Showing 6001 words to 9000 words out of 59518 words
Chapter 3 - FUSKA BIYU COMPLET BOOK PDF Writing by Halima k. Mashi.txt
zina
ba, na kwace hannuna na tafi , ya tsaya yana
kallona, can yace baby in nayi da wata baza ki
damu ba? ko juyowa banyi ba bare in bashi amsa
gabana ke mugun faduwa ganin hanya shiru,
lallai dare yayi na ciro wayata ina duba lokaci
12:30 na dafa kirji nace na shiga 3 ! na kara sauri
titi na mika babu kowa sai motocin dake wucewa
jifa jifa.
Wata mota ta tsaya da sauri na isa gurin dan
neman taimako samari ne guda 2 a ciki suna
shan sauti na bayanne yace shigo mana baby
nace taimako nake so sabon kawo zanje , suka
ce shigo mun kai badarawa sunata min surutan
banza, hardai na bayan ya soma dagamin kafada
tare da fadin baby ko zamuje mu dan huta na
awa 2 kacl ni awa 1 abokina awa1 ? na dube su
cikin takaici nace, ni ni ba 'yariska bace da zaka
ce muje a huta , sai naga sun hada ido sun
kwashe da dariya. direban ya ce haba yarinya duk
wanda ya dube ki yaga cikakkiyar karuwa sai dai
in zaki mana rowa takaci ya kamani nace kune
dai yan iska bani ba, suka ja suka tsaya ke 'yar
bariki kada ki gaya mana magana, sauka nace sai
me in an saukan na fita suka ja motor nace 'yan
iska kawai.
Tafiya nake har ma bansan gurin da nake jefa
kafa ba, sai jin taka birki nayi quuu a bayana kan
in kauce har motar ta bangaje ni sai gani a kasa,
fitilar motar ta dallare ilahirin gurin da haske, ban
tashi dga kasan ba naji taku tafiyar mai motor
tsoro ne ya kamani a raina nace kilama dan
yankan kai ne, takalmin shi na fara kallo gabana
ya fadi na dubi wandon soja ne , na fada a raina
shi kenan zai kasheni da duka, yce ke na dube shi
da sauri saboda muryanshi dana ji gabana yayi
mummunar fadywa na'am na ambata ya umar
jikina ya soma bari yace ke me sunanki ma? nayi
shiru ya dakamin tsawa ya sunan ki nace? nace
asma'u , yace tashi da tsawa yakemin magana na
tashi yana dubana tamkat yaga kashi cike da
tsana yace lallai yarinyar nan kin fita daga sahun
kananan karuwai kin koma cikin manyansu, lallai
an jibga asarar haihuwa wannan ai gwara barinki
da haihuwarki, amma bakiyi halin mama da alhaji
ba kai kaf gidanku kece fitinanniya banma san
sanda aka haifeki ba, amma har kin kware da bin
maza yaja tsaki tare da tsirtar. da miyau ya wuce
ya shiga motar shi
Hakika naji zafin zagin da ya umar ya min, amma
hakan bai hana ni yin saurin zuwa kusa da kofar
motarshi nace ka taimaka min ya umar don Allah
gida zani ya mini wani kallo sannan yace god for
bid in dauki najasa cikin motta? bani ba ban
kasance mazinaci ba ba zan dauki mazinaciya ba
ya tada motarshi tare da fadin ba kwanan gida
zaki je ba? dan rashin imani irin na soja haka ya
uwar ya tafi ya barni . ina tafe ina kukan bakin
cikin zuwana gurin partn nan nayi nisa da tafya
naji wata motar na kauce kar a buge ni, ashe
suraj ne haushinshi ya kama ni ya tsaya yana
baby zo muje in kai ki gida nayi mishi banza naci
gaba da tafiya, yayi parking ya fito haba baby yi
hakuri nima sai daga na gane ban kyauta ba, na
tsaya danaji haka ya iso zo muje nace kaje kayi
da wata dinne? yace iye, a'a haba dai ya shiga
'yan kame-kame naje na shiga motor na ce dubi
time suraj kai baka damu ba ko kashe ni za'ayi
kashe yi ko? yace a haba yanzun dai ya zamu yi?
nace ina kayana , yace gasu can gidanmu, can
muka wuce na can za sannan ya kuma dauko ni
har maigidansu
Har maigadinsu yana ce mishi surajo ina zaka da
dare nan yace yana zuwa. tun kafin mu kai
gidnmu muke ta neman mafita a karshe ya kaini
wani kemin aka dan sa min bandeji a ciwon da
naji na kafa sakamakon bigeni da ya umar yayi
sai ya kaini gidan wata kawar mama dake rafin
guza yace wai ya buge ni ne shi ne na suma to
ban farfado ba da wuri sai yanxun shi ne yace ina
ne gdanmu na ce rafin guza , na nuna mishi nan
gidan nayi shiru na sunkuyar da kai ina mamakin
yanda suraj yake tsaro karya . hajiya rabi ta
kama dama ta mijinta ya rasu daga ita sai
'ya'yanta shi yasa nace ya kaini can, ka bugu
biyu zuwa na uku ta bude gnina yasa ta shiga
rafka salati tare da tambayar ko lfy? kafin nayi
magana suraj yace ko kin san wannan yarinyar?
tace kwarai 'yata ce nan ya shga koro mata
karya ta hau kai ta zauna musamman da ya nuna
mata plaster kafata . ta shiga gero mishi godiya
sannan ta jani cikin gida, kafin na kwanta sai da
hajiya rabi tadafa ruwan zfi a kettle ta gasa min
kafar da nake ta dingishin karya , nayo
wnkasannan
Nayo wanka sannan ta tambaye ni yanda abin ya
faru, nan na karkacr na sharaara mata karya da
cewa ina tafiya n dwo gidan kawata kawai sai
naji taka birki ko kafin in ankare har motar ta
bugeni, daga nan ban kuma sanin komaiba sai a
kemis ni fa ma bansan sanda nace mas a rafin
guza gidanmu yake ba, sai da naga mun shigo
unguwar sai kuma Allah yasa na nagane nan
gidan barka da arziki hajiya rabi ke ta yi min.
kafa 'yar albarka dana dinga liliyata cikin dare
don ta kumbura kan safe har ta tashi gurin ciwon
yayi fushi ya kumbura , don haka nayi murna
sosai sanda muka isa gidanmu tuni hankular 'yan
gidanmu ya gama tashi banda maama wacce ta
ce yawon iskancina na tafi, har umma da hajiya
suna cewa ta bar cewa haka yanxun duniya ta
lalace. bayan an gama karade unguwa da
nemana sai gamu mun iso ina ta dingishi . hajiya
rabi tana min sannu.'yan gidanmu suka biyo mu
dakin mama suna tambayar meya faru? na yarda
da haj. rabi in dai gurin bada kanu ne, domin
yand take rattafo zancan babu mahalukin da zi ce
ba' gabanta abin ya faru ba,
[1:33PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1----6
Su anty aina'u da umma da hajiya sun tausya
min sabanin mama wacce tace ita wannan zncen
bai shige ta ba, na dai tafi yawon iskancina ne.
jin hakan yasa naa fashe da kuka tare da rantse
rantse cewa mota ce ta buge ni, umma tace haba
mama yarinyar tsautsayi ya same ta, mma kice
haka? hajiya rabi kuma mikewa tayi tana fadin ni
kinga tafiyata don na kula bamma miki gwaninta
ba . mama tace haj.rabi ba nufina kenan ba ,
nagode hajiya rabi tace dama tun jiyan take min
kukan tasan kila ace karya ne. hajiyan gidanmu
tace wani irin karya? nan dai mama tayi shiru ba
don ta yarda ba sai don ganin babu wanda ya
goya mata baya. haka makota suka yi ta zuwa
jaje amma da yawa gulma ce ta kawo su, lbrn
ma sa canza shi akeyi har da masu cewa an sace
ni ne, dayawa dai sunce party naje yan sanda
suka kawo hari gurin gudu mota ta bige ni, nace
kowa dai yayi ya gama ni dai dama Alhajinmu
nafi ji kuma tunda ya yarda har da kaini asibiti a
duba ni ko na bugu a wurin gurin mama ko
haushin maganar takeji domin ta hakikance karya
ne.
Momy da anty suka gaisa da mama tare da mata
jajen kade ni, tsaki mama taja sannan tace kema
hajiya aisha kin yarda? wannan zancen karya ne
momy tace haba ke ko maman su aina'u me yasa
zaki dinga biye ma surutun 'yan unguwa? duk da
rashin jin asma'u ai ba zata prtyn dare ba, dn
'yarki ta samu hatsri shi kenan ki bita da mugun
zargi, anty tace Allah ya shirya mana, mama ko
cewa tayi dama aike tuni baki son laifin asma'u
hajiya Aisha momy tace ai ni 'yar gidana ce duk
cikin yaranki babu wacce nakeso kamarta. mama
ta ce lailla don ba zaune kuke guri guda da ita
ba, sun fito mama ta dan tako musu suka tafi
gida suna shirin shiga ne anty tace momy ga
motar dan gidana yaushe ya shigo kd? mama ta
dubeshi yana kokarin parking tace kila ma nan ya
kwana ya karaso cike da fara'a yana fdin daga
ina ku ke? momy ce ta soma cewa Allah sarki
yarinyar nan ce 'yar gidan hajiya saude tsautsayi
ya same ta, yace 'yar gidan mama? tace eh yace
aina'u ko fatima? anty ta amshe da cewa asma'u
din nan, itace wai mota ta kade ta ta suma har
ta kwana gidan wata kawar mama din
Mamaki ya cik shi yace yaushe? momy tace
shekaran jiya da dare, zuwa gidan kawarta gada
maman kawar an ce bata ma dade ba a gidan su
rahman tsautsayi ya fito da ita tun kilama akan
layin ne motar ta kade ta har karfe dayan dare
bata farfado ba, ya umar yayi tsaki sannan yace
wannan 'yar iskar yarinyar ba wata mota
yawonta.... momy ta katse shi to sarkn zargi kai
da ba ma anan kake ba na kasan tana yawon
taja tsaki ta nufi ckin gida tana fadn ni banason
sharri wlh , anty tace momy kenan ta dai tana
son yarinyar nan , yace kin sani ne anty? can fa
na ganta guraran badarawa tana tafe tana hada
hanya kamar me maye, to karewa nine na buge ta
kuma bany zaton taji wani ciwon kirki ba, anty
tace kai haba? yace Allah kuwa shgarta ma in kin
gani rin ta manyn karuwai, Allah dai ya shirya
anty tace Amin, yaushe kazo? yace tun shekaran
jiya ina nan kd . bani n.d.a bani jaji kin san mun
kusan gama course dinnan kuma muna sa ran
karin girma ne ,tace Allah yasa yace amin suka
shiga ciki
WACECE FARIDA JUMARE?
Farida jumare 'yar asalin jihar yola ce kyakkyawa
tamkar balarabiya , mahaifin ta malam jumare
mutum ne shi mai tsananin son abin duniya ,
haka matarshi maimuna.'ya'yansa sune jarinsa
don baya yarda dan talaka ya auri 'yarsa. ya
aurar da yara 3 kafin farida daya tana aure a
abuja anty sa'adatu, any lami tana kano tana
auran wani shaharren dan kasuwa ne, sai anty
amina da take port harcout mijin ta sojan sama
ne mai babban matsayi yanxun burin malam
jumare yana kan farida wanda duk tafi suaran
yaranshi kyau . wannan yasa ya dage kan tayi
karatun zamani don yana da harn shugaban kasa
ne, itama farida har tafi mahaifinta kudi , tun
tana karamarta take sheka ma 'yan makarantar
su karya akn cewa mahaifin ta minister ne, amma
da aka gane sai wasu 'yan makarantar tasu suka
sa mata farida 'yar minister.
a. secondary kuwa ai sai ta soma bin samari don
ta samukudin siyan kayan kece raini,irin na
'ya'yan masu dshi, duk kuwa rin kokarin d yyyinta
suke yi na ganin sun fito da ita cikin tsara. ta
lakanci maza yanda ba'a zato in taga dan iska ko
ince mazinaci tasan shi, tun da in har ta gane
yana da kudi sai ta san yanda zata hada hulda
dshi manyan mutane take harka dasu tana jan
kudi. malam jumare yasan komai amma baya
magana tunda shima yana shakar kudi, sai yaga
hakan ma ya fiye mishi da ace auran tayi kai har
da nasani yayi na cewa suma saura da bai aurar
dasu ba tunda wannan hanyar an fi samun kudi
(Allah ya kyauta). domin kaf unguwar su babu
wanda ya kaishi samun kudi babu mai jan rin
motarshi duk lokacn da farida ta smi hutu takan
tafi abuja ko port a wani zuwan da tayi ne ta fita
farautar masu bayan tayi dan yawonta cikin
motar anty amina sai ta zame wani super market
ta shiga ta gama sayendn yan kayan bakinta
tafito jingina tayi jikin motarta tana neman
lambar wayarwata kawarta 'yaryola da tayiaure
anan port. din kanta gama wata shegiyar jeep ta
tsaya gabanta kadan
kasancewr idonta yana sanye cikin glass ya bata
damar tsurawaa motar ido batare da an gane
ba,musmman ma da ya kasance tana mai cigaba
da dan danna wayarta ba kyanmotar ko kuma
bata taba ganin irin motar bane a'a son take tfa
mi motar irin nasu ne? numfashin tane ya soya
dauke dan tsabar faduwar da gabanta yayi ba wai
don ganin mallakinmotar ya kasance soja ba a'
ba kuma ganin matsayin shina sojan ne ya
tsorata taba sai dangnin kyau dacikar zati tasha
hulda da sojoji amma bata taba ganin sojan da
kuma yayi mishi matukar kyau irin wannanba cike
(not clear) miskilanci tafiya daga ganinshi tasan
zaiyi girman kai , tke sonshi ya shige ta har ta
motsa, sun shiga cikin super market (not clear) a
motarta ta zauna tana tunanin yanda zata ba da
kanta gareshi karo na farko da ta soma tunanin
bada kanta ga namiji ba dankudi ba.layin rashi ta
soma nema cikin sa'a ksance itama. barikin soja
take,a rude tace ganinan ki min taimako,hoton
yaumar na nan manne a rana harta isa gidan
rashida taimakon waya,
a daddafe suka gaisa ta soma fadin taimakon da
zaki min rashida yanzu naga wani gaye shima
soja ne kyakkyawa mai mukamn sojanta fari
dogo yana da cikar haltta, dariya sosai rashida
takeyi kafin tace yaya sunan shi? farida tacenan
fa daya, yanzunnan fa na ganshi gskya ina
sonshi, ba xan boyemiki ba rashida tace ina zuwa
, hotunane na sojoji kusan hamsin amma bataga
wanda take neman bahakanne yasa tayi mata
alkawarin bincika mata. duk 'yan kwanakin farida
babu kwancyar hankali kullum tana zarya gidan
rashda ko an samu lbrn sojanta.yau kam cikn
sa'a tana sanye da doguwar riga baka
dagyalentakyawunt nakara fitowa tamkar sun
hada iri da larabawa , maza da yawasun so
tayawa tun kanhanya taki sauraren su,burin ta
taga sojanta , suna ckin hira da rashida a uwar
dakinta wato bedroom , sunusi mjinta y shigo
yana gayamata suna tare da abokin shi ne soja
umar tasan shi sai dai shi ba'a wannn barikn
yake ba tre suka fito tana cewa bari ta tafi amma
me? tana fitowa sukayi ido hudu da sojanta cike
da daga waya dauke kanshi , ta zaun tana gaishe
su msawa daya sojan umar yayi bai kara magana
ba,
amma daya dan gota sai ya gane ta, duk da
kallon tsoron da yayi mata ranar farko, kyawunta
baya da saurin gogewa a idon mutum ya mata
wani duba mai kama dana ranin wayo, kaman
naso na gane ki ko? ta dube shi cikin nuna
kamala da kunya irinta matan kwarai tace
nikuwa? hakan ya birge shi yce gidan sojan
sunusitadan dube shi sannan ta sunkuyar da kai,
hakane. yanzun ma can zanje sai kuma mai
mashine ya kawoni nan barkn yace ayya baki
kulabane? tace eh ban lura ba da yake ma ba wai
ina hawa mashn bane shiyasa duk na kasa skewa
dadi ya kara kamashi dama shi bayason mace
tana hawa mashin yace shigo inkai ki tace a'a ai
nayi dare gida zan koma na jima ina yawo saeda
baya ne na gane bama a barikin nake ba, yace to
shigo nakai ki gidan tace ayi haka kai ma ai kana
da wurin zuwa yayi murmushin da zuciyartaa
kara tsinkewa da kara mustuwa cikin kogin
sonshi yace ba komai cikin farinciki ta shiga.
[1:34PM, 13/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu1----7
Gidan anty amina suka je ya ce nanne gidanku?
tace mishi nan gidan yayarta ne, ita yar yola ce
yayi mata yan tambayoyi tasanar dashi duk game
da krtn tane, tace yanzu tana universty,100 lvl
tana karantar home economics, ya ce yayi kyau
hakan domin ina da kishi da yawa ba xan bar
mata ta tayi aiki ba. dadi ya kama ta kenan yana
sonta, dan haka sai tace ai nima nafi san na
xauna a gida dan na kula da mijina da tarbiyan
yayana, yace ba xan bari sai wani lkc ba yaya
sunan ki tace farida jumare,yace farida ina sanki
domin na sami irin matar da na jima ina roqon
Allah ,kanta a qasa wai ita tana jin kunya,
wannan ce farkon fara soyyansu.ya umar yana
tsananin san farida yaje yola har ba adadi, kuma
yana kashe masu kudi duk da farida tana nuna
badan kudin shi take son shiba. saidai wannan
bai hana farida hulda da wasu maxan kamar
yanda ta saba ba. cikin shekaru ciki ne ya umar
yai ta samun matsayi daya bayan daya,har xuwa
yanxu dayake saran xai samu muqamin captain.
Zahiri farida tana son ya umar, saidai babanta ne
bayaso tayi aure sbd kudin da uake narko
mishi,amma shi ba dan wani krtn taba.farida ce
kawai take ce masa haka.ni ko ayanxu nayi na
daman irin shigar da nake yi da, saidai na bar
shiri tun rani damin kaf unguwanmu har gidanmu
bani da shaida,na daina saka duk wani wando
inba na mkrnt ba,ina saka siket ne da xani tun
faruwan wannan abin sai naji ina jin kunyan
fita.satina daya ko waje ban leqa ba kullun ina
kwance.ashe hankalin suraj ya tashi rashin
haduwarmu gashi wayar daya bani tana cikin
jakar nan,kuma kayan suna gidan su.gashi sanda
muka rabu ina pushi sbd abin da yayimin.shi
harga Allah ba nufinshi in mun aikata wannan
xunubi ya barni ba. a ganinshi wannan baxai
shafa auranmu ba.mu qoqarinmu muna koyi ne
da nasara wannan shi xaisa mu kara kullewa.
kullun sai yaxo layinmu can farkon layin ya tsaya
da mota yana sauraran ta in da xan fito.yau ko
dayaga an cika sati yar guntuwan wasiqa ya rbt
tare da kayan daya saya min.
Har da hotunan da muka yi a gun party da
takarmi da jakar, nufinshi muci gaba da
mu'amala ta waya, kotsam sai ya hango aisha
yar autar mama,can tsallaken titi cikin wani
shago,bread taje saya an xubo mata su cikin
laida, taxo xata wuce ya tako da sauri ,aisha taja
ta tsaya ta dube shi fuska babu walwala tace
naam yace ina xaki ne? tace gida xanje, yace
asmau tana nan? tace eh, yace taji sauqi ne?
aisha cikin qosawa tace eh taji mana,yace gashi
in baki saqo ki bata? tace to.mota yaje ya dauko
wata laida ya bata sannan kice mata akwai saqo
cikin jakar nan xan kirata, har ya tafi sai ya juya
aisha, ta tsaya da sassarfa ya isa gunta kada ki
bari kowa ya gani fa in tana cikin mutanene ki
boye.tace to, bai san aisha da tsurku ba.kai tsaye
dakin mama ta je, tace mama kinga wannan suraj
dinko shi ne ya bani wannan wai in kaima asmau
kar na bari kowa ya gani, mama ta ansa sannan
tace aisha ta
fita.
kwarai hankaln mama ya tashi da taga abubuwan
dake cikin ledar , irin kayan da ta gani tare da
wayar, sai uwa. uba hotunan hawayen mama ya
kwanceya soma zuba laillai Asma'u tayi nisa a
haka Aina'u da fatima suka same ta sun dawo ne
daga aken da tamusu, hankalin su yayi matukar
tashi da ganin mma tana kuka domn bakon abu
ne gare su, tsakiya suka sakata sunatambayar ta
dalili sam basu lura da kayan ba ckn shasshekar
kuka take fadin, nce Asma'u yawonta taje kun
musa min to gashi dama yarnyar nan so take
taga bayana su kansu sun sha mamaki ganina
kwance jikn suraj muna rawaa hotunan kala 6 ne
duka muna manne da juna guntuwar wasikar da
fatima ta karanta tana magana ne akan ban
hakuri akan abin daya faru tsakaninmu. yace don
Allah kada ya zama sanadyar karshen soyayyar
mu, kuma yace ga wayan nan zamuci gaba dajin
juna a waya mama tace shi kenan ta lalata
rayuwarta ta kuma bada budurcinta don haka
babu ni babu Asma'u ku kiramin su hajiya su
zama shaida. Anty Aina'u tace a'a mama
wannanda ki rufa mata asir ganin wannan abin zi
kara zubar mata da mutunci anangda kila ya fita
cikin layin nan duk da hadin kan da muke da shi
bai dace ba.
Fatima ma tace gaskiya ne mama adai kirata aci
ubanta amma kayan konasuza'ayi. inakwance
kan gado anty fatima ta shigo ke kizo inji mama
daga ganin yadda tamin kiran gaba na ya
fadi,nasan