Showing 21001 words to 24000 words out of 59518 words

Chapter 8 - FUSKA BIYU COMPLET BOOK PDF Writing by Halima k. Mashi.txt

yasoma
sakkowa, momy tace to kudai kuka sani nidai
bazan yarda da batun wani Aure dai yanxuba, sai
Naga kamun ludayin yata a gidan nan, ya cire
hannu a cikin abinci Kamar ya'ya momy? Ta ce
to ganin farko da zanyi Mata banga tasiriba,ta
Kara baki ta rame sai idanu a warwaje .yace
tonidai gatanan Ki tambayeta me nake Mata?
Don ba a satina hudu da auranmu kikaxoba kafin
tasamu cikin Nan Kinga Kyan datayi Ga kiba
Kamar tafashe. Amma Tana samun cikin Kullum
muna hanyar asibiti, kaina sunkuye anata keramin
karya, momy tace kodai batacin abinci ne? Yace
tanaci Badai Kamar daba momy tace itama haka
tace Toh Allah ya kyauta sukace Ameen.
A kitchen ya sameni Ina harhada wanke wanke
yace ke dakina zakizo kuma karki soma
zuwanmin da datti batare da yajira amsa taba ya
fita. Bayadda zanyi haka nayyo wanka nashafa
turare na dakko kayan Bacci nasaka dama
bantaba saka rigar Bacci ba mai ya, na taje
gashina danma Allah yasa gashina mai kyaune
Amma da yadda ba kitso ba saloon din Nan ay da
ya lalace na daure da ribbon na daura zani akan
kayan nasaka hijjab na zauna kusa da momy tace
tashi Kije gurin mijinki nima Bacci zanyi saida
safe Haka naja Mata bargo nakara Ac najamata
kofa daidai kofarshi Natasha duk tsoro ya cikani
kilafa Yau nasha bakaken maganganu ,na tura
kofar ahankali tamkar mai tura kwai na leka yace
shigo mana cikin tsawa ya fada, nashiga na
Maida kofar narufe natsaya Ina raba Ido Ina
kallon shahararren dakin mai mutukar tsari komai
nadakin sky blue ne, tundaga gadon har shinfidun
xuwa kafet da labulaye zaune yake da Riga da
wando na Bacci a gaban computer idanunshi
sanye da glass, nazauna kasa gefen kofar Ina
karema dakin kallo hoton wata kyakkyawa nagani
Tana sanye da bakar jallabiya ta rufe kanta da
gyalen, Nan kuwa na tsuramata Ido tamkar jinsin
larabawa kusa da hotonta Shima nashine yayi
kyau cikin kakin sojoji, bansan yaxo kusa daniba
sai dai jinsanayi ya shakoni cikin hijab ya ruko
wuyana yajani har gaban gadon, yasaka hannu
ya ciro hoton wannan matar yace rike na rike da
sauri yayi kasa da murya. Matata kenan farida,
yaki ka ganta? Gaya min? Da sauri Nace Tana da
kyau Nace shigarfa? ta menene? Nace ta
mutunci, yace to mutuncin ya mace kenan shigar
musulunci ba irinkiba ya Maida hoton ya dauki
filo ya wurga min can sakon gadon da bango je
can Ki kwanta Sbda gadona bana kazanta bane.
Na kwanta da hijabina sbd sanyin AC na shi yayi
yawa.Can cikin dare na farka sai na ganshi yana
ta nafilfilu daga gurin da nake ya juyo min baya
ne,na tsura mishi ido.Ya Umar yana da kyau ashe
yana da Ibada sai dai mugunta,o Allah ban koma
baccu ba har sanda naga ya gama ya kwanta,ya
dauki waya ina jin shi ya lalubo abar son tashi
hira suke ta masoya ina zaton ana nema take
gaya mishi zata je fatakot dan yin shawara da
Anty Amina game da batun Auran su,shima ya
nuna jin dadin shi da yin haka sunyi sallama in
da yake ce mata ta yu mafarki mai dadi yana
kashe murya tare da kwantar da ita,hr mmkn shi
na riga yi, bacci ya sace ni naji an shure ni na
tashi firgigit! Tashi kiyi sallah har naje Masallaci
na dawo kina nan kina aikin bacci,tun jiya ko juyi
ba ki yi ba,kina ma sallar kuwa? na daga kai
alamar Eh. Na tafi ina mmkin ashe akwai
Masallac ni dai bn ta6a jin kiran sallah ba,naje
zan shiga bayin shi ya ce wa?Maza na ki yanda
cututtuka suka cika gari? Na ta fi na yi sallah
sannan na gaida Momy na shiga kicin.Satin
Momy daya suka soma shirin tafiya,kan su tafi
sai da ta ce lallai ya Umar ya nemar min mkrnt
ya ce zan shiga amma sau mun koma Abuja,sbd
nan duk sai a hankalu,mkrntn haka su Momy
suka tafi suka bar ni da kewarsu,na koma kamar
da uban aiki ga masifa in nai kuskur naci duka da
gwale-gwale cikin haka rannan ina fashin sallah
na kira masu gadi ta hanyar dannan kararrauwar
kar6ar abinci su,daya yazo na bashi naira 500 na
ce ya siyo min always,kudin d Momy ta bani dubu
biyu,ya dawo kenan sai ga Ya Umar ya tambaye
shi menene? ya zo nema ya ce na aike shi ne ya
amshi sakon ya shigo dashi ya duba yaga
always,ya ce dama su kike aiki siyan wannan
abn? Na ce na'am ya ce ina wasa dake ni,ina ina
miki mgn kin ji sarai ki dinga wani na'am sai kin
sani na ce au ba da shi nake amfani ba tsumma
ne nake amfani,ya ce to yanzy ina kika samu
kudi ko kin soma sata ne? Da sauri na ce a'a
Momy ta ba ni ya ce to bani su na ciro na bashi
ya wuce,haka na zauna gidan nan kullum
addu'ata Allah ya kawo karshen zamana a
gidannan.
Ni ban sani ba ashe tun da Farida taje gurin
Antynta Amina ta mata fa da ta ce ki zauna
rayuwarki ta kare abn maza su in ba ki sani ba
da kin tsufa shekarun ki sunja shi kenab sun
gama yayinki gara ki je ki bude wuta ta ce to ya
zanyi da shi na gaya mishi halin da kuke ciki zai
goya miki baya to ko je gurin Baffan ruga wane
ga baban nasu kuma ya bata dama ta turo mai
sonta nata don haka ta kira Sojanta kuma ya
amsa sun gana da Baffan kuma an ce tura manya
yaje ya samu Abba,Abba ya ce ba ruwanshi da
wannan mgn,sai ya nufi gurin Alhj, Alhj kam ya
goyi baya shi nema ya shirya ya nufi yola inda
aka yanke mishi sadaki dubu dari nai ga tsadar ta
ba tunda ya san zauki Amarya dal a leda ana
mishi tunanin an saka rana wata 4 a lissafe
september kenan biki zai kama. Duk da gargadin
da momy ta yi ma Ya Umar ya barni in zo bikin
su Anty Aina sai ya ce mata to tana tafiya ya ce
in dai ban yi kiba ba ba zan je ba.to ban ma san
takamaiman lkcn bikin ba shi dai nasan yaje.A
kwna a tashi gashi mun shiga October shekara
daya da wata kenan da yin auranmu kuma lkcn
ne ya Umar ya gama course din shi tun dare ya
ce min na shirya kayana washe gari muka dauki
hanyar Kaduna a mota.Direba ya jamu ya mu gun
ja min kunne kan cewa kar na sake aji wata mgn
a bakina,ni dau farin cikina zan je gida..
[1:53PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1----16
Duk da ba sona iyayena suke yiba,hakan ba xai
hanani shiga na gaishe su ba.mun cika mota da
tsaraba sai gurin isha muka iso duk da shegen
gudun da mukeyi tare da sammakon da muka yi
amma sai da mukayi dare.wannan gari da shegen
nisa da gudu na shiga gidan momy ta idar da
sallah kenan na fada mata ina ta murna nayi
sallolina kenan ina cin abinci yau dai jina nake
tamkar na fito daga kurkuku.sai ga rahma ta
muka rungume juna sai kuka, momy tayi tayi in
shiga gidanmu naqi nace saina huta ai suma basu
damu dani ba, da yanxu ko yara ne sun turo, in
ina wannan maganan momy dry take min tace
quruciya ce, haka sanda taje tana ji ina tambayar
kowa ban tambayi yan gidanmu ba, tace baki
tambayi su mama ba, nace bayan qilama basuce
a gaishe ni ba? momy tayi dry tace sunce a gaida
ke mana,dakin antx amarya na kwana ta ciromin
sababin dunkuna wai inji ya umar kada nayi kada
nayi amfani da kayana, na gane hikimarshi dan
kada ace baya min dinki.washe gari na shiga
gidanmu bayan na karya.
Hawaye taf idona bansan ko kunan menene ba,
haka suka xagaye ni suna min sannu dana shiga
dakin mama ina ganin ta na saki kuka, ita dai
kallona take nasan raman da bakin dana qara
take kallo, yan gidanmu duk sunyi qorafi kan
ramata, nidai bakina qanin qafata inji yan iya
magana,ina can har dare na tashi na dawo.momy
ke cemin ashe ya umar xai yi aure? duk da ba
xaman dadi muke ba saida naji daban,nace ai
banma sani ba, shine take ban rabarin sunqi
yarda alhj ne mai shige mishi gaba nace Allah
sanya alheri kada ki damu momy danni babu
matsala,nidai ki mishi xancan krt na tunda ynxu
abuja xamu koma ni konan kd ne ma ya
barni.momy tace a'a babu batun kd yaxo dai ya
min magana daya in baxai saki mkrt bane yamin
bayani. ya umar ya sha fada gun momy na cewa
bai gayan xancen auranshi ba, duk da yayi qaryar
cewa baya ran raina ya baci ne,shi yasa yaqi
gaya min haka nan tasa shi ya sai min waya mai
kyau bansan yana qera gida a kd ba saida momy
take cemin ai yanxu an yanke shawara inya gama
gininshi na badarawa.
In ya gama gininshi na badarawa nan xa'a min
daki,nace au momy dama xa'a min daki? tace
xa'a a miki man cae dinma ai shine yaqi,yace a
bari sai kun dawo nan arewa naje gidansu anti
aina da gidan salima da fatima. rahma ce ta
rakani,randa xamu gaida momynta mun ba ta
guri layinsu suraj ance tunda kika yi aure
iyayanshi sun rasa gane kanshi, amma sun maida
shi krt malesia, nace xaije ya qara lalacewa
kenan, agaban suma ya bi mata bare wata qasa?
tace lallai kam, nace ai ni inda ya suremin daya
nuna yanasan jikina, kinsan fa nan duniya na
tsani namijin da xai nuna yana san jikina. rahma
tayi dry tace da kenan yanxu ai dole ki sakarma
saja.na dubeta wane wai ya umar um ayi sha'ani
dai kawai, tace da fatan ba gudun miji kike yi ba?
nace rahma dama ina so mu kebe kiji
damuwata,sbd anan duniya kece mutum daya
dana ke fadama damuwata, kamar yanda kema
nasan duk damuwarki, tace hakane, na kwashe
komai tsakanina da ya umar na gaya mata sai da
tayi kuka,dan tausaya min sannan tace cabdi
yanxu tao ke a wace tuqa kike,
Kada fa kije gashi yanxu shi da matar shine suyi
ta cin xarafinki? nace ai ina ganin xan gaya ma
abba ne qila ya kashe auran nan tunda sam baya
qaunata, bakiga yanda na dawo bane? tace
yanxun ma aikin danyi kyan gani,amma batun
gaya ma abban shi ba ita bace mafita,sbda yana
nuna yana kula da ke sannan yana nuna sanki
gaban mutane, ta ki barshi shi da Allah ba
azzalumin bane,akwai ranar qin dillanci yanxu dai
ki sa krtn ki samu ko can abujan ne,in kin tafi ka
kya gidan ma bare kiga haushi,in kin dawo kina
daki,nace Allah na tuba rahma haushin me xanji
naga nifa ba sanshi nake ba ina ruwana da
matarshi? tace to sai abu nagaba.addu'o'ikin
shagala da yin nafilfilu,nace acan ina san tashi
amma ba xan iya ba naci aiki na gaji kamar jaka,
tace yanxu sai ki tashi kiyi ta addu'a,Allah ya
kawo miki sauki
Nace hakanne magani na gode. tace,ai ni ma xan
dinga taya ki addu'ar, Allah ya sani ina sanki da
ya umar saidai kuma yanda Allah yayi ba
makawa, na harare ta sannan nace dube ki kema
xaki shiga layin masu cewa yana birge su ko
kuma yana da kirki ne? tayi dry sannan tace baxa
ki gane abin da ake nufi bane.momy ta matsa
mishi da maganar mkrnt, hakan yasa shi nema
min ta kwana gayamin yake wai shi ba xan je in
hana shi sakewa da amaryanshi ba,gara in tafi ta
kwana.sannan yace turkish na kaiki, in har baki
tsaya kinyi krt ba Allah ba xanyi asaran kudina
ba, wuya xaki sha kin sanni,kuma kika yarda kika
yi wani abu na bata suna ko kibi maxan da kika
iya dan akwai maxa a mkrnt saina saka bindiga
na dauke ragowan nunfashinki duk mu huta,saura
kuma idan momy tace kina san mkrnt kice a'a ki
gamu dani.shi ke surutunshi amma ni ina
maimaitawa ne a raina ina qarawa turkish ni
asma'u a turkish? cab! komai yana da
hanya,amma da kamban sa rai ba.momy kam
tayi fadan yaya xaikai matar aure mkrnt kwana?
nace nidai zanje momy inason ta Allah.momy ta
yarda cikin kwana kalilan ya gama min komai
yace ya aliyu ya kaini momy taki yarda ta matsa
mishi saida ya bar komai ya kaaini. da duk abin
da dangata yake tafiya dashi makarantar saida
komai ya kammala sannan suka tafi don
haushina ko sallama bai min ba, ya alyune muka
yi sallama dashi na zauna bakin gado ina kallon
dakin namu kato ne mai dauke da gado 4 mu 4
kenan . dakin ga kafet labulaye ga ac ga
kumafankalafyayyun gadajantamkara gidan
uwarkaniko gidanuwatama ban da kamar shi
saurn 'yan dakin suna gurin wasanninsu domin
yau lahadi duk daliban na. ga suna gurin
wasanni. cangurinsha biyu da rabi saigasu sun
shigo duk sa'nninane gasu masu kyau, suka bi ni
da kallo nima sunake kallo,suka kalli kayana dake
lode gefe daya suka kalli juna. dayar ta taso ta
zauna gefena tace sannu da zuwa turkish, dyar
dake can itama tazo sannu da zuwa wannan
dakin namu, itako dayar gabana ta tsugunna tace
shin 'yaruwa yaya sunanki? nace ni asma'u
ahmad , kufa? ta gabana farar ciki itsce ta soma
fadin sunana Amina turaki, mahaifina mataimaki
nega shugaban kasar nan, ta gefen dama tace ni
ko sunana bilkisu salis marfa, mahaifina shine ne
gwamnanjigawa a yanxun ta gefen hagu tace
fatima shehu, ni daya ce daga cikin jikokin shehu
barno mahaifina shahararren dan kasuwane.
da fatan zaki saki jikinkidamu tare da bamu
goyon baya mu zama aminai,nce hakana fiso kun
tabajin inda zaman makaranta yafina gida? is
gurina kan na hada watana maida jikina nayi
kyau red house duk muke dasu mina haka muke.
kiranta tuni house captain ta zabeni a
saurauniya, duk da kyawawan makarantar
kokarina yasa kawayena like min, har ma da yan
class ss1 n shiga lokaci guda sunana ya koma
sarauniyar , duk cikin mkaranta muna da abokai
maza yan class duk da bana shigemusu amma
muna taimakon juna. zama da su mina yasa na
goge har na manta da duk wani bacin rai,ban
taba tunann akwae ranan da zatazo har inyi
dariya ba, dana zata dariyata takare . ashe
bahakabane, yau gashi masifataa ta dawo yanga
da tsiwa duk sun dawo,dama gasu mina 'yan jan
aji sai nace mana group dinmu yan jan aji mun
cika girman kai. bana mantaa lokacin inter
housee na yarda naci sunan queen.wayyo Allah
shigar da yan red housesukayi da shirin da
captain dinmu ta min zuwa farentinmu, mun
burge mu nemuka zo na daya.ya aliyu da ya
usman ne sukazo min su kansu sun yaba da
shigar queen. mune mukazo na daya sunce min
ya umar ne ya turo su dan an mishi waya ana
son iyayenmu suzo muyi a gabansu, shine ya turo
su, don shi suna ta shirin biki yana zarya
tsakanin yola , kd da abuja
sunyi kayatccen biki irin na masoya , amarya
tasha kayan matsi duk dan ta hade kada ango ya
gane wani ya riga shi bin hanyar. akwatina 12
dam da kaya masu tsada haka aka diba zuwa
yola, a ranar jajibarin daurin aure suka shirya
wani shegen lunchin kusan duk wani saurayin ta
ko nace abokin shashashancintaya halarta in ka
dauke alhaji sambo wanda kishi ya hana shi
zuwa, kuma yace to zo suyi na ban kwana kafin
nan da ta tare gidan mijinta, inko taki zaiyi yanda
mijnta zai gane. haka nan duk ya daga mata
hankali gurin lunchin din sai waya yake mata .
ango ya damu da tambayar wake ta kiran haka?
tace mutane , ta kashe wayar. da dare suna tare
da sojan ta har zuwa sanda ya tafi masauki
sannan ta kunna waya. alhaji sambo ya kira yace
ta rufa ma kanta asiri tazo yanzu inko ba haka
ba zai shirya mata tuggu, dole taje gareshi cikin
wannan daren ya kwashi garar da akayi wa ango
tana ji sai da safe ta dawo gida, bataso haka ba
duk da yawan kudin da ya bata , haka daai ta
kara wasu 'yan shirye shirye , an daura auren
bayan sallah azahar kasancewar ranar asabar ce,
ya umar jin shi yake yau tamkar sallah sunyi
dinner katafariyar dinner da abokanshi suka c
burn shirya mishi tun bara yace musu auran ya
mutu su bari sai zai yi wani su al-amin manyan
abokai sai yanxun suka shirya da ya umar sbd
yanda yayi mishi tonon silili lokacin. auran mu,
yayi ta tura wa yayita turawa abokan su na ko
ina da batun auran. son ya umar lokacin ayi
komai a boye .amma sai alamin ya yayi ta mishi
tallata a waya wannan ya kawo musu dan sabani
sai fa yanxun daya wanke kanshi gurin
bingimbyafi, yayi duka d aeso boki yayi agun. sai
dai farida bata kwanta mishi ba, duk kyanta nashi
gurin kyawu in ya cika yawa hadari ne.
*amma sai al-amin ya yayi ta mishi tallata a
waya wannan ya kawo musu dan sabani sai fa
yanxun daya wanke kanshi gurin bikin gimbiya ,
yayi duk abin da akeso aboki yayi aagun. saidai
farida bata kwanta mishi ba, duk da kyanta nashi
gurin kyawu inya cika yawa hadari ne.***
hafis lady ta dubi farida amarya tace in fata kin
gama amfani da duk kayan da inno ta hada miki?
farida tace ke dai bari,kinsan Allah , saida na
gama komai dan iskan nan ahj sambo ya rusa
komai, da sauri hafsi lady ta mike tana fadin
amma ke farida Allah yayi 'yar iskar baiwa,
yanxun dan jaraba da rashin hakuri ke da za'a
kawo gidan miji sabon jini shine kikaje kika mika
kanki ga wannan tsohon ya shanye duk dan
tattalin da tanajin da aka ma ango? farida ta dubi
aminayarta ta cikin damuwa tace wlh kawata ba
da son raina bane bana ce miki yana ta damuna
da waya ba? tace bana ce miki kada ki daga
wayar ba? tace in ban daga damun da yakemin
dole na daga, cemin yayi in har banzo munyi na
bankwana ba , zai min tuggun da soja zai gane
kinsan ko ba zan so haka ba. hafsi lady tace me
ya hana ki kira ki sanar dani? yanda kike son
soja haka yake son mulki sai kice mishi kema zaki
fito ki fada ma 'yan jarida alakarku tace kash,
duk tunanin baizo min ba , to yanxu na danyi
amfani da wasu, tace inma ya gane ki hada da
kissa da kuma kisisina, sai kice fade aka miki tun
kina karama, inko bai gane ba ki share shi. farida
taja filo tace aiko kin kawo shawara kawata
nasan zai gane yanda yake kurin ya auri salihar
mace ya sameni fanko dole hankalinshi ya tashi
sukayi dariya sannan suka tafa
hafsi lady tace sauaran yanda kike son shin nan
ki nuna zakewarki da zalamarki zai iya ganewa,
kiyi ta nokewa kina....sllamarango da abokanshi
ya katse hirr tasu, nan take farida ta ja gyale ta
rufe fuskarta,sun gais bayan barkwanci aka sai
baki haka ango ya raka abokanshi sannan ya
dawo. sun gabatar da sallar ma'aurata yayi 'yan
tamboyoyi game da addini babu (not clear) dama
ya zaci haka kasancewar ta kamila a nashi
tunanin. soyayyarshi ya shiga nuna mata tare da
wasanni tana nokewa tare da nuna tsoro hakan
yasa shi binta a hamkali, yana da ilmi
musamman na fikihu yasan sirrin mata da yanda
halittarsu take hakan ya shiga bin komai a sannu
amma sanda ya kai kofar da ya jima yana raya
ma ranshi yanda zai bude ta, sai kawai yaji ta a
bude, hakan ya saka jikinshi sanyi take komai ya
lafa, ruf da ciki ya kwanta sai yana ji tamfar
mafarki, kuka ta saka tana fadin innalillahi wa
inna ilaihir raji'un dama nasan haka zata kasance
a kaina, ya daure ya dube ta amma ya kasa
magana, ta mike tare da neman kaya tasaka
sannan ta dauki gyalenta ta rufa ta tsugunna
gaban gadon inda yake kwance ka yafemin kuma
Allah ya baka hakuri nasan ban caacanci ka zana
dani ba ta mike zata fita yayi karfin hali ya tashi
zauna a kua bakofayc z n,ta jyo fuskashi tamkar
bai taba dariya ba gaban ta ya fadi.
[1:56PM,

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login