Showing 39001 words to 42000 words out of 59518 words

Chapter 14 - FUSKA BIYU COMPLET BOOK PDF Writing by Halima k. Mashi.txt

Allah yasa yayi
zuciya ya sakeni, yace meyas bakya sona? nayi
shiru yace sbd laifukan danayi miki? na sunkuyar
da kaina mgn kasa kasa na keyi nace ko bama
haka ba dama ni tuni can bana sonka,ya saka
hannu cikin aljihu ya ciro hankici ya shre zufar
data tsattsafo mishi gurin goshi.toh shi kenan
xanyi tunani yanzun inna sake kina da wanda
kikeso? na dube shi fuskata a dan sake nace a'a
zan koma skul ne yace shi kenan zansan me
xanyi akai ya tashi yace koma gaba mu tafi, duk
muka koma gaba ya tashi motar bayan ya saka
disc din karatu cikin suratul najmi, muryar wata
yrny mai tsananin zakin murya, mai gadi yana
mishi mgn sam bai kula ba don nasani yana cikin
damuwa, ni kam raina kar nasan dole yayi xuciya
ya sake ni.
Tun dawowarmu ban ganshi ba da na zata yau
zamu koma sai naji shiru...shi kam tunda ya idar
da sallar isha'i yana kwance kan doguwar kujera
dake shashen baqi yayi zurfi cikin tunani.tabbas
yarinyar bata sonshi tunda ta iya buda baki a
gabanshi tace bata sonshi me ya kamata yayi
yanzun?ya tambayi kanshi,zuciyarshi ta amsa
mishi da cewa kurum ka sake ta dan baza ta taba
sonka ba wata zuciyar ta tambayeshi cewa yaya
zaka yi da sonta?ka sani dai yanzun kana
matsanancin sonta sannan ga dukkan alamu itace
uwar 'ya'yanka shikenan ka hakura da haihuwar?
take nan daya sashen na zuciyarshi ya amsa
mishi da cewa sai ka auri wata,ya furta da bakin
shi hakane zan iya auran wata kuma ta haihu
Ya tashi zaune dama cikin duhu yake ya kashe
wutar falon,ya dauki wayarshi dake gefan shi ya
kunna neman nambanta yakeyi karo na farko a
rayuwarshi,lokacin kwance nake cikin kayan bacci
riga da wando masu santsi na dora rigar sanyi a
samansu.na kwanta ne kan gadon momy ita tana
zaune kan sallaya hannunta riqe da carbi,wayata
ta soma ruri na duba babu suna, na dauka tare
da fadin hello saboda bacci da ya dan soma
dauka ta,dim ya yi domin muryata ta ratsa tun
daga kunnenshi har yan yatsunshi.
Yace asmy inason ganinki yanzun,jin muryar yaya
umar na wartsake bai taba kiran nambata ba,don
haka na yanke hukuncin saki ne zai bani, nace
kana ina ne?yace shashen baki nace to gani
nan,momy na kalla wadda tun shigowar wayar ta
zuba min ido nace ya umar yana kirana tace to
cikin fara'a ga zaton ta na soma saukowa ne na
fito na saka silifas dina nayi wajen baki na bude
kofar falon duhu dindim falon nayi sallama ya
kunna wayarshi tare da amsawa,yana kwance bai
tashi ba na isa gurin da
Yake nace gani ya tashi zaune ya matsa yace
zauna na zauna ba tare da wani dogon tunani ba,
ya zubamin ido yana kallona na gane yana
kallona ne ta hanyar yanda ya haske min fuska
da waya kusa minti 6 bai ce min kala ba, har na
soma gundura da zaman na dube. shi zanyi mgn
muka hada ido na sunkuyar da kaina sbd idonshi
yana da wani kwarjinina musmman fasa mgn nayi
ya ambaci sunana asmu, na dube shi yace zan
miki abin da kikeso. na zuba ma fuskrshi ido
sannan farinciki ya bayyanakan fuskata. na kula
har mamaki abin ya bashi ya soma shigo da
dabarunshi yayi tunanin amfan dasu yace amma
kfin in baki saki kin tanadi abin da zaki gaya ma
su alhj da abba da momy da kuma mama?
gabana yayi muguwr faduwa sbd sam na manta
da wannan matsalar, idona ya rufe ni dai burina
ya sake ni, yayi murmushn mai sauti yace me za
kice musu? in kin tanadi amsar da zaki basu to
yanxun in baki sakinki. jin haka yasa nace ka
bani kwai ni nasan me zance musu, na fada ina
duban fuskarshi yace a'a sai naji tukunna,na
sunkuyar da kai inawasa da yatsun hannuwana
nace zance kwai ka sake ni ya jeho min tambaya
da sauri kan wani dalili?
Na dube shi nace ban ganeba, yace insuka ce kan
wani dalili na sake kime zakice? nce zan ce ba
komai yace kin taba ganin anyi saki babu fada?
nace a'a zance nice na ce ka sake ni, yace to in
sunce meyasa kika ce na sake ki me zaki ce? na
ce zance sbd banason ka, yayi shiru sbd kalmar
tana mishi zafi, yce toh shi kenan zanbaki
yanzun, amma kin tanadi gurin zuwa? na dube
shi cikin rashin fahimta, ya cigab kinmanta batun
alhj da suka ce inkin kashe auranki ki nemi gidn
uba? mama cewa tayi ko danginta kada kije bare
alhj daya ce ya cireki daga cikin 'ya'yanshi.
numfashina sai da ya nemi ya dauke sbd faduwar
gaba na saka hannu na rike baki sam na ma
manta yayi 'yar dariyar nasara, ni ko dan shirme
sai nace to baga nan gidan ba? na cigaba ai dam
na dade wurin momy ka manta? nan yamin kllon
yarinta, yanzun ne ya gane wannn karamar
yarinya ce, kuma cikin lkc kalilan zai mata wayo,
ya jehomn min tambaya shekarunki nawa? na
dube shi sannan nace 18 da wata 7 a zatona
harda shekaru ake rubutawa cikin takardar sakin
shi kam ashe wauta ta ce. ta saka shi
tambayarta jin haka yayi murmushi laillai yarinta
ya raya a ranshi, ya sake
Ya sake cewa hakane na tuna anan gidan kike
zama, sai dai kuma kina ganin za ki iya cigaba
da zama da momy bayan kince baki son danta
ina nufin ba zakiji kunya ba? nan take na gano
kuskure na in har nasan kunya lallai ne nabar
gidan nan to ina zani? zuciyata ta amsa min sai
ki shiga duniya. na daga nace ba komai ka bani
kawai zan tafi koma ina ne. da sauri ya dube ni,
kina nufin zaki shiga duniya? nace eh, yace can
cikin duniyar zaki samu ci da sha da gurin kwana
da kayan ado da kuma uwa uba karatun da kike
so? bari kiji in sana'a zaki kama shekara nawa
zaki yi kafin ki samu registration, balle je batun
skul fees, banda books, nan mana gano kurena,
nayi shiru kawai yace inbaki ne? na dube shi to
kai baza ka taimaka min ba? yayi driya sannan
yace haba asmy cewa fa kikayi baki sona sannan
kuma kice in taimaka miki? nace ai naga lkcn da
baka sonama ka taimaka min na gama
secondary, yace to wannan baki ganin lkcn kina
da aurena a kanki? yanxun fa rabuwa zamuyi kin
manta? na sake yin shiru yace to yanzun ya ya
za'ayi? na dai kasa mgn dan naga gano bani da
mafita, duk mun yi shiru gidn ma yayi tsit domn
dama dre yayi
Can yace ga mafita da sauri na dube shi in gaya
miki zaki yarda,kuma zki yanda nace? na gyara
zama me zai hna in dai zaka sakeni? yce zan
sake ki mana, nace to ina jin ka yace zan biya
miki kudin skul har ki gama zan dauki nauyin yi
miki komaihar ki gama duk karatun da kike so,
sannan kuma zan cika miki burinki na sake ki, in
har kin yarda ki zauna dani ki haihu, kina
haihuwa zan sake ki, kuma in cigaba dabiya miki
kudin makaranta sannan zan gaya ma su abba
cewa nine na sake ki don kainaba wai don kin
min komi ba, na ce to in ban haihu bafa? yace
nan da 2yrs sai na sake ki to karatunfa? yace
daga mun koma abj zan nema miki jami'a ki fara
inmun rabu sai ki tafi inama kika ce ? nace
america inda su mina suka tafi yace ok, to me
kika ce? nace to zanyi tunani za gobe, yce shike
nan. tashi kije ki kwanta. sanda na shiga dakin
momy tayi bacci ko kuma tana jina tayi shiru ne?
oho na hau gado na kwanta shiru ina son yin
tunani ne game da magarnar mu da ya umar ,
damuwata daya yanda zn jure zama dashi har na
haihu, ko kuma in ban haihu ba yace 2yrs sai ya
sake ni kuma yace zamn 2yrs xan mishi biyayya
zan iya kuwa?
Na sake juyawa naci gaba da tunanin in ba a
wannan hanyar ba saidai in shiga duniya ga
tsinuwar iyaye, hka nayi ta tunani har kusan
asubahi, amma ban tuno wata hanya mai sauki
ba, bayan na tashi saidai na yanke zan kara
tuntubarshi da safe koda text ne inji ko zi
taimaka min a zaman da zamuyi kada ya kusance
ni? da wannan tunanin nayi bacci. shi ko ina fita
yayi dariya sannn yace yaro dai yaro ne,ban da
haka yaushe zata yarda da wannan mgn mai
kama da tatsuniya, fes ya kwanta zuciyarshi tana
shaida mishi ta same ta matsalar shi daya ce son
da bata mishi, saidai yayi alkawarin shi umar
faruk zai koya mata yanda zata so shi. da safe
ina karyawa momy tace in ba da wuri zaku tafiba
ki kwanta ki huta mana?na dube ta ban san
sanda zamu tafin ba, amma na gaji jiya banyi
barcin kirki ba, momy dama tasani shi yasa take
son jin shin me ya hana ta barci, don duk tana jin
motsnta da yawan jan tsakin da takeyi sai tace
me ya hana ki bacci jiya? a shirme na da zan
gaya matane sai wayata ta soma ruri na dauka
muryan ya umar ta sauka cikin dodon kunnena,
karki sanar da kowa halin da muke ciki,inason ya
zama sirri nace to ni ma zaka ga text dina yace
ina jira.
Na dubi momy dake jiran bayani nace me ma
kikace momy? tace cewa nayime yahanaki bacci
jiya ko baki jin dadine? nace kaina ne ya danmin
ciwo, sai na share mgnr, shi kam ya umar jikinshi
ne yabashi xaniya fadama momy, shiyasa ya
katseni kona ce yayi min kashedi. na fito wanka
ina zaune bakin gadoina shafa mai nan na tuna
da text din da zanma ya umar, na rubuta mishi
cewa donAllh ya umar ina son kayimn wani
taimako daya? in har zakamni toh xan amince da
shawarar jiya , na tura mishi nan da nanko sai ga
amsa ya turomin, sai na tura mishi cewa in har
ka yarda zaka kyale ni ina nufin ba zaka kusance
ni ba, na tura mishi sai gashi ya kirani kamar
kada na dauka sbd nauyin mgnr takemin, amma
sai na dure na dauka yace asmy kina jina?nace
eh,yace ai wannan ba zai yiwu ba, taimkon da
zaniya yimiki kenan, ki haihu min ni kuma inbiya
miki skul in wanke ki gurn iyayenmu bayan na
sake ki, kin yard ko a'a? yaci gaba da fadin ina
lallaba ki ne kawai amma kin san matata kike
addini ya bani dama ko da karfine in nuna gurin
saduwa dake wato in kika ki kenan,na dai duba
laifukan dana miki ne na baya shiyasa nakeson
wanke kaina gurin ki,
[7:40PM, 17/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu 2----6
Amma in kina son haka zan miki ya dan kausasa
muryarshi,sannan yace ki zaba ko yanda nace ko
kuma mu mukoma inta nuna karfina ina saduwa
dake kuma ki samu cikin ki haihumin,
sannanbaxan sake ki ba babu kuma karatun inma
naga dama duk shekara sai kin haihu da yardar
allah. .da sauri na ce don allah kayi hakuri na
yarda a na farkon yace shi kenan,na zabga
tagumi ina tunanin ta ina za'a fara?bayan na
shrya,ya umar ya shigo yana sanye da kaki yace
zai je ya dawo na zama cikin shiri ni kunyarshi
ma nake ji tunda wannan zancen ya shiga
tsakaninmu yana tafiya momy ta ciro wani galan
cike da wani abu da naji tana kira tsumi tun
farkon aurena da ya umar take dirka minshi sai
dai in banzo garin kaduna ba ko hutun makaranta
nazo lokacin sai ta bani nasha,niko uwar
kwadayn zuma tabani na cewa yauwa momyna
kamar kinsan nayi kewar wannan tsumin na ce
yauwa momy na kai kamar knsan nayi kewar
wannan tsumn na diddilo a kofi na soma sha
A mota yana ta jana da fira na dake nan take
yayi min tuni cewa har da fa biyayya cikin
sharadin shi kuma dole ne in ya min magana na
ba shi amsa,kuma na saki fuska,nace to a raina
nace zanko iya?...Mun iske farida da kawayenta
su lady na rigashi shiga ciki saboda ya tsaya
gurin su joseph,su farida surutu yaci karfinsu dan
haka basu ji shigowata ba.lady tana cewa ai ke
naga sakarcinki yaushe zan samu miji kamar naki
sannan in tona kaina,ki dubi yadda ya yarda
dake,yana alfahari matarshi ustaziya,sannankina
sha'aninki da abokan harka yadda ranki ke
so,kudi suna shigo miki yadda ya kamata,sannan
ki tsokani fada?dayar tace kyaleta lady,farida
sakaryace kina zaton da zaki kashe auranki su
haji jamilun auranki zasuyi?lady ta amshe da
cewa yaushe zasu aureki duk kyanki sun fi son su
auri kananan yara suna tsotse su,ba gamu ba
sun yarda harka ta duniya ayi ta amma da kin yi
musu zancen aure yanzun nan sai ku bata,Farida
tace nima tunanin danayi kenan shi yasa na
matsa na dawo.,
Domin alhaji sambo ya ce ynxn sunfi yayin hulda
da matan aure,Lady tace sosai ma,baki ganin
yanxun knfimu abokan harka farida ta ce
hakane,dayar tace ina xaton kila wani sihirine
'yan iska ni zan gaya muku haka,domin watarana
ni da wani wawa kum ma sanshi dan iskan
ministan nan tsohon banza,lady ta ce ATY kike
nufi ko?ta ce eh shi mana,har fa mun soma
harka sai dan iskan kawalinshi ya yi mishi waya
wai ga matar aure nan ya dagani ya bani dubu
goma,na ce Allah bai isa ba bazan amshi ten ba
shine ya ce to in jirashi..Ke a takaice gabana ya
ba matar auran nan dubu dari da hamsin dana
soma tsiya sai yace koni da ina da aure haka zai
bani da na so insan dalili sai yace wannan wani
sirri ne don haka kada na daga hankalinki kan
wannan yarinyar,lady tace ki dae hada da
kisisinar da muka gaya miki suka yi dariya suka
tafa,ni dai kaina ne ya daure,shin harkar me
farida ke yi?irin wacce kawayenta ke labari
yanzun?sallamarya umar tare da rufe kofar da
yayi da karfi ce tasa suka waigo,ya dubeni asmy
yaya baki shiga ciki ba?ni dai kallon su farida
nike yi lady ta zungureta da hannu nan da nan ta
tashi ta nufi ya umar da sauri tana fadin sojana
kun sha hanya ta dube ni shigo mana asma'u
Ta amshi jakar hannunshi ya dube ni kije dakinki
tafiya nike ina kallonsu,ya shafi gefen kumatunta
tare da fadin i miss you,ya dubi sashen su lady
ya ce yau su malama hafsa ne a gidan na mu?
tace wlh munji shirmen da faridar taka taso
tayine shi ne mu kazo don mata nasiha banda
abin farida duka duniyar na wa take?ya ce a ton
kuda ku ke waje ku za ku fita sanin me duniyar
ke ciki,dayar ta ce tabbas mun gaya mata,su ka
kalli juna su da farida naga sun kashe ido,tace
nima ai nagane kurena kuma na bada hakuri ko
sojana?dama shi ya dauki hanyar zuwa dakinshi
daga can ne yake fadin hakane my farida,dama
rigima ai ba halinki bane,ya shiga daki ta yi musu
alamar tana zuwa da hannunta itama ta shige
suka juyo dubansu gareni inda nike tsaye rike da
kit dina..Suka kalleni suka tabe baki,na tura kofa
na shige,Lady ta dubi dayar tace kinsan allah
Sara inda nice farida tuni zanyi waje da
shegiya,ba boka ba malam tsabar kissa bare ga
shaidar dakamin ita kuma ga mummunan
tambarin daka kamata ai sharri kala-kala zan
dinga hada mata,Sara ta ce ke bari irin yarannan
sune ake ce ma dan hakin daka raina sai kiga
yarinyar ta kere ta,amma tana da hanyar da zata
ma yarinyar korar kare....
Farida ta dubi sojanta don allah ka ba Asma'u
hakuri dan yanzun kunyar yarinyar nake ji bai
dace ina babba in dinga zubar da mutuncina
ba,ya dube ta cikin farin ciki ka da ki damu,dama
yana da kyau mutum in ya yi abun da bai dace
ba,in an fahimtar dashi ya fahimta sannan ya
nuna yayi kuskure,ta ce hakane nima banyi
amfani da hadisin nan ba,
Farida ta dubi sojanta dan Allah kaba asma'u
haquri dan yanxu kunyar yarinyar nake ji bai dace
ina babba in dinga xubar da mutuncina ba,ya
dubeta cikin farin ciki kada ki damu, dama yana
da kyau mutum in yayi abu da bai dace ba, in an
fahimtar dashi ya fahimta sannan ya nuna yayi
kuskure, tace haka ne nima ban yi amfani da
hadisi nan ba, wanda ya hore mu da soma dan
uwanmu abin da muke soma kanmu, kishi ya
hanani ganin gsky amma insha Allah daga yau na
daina xan yi koyi da irin kishin da matan manzon
Allah sukayi.da sauri ya juyo ya rungume ta tare
da fadin shi yasa kullum nake qara sanki my
farida, kuma ina san ko ba kece kika haifa min
yara ba xan baki su ki musu tarbiya ta qwarai,
tace na gode. bari inje muyi sallama dasu hafsat
gida xasu je, ya jawo dirowa ya ciro kudi ya miqa
mata gashi ka basu, haka ake san abota da
mutanan qwarai,gasu cikin shiga ta mutunch, ta
isa gunsu tana dry suma suka soma dryr tace
shegiya ni ,sukace me ya faru yar iska mai fuska
2
Ta koro musu komai suna ta dry,sara tace har
yana cewa munyi shiga ta mutunci bai san saida
na koyi yanda xan saka hijabin nan ba? lady tace
ni xafi ma ne duk ya dame ni muna fita daga
barikin nan xan cire shi,ta miqa muru kudin ga shi
kinsha sigari, sara tace gara mu ke fa shegiya me
juye giya a kwalbar cocacola tace naji ku tashi ku
fitar min a gida,ta raka su suna mata tsiya itama
tana musu.ina cikin juyayin me xaije yaxo ne a
cikin wannan xaman da xanyi danake mishi laqabi
da xaman waqafi. bayan sallar isha'i, xaune nake
na hada tagumi wayata ta soma rngng, na duba
na hadda ce no ya umar amma ban haddace
tawa ba, na dauka yace asmy ki fito ga munan a
dining nace na qoshi fa, yace ki fito kawai kinsan
kina cikin sharadi ne, na fito jiki ba qwari na ajiye
hijabina,riga ce da wando na kamfala rigan kamar
ta maxa aka dinkata iya cinya wandan kuma fela
na kama gashina da dan kwalin sbd ni ban cika
san daura dankwali ba
Zamanta kenan nima na iso gun ya nuna min
kujera xauna na xauna kusa da farida,ta xuba
mishi tuwon shinkafa miyar ogun, ga nama
manya ta xuba mashi farfesun kaji, ita kuma farar
taliya ta xuba da miyar kayan kayan
lambu,sannan ta saka soyayyan naman kaji ta
dubeni da fara'a me xan xuba miki qanwata?
nace a qoshe fa nake ni,tace me kika ce? shuru
na mata shi ko sai ya cika kofi da fresh milk ya
miqo min da strw na xuqa, yace kinga irin nata
nan, kinsan ita ba komai take ci ba,dama dai dan
wake ne a yanka mishi qwai.da sauri na dube shi
a raina nace waya gaya mishi? ban gama
mamaki ba naji yace kinsan ko farida yarinyan
nan ba girkin kowa take ciba,domin ko ita ta
hada abinta in bai mata ba xubarwa take yi ta
dora wani,na saki baki ina san tuno wanda ya
gaya mashi, to waye domin ba kowa sannan shi
bayanan. na kalle shi yayi min murmushi yaci
gaba da cin abincinshi, yanxu kuma ya s6a bani
tsoro domin ina xaton qila yana da aljanu,domin
haka ranan da mukaje ganin rabon gidan nan
yace jim da gun wasanni sbd ni.
Dan yaga akwai ni da san xuwa jim,nasan ko su
joseph basu san ina xuwa gun nan ba, inko sun
sani waya gaya masa na girki...ya ketse
ni,tunanin me kikeyi kisha mana, in kuma kinfi
san ki xuba xuma da madasa to kije ki dibo na
tsura mishi ido, ya dake tamkas ba shi yayi
maganar ba. jiki babu qarfi na dauki strw na
soma shan madara, araina nace allah abin tsoro
ya umar abin tsoro, sai kace mai gani har hanji,
ina jinsu na soma hamma, yace bacci ko asmy?
na daga kai yace tashi kije ki kwanta, farida tace
ya dace a sa mata ko da gado ne kadai a
dakin,yacf nima nayi wannan naxarin,ni dai kallan
su nakeyi, araina nace ke kika sani da
munafincinki, na

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login