin yanayi,




"yace karya kike kinsani karki manta sudin likitocin ne sun san aikinsu don haka faɗamun *Beenazar* kin kauce daga tarbiyyar damukai maki ko?...cikin tsananin kuka tace wlh abbu ban sakeba idan har akwai ciki ajikina to tabbas na yah *Bilal* ne domin tunda nake ban taba tarayyã da wani ɗa namiji ba idan badashi ba,




"Kai ya girgiza cike da gamsuwa da bayanin ta yace kiyi shuru kibar kukan haka nan tashi kije ɗaki ki huta ahankali tamike jiki asanyaye tashige ɗaki,




*Bassam* ne ya kalli abbu cikin bacin rai yace abbu me wayan nan mutanan suke nufi?...yace bansani ba *Bassam* amma yanzu tashi muje gidan naji tabakin su, da sauri yamike shima yatashi suna fita suka samu abin hawa.




********"
"Suna isa akai masu iso har falon zaune suka iskesu dad aunty *Bebe* da *Bulama* sai ko mutumin ku wato *Blue* wanda yaci kuka yagaji barci yaɗauke shi agurin sai sauke ajiyar zuciya yake gwanin tausayi, bayan sun zauna angaisa wanda *Bulama* ne ya amsa masu fuska asake sabanin dad da aunty *Bebe* da fuskar su take ɗaure,




"Cikin mutunci abbu yace Dr meke faruwa ne naga *Beenazar* tazo gida...cike da bacin rai yace "ita bata faɗamaka abinda yafaru bane?..ito kasan akwai ƙuruciya tare da'ita don haka bayanin natane banfahimce shiba shiyasa, nace bari nazo dakaina nasake jin karin bayanin daga bakin ka...




cike da hasala yace to y'arka ciki ne da'ita kuma bana ɗana bane shiyasa na koreta taje can tanemi uban shegen cikin ta,




"Abbu yace menene hujjar ka nacewa cikin jikinta" bana ɗanka bane?....yace yau wata uku dayin auren su ita kuma da'aka aunata cikinta watan shi hudu, kaga kenan bacikin Shiba ne sannan ma tayaya wanda bada hankali zaya'iya tarayyar aure eye?.. kawai dai tazo ta lika masane sai Allah yakamata,




"Murmushi manya abbu yayi tare da cewa wannan shine hujjar ka?...eh aini wlh bansan cewa "y'arka Bata da tarbiyya ba dabaz....cikin ɗaga murya abbu yace lah!...kai kasan yaniwa "y'ata tarbiyya me kyau wanda shika gani karokeni nabawa ɗanka auran ta, sannan don ɗanka bayada hankali shikenan sai bazaya iya tarayyar aure ba?...




"eh mana, to wannan ba hujja bace tunda yanada rai da lafiyar jiki dole zaya'iya tarayyar aure da mace har yayi mata ciki, don haka tabbas cikin jikin *"Beenazar* nashine domin na tambaye ta tafaɗa mun rabonta daganin al'ada yau wata uku kenan, kuma alissafi yau watansu uku da auren su harma dawasu kwanaki....




"Dakarfi dad yace to nidai wlh bazan ɗaukar wa ɗana wannan cikin ba tunda bana Shiba ne, wani irin murmushi bacin rai abbu yayi tare dacewa to madallah ni na ɗauka tunda sakakyyar dazakai mun kenan ko?....zanyi maka ko zakai mun?...to shikenan yanzu ya matsayin auren shi dake kanta?...yace ai yasaketa saki ɗaya to yayi kyau abani shaida to,




"Wata takarda dake kusada shi nannaɗe yamika mashi, karba abbu yayi tare fadin masha'allah shi *Bilal* ɗin ne dakansa yasaki *Beenazar* ɗin?...ahasale dad yace eh, to aishikenan saidai dr Lawai inasan kasani komin daran daɗewa *GASKIYA* zata bayyana,




cike da masifa yace ta bayyana mana sai me?..to shikenan tashi muje *Bassam* tashi yayi sukafita kamar zaya kurma ihu dan bacin rai,




"A zuciyace *Bassam* yace abbu wlh karya suke da sauri abbu yace kul! nasake jin kace babba yana karya baku kyau, ciki bacin rai yace to abbu amma dai abinda suka faɗa akan "aunty *"Beena* ba gaskiya bane?




wlh ƙazafi sukayi mata itada bata taɓa kula saurayi ba shine zasu ce haka wlh cikin yah *Blue*, Kuma wlh abbu ba yah *Blue* bashi yarubuta takardan sakin nan ba murmushi karfin hali abbu yayi tare fadin karka damu inshallah gaskiya zatayi halinta kai ya girgiza ahaka har suka isa gida,




kiran *Beena* yayi yaita bata baki sannan bai faɗa mata maganar sakinba domin shibawai ya yarda da sakin bane cikin kuka tace abbu yanzu shikenan mun rabu da yah *"Bilal*?....




"Kai ya girgiza cike da tausayin ta domin yasan zuciyar ta cike takeda kaunar minjinta saidai kuma gawata jarabawa da Allah yaƙaddara mata saidai aimata addu'ar allah yabata ikon cinyewa,




yace a ah baku rabuba tunda gakin nan ɗauke da cikin sa don haka ki kwantar da hankalin ki kinji ko?...kaita gyaɗa tare datashi tanufi ɗaki.




**********
*Hakan *Beena* tacigaba da rainon cikin cike da kewar mijinta da tunanin halin dayake ciki narshin ta kusa dashi, wanda ta tabbatar sai yashiga wani hali kamar yanda itama take ciki,




"Sannun ahankali cikin yashiga wata hudu wanda duk wanda yaganta yasan tana ɗauke da cikin domin gaba ɗaya jikinta ya baiyana hakan, gashi yana matukar bata wahala kusan duk abinda taci sai ta amayar ga gawani irin son kamshin turaren *Blue* datakeyi Allah ya taimaketa cikin kayanta tahaɗo dawata singlet dinshi don haka shi take shaka taji daɗi.




********
Aban garen *Blue* kam tsayawa fadin irin halinda yashiga narashin *Beenan* shi akusada shi bata lokaci ne,




"domin ko yayi mugun shiga wani hali duk yarame saboda yanzu aunty *Bebe* tasamu dai-dai din shi tana cigada dayi masa tsafi to hanyar hanashi barci,




kasan cewar yanzu *Beena* batasa mun yimasa ishasshen addu'a kamar da saboda yanayin datake ciki na laulayin ciki don haka idan kaganshi saiya baka tausayi matuka,




" kasan cewar tun bayan faruwar komai washegari sai ta tafida shi can abujar inji cewarta wai har yamanta da *Beena* koda sukaje sai wata muguwar ƙawarta tarkata gurin wani hatsabibin boka yasake burkuce kan *Blue* din,




domin kuwa wasu baƙaƙen aljanun yasake tura masa don haka yasake komawa tantirin majanuni sannan tace da bokan yarufewa dad baki karyasake maganar wata *Beena*, satin *Blue* biyu ta dawowa dashi, tare dabawa peter wani magani yaringa zuba mashi cikin abinci da abin sha don haka komai yasake jagulewa dad duk yashiga wani hali na damuwa.




**********
"Aban garen su ammu kuwa saida kawu muda yaɗauki tsawon sati uku sannan yahaɗa kan komai yakawo, cikin kwarewa abba yaraba kan komai inda ammu ta tashi da gidaje guda biyar da filaye biyu gida uku anan abuja har da guda acikin anguwar su abban,




"Sai biyu acan zariya da filaye biyu sai zunzurutun kuɗaɗe har naira miliyan bayan antabbatar da komai na nan cikin abujan, sannan yasa akaje can zariyan duk akaga komai sannan sai ta dankawa abba komai,




"Yayinda shikuma yasa aka buɗe mata account kazuba kudin sannan suka shirya dukkasu suka nufo Zariya.



******
Ranan lahadi

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login