Showing 15001 words to 18000 words out of 59518 words

Chapter 6 - FUSKA BIYU COMPLET BOOK PDF Writing by Halima k. Mashi.txt

bar shi ai kuma
naga kun cika motar,ya ce bari wasu su sauka
haka dai dole muka shiga.
Muna isa bn jira komai ba na shige gidan Abba,
na bar su suna mgn d Rah,a.Momy tana ta
kiciniyar shigar ma d baki wadanda suka iso
yanzn nan da abinci sai ta ganni tayi turus yaya
dai 'yar gidan Momy? Na ce kaina ne ke ciwo
gajiri,ta ce tofa,ina zuwa ta shiga da abinci
dakinta ta fito,ta kira Anti Amarya ta ce bani
makullin dakin Soja (Haka take kiranshi) ta ce
Momy me za ki yi a dakin?Momy ta ce kwanciya
matarshi zata yi ni dakina cike ke ma haka,Kin
san kuma ba hayaniya take so ba,Ni ina cn ban
son ma kome akeyi ba sai dai naga Momy ta
bude kofa ta ce zo ki shiga 'yar Momy,ni dai bn
ma san dakinshi ba ne tunda ni dai wayona ban
san shi ba,daga baya nake ganinshi gwanin
Kamshi na leka bedroom din naga ashe hr d Kofa
ina zaton kofar ita ce ta 6ulla waje kusa d ta Ya
Aliyu,na kwanta kn duguwar kujera idanuna fes
suka sauka kan hotonashi sanye cikin kaki,na
tsura ma fuskarshi ido yanayin hoton ya burhe ni
hannunshi yana gefen kanshi alamar sarawa,na
sani Ya Umar yana da kyau sai dai bana son
shine na rumste ido ina tunanin zamn doya da
manja da zanyi. Na tuna jiya jin wasu kawayena
suna min murna nayi dacen mijin nunawa
sa'a,sai wata ta ce ai bana sonshi,nan suka cika
da mmk. Samira ta ce ke ko me yasa ba ki san
shi gashi mai kyau gashi Soja mai mukamn
Captain Samun irin su locky ne ke da ba kya
gurin in kin tanka to na tanka,ina jin Rahma
Momy tana cewa ina nan dakin,muna nan kwance
muna hira jife-jife hr magrib tayi munyi sallah hr
da Isha'i ai bacci ma ya soma dauka na sai
kawai naji ana fesa min nono (wato salalle)ya
Allah bakin ciki kamar me? Na saki kuka Momy
ce ta zo ta hana,ta ce su fitar mata a gida nan ta
lallashe ni bata so in wannan kukan nawa samin
jikina ya tashi,tana dakin naji Abba ya kira ta
tana fitowa naji yana ce mata nayi waya da Umar
dole yazo daurin auranshi gobe in ma zai zi ne ya
koma shi ya sani amma lallai ina son ya zo cikin
jin dadi Momy ta ce hakan yayi in baya yazo ya
tafi da matarshi,kwana nayi babu bacci addu'ata
daya ita ce Allah ya dauki raina kafin gari ya
waye a daura min aure da ya Umar,da safe
zazza6i na tashi nayi kuka na gaji.rayuwa kenan.
Misalin goma naji ana ga Ya Umar tamkar in bar
gidan haka naji nan akayi ta shigowa da
abubuwan tsaraba,su katan katan na drinks tun
daga kan ruwa C way,hr zuwa kalolin Juice
hakan ya faranta ran Momy da Abba hr Momy
take tambayarshi ya sanar a gurin aikin nashi?
Ya ce wlh Al-Amin ne ya dinga tura ma abokan
mu da message ta waya,wadanda yasan Number
dinsu,ta ce ai Aminu yaron yana kokari ko nan
yana ta hidima da ita da kawayenta.ya mike yana
cewa Anti Fa? ta ce tana can tana fama da baki
'yan Bauchi d Gombe duk sun zo ya ce bari in
rage zafin nan ya dan tsaya ganin dakinshi a
bude kamar kar ya shiga sai dai ya auno kai. lkcn
ina kwance,Rahma d Jamila kanwarshi suna
kallo.Ya tsaya yana kallonmu,ya ce kai waya ce
ku bude min daki hr d kunna min TV? Cikin in ina
Jamila ta ce Momy ce ta ce mu zo nan ta kashe
TV ta mike Rahma ma ta mike suka fita,ni kam
jikina ba karfi amma duk da haka na yunkura zan
tashi jiri ya kuma yardani,ya ce min ke wace irin
macacciyar yarinya ce???
Ki bari a daura auran mana kafin kizo ki tare, na
mike sbd nan take naji karfi, na dube shi kamar
zanyu mgn,ya zabga min harara,na duka da kai
na fita ya rakani da dogon tsaki,dakin Momy na
shige ina kuka tayi-tayi in gaya mata dalili
naki,duk da kuruciyata ina jin nauyin gaya mata
abin da ke tsakaninmu da ya Umar yanda take
dawainiya dani an daura aure misalin karfe 2 gidn
su Momy tankam da mutane,ni ko na kule can
uwar dakin Momy ta shigo ta zauna kasa dani
tasa hannu a wuyana,zafi taji rau ta ce haba 'yar
gidan Momy wane irin zazza6i kenan? Ta shi kiyi
wanka mana?Na ce Momy bakin ce baki gayyaci
kowa ba?ta ce ai bn san wanda ya gaya musu ba
ne,na ce ni sanyi na ke ji ba zan iya tashi
ba,Momy ta yi tayi naki tashi dole ta barni na
sha magani na koma na kwanta. Can zufa ta rufe
ni da kaina,na tashi nayi wanka a bayi Momy na
cikin daki ta shigo ta same ni nayo wanka ta ce
yauwa ga Soja nan ya ce kizo ga abokan su na
gurin aiki da su Al-Amin suna jiranki,ta tsaya na
saka wani lallausan leshi fari mai fulawa blue ta
bani farin takalmi da gyale da jaka na ce bar
jakanan Momy.
Momy tasa min zinari kirar Dubai ta feshe ni da
turaruka duk da kasancewar ban shafa komai ba
sai hoda ina fitowa mutane suka soma fadin kai
Amarya ta hadu fuskata murtuk babu fara'a na ce
Momy ina suke? Ta ce dakin shi ne ko falon baki
ne je ki duba su Rahma suka shigo ashe 'yan
iskan hr anko suka yi,kallon banza nayi musu,
Shema'u ta ce kinyi kyau Asama'u na ce lallai
Rahma kema kin shiga layin makiya na ko? Ta ce
dana yi me? Na ce ga shinan hr da yin anko ko?
Ta ce ayya don Allah yi hkr nayi mama ta dinka
min zuwana kenan ko wanka da na kinayi Mama
ta matsa min Shema'u ta ce mune kenan
Makiyanki? To kije gida ki gani cike da 'yan
uwana ne sa dana kusa,wata motar ma yanzun
ta iso batun anko da kike yi namu dabn na su
Mama daban,dn haka sai ki san makiyan naki
suna da yawa naja tsaki a raina na ce kwaji da
shi Momy ta leko ta ce Asma'u ba ki je ba yana
ta waya wai suna falon baki na tafi tare da
Rahma a kofar falon naga Al-Amin ya ce yawwa
'yar Amaryarmu kin 6oye ki zoga bakinmu suna
son ganinki na ce gsky ba zan zhiga ba ya gaya
min mgn a gabn mutane Allah zan rama na gaji,
Al-Amin ya ce a'a ya Mafita muka daine abokan
shi ne na can gurin aikin su, Na ce to ni wai ina
ruwa na da abokan gurin aikinsu? Amin ya ce
dan Allah ki taimaka in mun gama bikin nan lfy
an fita kunyar mutane a san yanda za'ayi na ce
ni dai in zaka taimaka min ya sake ni to,Al-Amin
ba tare da wani tunanin ba ya ce to naga sun
kalli juna da Rahma sunyi Murmushi na ce
menebe na dariya?Harsuna hada baki gurin fadin
babu komai.
[1:44PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1----13
Suka shige gaba ina biye dasu muka shiga falon
kato ne falon abba amma cike da mutane suna ta
ciye-ciyen kaji da abinci ga kalolin juce naji kunya
sosai da ganinsu kadan kadn ko ina a hankali al-
amin ya ring zag ywa dni yana gabartarw muna
gam gaisawa ban tsaya jin wani dogon turanc ba
nayo waje ina jin sanda dayan da akace sunanshi
suleman yace amarya sai kinzo zamu yi namu
bikin a can ban dai tanka ba. rahma ma data
rako. ni nan baya na barota . sanda na iso tsakar
gidan nannaga momy suna tsaye da ya umar da
wsu kannanta yana mata baynin shi zai tafi tare
da abokin shi sbd akwai abubuwan da zasuyi kila
karin girma ne.momy taace Allah ya taimaka
kaga abbanku? yace yaana tare da mutane ne
amma xan gnsh yanzun tace to amaryar fa? yace
ai zamuyi sallama tana can gurin abokan nawa ,
momy tce gta can ta wuce ya faga sanda nazo
na wuce su amma sai yace bai kula ba, ya dubeni
har kun gaisa kaina na daga yace to shi kenan ni
zan wuce a raina nace kafi ruwa tafiya ,momy
tace amma dai ba sallamar kenan ba ko? kai da
kace sai wani satin za'a kaita ai ka bar mata
wani abun sannan ku dan zanta. yayi shiru
canyaace ko ina cike yake,momy ta harare shi
dakin ka babu kowa ai.
Ya dube ni sai kije ina xuwa na tsaya momy tace
jeki dakin nashi ki jira shi kinji yar momy?
hawaaye na nazuba shar na tad, ina zaune kan
kujera na bar hawayena su zuba son ransu tunda
ni nama rasa me zanyi inji dadi kamar yaqi ya
shigo dakin ya dube ni, har da sauri nace kije
ganinan sbd son maza. Allah yay wadaran mace
mar kamun kai mara aji, to bari ma in shaida
miki bana ga kanki yana rawa ba, tsautsayi ne
yasa kika aure ni gabana ya shiga faduwa, yaci
gaba shawarar da zan baki itace kada ki soma
gangancn yarda a kawo ki gidana,domin in har
kika yarda kaddara ta sa kika zo yayi dan
murmushin mugunta , sunanki sorry kada ki
manta kn tab watsa min ruwan dai fasiqa ba,
sallah 5 rana aikn hajj da ummura shida duk bana
mance rokon mace ta gari nasan Allah ba zai
barni ba, zai amsa minute na dube shi idona jajur
nce ka sakeni nima ai naga ba sonka nakeyi ba
da kace kar na yarda nazo inda kake mezai hana
baza ka fadawa su momy da kanka ba? yayi
murmushin mugunta , ni inaso na gama da
mahaifana lfy ba zan basu kunya ba , kuma
bazan ki jin maganar suba kuma abu na karshe
da xan gaya miki shine,zan aiko da komai kuma
xan tanadar miki masauki zan bada motocin da
zasuzo daukan amarya amma duk dan na faranta
ran iyaye na amma inkin yarda kn shiga motor
nanhar kika kai kanki inda nake ? yaja wani tsaki
tare da fadin hum-hum yayi wani guntun
murmushi
Ya saka hannu cikin aljihun wandonshi ya ciro
rafar yan dari biyar ya jefe ni a fuska da ita yace
ga sadaka bance kada kije yawo ba, amma ki
sani zina da aure babban laifi ne koda yake ke
laifin gaba kikaa saka shi ba baya ba, zuciya ta
ta baci nima cikin dacin rai nace ni di ba
mazinaciya ba ce sannan in har ka kawo mata
zan shiga kuma zanso don Allah kayi tsirena ba
laifin ka bane, iyaye na suka jamini na saki kuka
mai karfi yace kada kisake ki tara min jama'a nan
gurin domin in har momy da abba sukaji abin da
yake faruwa har ransu ya baci to saina kiyafi
nasu baci domin ni nasan zafin bacin ran mahaifa
duk karancin shekaruna nasan , habaici yayimin
kuma kafin nace komai har yayi waje don haushi,
kifa kaina nayi akan kujera ina kuka, is yaje yace
ma momy wai gani can ina kuka bai san dalili ba,
kuma ya rarrashe ni nakiyin shiru. momy tazo
tana lallashina wai inyi shiru yace ya lallashe ni
nakiyn shiru, ko dai zn bishi n? nace a'a kaina na
ne yake ciwo muka koma dakinta na sha magani
na kwanta. haka biki ya tashi ana ta son barka,
amma ban dani da ango, kullum zai yau waya
gidan yace a bani in amsa sai ya dinga gayamin
bakaken maganganu, niko inba'a gabanmomy
bane sai na aje in a gabanta ne sai na daure in
hakura, har kwana 8 dinnan kowa yasan na rame
matuka, ya aiko da kudin jirgi na kusan mutum 3
banda nawa yace a ciki har antyshi a cikin masu
zuwa kai ni ranar tfiya da safe nasha kuka, tun
ran sstters day sai yau na fito waje gdan mu
kuma tun randa momy ta kaini asibiti ban kuma
shiga ba sai yau su anty ne suka kaini amin fada,
duk sunmin nasiha su umma da hajiya mama
kam cewa tayi in naga dama in zauna in naga
dama kada in zauna ita dai ai ta gaya ma ya umr
in namishi rawar kai ya min dukan mutuwa. Alhaji
ya min fada da nasha, kuma yace umar da yake
namiji yayi na*am da wannan auran dan Allah
kada ni in basu kunya, inko har na zama sanadin
mutuwar auranbai yafemin ba duniya da lahira
sannan kada na doso garin kd da sunan aurena
ya mutu ko kuma yaji kai ganin gida ma baya
nemana sai nan da shekara, ina ta kuka ak sani
motar har filin jirgi rahma ta rakani da kyar aka
rabamu. mun rungume juna muna kuka har sanda
muka isa garin kuka nake, motoci ne sukazo
daukar mu gud 2 duk sojoji ne drivers din, dma
'yan rakiyar anty amarya ne sa hajiyar gidnmu,
sai kanwar mama inna shatu.
Katon gida ne mai dauke da manyan flat guda
hudu ginin iri daya ne ya tsaru, na farkon shine
na ya umar nan muka shiga ta qofar cikin daga
nan sai ka isa qatan falo mai masifar tsari da
kayan alatu, yana dauke da dakuna biyu dayan a
kulle danyan a bude,muka shiga na budan gado
ne mai kyau da sauran tarkacan shi sai toilet da
wordrop muka xauna ina ta lura wani yaro ne
kirista dan qabilan ibo ya shigo mana da abinci
ya ce oga yace ku jira shi ya fita.sun ci sun sha
suka yi dani inci abinci naqi dole suka barni, inna
shatu tace in sun tafi na ci nan muka kwana,sai
washe gari da safe ya dawo ina jinsu yana ce
musu legos yaje kuma bai samu gama abin da ya
kai shi ba sai dare, shine yayo sammako jirgin
qarfe shida suna karyawa suka soma shiri, kuka
nasa suna ta lallashina shi da kanshi ya kaisu
filin jirgi. farida ta xubama wayarta dake kan
teburin gacnta ido,ga wani dogm tagumi da
tasha, duk wanda yasanta yana ganinta yasan
yau sai a hankali ba harka.
Tunaninta daya yanxu sojanta yana can tare da
yar iskan yarinyan da tsinannun iyayanshi suka
xaba mishi,tana tsoro duk da yace sam baya
qaunan ko ganin yarinyan tasan mace fa mace ce
duk muninta musamman da ta tuna cewa ya
sanar da ita yarinya karuwa ce bin maxa take yi
danhaka baya sonta, inko xasu xauna tare tayi
imani har ga Allah sai yarinyar nan tayi yanda
tayi ta shawo kanshi ya saurareta. halama tana
bin malamai, wani dogo tsaki da taja shi ya jawo
hankalin alhj sambo dake ta amsa wayar
shugaban masu kamfe dinshi yayi sallama da shi
sannan ya dube ta yace na kula yau kina ciki
damuwa farida,gaya min menene damuwar?
kudine? ta ce a,a ta miqe tana cewa gida xan je
yau ba xan dade a club dinnan ba. ya miqe shima
xuciyarshi cike da yaudara idanunsa suna mata
kallan sha'awa ya kama hannuwanta ya maida ta
xauna, shin kin taba shan maganin damuwa? bai
jira amsar ta ba ya balle hancin kwalbar giyar
dake gabansa ya cika wani kofin glass ya miqa
mata,amshi faridata duk wata damuwa ta duniya
kinga maganita
Cikhn xafin nama ta amsa ba tare da wani tunani
ba, ta daga kofin sai data gama sannan ta aje ido
ta tsura mishi tana ganinshi ya koma mata
sojanta.murmushi ya ke mata irin wanda yake
qayata sojan ya miqe ya kamata sannan ya dauki
jakanta da kuma wayarta sai mota, tana ta mishi
sambatu har suka isa gidan shaqatawarsa suka
ci gaba da masha'ansu yanda suka saba,wal
iyaxubillah.da safe ko sai gurin tara ta farka,jinta
tayi wasai sai yar damuwar dan kadan, tayo
wanka ba batun sallah ta sami alhj sambo yana
karyawa dama shi mutun ne wanda ya ba ciki
gsky da amana dan haka ga lodin abinici nan
kala kala yaci wannan yaci wancan ya dube ta
yar kyakkyawa ta kin farka? ta xauna da dan
murmushi na tasg ya kk? yace lfy ba lau ba,da
me ya faru kace ba lau ba? yace da farko wanene
sojanki? kuma wanenf umar? ta mishi wani duba
sannan tace menene? yace jiya na shiga gurare
da yawa wanda ada baki bani damar shiga sosai
ba,saida giya ta gaya miki qarya cewa ni sojanki
ne tayi tsaki malam banasam binkice.
Tunda dai ni ba matarka bace, kuma umar inka
damu kasan shi to,ina mai farin cikin shaida
maka shine xan aura. alhj sambo ya tsura mata
ido.a ranshi yana raya aiko Allah bai qaddaro
aure tsakaninsu ba, ta auri wani, baxai so su
rabu ba, allah ya kaimu tace amin cikin isa.kuma
daidai lkcn wayarta ta soma tsuwa alamar saqon
waya ne ya shigo, ta ciro sai taga kiqan sojanta
har guda ashirin da takwas tun jiya xuwa yau,
koda ta duba sakon sai taga ban hakuri yake tare
da lallashi yasan fushi ne ya hanata daga wayar
amma ta saurari isowarshi yola nan da qarfe
daya. ta dubi lkc qarfe goma ta soma tattara
yanata yanata ya dube ta menene? tace babu
komai gida xanje, yace bari inyi waya akaiki dan
bai dace a matsayina na dan takara a ganni da
mace ba, xai iya kawo min matsala ta gefen
abokan gaba, tace bama sai ka kira kowa ba bari
in tafi,ta gama shirya komai sannan taxo
gabanshi yasan nufhnta dan haka ya soma
neman inda ya ajiye check dinshi ya miqa mata,
farida na yaba jiyan.
[1:46PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1----14
Dan haka gashi rbt duk yanda yayi miki ta
tsugunna ta rbt dubu dari biyar yace sun isa, tace
i, yace to nidai bana san abin da xai sa mu
rabune, ko kinyi aure, tace dan wannan ai babu
ji.Ina daki sanda ya umar ya dawo daga kai su
anty amarya. nasan hakan ne ta hanyar jin
danayo yana cewa yaran mai suna emeka yaje
but din motarshi ya kwaso plantain, sannan yana
son ganin shi tare da duk masu mishi aiki ma'ana
sauran yan aikin su biyu,mai ba fulawa ruwa da
kuma mai wankin motoci da shara ban da sojojin
masu gadin shi.ban kuma jin duriyarsa ba har
nayi sallar isha na kulle qofata na kwanta. sai fa
da safe nayo wanka na gama shafa mai raina a
cushe ga wata shegiyar yunwa da nakeji ta tun
jiya raina bai gama baci ba, sai da na bude kayan
sawana kaf babu nawa na gida, duka na lefe ne
na dai dauki wani material mai taushi fari mai
bulun fulawa na saka ina daura dan kwali naji
wata irin dukan qofa tamkar xa'a karyata,tsoro
ne ya kama ni na soma tunanin ko wani ne ya
shigo ya umar baya nan?
Amma sai naji muryanshi ce take fadin ke! ke!
malama xo nan ki bude ma mutane qofa, kamar
dakinta,da sauri naje na bude qofar yana tsaye da
wando 3kwata,na kakin soja sai singilet itama ta
kakin ce saidai mai santsi ce, fuskarshi murtuk
tamkar hadarin magariba, ya daka min tsawa
kallan me kike min? nayi maxa na kauda
kaina.yace ta mara kunya yau Allah ya shigo da
ke hannuna, xaki gane kuskuran da nace kada
kiyi, gashi kin qiji kinbi san xuciyarki ta xaki sha
wahala.duk masu aikin nan xan sallame su sbd
abu 2,na farko kema ai yar aikince, sannan inma
na barsu tunda kin riga kinsan dadin maxa to
xaki kafa min xina a gida, dan haka na sallame
su sai ki fito in nuna miki aikin ki,in kinyi kuskure
daya ki sha duka. haka xaki yi ta bauta har my
farida taxo kin dinga mata aiki, oya see your eyes
lk a mujiya kina kallona a gurin,qaryan masifa
kikeyi, na fito yayi gaba na bishi daga kitchen ya
fara, gashi nan xaki dunga maku abinci keda
masu gadi kada kisa dani dan baxan ci
jagwalgwalonki ba.
Sannan bana san qaxanta kada a barmin kitchen
da datti falo a share agoge komai wanke toilet da
gyara duk dakunan gidannan.sharangefanmu
xuwa mota,sannan kakina dakika jiqa duk dadai
basu bane yanxu suna cikin aikinki kina jina ko?
hawaye yana xubo min nace to,yace in kin yarda
na kamaki da wani kuskure sunanki sorry, ya juya
ya fita. a raina nace azzalumi ya

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login