Showing 15001 words to 18000 words out of 45490 words

Chapter 6 - ZAUJUN MAJNUN by AMEENA UMAR FARUQ-1.txt

07 Jul 2024

14072

tsanani,




Suna nan zaune saiga wasu karatan mutane su hudu sun shigo kallo daya zakai masu, ka kauda kai saboda tsoro domin fuskar su bakikirin babu annuri ko kad'an, yace yauwa nomasi kun iso ko?...




Cikin wata irin murya mara dad'in saurare yace ehhhh! Alh yace kunga wannan?...yafad'i tare da nuna masu Ammu dake zaune tana kallon abinda kawu muda yake kokarinyi, sukace ehhh alh munganta yaza'ai?...yace to tashiga gonata tayimun kane-kane don haka inason kub'atar mun da'ita adoron kasa banason asakejin labarin ko me kama da'ita cikin tashin hankali ta kalle shi tare da cewa.....








Muje zuwa




A




Alkalamin


✍🏼




*_LUFHAT_*


🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍


🎍 *_ZAUJUN-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_


🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍




Page1️⃣7️⃣to1️⃣8️⃣


WRITTEN
By


🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍


OR


🎍 *MEENAT*🎍




Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJUN-MAJNUN_*




SADAUKARWA GA


*_My lovely blood sisters 👩‍❤‍👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi out last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love💋💋💋._*




Littafin nan na kudi ne duk me bukatar zaya iya turo katin MTN ko AIRTEL na 200 a wannan 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi duk zaku iya tuntuban layin sai abaku account no ba nagode.


_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~




https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/




*_FREE PAGE_*




✍🏼


_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_






"Yaya muda me kake nufi?....cikin tsawa yace abinda kikaji haka nake nufi, aina fad'a maki muddun kika sake tako kafarki gidan nan sai nayi maki abinda zakiyi dana sanin sanina arayuwar ki,




don haka nomasi kuyi aikin ku mana dasauri ya amsa da to Alh sannan ya kalli daya daga cikin su yace mugu eye oga, me kake jirane?...aikam kafin duk ammu tayi wani dogon motsi tuni yaciro wani farin kyalle acikin aljihun sa, yasama ta ahanci take tashake sai inda numfashin ta yadauke jikinta yasaki zata fadi,




"Sai yariketa cak yadauke ta yadora akafada daya yadauki jakar ta yayinda sauran biyun suka bisu abaya, cikin bacin rai kawu muda yatashi yanufi ciki yana fad'in aina fad'a maki yayinda Safara'u tabishi, kasan cewar duk abinda yafaru tana zaune agurin,




tace kai! yau kam mun yarda kwallon mangwaro mun huta da k'uda haba "mata sai shegen nacin tsiya kai! haba, ya amsa da to ai yau taga karshen naci.




"Su nomasi kam suna fita da ammu sai suka nufi wata k'atuwar mota me bakin gilas irin wanda naciki yana ganin nawaje yayinda shi kuma nawaje baya ganin naciki, Allah sarki baba megadi yana ganin su yai maza ya'isa gurinsu cike da tashin hankali yace don tsarkin mulkin Allah karku kashe wannan baiwar Allah,




harara nomasi yawatsa masa tare da cewa aiba irinmu ake roko ba domin munan daka ganmu bamayin afuwa ga duk wanda aka bamu kudi mukashe yasen kuwa, da sauri yace to don Allah kuyi mun wannan afuwar badan niba ciki bacin rai yace kai! tsohon nan kafara batamun rai fa,




tsayama tukun ina ruwanka acikin wannan harkan ne?... jikinsa narawa yace d'an nan babu ruwana kawai dai Ina rokon kune saboda tanada iyali ga mijinta bayada lafiya, Cikin bacin rai yace yo mu Ina ruwan mu da'iyalin ta dawani ciwon mijinta eyee?...




kai! yasen tsoho idan baka kwauce ba zan tarwatse maka kainka da wannan bindigar yakareshe fad'i tare da fitoda yar karaman fisto, daga cikin aljihun wandon sa aikam da sauri Baba megadi yamatsa jikinsa sai karma yake da sauri suka bud'e motar suka sata sannan suma su kashiga da sauri, drive yashaga yatad'a motar suka nufi hanyar kofa da sauri baba ya karasa yabud'e masu get suka fita da matsiyacin gudu.




Cikin sanyin jiki yarufe kofar tare da zama abencin sa zuciyar sa cike da tausayi Ammu fili yace allah yasa karsu kashe wannan baiwar Allah, kai jama'a wai meyasa Alh bayada tausayi ne wai ace saboda abin duniya saika halaka d'an'uwanka kai duniya inazaki damu?..




jiyayi ance inda duk kakeso zatakai ka...da sauri yad'aga kai kawu muda yagani tsaye akansa yana huci kamar kumurcin maciji, zubewa kasa baba yayi cikin rawan jiki yace sannun da fitowa Alh cikin masifa yace sannun banza sannun wofi, yanzu nomasi yakirani yake fad'amun abinda kace masu nidama nadad'e Ina zargin kasamun ido alamar na,
konasa ankasheta inaruwan ka eye "yar'uwan kace ko tawa?...




cikin rawan murya me cike da tsoron abinda zaifaru yace takace Alh don Allah kani hakuri ni wlh bantaba saka maka ido alamarin kaba, kawai nidai nace karsu kasheta" to ko ankashe ta ina ruwanka?...wlh baruwana to tashi kabar mun gidana nakoreka daga gadin,




Cikin matsinancin tashin hankali yace don girma Allah kayi hakuri karufa mun asiri wlh Allah ne gatana wannan gadin ne gatana, kasan da haka amma ka tsaya sa ido cikin abinda baishafe kaba don haka tashi kafita kuma wlh kasake kasake shiga sha'anina sainasa ankashe ka,



da sauri yamike yana fad'in Allah yabaka hakuri d'akin gadin yashiga yadauko yar jakar bakon sa yafita jiki asanyaye, cikin bacin rai kawu muda yajuya zuwa cikin gida yanata masifar fad'in mutane basu iya komai ba sai sa'idon jaraba.




Su nomasi kam Koda su kafita hanyar dukko suka bi saida sukayi nisa sannan suka sauka kan titi suka shiga cikin daji tafiya me nisa, sannan suka tsaya suka fito da'ita suka jefar suka ciro jakarta suka zazzage suka dauki wayarta sai suka cire layin suka karya sannan suka yar,




har nomasi zaya halba mata bindiga sai daya yace oga aiba saika harbeta ba domin kuwa tuni naji numfashin ta yad'auke alamar ta mutu yace ok mutafi kawai cikin sauru suka shiga mota suka tafi.




*******


Koda su *Beena* suka dawo basu iske ammu ba sanin indata tafi yasa basu damu ba, saidai itakam *Beena* tarasa meyasa kirjinta yake bugawa sosai gawani irin fargaba datakeji,




Misalin karfe 4:20pm suka shirya suwa Islamiya bayan sun sallami Abbu sannan suka tafi, ko a islamiya *Beena* takasa samun natsuwa har tayiwa yara karatu kamar yanda tasaba saidai abokin koyarwar wanta ne yaimasu, domin gabadaya jitayi zazzabi yana neman rufeta,




suna cikin karatu sai tace don Allah malam saminu idan kanada kudi acikin wayarka kad'an aramun zankira "ammun mu, najiko tadawo ko kuma tana hanya yace Ammun tayi tafiya ne?...eh wlh, Allah sarki Allah yadawo da'ita lafiya amin to gashi karba tayi tare da fad'in yauwa nagode, koda tasa lambar ammu takira saita jita akashe tanata kira amsa daya ake bata hakan yasa taji wani matsananci fad'uwar gaba,



Cikin Dan firgici tace ah! kaji wayar wai akashe yace to ko babu chaji ne?...tace a ah akwai chaji to kila tana gurin da babu sabis ne, eh to kila nan dai tamika masa wayar shi tunda tayi takira baije ba.




Bayan antashi suna cikin tafiya *Bass* yace kila yanzu "ammu tadawo, *Beena* tace eh kilan ko tana hanya eh cike da yarinta *Banu* tace yeeee! ammu na zatadawo dariya sukayi mata ahaka har suka isa anguwarsu,




Saidai koda suka shiga gida basu iske ammu tadawo ba hakan yasa kirjin *Beena* cigaba da bugawa domin dai idan har taje bata" kwana, *Bass* yace ah! kinga bata dawoba to koyau lafiya?...aishi ne to Allah dai yasa lafiya to ameen.




Bayan sun cire kayan islamiya sun sawasu sai itada *Bana* suka d'ora girkin tuwo har suka gama akayi sallah magrib akayi isha'i ammu bata isoba, bayan sun gama cin tuwo suna zazzaune sai *Beena* tace abbu kilan bayau ammu zata dawoba,




"eh to da'alama amma kuma batace mun zata kwana ba eh nima bata fad'amun ba, amma bari naje gurin maman abdul tabani aron wayarta" nakirata naji ko tana hanya ne kilan bata taso dawuri bane ko?...




yace eh hakan zaya iya faruwa ko motar tasamu matsala ahanya ba, eh shidin ne bari naje to sai kindawo *Banu* tace aunty *Beena* zan rakaki tace to zo muje,




koda sukaje takira amsar kenan guda daya wato akashe wayar take hakan yasake fad'ar matada gaba sosai, gashi ita ko kad'an bata tab'a tunanin rike lambar "kawu muda ba balle takirasa domin yana d'aya daga cikin mutanan data tsana arayuwar ta,




haka nan takoma gida tafad'a ma abbu shikansa saida yaji fad'uwar gaba amma bai nuna masuba saidai yace duk yanda akayi kilan sai gobe zata dawo,




shuru *Beena* tayi tsawon wani lokaci sannan tace to Allah yadawo da'ita" goben lafiya, amin suka amsa amma dai haka suka kwana zuciyar su cike dakewar ammun da kuma fargaba musamman *Beena* da abbu, domin wannan shine kara nafarko arayuwar su dazasu kwana batare da'ita ba.




*******
Kamar koda yaushe atsakiyar katafarin falon tulin toys ne watse, sanye yake da riga t-shirt fara me hoton zuciya da wando jeams blue crazy lallausan suma kanshi yasha gyara kamshi sai tashi yake ajikinsa, fatar nan tashi sai sheki take alamar tana samun kulawa yanda yadace,




fuskar nan tashi fayau wanda yake nuna alamar bayada cikkakken lafiya, kwance yake k'asan kafet yayi ruf da ciki kafafunsa asama sai wasa yakeda su hannun sa duka biyu ya tallabe da kyakkyawar fuskarsa me cike da lafiyayyen sajen dayake shan gyara agurin masu kula dashi, yayinda ya kurama t-v ido yana kallon catoon din tony da Jerry sai kyalkyatan dariya yake abinsa *Blue* kenan,




"Gefensa masu kulada shi ne sai kallon sa suke cike da tausayin halin dayake ciki musamman peter, gashi ba musulmi ba amma yanada matukar tausayi tunda d'azu ya gama abincin dare yake fama dashi yazo yaci yakiya, kuma yana jin yinwa tunda rabonsa da abinci tunda rana amma saboda kallon catoon yadauke masa hankali shiyasa,




Daya daga cikin su yace idan bamu kashe catoon din nan bafa bazaya tsaya yaci abincin ba, kuma kusan me gida yakusa dawowa kuma kunsan fad'a zayayi mana yace" mun barmasa yaro dayinwa, daya yace haka ne to idan muka kashe kuma damun mu zayayi da kuka peter yace dole akashe yaci abinci haka akayi,




Aikam ana kashewa yamike zumbur yafara ihu yana shura kafafu saikace yaron da'aka anshe masa mama daga bakinsa, cikin lallashi peter yace yi hakuri me gidana idan kagama cin abinci zan kunna maka kaji?...




shuru yayi yana kallonsu, sai kuma ya makye kafad'ar shi alamar bai yarda ba kai peter ya gyad'a masa tare da cewa nayi maka alkawari dakyar dai suka samu yaci abincin sannan suka kunna masa catoon din yacigaba da kallon sa,




yana cikin kallon sai ga *Bulama* yashigo da sallama hannunsa rikeda jakar aiki da leda, zumbur *Blue* yamike cike da murna yanufe shi yana tsalle kasan cewar tuni yasaba dashi sosai, da sauri *Bulama* ya ajiye kayan hannun sa ya rungume shi suna ta kyalkyata dariya.




Kasan cewar tun bayan da *Bulama* yafara zuwa aiki duk lokacin da yataso daga aikin sai yafara biyowa tanan gidan su *Blue* yakawo masa tarkacen ciye-ciye, sannan yaciro takardu yana nuna masa yace kaga my _guy_ yau anyi kaza munyo odar kaza ansiyar mun kuma samu ribar kaza, anraba nasamaka naka acikin akawun dinka kaji my _guy_




shidai baya fahimtar abinda yake cewa saidai yayi dariya ko yace kai abokina ne ko?....sai *Bulama* yakai gyad'a masa kai wani lokaci kuma sai yafashe da kuka, yayinda shima *Blue* sai yafeshe da kuka dazaran yaga haka sai yayi shuru.




Kamar yanzuma zama sukayi suna kallon juna suna daariya bayan sun nutsu sai *Bulama* yadauko tarkacen daya siyo masa yamika masa, karba yayi yana dariya yabud'e yaciro pizza yafara ci yana kallon sa can kuma sai yadauko jakarsa yaciro takardu yafara nuna masa, saidai yauma ko kallon sa beyi ba,




asalima dariya yake tare da nuna masa t-v wai yakalli catoon wasu hawaye ne masu zafi suka taru acikin idonsa, don haka da sauri yamayar da takardu tare da daukar jakarsa zaya fita da sauri *Blue* yarike masa hannu batare da yakalle saba yace zandawo anjima kaji my _guy_?....




kai ya gyad'a masa sannan yasaki hannu tare da yimasa bye bye, sannan yafita da sauri zuciyar sa cike da tausayi halinda amininsa yake ciki.




"Aban garan mom kuwa duk bayan kwana biyu tana zuwa tagansa, saidai rabanta da gidan tun wani rana datazo ta'iske masu kula da *Blue* sunata damben rikesa saboda wani irin ihu dayake yana rikeda kansa alamar shike damunsa,




Dakyar suka rikesa tayi masa addu'a har yasamu barci sannan ta tafi gida tana kuka wanda tun ranan ne batasake zuwa ganinsa ba, domin bayan kwana biyu da komawar ta sai zazzabi yarufeta yanzu haka sai ankwantar sai antayar abin zan mamaki domin kuwa magani ake kamar ba'ayi,




Itama aunty bebe duk bayan kwana biyu sai tazo ganin *Blue* duk lokacin dazata tafi da kuka haka dai abin yaketa tafiya.




*_Bayan kwana biyu_*


*****
Su *Beena* kam hankalin su yagama tashi ganin har yau kwana biyu ammu bata dawoba don haka suka yanke shawarar *Beena* tabita tagani ko lafiya, tunda ko ankira layin ta baya zuwa don haka sai taje gurin maman abdul tabata aron dubu biyu dama akwai dari biyar da akabata kudin wata, *Bass* ma yabata dari biyar da ogansa yabashi saita had'a dashi takama hanyar abuja.




"koda ta'isa batasha wahala ba tunda dama tasan anguwan don haka ta hau tasi yakaita, bayan tabiya shi kudinsa sai tanufi get din gidan tana turawa taji kofar arufe don haka sai tafara kwankwasa wa,




sabon me gadi ne yazo yabud'e fuska had'e yace lafiya ke wacece?...saida tagaida shi sannan tace sunana *Beenazeer* nazo daga zariya ne ni d'iyar kanwar me "gidan na ce ba tare da yace komai ba yabud'e mata tashiga,




"Da sallama tashiga falon kirjinta yana bugawa cikin sa'a ta'iske kawu muda zaune shida Safara'u suna ganinta suka kalli juna cike da munafurci tace a ah lale maraba yau *Beenazeer* ce agidan namu?...,




murmushin karfin hali tayi tare da zaunawa kirjita yana cigaba da matsananci bugawa tace eh nice aunty Ina wuni lafiya lau, kawu Ina wuni yace lafiya lau ya mutanan gida?.. tace lafiya lau, yauwa ya'akayi ne?...tace umh! kawu dama munji Ammu shuru ne shine abbu yace" nabiyo ta ko lafiya yace kina nufin Fatima?.tace eh yayinda kirjita yake masifar bukawa yace tun yausheta wuto nan din?..




cikin fargaba tace tun shekaran jiya, kai! aiko batazo ba Safara'u ko kinganta"?...a ah banganta ba ido *Beena* tazaro cike da matsananci tsoro tace.....






Muje zuwa




✍🏼



Alkalamin


✍🏼


*_LUFHAT_*
🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍


🎍 *_ZAUJUN-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_


🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍




Page1️⃣9️⃣to2️⃣0️⃣


WRITTEN
By


🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍


OR


🎍 *MEENAT*🎍




Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJUN-MAJNUN_*




SADAUKARWA GA


*_My lovely blood sisters 👩‍❤‍👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi out last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love💋💋💋._*




Littafin nan na kudi ne duk me bukatar zaya iya turo katin MTN ko AIRTEL na 200 a wannan 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi duk zaku iya tuntuban layin sai abaku account no ba nagode.


_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~




https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/




*_FREE PAGE_*




✍🏼


_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_






Kawu batazo bafa kuka ce?...eh mana yo karya zamuyi maki?... hannu ta yarfar tare dafa kirji ta furta innalillahi! wlh kawu ammun mu tun shekaran jiya tabaro gida kuma nan tace zatazo, don Allah kawu idan wasa kake kabari wlh kirjina zaya iya tar watsewa dajin wannan wasan,




Cikin tsawa yace ke! nataba wasa dake ne koni abokin wasanki ne dazanyi maki wasa eye?...ance maki batazo ba batazo ba ko idan tazo zamu boye tane eye?...,kai ta girgiza yayinda jikinta yake mugun rawa bugun kirjin ta yatsanan ta wanda bayada misali, cikin rawar murya tace yanzu kawu da gaske kake ammun mu bata zo nan ba?...




Wani lafiyayyen mari yasakar mata akan kyakkyawar fuskar ta ido tarinte, ciki masifa yace ke! dan uwarki da ubanki karya zanyi maki nace karya zan maki eye?...,ke! Dan ubanki tashi kibar mun gida "uwarki kikazo nema ko?..to batazo ba, don haka tashi ko nayi mugun saba maki kinji ko?...




Ahankali ta bud'e idon wani irin duhu tagani amma haka ta mikewa jikinta sai karma yake, tadauki jakarta taku daya ana biyu ta zube kasa sume.




Zumbur Safara'u tamike tare dafadin mun shiga uku Alh kar yarinyar nan tamutu mana agidafa...tsaki yayi mtw! tare da fad'in ko ta mutu babu abinda za'ayi, cike da tsoro tace a ah alh garadai karta mutu mana anan ta kareshe fadi tare da fara girgiza *Beena* tana cewa ke! *Beenazeer!* ke! *Beenazeer!!*




shuru bata motsa ba hakan yasa tace Alh mun shiga uku tamutu fa, tsaki yasake tare da fad'in suma tayi ki dauko ruwa kizuba mata ta tashi tabar mana gida kinaji ko?...to, Da sauri taje ta dauko ruwa afirj in ta yayyafa mata ta dauki lokaci kafin ta farfad'o bakinta dauke da salati,




"Ahankali tamike zaune tare da dafa kai tayi shuru kawu yace ke! da sauri tad'aga kai ta kalle sa yace tashi ki koma inda kikafito domin dai "uwarki batazo nan ba kinji ko?.. kuka ta fashe dashi tare dafadin don Allah kawu kanemo mana "Ammun mu wlh bata gida, cikin tsawa yace ke! Dan ubanki nizan nemo maki ita nasan inda takene?...




cikin rawar murya tace a..a...h! Ina nufin kasa anemo mana ita don Allah, yace bazan saba tunda batazo nan ba idan kuma tazo to bansan gidan ubanda ta tafi ba balle nasa anemo ta, don haka tashi kitafi ga kudin mota kije kifad'ama

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login