Showing 24001 words to 27000 words out of 45490 words

Chapter 9 - ZAUJUN MAJNUN by AMEENA UMAR FARUQ-1.txt

07 Jul 2024

14071

iya tun da Allah yahad'a mu dashi,




Dasauri taja hannun *Bana* suka shige tana waiwaye *Blue* daketa sharban kuka tamkar wanda ake yankan naman jikinsa yayinda *Bash* yabisu.




Ahankali *Bass* yakalle sa cike da tausayi gadai mutun kam har mutun amma ba hankali, murmushi yayi masa tare da cewa abokina kayi shuru kabar kukan haka nan kaga mu bamusan gidanku k da dad din kaba,




saidai idan zaka zauna agidanmu har agano gidaku bin shuru yayi yana kallon *Bass* din da'alama be fahimce abinda b yafabida ba, don haka cikin harshe turanci yace zaka zauna gidanmu har agano gidan ku?..kai ya gyad'a masa alamar eh to zomuje sannan suka shiga gida nan yana biye dashi.




Bakinsu dauke da sallama suka shiga falon wanda kusan tare da su *Beena* suka shiga, kasan cewa Saida ta tsaya tashare hawaye tukun, bayan abbu ya amsa sallamar sannan suka zazzauna kamar yanda suka saba shima *Blue* zama yayi idonsa akan *Beena,*




sukace sannu abbu ya amsa da yauwa kundawo? eh abbu anyimana hutu masha'allah bako mukayi ne?.. *Bass* yace eh to amma nan yafadawa abbu duk abinda yafaru tundaga gurin me awara har zuwa yanzu, cike tausayi abbu yace ikon allah to abbu yanzu saboda Allah me hankali ne zayayi haka?...yace a ah kam bawon allah har yabani tausayi gashi dai mutun har mutun gacikar Kamala amma ba hankali wlh kuwa abbu, oh allah sarki ko dan wanene?...




yace Allah masani gashi tabarakalla mekyau dashi abbu shine aunty *Beena* tace wai aljani ne dariya yayi yace aikasan ita sarkin tsoro ce, cikin sanyi murya tace to abbu aini tsoro yabani daga taimako yabiyo mu sannan daga tmbyrs saifaman kuka yake kamar karamin yaro har da kokarin rikemun hijab fa yayi yace dad kuma sai faman kallo na yake, murmushi abbu yayi yace saboda kece kika kwacesa ahannun me awara,




baki ta tab'e tare da satan kallon *Blue* din wanda shidinma kallonta yake da sauri tace abbu kalli ko yanzuma sai kallona yake, dariya yayi yace to *Beena* yana kallon kine amatsayin wacce ta taimaka masa tarabasa da fitinar me awara, kallon *Blue* tayi cikin sa'a shima ya kalleta tare da sakar mata dariya cikin turanci yace ke abokina ne ko?...ido tazaro cike da tsoro tace Kai abbu kajisa ko?..




Aaikam mesu *Bass* da abbu zasuyi idan ba dariya ba shima *Blue* dariyan yayi tare da kallon *Bass* yace and u ko?..cikin turanci yace yes dukkan mu abokanan kane ni suna *Bassam* ita kuma *Beenazeer* wannan *Banafja, Bashir, Banuja* wannan kuma abbu kaifa ya sunan ka?...dariya yayi tare cewa *Blue,* cike da mamaki *Bass* yace *Blue* ne sunan ka?...




kai ya gyad'a masa yace ikon Allah blue kam ai kalo ne ko?..to shiken tunda yace" sunan sa kenan sai muringa Kiransa yah *Blue* ko?..abbu yace hakan yayi domin girmama babba abune me kyau ko manyan mu sunce bin nagaba bin Allah don haka akoda yaushe nake horonku da kuringa girmama nagaba daku banda rashin kunya kunji ko?..




sukace to abbu inshallah zamu kiyaye, sannan *Bass* ya kalli *Blue* yace aikanaso mukiraka yah *Blue* ko?..Kai ya gyada yana dariya, cike da mamaki *Beena* tace wai Kai *Bass*
zama zamuyi dashine?..yace eh Mana har mugano gidansu ko abbu?...




yace gaskiya ne don idaรฑ mukabarshi yatafi bamusan hannun wa zaya fad'a ba cikin sanyin murya *Beena* tace haka ne kuma fa, suna cikin haka aka Kira sallar magriba abbu yace to kutashi kuje kuyi sallah suka Mike dukkansu har da *Blue* daketa faman yiwa *Beena* dariya yana fadin u are my friend (ke abokiya na ce)




Dariya tayi tace yes aikam har da tsalle murna dariya sukayi dukkan su harda abbu, sannan suka fita su uku zuwa masallaci
*Blue Bass Bash* sukuma su *Beena* suka shiga daki don yin nasu sallah.




*******


Aban garen dad kam idan hankalin sa yakai miliyon to yatashi narashin ganin liton dansa Wanda besan awani Hali yakeba, gashi bayada lafiya cikin tashin hankali yakira *Bulama* da aunty *Bebe* yafada masu aikam hankalinsu yatashi sosai,




Aunty *Bebe* sai kuka take tana fadin Allah yasa agansa, cikin lokaci kankani *Bulama* yabaro gurin aiki ya'iso shi kad'ai kasan cewar "papa baya kasar yaje UK yinwani Kos na shekara daya.




fad'a *Bulama* yafarayi da megadi da kuma peter musamman me gadi shidake da hakkin kulada masu shiga da be fita, dama su masu kula da *Blue* din yafara zargin kamar basu kulawa dashi dakyau saboda dรบk yaga yarame cikin kuka peter yace yallabai wlh basu kulawa dashi" dakyau asalima cutansa" suke sosai,




cike da mamaki dad da *Bulama* suka kallesa sukace shine baka tab'a fad'a Mana ba?..yace suyi hakuri cewa "sukayi idan yafada sai sun kashesu shida *"Blue* shiyasa be tab'a fad'aba saboda yana tsoron karsu kashe su,




Cikin tsananin bacin rai dad yakira shugaban yansanda yace suyi ta dukan yaran dasuka tafi dasu har sai sun fadi inda yaronsa yake sukace angama.


*****
*_Bayan sati daya_*


Har tsawon kwana biyu ba *Blue* ba labarin sa hankalin dad da *Bulama* yatashi sosai dad harda zazzabi, aunty *Bebe* tazo hankalinta atashe sai kuka take kwanan biyu da yini dad yace ta tafi gida takula da mijinta da yaranta inshallah za'agansa,




abu kamar wasa har kimanin sati daya duk cigiyan da'ake na *Blue* ba'aganshi ba dad da *Bulama* duk sun rame saboda tashin hankali na rashin sanin halinda yake.




*_Abuja_*
*****
Abangaren ammu Kam ta warke garas tasaba sosai da iyalin alkali sasu musamman *Basma*


sun shaku sosai da ammu wacce take kirada umman ta kasan cewar idan tadawo makarntar boko batazuwa ko'ina don haka suna tare hakama idan tadawo islamiya saita shige d'akin ammun tayi tabata labarai na kawayan ta,




saidai kuma har yanzu wannan lokacin tunaninta be dawoba gashi lokaci sai Kara tafiya yake duk alkali sasu yadamu matuka,




shi tunanin sa besan halinda yan'uwanta suke ciki ba.




Aban garen Kawu Muda kuwa ba abinda yadame sa tun ranan dayasa aka salwantar da ammu besake tunanin taba,



daga shi har matarsa hankalin su kwance sukecin duniyarsa da tsinke batare da tunani baiwar Allah da halinda iyalanta suke ciki ba.




*_Zariya_*
*****
Abagaren *Blue* Kam hankalin sa akwance cikin su *Beena* cikin sati daya yayi matukar sabo dasu sosai kasan cewar yanzu sunyi hutun makarantar islamiya, gashi maman abdul tayi tafiya don haka *Beena* da *Bana* da *Banu* suna gida basazuwa ko'ina don haka suka shak'u matuka,




yanzu kam ya'iya wasu abubuwan dakuma fahimtar su wayanda ada sam be iyaba kuma baya fahimtar su irisu magana da hausa dakuma fahimtar abinda ake nufi, da sakaya duk yanzu ya'iya dakansa sabanin da sai antayasa sakawa, haka sunaye mutane ma yanzu duk ya'iya kiran sunayen su *Beena* musamman ma *Beena* wacce duk cikinsu yafi shakuwa da'ita sosai yake shige Mata komai takeyi sai yace shima zayayi,




ita kuma Bata cikason haka ba saboda kwarjini yake mata sosai gashi har yanzu idan yakura Mata ido, gabanta fad'uwa yake gashi takula ba'abinda yakeso irin yatasata agaba yayita kallo,




idan taga yayi haka sai tafuske tace yah *Blue* meyasa kake kallona haka sai yayi dariyar sa me matukar burgewa, sannan yace u are my best friend *Beena* sai tayi dariya itama tace masa kamar yanda yace Mata.




kasan cewar yanzu batajin tsoron sa bakamar farko had'uwar suba saidai kam yanzu wani irin mugun tausayinsa takeji musamman idan ya tafka wani abin kam tuni zaka fahimce tabbas bayada hankalika, don haka sai tashiga daki ita kad'ai tayita kuka tana rokon Allah yabasa lafiya,




Kasan cewar tunda "maman abdul tayi tafiya sai baban Abdul yanayo masu chefane har dashi idan sukayi sai su zuba masa, tunda shidin ba ma'abocin cin abinci siya awaje bane don haka kullun cikin yin girki suke me kyau domin baban Abdul mutunne Dan galari bayacin cimar banza so yanzu basuda matsalar abinci kokad'an, saidai matsalar rashin ammu wannan Kam sunbarwa allah ikonsa,




don haka balaifi azahiri sunyi kyau abinsu haka idan kukaga *Blue* shima yayi kyau abinsa saboda hankali sa akwance yake, (kodaya ke dama komai cin dad'in da mutun yake idan hankalin sa ba akwance yake ba to bazaya tabayin kyau ba).






_*Kuyi hakuri don Allah koda kunga typing error banajin dad'i ne amma banan naso tsayaw ba*_






Muje zuwa






Tareda




โœ๐Ÿผ




*_LUFHAT_*


๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ


๐ŸŽ *_ZAUJUN-MAJNUN_*๐ŸŽ
_(miji mahaukaci)_


๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ
๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ๐ŸŽ




Page2๏ธโƒฃ4๏ธโƒฃ


WRITTEN
By


๐ŸŽ *AMEENA UMAR FARUQ*๐ŸŽ


OR


๐ŸŽ *MEENAT*๐ŸŽ




Marubuciyar
*_DA SANNU_*
*_ZUCIYATA CE_*
*_AFSANA_*
*_KYAUTAR ALLAH CE_*
and now๐Ÿ‘‡๐Ÿฝ
*_ZAUJUN-MAJNUN_*




SADAUKARWA GA


*_My lovely blood sisters ๐Ÿ‘ฉโ€โคโ€๐Ÿ‘ฉHadiza (aunty)and Nana Firdausi our last bornnn, do u know what? sisters humm l really love love love yous irin babu adadin nan fa so muchhhhh love๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹๐Ÿ’‹._*




Littafin nan na kudi ne duk me bukatar zaya iya turo katin MTN na 200 a wannan layin 08161850024, idan kuma tresfa zakuyi zaku iya ta account no kamar haka 0047769671 Abdullahi Amina gt bank nagode.


_____________________________
ยฎ _PEN : WRITERS ASSOCIATION_
_______________________________
~_only the exquisite and whizkid writers are opportune to be pen writers_~




https://www.facebook.com/groups/1061983803858837/










โœ๐Ÿผ


_*Bismilahirrahamaniraheem!!!*_








"Haka abin yake agurin *Blue* alokacin da yake gidan su cikin daula me tarin yawa duk sai yarame saboda bayada kwanciyar hankali agurin masu kulawa dashi,



sai gashi yanzu baya cikin daula amma hankalin sa kwance wandan haka yasa yanzu bayada damuwa ko tsoron wani,saidai yana yawan Kiran dad da aboki da aunty *Bebe* wanda haka yanuna ma su *Beena* cewa sudin mutane ne masu matukar mahimmanci arayuwar sa,




haka saurin kukan nan duk yadaina domin dazaran yakwab'e fuska zayayi sai *Beena* tayi saurin ce masa Oh! yah *Blue* abokina karkayi kuka bakasan kai babban yaro bane?...kuma shi babban yaro ai baya saurin kuka,




"Kaga shima *Bass* baya saurin kuka kuma kafisa babba so kaima kadai na to datace masa haka sai yafasa yakama dariya yana fadin yes ni babban yaro ne kuma ni abakin ki ne ko?..sai itama tayi dariya tace eh mana, sannan fanin surura bashida matsalar su domin tun ranan dayazo gidan dayai wanka sai yaki maida wannan kayan nasa da yacire,






"dasuka fadawa abbu sai yai murmushi yace da'alama idan yai wanka baya maida kayan, to suduba cikin kayansa suciro masa riga da wando tunda ai kayansa zasuyi masa haka
nan akayi suka ciro masa suka bashi yasa aikam yanata murna da dariya,




har yana nunawa *Beena* tace aikam sunyi maka kyau don haka tundaga sannan yake saka kayan abbun, haka zalika tuni baban abdul yasan da zama *Blue* agidan kasan cewar wani lokaci idan yakawo masu chefane yana shiga yagaida, abbu don haka ranan da yashiga yaga *Blue* sai yake cewa sunyi bako ne?...






abbu yafad'a masa abinda yafaru aikam shima ya tausaya wa *Blue* matku wannan kenan.



"Yau lahadi Wanda yai dai-dai da kwanan *Blue* takwas agidan su *Beena*, kuma yausu *Bass* basuje gurin aiki ba saboda zasuyi wanki kasan cewar dama aduk lokacin da kayansu yai datti sai sukwaso kayan su hadu duk su wanke, don haka yauma haka ne sai sukwaso zasu wanke sun kusa gama wankin kenan sai ga *Blue* yafito kasan cewar dama yana ciki yana barci,




Kai tsaye gurin *Beena* yanufa wacce take kokarin yin dauraya kawai sai duk'a yasa hannunsa cikin bokitin aikam da sauri ta dago Kai sakamakon numfashin sa daya bugi fuskarta yayinda hancinta ya shaki mayatatcen turaransa wanda yau kimanin kwana takwas kenan Amma har yanzu bai bar jikinsa ba,




Cikin fad'uwar gaba tace wash! yah *Blue* me zakayi?...cike da shagwab'a cikin muryarsa me yanayin barci yace umhm!! wannan abin, murmushi tayi sannan tace wanki sunansa ba wannan abin ba zaka tayani ne?..




murmushi yayi me kayatarwa tareda gyad'a Kai alamar eh, itama murmushi tayi tare da fadin to nagode kaje ka zauna ka huta abindama nagama kagafa d'aurayewa kawai zanyi nashanya, badon yasoba yakoma gefe ya zauna yana aikin kallonta yana dariya da murmushi.




"Bayan sun gama sai suka dora girkin ranan wanda dama tuni baban abdul yakawo musu chefane, dafadukan shinkafa da manja sukayi wanda yaji alaiyahu da busasshan kifi bayan sun gama sunci,




"sai suka kwaso kayansu da suka wanke suna ninkewa ana cirewa kowa nasa har da *Blue* shima yana ninkewa, saidai bai iya ninkewa dakyau ba don haka sai su *Bana* nayi masa dariya kallon *Beena* yayi yana kwab'e fuska tare da tabe baki kamar zayayi kuka,




"yanda dai karamin yaro yake idan anyi Masa abundan beso, da sauri tace kyale su yah *Blue* abokina kaji kawo nagyara maka kaji?..dariya yayi tare da mika mata da sauri karba tayi taninke dakyau sannan tabashi tace kaga haka akeyi to ajiye sai kaninke wani ko?...




"Dariya yayi yace yes u are my *Beena* friend, haka suke rayuwar su gwanin sha'awa kamar wayanda suka shekara takwas ba, kwana takwas ba.




*_Bayan kwana biyu_*
*****
Ranan jumma'a wanda yai da-dai da kwanan *Blue* goma gidan su *Beena*, da misalin karfe 8:30pm nadare alokacin sun
*Beena* suna zaune adakin abbu suna fira abinsu gwanin sha'awa,



"kasan cewar haka sukeyi dazaran sun ci abincin sunyi sallar isha'i, sai aje dakin abbu azauna ayita fira inda rabin firan duk shirmen *Blue* suke saurare suyi ta dariya har da shi domin idan yayi wani abin ko bakaso sai kayi dariya, saidai idan yaga dariyar tayi yawa Wanda dama su *bana* da *Bash* da *Banu* ne keyi masa dariyar sosai,




"don haa sai ya kwabe fuska tare da turo baki yana kallon *Beena* alamar dai kai karansu, don haka sai tace subari sannan gashi komai zayayi sai *Beena* tace yayi sannan yayi idanma na barine saitace yabari sannan,




"Kamar yanzu kallonta yayi yana b'ata fuska tare da rike ciki da sauri cikin tsoro tace meya faru yah *Blue* abokina ko cikinka yana ciwo ne?...,kai ya girgiza to mene?...cikin turanci yace kashi, aikam me zasuyi ba dariya ba har da ita da abbu baki yaturo tace sorry yah *Blue* abokina kyalesu tashi kaje kayi da sauri yashi yashige dakin su *Bass* wanda dama nan suke kwana,




Cike da tausayi abbu yace allah sarki idan ba laluran tabin hankali yana tareda mutum ba tayaza ayi yai haka?...yaron Nan yana bani tausayi matuka har nakanyi tunanin menene dalilin tab'in hankalinsa,




cikin muryar tausayi *Beena* tace wlh abbu koni ma haka
nake tunani wani lokaci har tunanina yanabani wata kila haka aka haifesa, *Bass* yace konima haka nakanyi tunani har nace to ko asiri akayi masa sai Kuma nayi saurin kawar da hakan domin zato ne shikuma zunubi be bayada kyau,




"Abbu ya girgiza Kai tare da fadin haka ne saidai bana tunanin dashi aka haifesa" saidai ko idan daga baya yasamesa, koda yake nibansan gaibi ba allah shine masani dalilin wannan tab'in hankalin nasa koma dai mene allah yabasa lafiya suka amsa da amin,




sannan kuma kucigaba dayin addu'ar danace kudingayi ta'idan "ammun ku tana araye allah yatsareta"daga dukkan abinki, yakuma bayyana mana ita cikin amincinsa sannan "Shima kuringa yimasa addu'a samun lafiya kunji ko?...cikin sanyin jiki sukace to abbu, suna haka sai gashi yafito yana sauke numfashi tareda daure zariyan wando zama yayi kusa da *Beena* yana kallonta yana murmushi dama gurin zamansa kenan kusada ita,




yace my *Beena* friend i do it tace ok sannan sukaci gabada firansu me cike da nishad'i,




Sai ga baban abdul yashiga dakin da sallama tamkar anjefosa, cikin sauri yace abbu kaga yanzu nake sauraran labarai sai naji ana cigiyar *Blue* ance don Allah duk wanda yagansa,




yataimaka yasadashi da mahaifinsa Dr Lawal usman
ta hanyar kira wannan lambar, kaganta abbu har na dauka shine nace bari nakawo akirasa asanar Masa yanan,




Abbu yace kai masha'allah naji dad'i kwarar da gaske damanasan duk inda yan'uwan sa "suke sunacen suna ne mansa cikin damuwa darashin sanin inda zaya fada tunda ba hankali yakeda Shiba,




yace wlh kuwa abbu aiko me lafiya dole adamu yanzun baga "ammu ba Allah kadai yasan inda take tana araye ko amace ko tafad'a hannu nagari ko akasin haka, duk Allah ne masani Kai abbu ya girgiza cike da wani abu aransa yace haka ne to kakira sai asanar masu, yace to tare da Kiran lambar cikin sa'a tashiga tafara kara har ta tsinke ba'a dauka ba,




Saida yasake kira sannan aka daga yai sallama bayan gaisu sai baban Abdul yace don muna neman Dr Lawal usman daga chan akace a ah kashi bane tare da kashe wayar cike da mamaki baban Abdul yace lambarce fa,




abbu yace Allah sarki kila kayi kuskure gurin sawa yace eh kilan ajiyar zuciya *Beena* tayi wacce tunda baba Abdul yashigo da maganar anacigiyar *Blue,* taji kirjinta yana bugawa Wanda tarasa dalilin ta najin haka.




******
Aban garen dad kam sai ahankali domin saida yakwana biyu agadon asibiti saboda damuwar rashin ganin *Blue,* abin gwani tausayi duk yarame saboda ko abincin kirki bayaci,




garashin barci haka Shima *Bulama* duk yarame saboda damuwa rashin ganin abokin sa ga aiki ga kula da dad wanda idan ba *Bulama* ya matsa masaba baya cin abinci,




Kamar yanzu dakyar *Bulama* yasamu yasha ruwan shayi ba madara, cikin sanyi murya da mutuwar jiki yace da *Bulama* son nafarajin tsoro kada "yarona yafada mugun hannu,




dasauri yace a ah dad inshallah hakan bazaya faruba ahankali yace to Allah yasa haka amma fa kaga yau kwana goma kenan da batanshi,




"amman
har yanzu ko labarin wanda yaganshi bamuji ba balle musaran za'a kawoshi garemu tundashi bayada hankalin dazaya iya dawowa da kansa gida ko?..cikin sanyi murya yace haka ne dad inshallah za'aganshi to Allah yasa son,




Sai Kuma yayi ajiyar zuciya cikin tsananin damuwa yace son idan narasa yarona bansan ya rayuwata zata kasance ba, son ina tsananin kaunar yarona fiye dakaina da komai da sauri yace pls dad don't say that aiza'a ganshi ne very soon kaji?..




kamar zayayi kuka yace to Allah yasa yace amin, jiyama munyi waya da aunt *Bebe* wlh itama duk tadamu harda kuka tayi kai ya girgiza cike da damuwa, yace kusan kullun

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login