Showing 18001 words to 21000 words out of 59518 words

Chapter 7 - FUSKA BIYU COMPLET BOOK PDF Writing by Halima k. Mashi.txt

xanyi dole inyi
tunda iyayana sune suka bada ni dole na haqura.
da abinci na fara duk da cewan ban soma sakar
mana girki ba ina ganin yanda su anty aina suke
yi, dan haka na dafa ruwan tea na soya uban
dankali sbd nasaba ganin na gidanmu da yawa,da
makunsan ance duk abin da iyaye suke yi ko
kuma nace ya mace duk abinda ake yi agidansu
krt ne itama shi xata yi a gidan auranta.na gama
na soma da dakina sannan falo na shiga kitchen
ina gogewa ya umar ya shigo fuska tamke yace
ina abincin masu gadin? na bude kula shaqe da
dankali da qwai ya xuba min ido cikhm takaici
baki da hankali dama nakula da haka,wannan
uban abincin fa?
Na xuba mashi ido cikin tsoro yace bar kallona da
idanun mujiyanki a gun, na sunkuyar da kai yace
ke da wanene wannan dankalin? na ce ta to to
ban san yawan masu gadin bane, yaja tsaki ba
xan dauki almubaxxaranci ba, dan haka sai ku
cinye rar dare ga gun da xaki danna nan xasu xo
su amsa ya fita na bishi da kallo yau ne na soma
ganin shi da shadda ba kaki ba yar garke ja sai
maiqo takeyi. araina nace ga mutun har mutun
amma a cikin xuciyarshi mugu ne a mugunta
bashi da abokin tarayya. na ci gaba da aikina na
gama na fita na share cikin gidan sannan na hau
wankin motocin guda uku ne duk na wanke, ban
taba wanke mota ba sai yau a gajiye na koma
kitchen na danna gun daya nuna min, sannan na
xuba musu cikin wata kular na xuba musu komai
cikin jug wato tea dana hada, na basu kofuna ya
leqo ta windo ya ce gud mrng madam, na danyi
fara'a kadan na ce, mrng naci gaba da aikina ya
miqo hannu na bashi ya tafi.na xauna falo na
soma karyawa kenan, na dubi agogo sha biyu a
raina nace lailai na sha aiki.
A raina nace lalle na sha aiki inko haka xanyi
kullun aiki ya same ni, ni asma'u, ina cin abincin
nan ina hawayen tausayama kaina,ina gamawa
naje na kwanta, wani wawan bacci ne yayi awon
gaba dani sbd gajiya ban farka ba sai karfe 2 da
rabi ina ganin lkc na duro daga gado na shige
toilet wanka nayo tare da alwala na idar da
sallah na saka doguwan bakar riga na daura dan
kwalin ban ko shafa mai ba sbd bashida amfani
in tsaya yin wata kwalliya. na danna kiran
maigadi sai gashi da sauri ya ce wldn madam
ban ma tanka shiba na miqa mishi dankalin cikin
wata kular ya miqo kayan daxun nima na diba na
bude fridge, ina neman ruwa, sai naga ashe frixer
ne shaqe da kifi,nama, kaji dadai sauransu na
komo falo, can soqon tsakanin kujera da kujera
naga wani dan mitsilin abu kamar fridge naje
amma na kasa budewa.ina xaton ya umar dan
kanshi ya aje wannan fridge din tunda daga gefen
kujeran xamanshi take, na gane kujeran xamansa
ne ta hanyar ganin jaridu da sauran takacan shi
a kanta.
Hatta phone landline a gefen kujerar take na
koma kitchen na taro a gun wanke wanke na
dawo haka na yini iar dare muka cinye wannan
dankalin da qwai gyatsar magwas ta dame ni shi
dai bansan shigowar shi ba ban kuma damu da in
saninba. suna tare da abar sonshi,wanda ta
canxa shiga xuwa atamfa yar holan da qaton
hijabi maimakon riga da wandon da ta fita dashi,
yayi lallashi tare da qara nuna mata tsananin
tsanar da yayi ma amaryan tashi tare da qara
karanto mata mugayan halayan amaryan,sannan
ya labarta mata irin matakin da yayi niyar dauka
na axabtar da ita, har sai wuya tasa ta kama
gabanta.farida taji dadin hakan amma bata nuna
ba sbd iya bariki, sai tace kar dai a tsananta
fa,yace ke dai ki ta mana addu'a baba ya sauko
duk randa kika shigo gidan xata bari.farida ta ce
iyayanku fa? yace ko ban sake ta ba sai dai ta
koma gun su da xama kiyi qoqarin shawo mana
kan baba mu samu ya yarda kafin na koma abuja
dan Allah ya sani baxan koma abacha barrack da
wannan yarinyan ba.ya je yanemi masauki..
Da safe ya zo sunyi sallama in da ya cika su da
kudi ya tafi jirgi ya biyo zuwa gida. Tun tuni ya
dawo amma bai shigo ba sai 5 ni ko a wannan
lkcn na gano wani dan fili can baya gurin da
yalwar iskar Ubangiji ba kamar sanyi falon nan ba
abu kamar hauka, AC 2 ga fankoki hr 3 bayan ko
wani dan couredor na gani kusa da dakina na bi
sai naga kofa ina budewa sai naga fili hr da 'yan
fulawowyi da kujeru 2 tun da na gama abnci rana
dama jalof din taliya nayi,ina gama wanke-wanke
na dau abncina na nufi can. A can na yi azahae
haka La'asar na kwanta kan sallayar na saka filo
sanda ya shigo ya bi ta garejin shi na aje Mota
anab ranshi ya soma 6aci sdb yanda yaga
motarshi duk jirwaye duka 3n ashe 6acin rai na
gaba sai da ya bude motar yaga yanda na lafge
motocin da ruwa takaici ya ishe shi ya shigo ta
kitchen bai ganni ba ya nufi dakin,shi ne hr toilet
bana nan,ya dinga fadin ke ina ki ka shiga ne? Ke
sam ni ban ji ba,bam san duniyar da nake ba,ina
ta shara baccina ya ce lallai kenan hr ta soma
zuwa yawon gulma a mokata don yasan ba za a
bar ni fita ba sai da izininshi wato masu gadi hr
zai fita sai kuma ya tuna da baya nan take ya
zagayo ya fito bayan. Saukar Marin da naji ita ce
ta katse min mafarkina da nake yi wai gani ga
Rahma a mkrnt muna ta lbr. Firgigit na tashi tare
da rike kumatuna tsananin tsoro ne ya ratsani....
Na zaro ido jikana yana rawa ya ce uban wanene
ya saka ki ki jika min mota? Cikin in-ina na ce na
na na wanke ne,hk ake wankin mota a garinku?
Fuu!ya fita sai ga shi ya dawi da belt ya zane ni
ya hana ni kuka sannan ya ce in yi ta tsallan
kwado,ya fita ya saka direba da maigadi suka kai
motocin gurin wanki ni ko nasha kuka hr na gode
Allah da na gaji na fadi a raina ina tuba uwar
wuyar da na sha gurin wankin motocin ban ta6a
wanke mota ba ban san yanda zanyi ba,shi yasa
nayi ta maka ruwa ko ta ina ina sa6o omo,jiya
ma haka nayi na zata gida ya kwana yaga sun yi
ne shi yasa yau ma na sheka musu ruwa ashe
bai ma dawo ba tunda sanda ya fita ban riga na
wanke ba. Bai kuma biyowa ta kaina ba hr bayan
magriba na rarrafo na shigo ruwan dumi nasa na
gasa jikina sannan nayo alwala.A zaune nayi
sallah sbd kafufuna sun gaji, nan na kwanta kan
abn sallar ina kuka,ni dai ban zo duniya cikin sa'a
ba,bn d Suraj da Momy Da Rahma bani da mai
sona ina nan hr 8 tayi nayi Isha'i tunda daji ne
cikin Inyamurai ban ta6a jin kiran Sallah ba sai
dai ka aduba agogo. Asuba ma dan dai jiki ya sa
ba da tashi duk gajiya asubahi tana yi zan
farka,na idar na koma na kwanta can naji tsawa a
kaina,na tashi shegiya ba ki ba masu gadi abincin
dare ba? an gaya miki gidana ana yinwa ne ko
rowa?
See translation
[1:52PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1----15
Nan fa gabana ya fadi na tuna bamma yi girkin
dare ba,da sauri na tashi da gani sai zani da
hijabin sallah Makaroni na dora nan na zauna a
cikin hr tayi na juywe musu na kira su suka
dauka na koma daki sanda zan wuce yana zaune
kan kujera da dama na zargi cewa tashi ce yana
waya da Gimbiyar tashi suna Syy Na gane
hakanne ta hanyar kiran sunanta da yayi ya ce
Farida my sweet heart kada ki damu na ce ban
ta6a ganinshi yana fara'a ba sai yau na wuce
daki a raina ina fadin bakin mugu. *************
Haka rayuwata ta kasance cikin wahala da bauta
tun ban iya wanke mota ba har na iya, don ya ce
ni zan ci gaba da wanke mota in nayi kuskure
insha wuya wankin kaki ma na kware hr Azumi
yazo ina jin shi ranar wata Asabar da aje saran
ganin watan na Ramadan ina goge -goge a falo
shi kuma ya na zaune yana shan tea. Da kanshi
ya dafa, wayarshi ta soma ringin ya dauka,naji ya
ce Momy ina kwana? Na juyo da sauri tunda na
zo nan gidan sai yau naji ya ambaci sunan wanda
na sani.tun da ba zama yake ba kamar in amshe
wayar in ce Momy ki zo ki cece ni don Allah
amma babu hali naji ya ce tana lafiya.
Ai tana bacci bata tashi ba na sanni aka tambaya
ya 6ulla min harara na ci gaba da aikina hawaye
ya ce duk san da za ki kira Momy bana gida yau
kuma bacci take kada ki damu Momy ai zamu zo
da sallah in na samu hali amma zaku ga aike na
Azumi a raba ma makota naku da na gidan Baba
Alhj,kudi zan turo Aliyu ya je ya cire sai a sai
komai hr na hidimar Sallah ko? Haka Momy tayi
ya nacin son Magana dani amma ya Umar ya ki.
Ranar Mndy ko ba ya nan na dauki landline din
falo zan kira amma abn haushi ban rike number
momy ba, sai fa gidanmu su kam kiran me zan
musu suna Murna sun rabu da kaya.Don haka
tsabar mugunta ranar Azumin farko dore nayi don
ya ki tashina da yake ban san anga wata ba sai
da safe na jiyo yana jin Radio ana fada a labarai
shine na kama baki duk da ban ci komai ba. Haka
Azumin yayi ta tafiya ban san in da yake shan
ruwa ba haka sahur. Masu gadi ne kullum sai na
musu da rana da safe direba ne kadai ke Azumin
shima bn san inda yake Sahur ba,ni dai dama sai
dai in na tashi akan lkc in dan hada tea insha in
ban tashi ba inyi dore,akwai ranar da har na hada
tea saina dubu a gogi naga ashe shida ma tayi
ban lura ba kai da Azumin nan nasha wahala
mara misaltuwa.
Duk na rame na lalace na fige sai ido a waje na
bakin shi yana cewa kamar na mujiya haka hr
sallah tazo shi kadai ya tafi kaduna kan ita zuba
ido ya ce in shirya shiru sai ma gurin direba naji
ya ce Madam Ke ba ki bi oga kaduna ba?Sallah a
garin nan ba dadi duk Hausawa sun gudu garin
su na ce eh sai ya dawo zan je kai ranar nayi
kuka hr na gaji dan nasa rai. Kwananshi 2 ya
dawo ina kwance ina jin shi ya turo kofata ya
jeho wata leda baka mai dan girma ya juya, na
tashi na dubu ledar kayan miyan ne irin kuka,
Ku6ewa, da garin yaji da daddawa. Sai Kuma
wata ledar mai dauke da wasu tarkace kamar
magani sai wasu wasiku guda 2 daya daga momy
daya daga Rahma, na rungume wasikun ina kuka
na soma duba ta momy. 'Yata ina fatan kina lfy?
Na yi kokarin jin Muryarki amma soja ya ki, Sai
ina ganin kamar yana wahalar da ke ne kada ki
damu ina nan zuwa cikin watannan zan sa Aliyu
ya rako ni in ganki. YA JIKI? Ya ce Kinyi 6ari
kwanaki Allah ya ba da mai amfani sannan ga
dan tarkacen mata nan duk kisha da madara sai
na zo. Momynki. Shiru nayi ina mmkin Ya
Umar,wai nayi 6ari? Kai namiji sai a barshi na ji
dadi in Momy tazo kafarta kafata, ba zan zauna
ba. Bayan na krnt ta momy, na kuma warware ta
kawata Rahma domin itama naga abn da ta
kunsa. Sis.....Asma'u Nayi Yi kewarki da zaton ki,
Musamman a mkrnt Malamai sun kewarki hr gobe
na kan yi kuka idan na kalli gurin zamanki a cikin
ajin Islamiya,sai dai na ka ji dan dadi in na tuna
Ya Umar mutumin kirki ne rike ki amana. Munyi
jarabawa yanzu muna SS1 kuma ni da Ya Usman
mun shirya don hr iyaye sun shiga ciki.A kwai
labari da yawa sai kin zo bikin su anty Aina'u
sauran sati 4,nasan kin sani. Aminiyarki, Rahma.
Haka wasikar ta zamar min tamkar Kur'ani,
kullum sai na karanta ina kuka ina fadin nima ina
kewarki Rahma, ina kewar mkrnt.Rayuwa ta haka
ta ci gaba da tafiya hr ranar wata Jumma'a na
zauna kenan a falo sai ga shi ya shigo tamkar an
jeho shi na tashi da sauri zan gudu dan ya min
gargadin kan zaman falo,wata rana ya same ni
ina zaune ya min duka sannan ya ce duk randa
ya same ni sai ya harbe ni tunda bai hada
falonshi da sunana ba. Don haka yau ma na ruga
daki ina kokarin rufo kofa sai gashi ya banko na
tsaya jikna na 6ari shi kanshi yasan ina matukar
tsoronshi sai dai ya ce haushen da nake bashi ko
zai kashe ni ba zan ce yayi hkr ba sbd tsabar
taurin kai,ya ce ke da karfi na dube shi ya ce bari
kiji ina ma dai zuwa ya fita can sai gashi da wata
'yar bindiga nan na soma sakin fitsari sbd tsoro
nasan zai iya harbina, ya saito ni sosai,sannan ya
kauce ni ya harbi bango nan na dauke numfashi
na na fadi tare da salati ga zatona ni ya bindage
ashe bango ya harba suma nayi sai da ya debo
ruwa ya zuba min na farka ya san na kara
tsorata dashi ina da daga kwance ya ce tashi na
tashi da sauri ya ce Momy zata zo gobe kinga
bindigar nan?na kalleta ta cikin tsoro ya ce yanda
kika ga na harbi wannan bangon ya huje haka
zan huda cikinki in har kika yi kuskuran gaya
mata halin da kike ciki.
Hawaye na zuba na ce bazan gaya mata ba,ya ce
ke ki ka sani dai ya fita kai Soja babu imani. Duk
da haka nayi murna da zuwan Momy da wuri na
gama aikina ya ce yau ban da wankin mota,nayi
wanka nasa sabon kaya wani yalon leshi mara
nauyi,dama tun da nazo kayana uku ne, daga
jallabiya sai atamfa da wani matarial wannan
yayi datti in sa wannan,to wace kwalliya zanyi
tunda nazo ko bakin gate ban taka ba,ban na
ta6a ganin kowa ba daga shi sai masu gadi suma
in sun zo daukan abncu,inazaune a bakin gado
ina tunanin yanda zanga Momy,oh Allah yau zan
ga na gida. Kiran Ya Umar na ji "'Ke!" Na taso da
sauri ya dube ni na dan lkc sannan ya ce to haka
yayi saura ki je ki saka sarka da dankunne kiyi
shafe-shafen ku na mata,bana son ki yarda
Momy ta gano halin da muke ciki za ki koma
kwana dakina hr ta tafi na dube shi da sauri ya
ce kada ki zata ko na soma sonki ne ba zan ta6a
sonki ba,ya ci gaba zan daure in ci
jagwalgwalonki hr ta tafi sannan yanzun in kin
gama ki zauna nan falo zanje na dauko su,zan
kara tuna miki kada kiyi ka sadar sanar da Momy
komai dan nasan kanki zata yi fushi dani kamar
yanda kema zan ha da ki da naki iyayan duk da
ke baki dama d fushin su ba,amma ki sani in ba
kya gidana sai dai ki shiga dny ce war
Mahaifinki,ko fa da ki ka yarda Momy tayi min
Allah in ta tafi zaka gane kuskuren ki,ya tafi
dauko su haka nayi jigum a gabn madubi ina
kallo kaina ni Asma'u wannan shi ne a dake ka a
hana ka kuka,lallai ban da ya ki ina ganin har da
sharri ake koya ma Sojoji, Da na yi kwalliyar sai
naga nayi kyau,na juya kwayar idunana da Ya
Umar ke kiran su na Mujiya irin idanun nan ne da
kwayar su ke da girma kuma sun fito na sha jin
mutune na cewa suna son idanuna,haka Suraj na
saka sarka da dan kunne na koma falo na zauna
ko in ce nadofanu ina kallon tashar Aljazira ina
zaton ahi ne yake kallo ya tashi ya tafi dauko su.
Sallamar Momy da Aliyu da Ya Umar ce ta dawo
dani daga kallon,da gudu na taso ina tsalle na
rungume Momy,itama cikin farin ciki ta ce 'yata
Asma'u oyoyo 'yata,sai kyma naga ta ciro ni
daga jikinta ta tsaya tana dubana, ta kai hannu
wuyana ta shafa ramin kirjina ta ce wannan
kashin wuyan fa? Na dubi Ya Umar ya 6allo min
harara nayi saurin fadin tun da tunda ya Umar ya
amshe tunda tayi 6ari ne nima na kakaro 'yar
fara'a na ce eh mana ba?tun lkcn ne kuma bani
da lfy ne ai Momy ta dube shi sannan ta dube ni
kin zubar da jini ne?Daga ganin jikin nan naki
babu jini na ce eh na zubar na kama hannunta zo
muje ki zauna,Momy na ce ya Aliyu sannu da
hanya ya ce yauwa Asma'u Ya umar ya ja shi
suka zauna Momy ma ta zauna naje da sauri na
soma loda musu abnci da na sha kala-kala
ga.farfesun kaji ga na kan rago ga farar taliya da
miyan kwai ga jalof din shinkafa momy fadi take
sannu 'yata da aiki duk namu ne? na zuba ma Ya
Aliyu komai ga mamakina sai naji ya Umar yana
cewa Madam sbd yau kinga su Momy watan kin
manta da ni ko? Na yi dan yake na ce to me zan
zubo maka? Ya ce sa min Farfesun kannan na
zubo Mashi na koma kusa da Momy nima na
saka cokali cikin nata....
Muna ci na kalli Ya Umar ya harare ni,Momy
ni,Momy ta kalle shi sai abu yake kamar hararar
wasa yake min yana yi yana murmushi,Momy ya
ce me ki ka gani? Ta ce Harararta naga kana yi,
ya ce ai ita ta sani Momy da da ni ta ke cin
abncin yau gulma ta tashi wato ta gan ki,ai
Momy za ta ta fine .Ni dai sai naji abn wani
banbarakawai wai namiji da Suna Hajara. Yanda
na lura ya ji dadin naman kannan sai da ya
kara,kun san yin girki yau da gobe kan sa mutum
hannunshi ya goge, don haka da ba ma yi a gida
muna gani in su Anty Aina suna yi akan ce muje
muna yi musu irin jajjage ko yankan albasa ko su
Alayyaho,hakan yasa na riga lura tunda ina
sha'awar girki shi ya sa yanzun ba ya ba ni wata
wahala.Bayan mun gama na ja Momy dakin muna
ta hira na tambaye ta Rahma ta ce ga ma
sakonta nan na hotuna ta ce kema ki bata naki,
da zumudi na amsa ina dubuwa ina fadin Allah
Sarki Rahma ina naga hotunan da zan bata?
Momy ta ce ba ku ta6a daukar hoto ba ne? nayi
saurin tuna gargadin Ya Umar (Da har zan ce
yaushe na samu 'yancin yin hoto)Amma sai na
wayance na ce mu da ke cikin bariki anya ma
muna da gurin hoto,ban dai sani ba.
Momy ta tsuramin Ido ,Anya dai zamannan naku
da soja Baya takuraki kuwa? Ni Naga lalacewar
tayi yawa Ne Nace bakomai momy Ko mai
yanamin daidai gwargwado, abincima sai yadda
Naso zanci (A Raina Nace farin abinci bazan
Kona namanshi ba; dakanshi yake duba store da
firiza duk Wanda babu xai kawo haka drinks)tace
shin kodai yana matsamiki ne? Nace a'a momy
sai dai Ko Xaki rokarminshi yasani
makaranta,Amma fa kadafa kice ninace fa Sabda
namishi magana yace a'a yace to Xan mishi (a
Raina Nace Allah dai kasa Yaya ya ambience).
Munyi magariba da Isha'i tuwon semo na tuka
mana da miyar kubewa busasshiya Ga man
shanu dayazo dashi damuna cinema yake cewa
momy baban farida nema yabashi sanda yaje
yola.momy ta tabe baki haryanzu haryanzu kuna
tare da farida? Yace to momy aydama ba
matsalar tabace babantane kuma

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login