Showing 51001 words to 54000 words out of 59518 words
Chapter 18 - FUSKA BIYU COMPLET BOOK PDF Writing by Halima k. Mashi.txt
gani
akan kaina domin ada naki ki asma'u amma a
yanzun ya matso da bakinshi cikin kunnena,you
are the one I love, Allah shine shaida ta yanzun
ne nasan meneneso, koda baso nayi ba,ya mike
zaki yarda nan gaba ya fita. farida ta koma
mazauninta cikin sauri daga leken da takeyi taso
taji menene ya umar ya gaya ma asma'u cikin
kunne?
Akwati guda haka ya umar ya ciko min da
atamfofi,shaddoji da material suka kaima tela
daga buba sai play da xani aka min sauran anko
din ma duk manyan dinki akai min. ya umar xasu
tafi da faridanshi washe garin daurin aure, dama
yace ni inyi sati 2. ya kira momy falan abba
sannan ya kira ni cikin waya, na same su yace
ma momy kingan ta nan ta qi muje asibiti su yi
mata awo dana mata magana sai ta saka min
kuka, ga kumburin da take yi,na rasa yanda xanyi
da ita gata nan xan barta sai ki kaita asibiti,ya
ciro rafar yan dari biyar guda biyu gashi nan duk
yanda akayh momy kin min waya, momy ta dauki
kudin sannan tace shi kenan Allah ya kiyaye
hanya ina faridar? yace tana dakin anty,momy ta
fita nima na miqe xan fita ya kamo ni ya saka a
jikinshi yace haba asmy ki bari muyi sallama da
bebyna mana. nace daka sani tun kafin inxo kd
ka gayamin cewa in mun xo xanga doctor
mana,ka sani inhar ka gaya min baxan xoba, ka
dinga tunawa sharadinka babu tursarawa, yace
haka ne husna amma dan lfyrki da beby xaki
asibiti
Ke matsalarki daya ce baki san allura,tuncan
abuja nace baxan bari a miki allura ba kinqi
yarda dani na cire jikina daga nashi nace har
abada baxan yarda da kai ba, ka tuna har qofar
gidanmu ka dauke ni da sunan xan gwada
takalmi ka kaini asibiti suka caka min allura da
nufin xa amin gwajin HIV,ni xa ama gwajin HIV
ka cuce ni, jikin ya umar yayi sanyi ya durqusa
gabana gwiwa 2 yace ba kya yfy ne asma'u? ki
xama daga cikin masu yfy ga yan uwansu a yayin
da aka bata musu na sani na cuce ki ni mijinki ne
amma kalleni gwiwa 2 aqasa ki yafe min ina so ki
sani inna tuna abubuwan dana miki ina jin
haushin kaina nasan laifukan dana makh ne ya
hana ki sona, na kuma shaida ki na da haquri. na
dube shi ya ban tausayi amma na dake na ce xan
yafe makd ya umar amma sai randa ka sake ni
na fita na barshi a gun.tsakar dare ya umar ya
kasa runtsawa yanda ya tsani ciwo haka ya tsani
asma-u ta furta kalmar saki, kana ya tsani ya
xauna da laifin wani kanshi domin bai san ranar
mutuwanra ba,
Sakin asma'u baya cikin tsarin shi wayo kurum
yake mata saidai yanxun yana ganin dole ne ya
sake ta ko dan ta yafe mishi laifukanshi, wata
xuciyar tace yaya xaka yi da santa? ya miqe yana
xaga dakin ya dubi farida dake ta faman shirga
bacci, ya sani yana san farida so na yarda da
ganin girma da kuma mutunci amma san asma'u
daban ne a hankali ya shige shi kuma har yau
yana shigarshi kadan ya rage ya gama xagaye
dukkan jikin shi ya xauna bakin gado tare da
furxar da xaxxafan huci,sai yace menene maganin
xuciyarshi can sai tabi amsa da cewa Allah,da
sauri ya miqe tare da dauro alwala nan ya duqufa
neman mafita gun Allah.Diamand hospital muka
je da momy sunmin awo tare da dubani sunce
baby lfy amma jininta ne ya dan hau, wannan
kuwa ba wata matsala ce mai xafi ba yawancin
masu ciki kan sama haka inka haihu sai ya tafi
sun min allura,kuma sunce 3 xa-a min kudin in
haihu inna haihu kuma amin 2 dama wai 5ce.ya
umar ya saka ma ranshi dani,shine xaisa ya iya
haqura dani dan gaka ya yanke shawaran barina
kd....
[7:49PM, 17/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu 2----12
Yawancin masu ciki kan samu hk in aka harfu sai
yatafi sunmin allura da dabara sun ce uku za ai
min kafin inhaifu in na haihu kuma aimin 2 dama
5 ce ya umar ya saka ma ranshi wani sonta dani
shine zai sa ya iya hakura dani don hk ya yanke
shawarar baring kd inyi goyon ciki bayan na haihu
sai ya sawwake min gidansu momy na cigaba da
zama kafin cikin ya cika wata 9 kowa tausayamin
yakeyi satin yaumar 4 sannan yazo yaci fada gun
momy ya ce kiyi hkr tana raina yrny nan bana
samun zamane shi yasa hkln shi ya tashi da
ganin yanda na kumbura ciki yayi kato kowa
cewa yake bai taba ganin ciki maigirma irin
wannan ba sukan likitoci sunka hoto sun ce lfy ta
lau hk ma cikina kuma watan cikin 8 bai isa
haihuwa ba ya umar yaza kullum yana hanyar kd
da abj dr ya ce indinga zaga gari hkn yakan
tasani gaba mufita zagaye duk inda muka muce
sai anmin sannu inko ina zaune ne hk zaita
matsamin kafafu su dan saki yanaga min kalamai
masu sanyaya rai inshallahu zaki haihu lfy kada
ki damu kinji? Duk addu'a muke miki cikin
sallolinmu kema kina yi? Me zaki ci? Hk zaita
lallabina wani sa'in har tausayi ya ke bani.
Cikin bacci naji kaman an tsungule na farka da
kyar na sauko daka kangado ba nason nayi motsi
mai karfi momy ta tashi bata samun bacci sosai
bayan gida naji inaji don hk na shiga toilet amma
yaki fitowa dg nan basai ciwo ya matsamin ba na
fito na kafa kai jikin gado momy ta farka da sauri
ta ce yayane asma'u ? Na ce bayana marata zan
mutu momy ta ce kiyi salati da addu'a bari inyi
waya usman yazo ko aliyu atare suka iso aliyu
ya dauke mu nida momy usman kuma yaja su
abba da anty dr na dubani ya ce haihuwa da
saura yanzu ma nasoma nakuda domin ban bude
ba jin hk yasa nasadakar mutuwa zanyi ban taba
jin irin wannan ciwo ba don hk na sama raina
tawa ta kare Shi kam yaumar tun dare jikinshi ya
bashi kd babu lfy sbd mafarkai barkatai da yayi
aranar tun asubahi yake kiran wayata amma
shuru babu wanda ya dauka hankalin shi yatashi
sosai yasan da tana kusa zata dauki wayar ko da
masifa zatai mishi yakasa natsuwa sai kusan
A zaton shi ni ce ya ce Asmy jamila ta ce ba ita
bace ya ce tana ina? Ta ce em tana bayi don
ance kada su gaya mishi ya dan ji sanyi har ya
shirya fita kafin yakai ofis dinsu ya koma kira ta
dauka ta ce bata kusa cikin tsawa ya ce ina taje?
Nan ta dabure tarasa me zata ce can ta ce bari
na nemota takashe wayar ya dubi direba ya ce yi
paking a gefe nan ya nemi momy akashe ya nemi
abba tana ringing ba'a dauka ba ya kira antynshi
akashe duk lkcn su kam wayoyin su suma gida
nan fa hkln shi yatashi zuciyar shi tagaya mishi
asma'unshi tarasu nan take ya ce da direba
sukama hanyar kd sun iso 11 gidan bakowa sai
nafisa ya ce ina momy ? Ta ce na asibitin
diamond ya ce shine don iskanci kika cemin
asma'u tana bayi? Yana magana ne yana fita don
hk bai ji amsa datake bashi ba sanda ya iso
asibitin na jigata ba kowa guna sai likitoci
yaumar ko gaisuwa baiyi da su momy ba ya ce
musu ina nake? Suka nuna mashi dakin haihuwa
sai ya shige dr ya ce yanlabe kayi hkr kajiramu
waje ya ce madam nima kimin hkr naga matata
ya nufo ni ya rungume ni sannu ya ke min tamkar
shi nakudar take jira ta tashi gadan gadan amma
haihuwa shuru likitoci sun ce dayan rana zan
haihu amma har 2 shiru yaumar hkln shi yakai
karshan tashi ya ce sumin aiki su cire adan in
huta sun ce in ankai 4 ban haihu ba zasuyi min
aiki ya fita don yo salla tunda sauran karfina har
nakai bana iya koda nishi biyar dai dai anmin
shirin aiki yan uwa sai addu'a wasu na kuka kada
ma momy taji,
A dakin tiyata wani sabon ciwo ya tashi wani
uban nishi nayi sai ga yaro ya fito fit jim kadan
sai ga sabon ciwo nan suka gane yan biyu ne
suka taimakamin aka fito da ita nan suka fito da
yaran don gyara dangi suyi matukar farin ciki da
sauka lfy anshiya yara anata murnar ganinsu shi
kam ya umar ni yake son gani dr ta ce kada
yadamu ana kimtsa nine sun min allura sannan
suka kaini dakin hutu bacci nake bansan irin
hidimar da nake su ba sanda na farka tara tayi
momy ce da ya umar ya taso da sauri sannu
asmy kin tashi? Kallon shinake kurum a raina na
ce badole kai min sannu ba tunda ka hada ni da
aiki sai kuma naji dadi dana tuna yau ko gobe
zamu rabu da shi ya ce momy a hada mata tea
bari ta wanke bakinta shi yatadani na wanke
bakina cikin wani kwanon silba sannan na dan
sha tea kadan momy ta ce yarta baki ce ina
abinda kika haifa ba? Shuru na mata araina ko
fadi nake ina ruwana da abinda na haifa ya umar
yaje gadon su yadauko daya ya ce kinga arzikin
da Allah ya bamu asmy na kwanta naki kallon su
da momy ta matsamin sai na ce ni ina ruwana
dasu
Shuru yayi yana kallona momy ta ce wanna karon
zamuyi rigima dake asma'u suka fita fatima na ce
yaya babu wani lallash ka bude mata wuta ba'a
bada nono ke aka baki? Suka fita yazo gaban
gado na ya zauna bakin gadon zcy shi tana har
bawa yanzu ma bai san ta inda zai soma ba can
ya tashi yaje ya dauko maccan ya zauna kusa
dani ya ce asma'u ki hkr nasani duk komai laifina
ne kada kiyima yaranki horo da laifin babansu ki
bada nonon nan domin Allah ba don ni ba kinga
ita macce tanada rauni na dube kasan baka
mukayi dakaiba don hk bazan bada nona na ba
yanzu ina takarda ta? Yayi ajiyar zcy kinsan zan
baki tunda nina ce zan baki amma yanzu kisan
zuyi ta jin haushin yan uwanmu zasu tsaneki na
soma hawaye wannan karon na shirya na yarda
in fuskanci ko wace irin matsala ce kai dai ka
sallame ni yamike yana jijjiga yarinya sbd kukan
da take yi yasa mata lebanshi abaki ya dan
jijjigata sai tasoma bacci ya mannata akirjinshi
sannan ya zauna bai san me zai ce mata ba yaje
ya kwantar da ita sannan ya fita gurin dr yaje ya
bashi bayani kan babies suna jin yunwa mamansu
tana fushi ta hanasu nono dry likita yayi sannan
ya rubuta kalar madaran da ta dace dasu ya ce
koda tana basu nono ba dole ne ya ishe su ba
dama sai an hada da madara yaje ya sayo ya
kawo nan da nan aka dama masu suka soma sha
shi kuma ya koma abj sbd bai sanar ba gashi
suna cikin wasu bincike ne washe gari yayi lagos
Nikam har sannan naki bada nono na, kwananmu
uku aka sallame ni mukayi gidansu momy dama
su abba basu sani ba haka nan momy ta hana a
fada ma mama. Ran kwana hudu ya iso da kaya
niki niki mota guda tamkar masu kayan tashi, duk
na yara ne. Su rahama suka fita da su hadiza
kowa baya jin dadi yanda yake ganina rai cunkus,
bana cin abinci. Hadiza tace Allah yau sai na
gaya wa mama, su anty aina'u. ma da gangan
suka yi shiru har alhaji ma sai yaji. Rahma tace
a'a ya umar ne yace likitocin sun ce kada a
matsa mata fa! Hadiza tace ba dai ya son ya
matsa mata amma na taba ganin mai jego ba cin
abinci kuma ba zata ba yara nono ba sai shegen
bakin rai? Ni kam dama na kosa su fita tunda
naji zuwan ya umar yau kama sai ya sallame ni,
ya zauna bayan ya dauko yarinyar. Bansan me
yasa yafi daukar yarinyar ba, maman 'yan biyu na
same ki lafiya? Banza nayi mishi yace yarinyar
nan tana kama dake sosai, shi ya sa nafi sonta.
Na harare shi, wannan ba damuwa ta bace ni
yanzu damuwata ka sake ni, ban ma kaina adalci
ba in har naci gaba da zama da kai. Duk sanda
na dube ka ina tuna wuyar da ka bani tare da
bakaken maganganun da kasha gayamin amma in
ka sake ni zan yafe maka kuma raina ya huce. Ya
tsugunnan gabana yanzun to wa zai shayar min
da yarana? Wai zai kula min dasu? Nayi
murmushi sannan nace ka manta da faridarka?
Wacce ta iya yiwa yara tarbiya kuma 'yar masu
tarbiya?
Ya zauna kasa, ban da magana a yau amma kiyi
hakuri. Nace na daina yarda kana min wayo da
yawa, gashi ka samu yaran da kake muradi,
san...sallamar mama ce ta katse ni, ina take
mara hankalin yarinyar, dan ubanki ba a bada
nono ni na baki nawa? Ta shigo bata 'yar ta bata
nono ko in tsine mata yanzun nan. Ko kuma ki
biyani nawa. Don kin sha wuya su suka dora
miki? Ba Allah ne ya doro miki ba? Gani nan tun
daga haihuwarki na samu hawan jini amma ban
hana ki nono ba sai ke? Kuka na saka su momy
suna ta ba mama hakuri tace ba fa zata tafi ba
sai na basu nono. Ta dubi ya umar tace kai kuma
faruk baka gaggaura mata mari? Yarinya mara jin
magana. Ya umar yasa ta cinyata, momy ta ciro
nonon ina kuka aka sa mata. Nan ko ta kama sai
sha tace, shima yana bacci ya umar don mugunta
sai da ya taso shi shima suka saka mishi nono
ya hau sha, ranar nayi kuka har da ciwon kai.
Da dare ya umar ya shigo na dan dube shi
wallahi duk ya rame. Ya ce me da me kike so
game da suna gobe zan koma jibi zamu zo da my
farida saboda tana dubai yau zata dawo, na dube
shi ina ruwana da suna? Ni fa babban sunana ka
sallame ni. Yace zan sallame ki amma ki bari ayi
suna mana! Nace ran suna? Yace da dare ba.
Nace shi kenan yace to ki saki ranki ki dinga cin
abinci kina basu nono, na ce nifa ba zan iya ba
da nonon nan ba. Ya ce ke da su daya ne a raina
kinji asmy? Yanda yayi maganar cikin muryar
tausayi don haka sai ya bani tausayi.
Ya umar ya kashe kudi da sunan nan tamkar a
kasa yake hako su. Ni kallonshi ma nake yi.
Akwati saiti daya yayi min guda biyar, zannuwa
talatin da shida ga key din mota ta academy 'yar
mai kyau sabon sanfur ga hajji da umara sannan
ga takardun gidan shi na nan kaduna, yace na
wane halak malak ko bayan ranshi ko ba ma tare
nawa ne. Alhaji da mama fada suka kama yi wai
duk iskancin da nake yi har ya birge shi ya min
kyauta haka? Abba da momy cewa suka yi babu
ruwanku wannan tsakanin miji da mata ne. Haka
yasa ni jin tausayin ya umar nasan yana yi ne
don in zauna dashi in daina maganar saki to ni
bana son shi haka nan bana son 'ya'yanshi.
Farida ma tayi hidina sosai, dangi sunyi hidima
da mu. Akayi suna yara suka ci momu da abba,
kowa ya wadatu da kayan suna. Rago biyu shanu
bibbiyu haka ya umar ya yanka. Daren ranar na
jira shi dan ganin takarda bai zo ba har sai da
nayi bacci. Ya shigo yaran yaje ya tsuguna
gabansu yayi musu adduo'I sannan ya sunbace
su, yazo kusa dani ya sunbaci kumatuna sanna
ya aje min wata 'yar farar takarda kusa dani,
sammako yayi don haka bamu hadu ba, ni kam
ban ma ga takardar ba sai da ina karyawa naga
takarda na dauka da sauri ina dubawa. Cewa
yayi: “ki min afuwa ba zan iya sakin ki ba saboda
son da nake miki, ki zabi wani horo mai tsanani
wanda kike ganin yafi kowanne horo wahala ki
min shi, na yarda in dai zaki janye batun saki.
Sannan ki taimaka ki kula mini da yarana domin
ki tuna ko ba aure na san zaki iya kula min da
yarana don zumunci. Kina da hakuri, ki kara
hakurin na gode”.
Tsaki naja sannan na yaga takardar, nace ba zan
iya zama da kai ba in ko ka ki wallahi zaka ga
wulakanci ganin idonka. Haka mukayi ta yin
wankan jegon nan yara kam ko kallonsu bana yi,
nono kuma sai momy ta tsaya a kaina sannan
zan basu, in ko ba ta nan in dage ince sun sha.
Satinmu uku ya umar yazo dubamu sanda shigo
suna ta kuka ni ko ina kallon filn dina, kuma ina
jinsu dama ko suna kuka sai dai wani ya dauke
su ya basu ruwa, har mamakin su momy keyi wai
ko da labari basu taba jin labarin shashashar
uwa uwa irina ba, kashe TV yayi sannan yayi
bedroom, ya dauko su yana duba na ranshi bace.
Ban san irin qin da kike min ba asma'u, ko baki
sona ai kya so 'ya'yanki. Na dube shi in dai ba
zaka sake ni ba toh baka soma ganin takaici ba
ya umar. Yayi shiru can yace toh bata nono shi
kuma sai in bashi madara, nace bani dashi. Na
mika na fita. Innalillahi wa inna ilaihir raji'un
kurum yake ambata a zuciyarshi. Haka ya basu
ruwa da madara, gashi ba aikin shi bane duk ya
bata jikinshi. Sai ga nafisa ta dawo daga
makaranta, nan ta taimaka mishi ni kam ina
tsakar gida.
Haka muka yi arba'in ko yawon arba'in bamuyi
ba su abba suka ce maza in shirya zasu kira
mijina a waya mu tarkata mu koma tunda
iskancin da nake ma yaran kenan. Inje in ma zan
kashe su ne in kashe su. Da na sa ma momy
kuka sai tace kada in mata kuka itama tafi son
yaran a kaina don haka bazata iya kallon cin
fuskar da nake yi ma yaran kuma jikokin da tafi
so duk cikin jikokinta, haka na hakura saboda
dama gurinta kadai nake ganin fuska yanzu kan
yaran nan har rahma tsiya mukeyi da ita. Waya
abba yayi ma ya umar kan cewa yazo ya kwashe
mu yace toh amma ba cikin wannan satin ba,
saboda farida bata da lafiya yanzu ma asibiti
zaije kaita. Abba yace assha, me ya same ta?
Yace wallahi ciwon ciki haka ta kwana abba yace
Allah ya sawake mata. Farida tana ta murkususu
tamkar zata mutu, likitoci suna ta bincike kanta,
ya umar tare da wasu abokanshi suna ta kai
kawo a kofar da aka rubuta emergency. Kusan
awa daya likitocin suka yi ta fita daya bayan
daya, duk wanda ya umar ya tunkara sai yace
yana zuwa. Daga karshe babban likitan ya fito ya
dubi sy ya umar yace wanene mijinta? Cikin
fargaba ko ta mutu ne ya umar yace nine. Likitan
yace biyo ni office.
Bayan likitan mai suna dacta bashir M ya bashi
hannu sun gaisa yace matsalar matarka nake son
shaida maka. Ya umar ya gyara zama. Dacto ya
bar rubutun da yake yi yasa gindin biron akan
habarshi. Kasan matarka tana shan giya? Ya
umar ya mike da sauri, dr kace me ne? Kasan me
kake fada kuwa? Dr yace calm down my friend.
Da yawa matanmu suna irin wadannan dabiun.
Ya umar ya katse shi to ni matata bata shan
komai sai da coke ina zaton baka san aikinka ba.
Ya fita yana masifa ya isko su aminu in da ya
bar su. Yace kunji wannan wawan likitan wai
farida tana shan giya, kuzo ku taimaka min in
canza mata wani asibiti. Likitan yayi kokarin
fahimtar da ya umar amma abin ya faskara dan
yayi fushi sosai. Aminu da sali kam basu ji wani
mamaki ba, domin sun jima suna zargin farida
dan dai basu da shaida ne, amma sun taba
ganinta da wani alhaji a wani