Showing 30001 words to 33000 words out of 45490 words
sarkin tausayi da saurin kuka tuni tafara rerawa ahankali ba tare da kowa yasani ba, yayinda kuma kirjinta yake cigaba da matsananci bugawa can kuma sai *Blue* yasaki dad yaje yarungume *Bulama* yana dariya tare da faɗin abokina, cike da farinciki yace yeṣ my guy we miss you alot ashe kana nan ko?...
cike da farinciki ya gyada masa Kai, sai Kuma *Blue* din yasaki *Bulama* tare da kallon shi sannan yakalli dad sai kuma ya kwaɓe fuska, Cikin turanci haɗe da shagwaɓa _kamar dai yanda dai yara suke_ yace baruwana daku kuma bazan sake yimaku magana ba tunda kuka tafi kuka barni da saurin dad ya juyo daṣhi, yayinda *Bulama* yarike masa hannu sukace yi hakuri bazamu sake barika ba kaji,
Shuru yayi kamar yana nazarin maganar dazaya faɗa, can kuma sai yai dariya tare da faɗin really?..sukace yes tsalle yayi tare faɗin yeeeee! dad see my *Beena* friend yafaɗi yana kokarin riko hannun ta da sauri ta tura hannun ta cikin hijab,
tare da gyara zama tace da dad sannu ina yini?...
cike da farinciki yace yauwa lafiya lau yakukaji da rigimar boy murmushi tayi, nan suma su *Bass* suka gaida shi ya amsa cike da tsananin murna,
"Abbu yace dasu ku zauna mana sannan suka zauna sai alokacin *Blue* yaga peter cike da dariya yace u?..
Cikin farinciki yace yes is me my oga dariya yayi tare da rike hannun sa cike da shagwaɓa yace barka barni Kuma cikin girmamawa haɗe da russunawa yace I promise my boss dariya akayi, bayan sun sake gaisawa sai abbu yasake koroma dad bayani,
"inda yakaransa dacewa kagansu nan y'ay'an nawa wannan ce babba sunanta *Beenazir* mutumiyar *Blue* kenan, sannan wannan haka yaita faɗa masa sunayen su cike da farinciki dad yakalli *Blue* dake nanike kusada *Beena,* yace alh usman nagode nagode kwarai da gaske allah yasaka da alkhairi allah ya'albarkaci zuri'arka,
abbu yace amin ba komai aiyiwa kaine kaga yanzu haka bamusan inda "matata uwar ya'yana take ba, nan abbu yafaɗa masa komai akan ɓatan "ammu wanda daga zuwa abuja gurin "yayanta shikenan batadawo garesuba cike da tausaya masu yace Allah yabai yanata suka amsa da ami, abbu yace shin yasunan yayan su *Beenazir* din ne domin dasuka tmyshi sai yace masu *Blue* ne sunan sa,
"Dariya dad yayi tare da kallon *Blue* din dayaga hankalinsa gabaɗaya yana kan *Beenazir* wacce tun da akace masa yafi yarda da'ita yaji ta kwanta masa arai, yace sunansa *Bilal* abokansa ke kiransa da *Blue* wato Bilal Lawal Usman abbu yai dariya tare cewa Allah sarki bawon Allah, yabashi lfiya amin amma kuna nemar masa maganin addini kuwa?..
batare da dad yafahimci abbu ba, yace anayi sosai makuwa yanzu haka akanyin sama ake yace to allah yasa adace, amin amin nan sukafara taɓa fira kamar sunsan juna har abbu yana faɗamasa sanadin rashin lafiyar kafafunsa aikam ya tausaya masa matuka nandai sukayi tafira sosai,
"Sannan kalli agogon hannun sa yaga karfe 10:00pm yace alh Usman zamu tafi nagode sosa yakarasa faɗi tare da mikewa to Dr Lawal saida safe, da sauri *Blue* maya mike ya'isa gurin dad ya rungumesa murmushi dad yayi tare da kallon shi yace mutafi gida ko?...
"Kai ya gyaɗa yana dariya sai kuma yasaki dad din yaje gurin *Beena,* zaya riko hannun ta da sauri tamike gabanta nafaɗuwa cikin rawar murya tace yah *Bilal* menene?…cikin turo baki yace dad say mutafi gida ido ta zaro cike da tsoro tace......
Muje zuwa
Tareda
✍🏼
*_LUFHAT CE_*
🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍
🎍 *_ZAUJUN-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_
🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍
Page2️⃣6️⃣
WRITTEN
By
🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍
OR
🎍 *MEENAT*🎍
Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJUN-MAJNUN_*
SADAUKARWA GA
*_My lovely blood sisters 👩❤👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi our last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love💋💋💋._*
Littafin nan na kudi ne duk me bukatar zaya iya turo katin MTN na 200 a wannan layin 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi zaku iya ta account no kamar haka 0047769671 Abdullahi Amina gt bank nagode.
_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/
✍🏼
_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_
"A ah! badani ba fa so kutafi, kallon dad yayi tare da taɓe baki cikin turanci yace dad kace mata mutafi gida,
murmushi yayi tare da karasawa gurin shi ahankali yarike hannun sa tare da rungumo kafaɗarsa yace a ah yarona bada "ita zamu tafiba, kai ya girgiza tare da barin jikin dad din yaje gurin *Beena* cike da rigima yace pls my *Beena* mutafi,
"Cikin rawar murya tace no yah *Bilal* katafi kaga dad yana jiranka kaji?...kafaɗa ya makale alamar shi bazaya ba idan bada ita ba, wasa-wasa *Blue* yatubuer shi bazaya tafiba saida *Beena* gashe anyi tsaye anajiran shi su tafi amma yakiya,
"kawai saima yafashe da kuka har da buga kafa yana faɗin pls my *Beena* friend mutafi gida, jikinta ne yadauki rawa dama kirjinta sai lugudan bugawa yake, idonta tuni yacika da hawaye muryar ta yana rawa tace pls yah *Bilal* abokina katafi mana kaji?..,
kafaɗa ya maƙale tare da zuwa gurin *Bulama* yafaɗa kirjinsa cikin kuka sosai yace masa wai yace ma *Beena* tazo sutafi, rungumesa yayi cike da tausayi halin da abokinsa yakeci cikin lallashi yace to yayi shuru yadaina kukan bari yaimta magana.
"Dad Kam gaba ɗaya hankalinsa yatashi har bai iyacewa komai ba, abbu Kam Kai ya girgiza aransa Kuma yana faɗin dama yasan za'arina irin wannan shaƙuwa dole ranan rabuwa sai haka tafaru, balle dama
mahaukaci rabasa da abunda yasabu dashi wahala ne,
"Gyaran murya abbu yayi inda duk aka ka kallesa banda *Blue* dayake tasharban kuka kallon shi abbun yayi cike da tausayin halin dayake ciki, cigar lallashi yace haba yayan *Beenazar* babban yaro kayi shuru haka nan badai *Beena* tabika kutafi gidan ku ba?..Kai ya gyaɗa yana turo baki yana kallon *Beena*, to zataje kai mansur yace na'ma abbu kutafi kurakasu dakai da *Bassam* da'ita *Beenazar* din kunga sai kuga gida saboda watara na ko?...
"yace to abbu aihakan yayi wani sanyayyan ajiyar zuciya dad yayi, yayinda abbu yace yauwa nasan kuna zuwa bada daɗewa ba, yayan *Beenazar* zayayi barci kodan wannan kuka dayayi ko ba haka bama lokacin barcinsa yakusa, kunga sai kudawo ba tare da wata rigimar tasa ta motsaba bako?....yakarashe faɗi tare da murmushi akan fuskarsa,
hakan yasa duk akai dariya banda *Blue* dayake ta turo baki dama ita *Beena* tuni ta balle da kuka ajiyar zuciya *Bass* yayi domin tuni Shima yafarajin kewar *Blue* tunma kafin yatafi, sai Kuma yakalli *Beena* dake sharban kuka murmushi yayi sannan,
yamaida kallon sakan *Blue* cike da tsokar dayake masa yace kai yah *Bilal* ashe daman Kai karamin yaro shiyasa make ta kuka, to aigashi nan itama aunt *Beena* dinka tana kuka,
"Dasauri yakaran sa gurin ta yana leken fuskasta datake boyewa da hijab cikin kuka haɗe da shagwaɓa, yace my *Beena* friend ninasa ki kuka?..dagowa tayi fuskar ta sharban da hawaye cike da shagwaɓa tace eh bakaima kana kukan ba, dasauri yace to sorry kidai kuka nima nadaina kinji kuma aikice ni big boy ne ko?..
"kaita gyaɗa masa to kicewa *Bass* friend yadaina cemun karamin yaro kinji?..still kai tasake gyɗawa to tare zamu tafi ko?.. ahankali tace "eh cike da murna yace yeeeee! tare da zuwa gurin dad yace dad my *Beena* friend cikeda murna yace tace zataje?..
kai ya gyaɗa yana dariya sai kuma yaje guri *Bulama* shima yana faɗa masa, dariya shima yayi tare da cewa to mutafi d sauri yakoma gurin *Beena* cikin tsananin murna ya kalleta alokacin tashare hawayen ta harda murmushi akan kyakkawar fuskakar ta,
yace less go my *Beena* friend ahankali tace ok am coming let me talk to abbu, gurin abbun taje taduka cikin ladabi tace abbu zamuje sai mun dawo, yace to kudawo lafiya sannan duk suka fita harda su *Bash* don suraka *Blue* kofar gida yayinda yaketa murna kamar zaya dauki *Beena* don farinciki.
"Akofar gida kam saida ta tsorata dagani tsala-tsalan motoci dasu dad sukazo dasu, mota ɗaya suka shiga da ita da *Blue* da dad dakuma *Bulama*, dayar kuma masu tsarone da *Bass* baban abdul da peter suka nufi gidan su *Blue*.
*******
Tsoron *Beena* yakaru lokacin dataga sun shiga katafaran gidansu *Blue*, bayan sun fito mota sai suka nufi cikin falon nanma saida *Beena* ta tsorata matuka, zama sukayi *Blue* yana like da'ita yana dariyar farinciki gashi tare da *Beena* shi, sai zubamata surutu yake wani tana fahimta wani Kam bata fahimta,
dasauri yajeya kwaso mata tedy dinsa yana dariya tareda nuna mata tedy, dad kam cike da farin ciki yake sake yiwa su *Beena* godiya sannan yasa akacika masu gavansu dakayan motsa baki, sannan yaɗaga waya yafara Kiran yan'uwa yana faɗama su anga *Blue* sunata murna,
"Aunty *Bebe* ce kawai be samu wayarta ba harda ta mijinta don haka sai yabari saida safe yakirasu yafaɗa masu.
Yayinda *Bass* yake taba *Bulama* labarin irin abubuwan da *Blue* yayimasu, wani yai dariya wani Kuma ya girgiza kai cike da tausayin halin da abokisa yake ciki, daga nan kuma sai firar kwallon kafa tabarke tsakani baban abdul da *Bulama* da *Bass* kasan cewar dukkansu ma'abota son kwallon kafane,
Sosai suke firansu kamar dama can sunsan juna yayinda cikin wasa *Blue* yaketa jifan *Beena* da tedy cike da jin kunyar dad take fakar idonsa tarama, ahankali wani lokacin ma Bata ramawa saidai tayi dariya ko murmushi ko tace stop it ahankali shikuma sai yamaƙe kafaɗa alamar yaƙiya,
"Ahaka har lokacin yaja basu saniba tuni *Blue* bawan allah yaɓingire akan kafet yai barci kusada *Beena* yana rungume da tedy akirjinsu,
"Sai dad ne yakalli agogon falon inda yanuna karfe 11:15pm sannan yakalli tarkacen da'aka ajiya musu basuci komai ba murmushi yayi aransa ya yabada tarbiyyar yaran matuka, yace son katsaresu" da tafira gashi har basuci komai ba dariya *Bulama* yayi tare da cewa wlh kuwa dad,
Mlm mansur kuci wani abumana saiku tafi ko?...dad yace gaskiya yakamata kuɗanci ko kaɗan ne sai kutafi gida saboda dare yafara dasauri *Beena* tamike da'alama dama atakure take,
Suma mikewa sukai baban abdul yanacewa wlh alh akoshe muke, yace to peter kazuba masu aleda sutafi dashi yace to ogo bayan yayi yanda dad yace sai yabasu *Bass* yakarba,
Sannan suka fito rakasu dad yanata sakeyi masu godiya sannan yasa direba yakaisu bayan yacema baban abdul yazo gobe karfe 11:00am nasafe yanason ganinsa, yace to sannan suka koma cikin don yau nan *Bulama* zaya kwana.
*_Washer gari_*
*****
Tunda gari yawaye
*Blue* yake neman *Beena* duk yazagaye gidan yana faɗin my *Beena* friend where are you?....bai ganta ba hakan yasa ya zauna yana aikin rigimar kuka,
"gaba ɗaya hankalin dad da *Bulama* yatashi, domin sunyi lallashi yaƙi yaishuru har d aunty *Bebe* dayakira yafaɗa mata anga *Blue* cike da farin ciki tace" abashi wayar amma yaƙi karba shidai *Beena* kawai yakeson gani, ko breakfast yaƙi yayi balle Kuma yai wanka har 9:00am nasafe gashi dad yanata kiran layin baban abdul be samu ba, sai da kyar yasamu ajiyar zuciya yayi bayan sun gaisa sai yake faɗa masa rigimar da *Blue* yake tason ganin *Beena* yace allah sarki shaƙuwa ce yace eh don Allah yakaima *Beenazar* wayar,
yace to tare dazuwa yakai mata cikin ladabi ta gaida shi harda russunawa kamar yana gabanta nan yafaɗa mata rigimar da *Blue* yace, cike da tausayi tace dad "yabashi wayar bashi yayi tare cewa boy ga *Beena* friend dasauri jikinsa har yana kyarma yakarba yana turo baki,
"Cikin kuka yace my *Beena* friend am angry with you kuma baran kara yimaki magana ba yafaɗi yana turo baki haɗe da shasshekar kuka, ahankali tace am so sorry kaji yah *Bilal* abokina?..
"Cike da shagwaɓa yace yes to kina ina?..kuma inata nemanki pls come to me i want to see cikin tsananin tausayin sa tace to zanzo, amma saikayi shuru kadaina kuka dasauri yashare hawaye da bayan hannu tare da cewa to nadaina,
yauwa my *Billo* abokina to kayi breakfast sannan kayi wanka kasa kaya masu kyau kafin nazo kaji?...cike da farinciki yace really?...yes, yace yeeee! pls come soon tace to kabawa dad wayar, dasauri yabashi cike da murna yace dad my *Beena* friend is coming cikin murna yace really?....yace yes tare da nufar dinning table, kai dad ya girgiza suka haɗa ido da *Bulama* cikin sanyi muryar yace dad gaskiya my _guy_ sun shaƙu sosai da *"Beena* din nan,
yace sosai ma kuwa ni abun har yafara bani tsoro gashi tace" masa zatazo, to yanzu da kaske zatazon?...to bari mugani wlh banason jin kukan boy ko kaɗan wlh dad konima sannan suka nufi gurin breakfast din domin basuyi ba suma saboda rigimar *Blue*.
*_Abuja_*
*****
Aban garen ammu kam tunsuna saran tunani ta zayadawa harsun fitarda rai don haka sai rayuwar ta take abinta hankalita kwance acikin ahalin alkali *sasu* tayi ƙiba tayi kyau abinta sosai suka shaƙuda ita musamman *Basma,*
Kamar yanzu ma *Basma* ce da gudu tashiga dakin ammu tana faɗin ummana kina inane?..dai-dai lokacin da ammun tafito daga bayi da'alama wanka tafito domin kanta rufe yake da tawul,
"Gungume ammun tayi tana juyida ita atakar daki cike da farinciki tace ummana albishirin ki?...cikin dariya tace goro *Basmati* umma Amma daina juyi dani haka karki kadani, zama sukayi abakin gado suna dariya,
sannan tace Abba yace idan nacinye jarbawata dukka zaya kaini alhikimat school tace kai madallah makarntar nan dakike so ko?.. tace eh kai amma najidaɗi sosai, tace ummana kiyimun addu'a kinda yau mungama jarabawa guda saura guda Allah yasa nacinye duka,
tace inshallah dukka *Basmati* umma zataciye jarabawa tace Allah yasa ummana amin sannan ammu ta tashirya cikin riga da zani nawata jar atamfa, sai kunganta tayi kyau abinta daga nan kuma suka fita falo akafara fira kamar yanda suka Saba har da alkali *sasu* kasan cewar yau asabar ba'aiki don haka yana gida.
********
Wata dalleliyar baƙar motace take shiga wani surƙuƙin bakin dajin da babu gida gabas da yamma kudu to balle arewa, gudu mota take sosai wanda dagani tasaba shiga cikin dajin saida tayi tafiya me matukar nisa sannan ta tsaya,
"Ɗan nesa kaɗan dawata yar bukka datake lulluɓe da bakin yadi da ja bukkar ita kadaice kwanƙil acikin daji bayan ankashe motar sannan aka fito, macece sanye takeda wani tsaddan materiya yalo da ratsin ja ɗinkin riga da siket irin me tsagan baya din nan banga fuskarta ba saboda tarufe da mayafi tamkar yanda amare keyi,
"tafiya tafarayi ahaka saida ta kusa isa gurin bukkan sannan ta tsaya tacire takalmi, da mayafi da ɗankwali da riga da siket ya kasance dai tayi tsirara, _wa'iyazubillah!_ sannan ta kalli gabas yamma kudu alokacin da tajuyo baya zata kalli arewa naga fuskarta, ido nazaro cike da tsananin tsoro ganin ko wacece......
*_Shin reades wacece?_....*
Muje zuwa
Tareda
✍🏼
*_LUFHAT CE_*
🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍
🎍 *_ZAUJUN-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_
🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍
Page2️⃣7️⃣
WRITTEN
By
🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍
OR
🎍 *MEENAT*🎍
Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJUN-MAJNUN_*
SADAUKARWA GA
*_My lovely blood sisters 👩❤👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi our last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love💋💋💋._*
Littafin nan na kudi ne duk me bukatar zaya iya turo katin MTN na 200 a wannan layin 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi zaku iya ta account no kamar haka 0047769671 Abdullahi Amina gt bank nagode.
_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/
✍🏼
_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_
"Aunty *Bebe* ce ya ilahee! juyawa tayi tabaya tashiga cikin bukkar tsirara! tsirara!! tsirara!!! wa'iyazubillahi!,
"Cikin wata kakkausan murya akace sannu da zuwa b'atattaciya asararriya sallamammiya me fuska biyu inji cewar wani bakin munannan mutun, kazami marakyan gani dake zaune tsirara wanda koba afadama kaba kallo Daya zakayi Masa kagane boka ne,
Domin kuwa jikinsa duk daure yake da layu bakake da jajaye ta kota'ina, haka dakin tarkace ne da yadangacin tsafe tsafe da tsubbuce-tubbuce, wani irin zama tayi agabansa me cike da takaici da bakin ciki amatsayinta na yar muslumai,
"domin kuwa gaba daya tabude kafafunta yayinda idon bakin bokan yake kan tsiyarcinta sai faman lasar Baki yake kamar tsohon maye, cikin karaji tace yauwa sannu boka me aljanu me biyan bukata dungu yakarasa mata dafadin mugun hannu wanda yajira taimakon ka yayi asara,
(kujifa masu karatu sannan har mutun ya yarda da haka saboda batar basira da toshewar kwakwalwa Allah kaganar damasu aikata haka gaskiya mukuma karabamu aikata haka ameen,)
"Cikin kakkausan murya me cike da bacin rai yace meke tafeda ke awannan lokacin ne?...wanda kinsan bana sauraran mutane acikinsa, cikin kaskantar da kai tace aljani yahuci zuciyar boka me biyan bukata.... hankalina ne atashe shiyasa nazo ba lokacin zuwaba...., cikin tsawa yace inajiiki meke tafeda ke?....
cikin bacin rai tace "boka anganshi" boka meyasa kabarshi nan kusa meyasa baka turasa" uwa duniya ba yajecan ya mutu...tunda kai kaki kasheshi....boka nafada maka natsaneshi" banasanshi...boka nafada maka duk duniya shine mutumin dana tsana dashi da "uwarsa bok.....
tsawa yadoka mata sai kuma yasaki wata mahaukaciyar dariya maradadin sauti sannan yahad'e fuska ciki kakkausan murya yace ke!, ɓatattaciya aciki ayyukan dakika sa'akai maki wani bukatarki bata biya ba?...tace babu dakika ce akashe shi tun farko me nace maki?....
tace aljani yace" bazaya iyakashe "Saba saidai ya haukatar dashe...cikin bacin