Showing 6001 words to 9000 words out of 45490 words
daya ba domin Aunty Bebe tanada shekara 8 aduniya ciwon kansar mahaifa yakashe mahaifiyar ta me suna Hafsatu, bayan shekara daya da rasuwar ta sai Dad ya auri mahaifiyar *Bilal* me suna Hauwa wacce take shuwa arab ce kyakkawa ce, suma asalin su yan boko ne sosai sannan sunada kudi.
Dad yana matukar son Hauwa domin tanayi masa biyayya sosai kusan duk, abinda yakeso tanaso saidai ra'ayin su yasha bambam kad'an,
Dad yanada akidar boko sosai komai nasa na boko ne itama tanada shi saidai shi yafita, amma kuma duk da haka basa fad'a akan bambamcin ra'ayi, saidan kaji fadan su akan *Bilal* domin tun da aka haife shi bata sake haihuwa ba hakan be damu Dad ba tunda dama shi bayada ra'ayin tara yara dayawa,
don haka yadauki so da kaunar duniya yad'ora akan *Bilal* sosai yake matukar son shi bayason abinda zaya bata masa rai ko kad'an, hakan yasa duk abinda *Bilal* yakeso shi yakeyi shiyasa yatashi shagwababb'e domin Dad yabashi gata sosai,
wanda hakan shike hadasu fad'a da Mom dinsa kuma idan tana koya masa akidar gargajiya tareda ta addini sam Dad bayaso amma duk da haka saida ta matsa ya sauke al'qur'an yakuma sannan wasu littafain addini,
Tun *Bilal* yana yaro suke rigima akan haka har ya girma ba adaina ba wanda shine dalilin rabuwar su,
Saidai tunda suka rabu ba wanda yayi aure cikin su har yanzu, tun *Bilal* yana secondary har yayi digren nafarko akan pharmacy wanda ra'ayin Dad ne, inda yaje chana yayi digren sa na biyu akan business administration Wanda ra'ayin sa ne wannan dawowar su kenan, wannan bakon al'amari yafaru dashi wanda bamusan komene ba amma dai bari mubisu asannun muji.
*BUHARI TAHIR BULAMA* shine cikkakken sunan shi sai abokan suna kiran shi *Bulama* kawai,
D'a ne ga papa wato *Barrister* Tahir Bulama asalin su mutanen barno ne tajahar meduguri aiki ne yakawo sa zaria,
Shidin kuma babban Lawyer ne me zaman kanshi shima d'an boko ne sosai saidai bashida ra'ayi irin na Dad,
Aminaine sosai shida Dad tun suna makaranta har yanzu, papa d'an sa kenan kwara daya wato *Buhari* wanda suka haifa tare da matar sa me suna Falmata.
*Blue* da *Bulama* suma aminan juna ne sosai tun suna yara tare sukai karatu tun daga primary har degree saidai shi *Bulama* law yayi a degree farko Wanda shima ya'ayin papa ne, domin duk suna San yaransu su gajesu sai degree na biyu shine yayi business administration shima ra'ayin sakenan,
Don haka kusan ra'ayinsu daya nason akidar boko shida *Blue* saidai halinsu yasha bambam, *Blue* ya kasance dan gaye miskili ne sosai ya'iya daukar wanka don haka yanada mutukar tsabta ga masifar kyankyami bakomai keyi masa ba,
yanada mugun high test yana kuma matukar kyamar zina shiyasa yake gudun yanmata don gudun afka mata, yayinda su kuma suke mugun son shi sosai suke bibiyar sa amma baya kulasu ko kad'an basa gaban sa.
Shima *Bulama* yana da tsabta sosai Dan gaye ne ya'iya daukar wanka kamar *Blue,* saidai shikam mutun ne me barkwanci sannan yana kula yanmata sosai shima yana kyamar zina saidai yana buga soyayyar shan minti da su, wannan kenan.
*Cigaba*
******
Su Dad kam basu tsaya ko'ina ba sai anguwar tudun jukum duk dacewa Dad shima yanada gida anguwar amma beyi nufin shigaba saidai kawai aka sauke su *Bulama* ,
Sannan yanufi gidan shi dake anguwar kwarbai suka nufa wani tsararran gida suka shiga bayan me gadi yabude masu get, bayan driver yabude masa kofa yafito direct yanufi cikin gidan yayinda escorts din sa sukabi shi abaya dauke da tarkacen *Blue*.
Masha'allah wani tsararran falo suka shiga wanda yasha blue and white din labule, gawasu manya manya set din kushin masu asalin kyau dasuka zagaye falon suma blue and white ne kai gaskiya falon ya tsaru wanda tsayawa fadin tsaruwasa bata lokacine,
Bayan escorts sun ajiye kayan sai suka fita yayinda Dad yashiga bedroom be dad'e ba yafiti sanye da jallabiya fara hannun sa dauke da wayoyi, wani table yanufa me dauke da manya manyan littafain,
zama yayi akan kujeran dake gaban talble din tare da ajiye wayoyi sannan yabude wani babban littafi,
Dai-dai lokacin da wani me aiki yashigo cikin girmamawa yaduk'a yace wlcm Sir....yace yauwa peter yace Sir u need something?..
yace no peter I want to be alone ok Sir" yajuya yafita dai-dai lokacin da daya daga cikin wayoyin sa tayi kara, ganin sunan daya bayyana akan wayar ne yasa yai murmurshi be dauka ba saidai yayi receive tare da bud'e kara,
Ajiyar zuciya akayi tukun kafin ace thank God Dad me yake faruwa ne tun d'azu nake kiran layin *Bil boy* be dauka ba kaima haka I hope dai lafiya?.
yace hum! Bebe ba lafiya, cikin tashin hankali tace oh! God Dad me yafaru?....nan yafad'a Mata abinda yafaru da *Blue*.
Kuka tasaki cikin tashin hankali tace Dad meya same shi haka?... yace I don't know saidai wata maganar banza inji Dr I B wai yana gani kamar aljanu ne suka "shafe sa, da sauri takatse shi dafad'in na Lia Dad don't trust, tsaki yayi yace is big lia makuwa so how can't I trust?..
cikin kuka sosai tace Dad yanzu meye abinyi?...yace sai "yafarka tukun munga yanayi jikin nasa tukun if bawani cigaba zanfita dashi waje, yanzuma zand'anyi wani bincike ne so karki damu ki kwantar da hankaliki everything will be ok,
tace ok Dad I will come tomorrow morning zanbiyo jirgi, ok sannan takashe waya shima ya'aji tasa tare da fara reseach.
*Abuja*
******
Ammu kam ta'isa Abuja lafiya cikin yardan Ubangiji direct gidan Kawu Muda tanufa dake garki, bayabo ba fallasa Safara'u ta tarbeta bayan sun gaisa sai tasa aka kawo mata ruwa da abinci saidai ba taciba saboda bakinta dauke yake da azumi,
Sannan Aunty Safara'u yaya Muda yana nan kuwa?....cikin had'e fuska tace lafiya murmurshi Ammu tayi tare da cewa lafiyar nazo ne akan maganar gadona, tsaki tayi tare dacewa wai ke Fatima meyasa bakigane karatun ne?....
tace aibazan taba ganewa ba muddun ba'abani hakkina ba, tace to yace bazaya bayar ba don haka sai kiyi hakuri amma kinnace sai kace maiyya, gaskiya kin takura wa rayuwar mu eheee! ta karesa fad'i tare da girgiza jiki,
Still murmushi Ammu ta sakeyi tace aikune kuka takurawa rayuwata dai-dai, lokacin da Kawu Muda yafito yanacin magani, zama yayi kuda Safara'u yana me ballawa Ammu harara cikin masifa yace wai hardama abinci ki kabata?..fuska tayamutse tare da fad'in eh badan halinta ba,
harara yasake watsama Ammu sannan yace malama lafiya?...tace lafiyar kenan nazone karban gadona don Allah yaya Muda kayiwa girman Allah kabani hakkina, wlh inacikin wani hali kasani "mijina bayada lafiya yau kimani shekara uku kenan, yarana sai sai korosu ake daga makaranta,
Yaud'in nanma suje ankoro su.
Cike da masifa yace to Ina ruwana da halin da ku keciki kuma mutu mana ba abinda yadameni, gado ne nace bazan bayar ba, don haka kitashi maza kibarmun gidana konayi maki mummuna rashin mutunci kinji ko?....
kuma kika sake tako kafarki ciki gidan nan narantse sai yani maki abinda harki mutu bazaki manta ba,
cikin tsananin mamaki ta kalle sa tare da cewa.....
Muje zuwa
*LUFHAT CE*✍🏼
🎍🎍🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍
🎍
🎍 *_ZAUJUN-MAJNUN_*🎍
_(miji mahaukaci)_
🎍
🎍🎍
🎍🎍🎍
🎍🎍🎍🎍
Page9️⃣to🔟
WRITTEN
By
🎍 *AMEENA UMAR FARUQ*🎍
OR
🎍 *MEENAT*🎍
Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now👇🏽
*_ZAUJUN-MAJNUN_*
SADAUKARWA GA
*_My lovely blood sisters 👩❤👩Hadiza (aunty)and Nana Firdausi out last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love💋💋💋._*
Littafin nan na kudi ne duk me bukatar zaya iya turo katin MTN ko AIRTEL na 200 a wannan 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi duk zaku iya tuntuban layin sai abaku account no ba nagode.
_____________________________
® _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~
https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/
*_FREE PAGE_*
✍🏼
_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_
Rarashin mutuncin ka kam aiba bakon abune agurina ba, kuma kasani bazan daina zuwa gidan ba har sai kabani hakkina,
Cike da masifa yace haka kikace ko?...eh ke! wai bakizuwa ki kwaci hakkin naki eye?..tace aidan kasan bazan iya kwata bane shiyasa kake kokarin danne mani hakkina Oho! to aisaiki kyale ni dashi, wlh bazan kyale kaba sai kabani hakkina.... to kira akwatar maki mana,
Murmushi tayi wanda yafi kuka ciwo sannan tace babu wanda zankira ya kwatar mani sai Allah wanda kullun nake kai masa kuka na, kuma nasan inshallah zaya sharemun hawaye ya kwatar mun.
Tsaki yayi tare da mikewa cikin b'acin rai me had'e da masifa kamar zaya rufeta da duka yace tashi ki barmun gida, konayi maki dukan tsiya yanzu na cike da mamaki tace dukafa kace yaya Muda?...eh ko kinfi karfin dukan ne ko kuma kina ganin bazan iya dukan ki ba?....
kaita girgiza yayinda idonta yacika da hawaye zuciyar ta cike da bakin ciki tace tabbas, ayanzu kam nawuce duka saidai agurin azzalumi irinka banwuce ba, cikin tsananin bala'i yace ke! Dan ubanki nine azzalumi?....
Itama cikin tsananin b'acin rai tamike tare da fad'in eh kaine azzalumi mugu macuc.....bata karasa ba yadauke ta da lafiyayyan mari, dasauri tarike kumatu tana me kallon shi cike da mamaki yayinda shi kuma sai hura hanci yake.
Yace wlh idan baki fita harkata ba sai nayi maki fiyeda haka, ke! abinda zanyi maki nan gabama sai
kinsha mamaki sai kinyi danasani sanina arayuwar ki, don haka fitarmun agida ko yanzu nasa afitar dake dakarfin tsiya....
Cikin kuka tadauki Jakarta sannan tace aiko bakace ba zanfita ne kuma Allah saiya saka mani akan zalunta tadakai, kuma wlh saina nadawo kabani hakkina kozaka kasheni oh! Ko ?..eh tafadi taname karasa kaiwa bakin kofar fita,
yace ok to muzuba dani da ke shege kafasa kisake dawowa din kiga abinda zanyi maki, sannan yanufi ciki rai b'ace yayinda Safara'u ta tashi tabishi tana cewa yauwa kayi mana magani me shegen nacin tsiya Mata saikace mayya.
******
Ammu kam datafita saida ta tsaya bakin get taci kuka takoshi wanda dama tasaba yin haka aduk lokacin da taje gurin Kawun Muda suka rabu baranbaran, yayinda dattijo Baba megadi yakeba ta hakuri cikin tausaya mata kamar koda yaushe idan tazo,
murmushi tayi me cike da bakin ciki sannan tamike tana goge hawaye da bayan hijab dinta, tare da cewa nagode Baba nizan tafi dasauri yace y'ata sake dawowa zakiyi?...tace eh Baba dole saina dawo, yace to ga wannan yafadi yanasa hannu acikin aljihun gabar rigar sa yaciro kudi nara dubu guda yace to yata karbi kikara kiyi kudin mota kinji?...
yakarasa cikin tausaya mata, shuru tayi tana kallon kudin tsawon lokaci tana tunanin itada yakamata tabashi sai shine zaya bata kai! yaya Muda yazalince ta kuma sai Allah yasaka mata yakwatar mata hakkin ta, cikin katse mata tunani yace karbi mana yata,
Murmushi tayi tare da duk'awa takarba tana fad'in nagode Baba Allah yasaka da alkhairi yabani ikon saka makada abinda kayi mun, yace bakomai Allah yayi maki albarka yashige maki gaba adukkan al'amuran ki yakuma albarkaci zuri'ar tace amin ki sauka lafiya to Sannan ta tafi taxi ta tare tare da fada mashi yakaita tasha.
Sai da yamma lis Ammu ta'isa zaria duk tagaji saboda azumin datake fauke dashi ga kuma gajiyar tafiyar mota, don haka agajiye tashiga gida duk su *Beena* suna tsakiyar falon zazzaune dasauri suka mike suna fad'i sannun dazuwa Ammu tace yauwa *Bash* yakarbi jakarta yayinda *Banu* taje ta rungumeta tare da fad'in Ammu danatashi bacci banganki ba,
Murmushi karfin hali tayi tare da fad'in gani nadawo my *Banu* kije gurin su Aunty kijirani bari naga "Abbun ku kinji?..kaita gyada tare da komawa gurin su ita kuma tashga d'akin Abbu.
Yayinda *Beena* tabi bayanta da kallo kirjinta yana bugawa ganin yanda idon Ammun yayi jajir alamar tasha kuka, ahankali ta zauna yayinda taji tausayin Ammun su yakamata har taji kuka nashirin kwace mata, hakan ne yasata tashi dasauri tashige daki
tafada kangado
Tana wani irin kuka me cike da tausayin halin da suke ciki wanda duk "Kawu Muda shine silar shigansu, haka yasa tasakejin tsanar shi yasake samun gurin zama acikin zuciyar ta, Saida tayi kuka me isarta sannan ta tashi tashiga toilet tawanke fuska sannan tafita takoma falo gurin yan'uwanta.
Ammu nashiga tayi tsaye kad'an daga inda Abbu yake tare da tsura masa idonta dayacika da kwalla shid'inma itayake kallo, zuciyar sa tana wani irin bugawa wanda yake tabbatar masa yauma babu nasara kamar ko dayaushe,
Cikin sanyi murya yace sannun da dawowa Fatima ta uwar ya'ya'na farin cikin na karaso gareni, ahankali takarasa kusada shi tazube tare da fad'awa kan kirjinsa, tafashe dawani irin kuka me taba zuciyar me sauraro, ido Abbu yarintse domin jin kuka har cikin zuciyar sa.
Ahankali yadago hannunsa nadama yad'ora akan bayanta yana shafawa alamar lallashi ba tareda yace komai ba,
Saida taci kukanta sannan tayi shuru ciki sanyi murya yace ni nasan yaya muda bayada ninyar baki hakkin ki ne, don inda yanada ninyar baki da tuni yabaki don haka kiyi hakuri ki kyale shi, dasauri tadago ta kallesa tace bazan kyale shiba kaduba kaga halinda muke ciki shine zan kyalesa?...lallai bazan iya kyale "saba har sai yabani hakkina,
Wanda inaji ajikina zaya bani saidai kafin yabani zansha wuya, don haka zanjure duk wuyar har sai nakarbi hakkina fatana kacigaba datayani da addu'a,
Cikin sanyi murya yace inshallah bazan fasaba Allah yad'oraki akansai tace amin, sannun yajiki?.... murmushi yayi tare da fad'in da bakinan sai jikin yayi zafi sosai amma dakika dawo sai yayi sanyi, kinga hakan yana nufin ked'in sanyi nace don haka dan Allah kiyi hakuri karki gujeni wlh idan ki kabarni bansan inda zansa rayuwata ba kinga banida kowa sai Allah saike da y'ay'an mu, cikin dan bacin rai tace taya zanguje ka?....acikin wannan halin saikace wacce batada digon imani acikin zuciyar ta?...
To ma idan na gujeka inazani tunda nima banida kowa daga Allah sai kai da yaranmu, don haka kabar irin wannan tunani gaskiya ni banason irin wannan maganar tafadi tana me kauda kai gefe.
Ahankali yajuyo dakanta gurinshi cikin sanyi murya yace yi hakuri Fatima ta karkiyi fushi dani, wani lokacin nikanji tsoro ne saina gakamar hakan zaya iyafaruwa, tace bazaya faruba har abada ta kareshe fad'i dai-dai lokacin da aka fara kiran sallah magrib,
Shuru sukayi suna bin kiran sallar azuciyar su har aka gama sukayi addu'a tare da shafawa sannan yace to tashi kije kisha ruwa kiyi sallah nima bari nayi yakaresa fad'i tare da daukan dutsen dayake taimama dashi, tace to tare da tashi tafita.
*Washegari*
*********
Tun 7:30am Dad ya'isa asibiti kasan cewar ranan bayada duty dare don haka kusan kwana yayi yana bincike, tare dayin waya asibitin don jin yajikin *Blue* yake, inda suka tabbatar masa baifarka ba har lokacin sai yau tunda 6:00am,
Tukun na aka kirashi akace masa yafarka saidai still yanata fisge-fisge, wani abin mamaki ansakeyi masa alluran koya sake komawa bacci Amma ko gyangyad'i bai kamashi ba balle bacci duk yafita hayyacinsa gwanin tausayi,
Hakan yasa suka saka masa ankwa kafa da hannu sannan suka maida daki suka kulle gudun karya fito.
Koda aka bud'ema Dad dakin yashiga mamaki ne yarufe shi nagani yanda aka hada yaronsa dagado aka daure kafa da hannu tamkar hauka sabon kamu, cikin masifa ya kalli nurse din tare da ballamasa harara yace wannan wani irin walakanci ne?...
yaron nawa zaku daure da ankwa saikace mad ko kun bincika kunga ya haukace ne?..
yace Sir wallahi bai bada damar ayi bincike ba saidai ya nayinsa yanuna kamar kwakwalwar sa ta tab'u, cikin tsawa yace keep quiet! jo,
Malam zoka kunce mun yaro kaji ko?.. dasauri yace Ok Sir yaje yafara kokarin kwance masa hannuwa, shikam *Blue* yana gani Dad yasaki wani irin mahaukacin kuka me cike da tsabar shagwabar da ko yaro dan shekara uku albarka, hannun yamikawa Dad tare da sake b'are baki yasaki wani kukan dayasa Dad saurin karasawa gurin shi,
kirjinsa yana wani irin halbawa saboda tsananin tsoro daya ziyarce sa alokaci daya, nagani wannan sabon al'amari dayasamu yaron sa.
Rungume shi yayi akirjinsa dake matsananci bugawa, ahankali yasa hannun sa yanashafa masa lallausan gashin kansa cikin rawar murya me cike da tsoro yace it'.....s O.....k m.....y bo.....y, fadamun inayake maka ciwo?...
beyi shurun ba kamar yanda Dad yabukata balle yabasa amsa tambayar dayayi masa, asalima sake b'are baki yayi yana wani sabon kukan har sheshshaka wanda yasa Dad sake tsorata tare da fad'awa cikin tunani.
Tabbas yasan yaronsa shagwab'abb'e ne saidai kuma aishid'in jarumine Wanda duk wahala abu bayayi masa kuka amma yau meke faruwa ne?...yake irin wannan kuka haka kamar wanda ake yankan naman jikinsa,
Dasauri yaduba hannun *Blue* aikam abuga fari gurin da'akasa masa ankwa duk yayi jajir, ayya no wonder yake wannan kukan kuce dama sokukai ku kashemun shi ji hannunsa fa haba wannan wani irin zalinci ne haka eye?....yace sorry Sir wlh munyi iya kokarin mu don yatsaya amma yakiya shiyasa muka yanke hukuncin dauresa, yace Ok yayi kyau yi shuru my boy kaji?...
Cikin wani irin muryar da Dad be tabasanin shi da'ita ba yace Dad I want to go home now, cike da tsoron Dad ya kallesa tare da tab'a wuyan sa yace boy what's wrong with you voice?....,baki yasake b'arewa tare da buga kafa cikin shagwaba yace Dad I say i want to go home now, dasauri yace ok tashi mutafi, tashi yayi yana me sake kwakume Dad tamkar wanda za'akama.
"Sir zaka tafi dashi ne kuma?...eh kar ku kashemun shi abanza, "Sir yana bukatar good treatment fa, yace zanyi masa ko kamanta Ubansa Dr ne?... No "Sir ok to bani hanya da sauri yamatsa suka fita, drive yana ganin su yabude masu mota suka shiga yaje yaja suka nufi gida.
Suna isa gida direct main falo suka nufa dashigar su *Blue* yasaki Dad tare da buga wani irin tsalle yafada saman kushin, yadauki pillow yafara jefasa sama yana chab'ewa yana dariya me had'e da ihu irin dai idan yaro yasamu abinda yaimasa dad'in, chan kuma sai
yatashi zumbu yasake fad'awa saman wani kushin d'in,
yadauki pillow