Showing 30001 words to 33000 words out of 59518 words

Chapter 11 - FUSKA BIYU COMPLET BOOK PDF Writing by Halima k. Mashi.txt

gyale na saka, muka
shiga motar su fatima shehu da yake duk drivers
da suka kawo su sunanan sai. gobe zasu tafi
dasu. muna gadan har dare inda muka shiga
motocin kai amaryazuwa gidan ya usmandake u/
dosa kusa dana ya abubakar , sai shirin zuwa
dinner can ma mun cashe. sosai ban sanma ya
umar yana gurin ba sai sanda muka zaun daga
rawar da muka sha lkcn za'a fara ciye ciye , ko
wani yebur mutum 4 ne, muma mu 4 ne dasu
mina jamila tace bari ta samo kujera ta zauna
nace a'a tace wurin su anty salima,(dama dinner
din tare akayi) muna ta ciye ciye mu tare da
barkwanci da muka saba.jin wani mutum nayi
tsaye kusa da kaina, yace donAllah minti 1 nace
wa? yace ke don Allah nace duk abin da kake son
fada fadi a gabansu aminaina ne yace to don
Allah sunan ki fa? in da hali kuma hour gidanku
zanyi mgana fatima shehu ta rigani malam tana
da miji matar aure ce na duke ta nace karya ne
kaga nayi kama da matar aure?
Kafin yayi magana wayata ta soma ringing cikin
jaka na ciro number na gani ba suna, na duka
nace hello...."muryar ya umar ta katse ni. tabbas
ba kiyi kama. da matar aure ba sbd baki ba aure
daraja ba, to maza ki sallame shi kafin nazo na
bata muku rai dukkanku, nunawa nayi bangane
mai maganar ba, nace wanene ke magana, yace
zaki ganshi yanzun in baki sallami bakon ki ba ya
kashe wayar. na shiga waige waige na dubi bakon
nace kada ka damu bani number dinka xan kira
ka nama bayan, sbd yanxun xamu wuce gida. ya
ya fadamin number dinshi yace sunan shi
kasimmuktar,nace sai ya jini. ya tafi su mina
kallona kawai sukeyi suna mamakin yanda na
tsaya sauraron wani namiji, na dinga waige wige
ban ga gurin da ya umar yake ba na dubi gurin
amare rahma ta min alama da hannu, wai ni ko
zangamu da soja (ta nuna da alamar sarawa)
nace e din, haka dinner ta ci ta cinye sannan aka
kwashe mu nace gida xankoma ba zanje gidan
rahma ba, saida su anty salima suka sa baki
sannan mukaje washe gari budan kai ni dai tunda
safe mu ka dwo sbd su mina zasu dauki
hanya.kayan biki su momy mama da momyn
rahma sun hada musu , ni kam momy ta bani
kudi na hada musu kayan shafa suka tafi kowa
ya dauki hanyar garinsu suka barni da kewa ya
umar ya shigo dan sallamar su momy yana
fitowa yaci karo da alhaji suka gaisa, yace dama
inason shiga gurinka muyi sallama.alhaji yace
madallah har zaka tafi? to ina kuma iyalin?
Yace ta tafi tun jiya, yace to ita kuma wannan
zaman ta kenan ko dai akwai matsala ne ? kafin
yayi magana saiga motr abba, ya fito ya nufo su
abba ya mika ma ahj hannu suka gais,ni kuma na
fito zan shiga gidanmu, ahj yace yauwa ke zo
nan, nazo gabana sai faduwa yakeyi, ahj ya dubi
abba sannan yace na rasa zaman da yarinyan
nan ke yi? bba yace shidin ne nima nayi magana
da momynta su tace kacesi ka gama gininka na
nan? ya tambayi ya umar, ya umar ya dube ni
sannan yace e to , da haka nace amma yanzu na
fasa bar na tafi da. ita. na dube shi da sauri
sannan na dubi su abba nce ni dai donAllah ba
zanje ba gaskiya yabani takar.... saukar mari naji
tas, ban karasa magana ba ahj yace maza dauko
kayanki ku tafi, ya umar yace a'a tabar kayan
zanzo na dauka, tzo muje jin haka nayi cikin gida
da gudu gurin momy ina kuka, tasaki bokitin
hannunta mai dauke da ruwa, lfy asma'u? cikin
kuka nake fadin su abba ne da ahj suka ce nazo
nabi ya umar yanxun nan,momy tace daina kuka
babu inda zakije,nayi ckin dakinta da gudu na.
fada kan gado na kudondune. ina jiyo muryan
abba yana fadin ina sma'un?
Mu hadu a kashi na 2 don jin yanda xata kaya,
domin akwai lbr. Insha Allah zan kare daga na 2
na gode Taku HALIMA ABDULLAHI K/MASHI.
[7:25PM, 17/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: FUSKA BIYU PART 2
NA
HALIMA ABDULLAHI K/MASHI
Fuska Biyu2----1
Ya dubi agogo shida agogon ya nuna yanzu ta
cika. Daidai sannan farida ta turo kofa ta shigo
tare da sallama. Jikinta sanye cikin dogon hijjabi
mai hannu.hijjabin ya sauka har kasa don ya rufe
takalminta. Ya umar ya dube ta cikin sakin fuska.
Har ga Allah yana kara son farida sbd kamewar
da ke gareta. Itama cikin kulawa ta iso gare shita
dube shi ta ce "yau ka riga ni dawowa sojana,
wlh wani leacturer ne bai shigo ba sai to 5,inata
sauri don nasan baka son ka dawo bana gda "ya
ce, "kada ki damu, tace ina zuwa baki ta shiga
wata bedroom dinta cikin sauri ta cire kayan
jikinta don tasan zaya iya biyo ta dakin jis ne da
wata yar riga mai kama da singileti sai ta dora
after dress kan su sannan tasa wannan hijabin.
Tana isa makaranta ta cire hijabin cikin mota ta
barshi sai fa da ta gama gantalinta da malamai
sannan tasa ta dawo gda.
Atamfa ta saka riga da zani ta fito falon gurin
frigde ta nufa maltina ta ciro na gwangwani masu
shegen sanyi ta nufi gurinshi,ta balle hancin
gwangwanin ta mika bakinshi, ta kama
gwangwanin tare da hannunta kanciyarshi yayi
mata masauki,ta zaba mishi maltina cikin bakin
shi,ya sha yayi ajiyar zuciya ya dube ta."shi yasa
nake kara sonki farida domin kinsan abun da
nakeso da kuma wanda banaso burina shine ing
dan mu ko 'yar mu ke yara ma da yawa son
samu" ta dan dube shi " nima nawa burin
kenan,amma lokaci ne" yace ga shawara ta dube
shi da sauri ta me fa? Ya kara janta jikinshi me
zai hana muje muga dokto? Gabanta ya fadi lallai
in har ta bari suka je gurin dokto asirita zai tonu
domin Alhaji Sambo yasa an daure mata mahaifa
ya umar ya katse mata tunani kinyi shiru my
farida, nan take ta dawo nutsuwarta. Duk da tna
cikin rudu ta daure tace ka gane ne? Ita rayuwa
komai saika yi hakuri kada ka damu tunda ka
taba mun ciki nida kai duk mun san muna
haihuwa. Sannan in mun ce sai munje an duba
mu wannan yiwa Allah shisshigi ne tamkar mun
raina baiwar lafiya kyau da kuma arzikin da ya
mana ne in ko mun yi hakuri sai ya bamu ta in
da ba ma zato
Don haka mu dogara gare shi ta dubi fuskarshi da
alama maganar ta soma tasiri gareshi a ranta
tace danne ma tunda kai sai ance Allah sannan
zaka yadda haka zanta bi ina shigar da kai ta ci
gaba, ka duba wani ba kudin ba lafiya sannan
bbu haihuwa, wani kuma a bashi haihuwar amma
bashi da abun da zai koda ci da su. Ta rugume
shi kayi hakuri sojana mai nema yana tare da
samu ,nasan Allah bazai barka haka ba yanda ta
kasance mai taka tsan-tsan doki kai shi lokacin
ne yace ngd farida duk zantukanki haka ne Allah
zai kawo lokaci nga. Ya mike don zuwa
masallaci, yayin da farida ta fada daki ta haye
gado tana kwasar dariya. Layin Alh. Sambo ta
kira tana sheka dariya sunan da ta saka mishi
Hajiya Sabuwa haka ta ke yi duk lambobin maza
abokan harkarta sai ta saka sunan mata sbd
kada sojanta ya gani dama baya daukar wayarta
sbd zaton shi duk mata ne
Ta kira Alh. Sambo tan bashi lbrn ynda suka yi
yanzun da sojanta shima dariyar yake yi tare da
fadin sakarai shi zatomshi wata malama ce ke ta
ce kyale shi yaushe zan tasya ga kyautar shida
bata wuce dubu dari. Alhajina gaku masu kyautar
miliyon. Babanmu yayi min waya ya ce in maka
godiya ka canza masa mota ko? Yace a'a yafi
karfin haka gare ni tace mun gode sai anjima
firgigit! ya umar ya farka daga mummunan
mafarkin nashi, yayi shiru xuciyarshi kuma tana
maimaita mishi ddu'oi, zufa ce yayi tamkar
wanda yayi wanka , ya dubi farida dake shara
bacci, ya som tuno mafarkinshi. farida ce da
wuka take binshi xata sara mishi ya gudu tan bin
shi har ya fadi tazo zata luma mashi, sai ga
yarinyar nan da zai iya tuna sunan ta wacce aka
aura mishi tazo ta fisge t luma ma faridan,
sannan ta kama hannunshi sukanufi wani
lambu,sai waigen faridar yakeyi yana mamakinta
a ranshi yana cewa , laillai makashinka yana
gindin ka, sai wannan yarinya ta nuna mshi wasu
kyawawan yara ta xe kaga yarnka can, gudu ya
soma dan xuwa gare su, amma sai gurin yayi
mishi nisa tun karfinshi yake gudu amma har ya
gaji bai kai banan ya farka firgigit.shikamba shi
da ilimin sanin fassara mafarki don haka sai ya
barshi a cewa rudi ne irinna shaidan, in ma da
wani abu ya bar ma ubangiji damashine mafi
sani, sannan ya tashi yayo alwala dan yin nafila,
ubangijin talkai ya shiga kai ma kuka tsawon
lokaciyana ibada kafin dagabasani ya koma
makwancinsa , kasa rintsawa yayi cikin tunanin
ya nutsa gaskiya zuciyarshi tana matukar son
yara yaso yazo da yarinyarnankilaitace keda
rabon haihuwa ma a tare da shi, duk da iya bakin
kokari ranar da zai dawo yayi donmomy ta yarda
ya taho da ita amma momy taki duk da bkin da
abba yasa,amma tunda sunce zasuneme shi zai
jira, shi ba wai yana sonta bane yana dai saka rai
zata haifa mishi yara ne, in ma yana gudun kada
ta musu muguwar tarbiya sai ya ba farida tayi
musu tarbiya irin ta addinin musulunci. addua
yayi ya rumtse ido har bacci ya dauke shi
niko tun ranr dasu alhaji sukace in bi ya umar duk
sai hankalina ya tshi an dan so a kai ruwa rana
da abba da momy sbd tace lallai ba inda zanje.
yanxun ne yasn danin ahj ma y shigo sukace
lallai na fito na boye momy tace ba xanje ba, ya
umar daya shigo dan tararshi tayi gami da cewa
yayi maza ya bace mata da gani jinhaka yasa
yace su tafi abba yace kaje zamu kira ka suk
fita.fushi sosai abba ya dauka da momy cikin
kwanan kin zaton su momy ce ke zugani, ita ko
lallashna take in yarda in koma zata mishi
fadanshare ni da yayi, domin in 'yarta aka ma
hakaba zata so ba.cikin kuka nace momy ni wlh
dan yakikulani b shi bane damuwat ba, ya umar
ya ganamin azaba a zamanmuna kudu, nan na
kwashe komai na gaya mata. shiru tayi tana
kallona, can ta numfasa sannantace , hakika yayi
kuskure kuma xan nuna mishi kuransa, yanxun in
sun matsa sai kin tafi tokije amma kafin ki tafin
zaki kunyarshi, sannan zan ba ki kudin mota
dakin gayaya ki taho gaa kuma waya xan dinga
kiranki ina jin halin da kike ciki? kuka na ska ina
cewa ni dai Allah mony kiyi hakuri ba zanje ba, ta
lallashe ni da cewa to kiyi shiru shi kenan kiyi
xamanki nan in ya gama ginin shi na nan kd sai
ki koma, shiru dai nayi amma dana koma gidan
ya umar ai gara na shiga uwa duniya. abba da
ahj kullum mitin suna magana kan nida ya umar
ban san me suke tattaunawa ba,har kwana5.
cikin kwanakin na kula da rshin shirin dake
tsakaninabba da momy, haka baya min dadi
sam,ranar kwana 5 da maganar tun a safe ina
kudundune cikin bargo sbd sanyin da ske tsulawa
. jamila ta shigo dakin momy inda nike kwance
tace kizo asma'u su abba suna kiranki a falo
nace to, tashi nayi na nufi falon abba , duk da
barin da jikina yake yi.
kamar yanda na zatashi da ahj na same su zaune
duk fuskokinsu babu annuri. ahj ne ya soma mgn
tunda bazaki gaishe mu ba, to dama ba ita muk
akira kiyi mana ba, da saurinace ina kwananku?
ahj ya kara katse nikirike abinki,mun kira kine mu
shaida miki ki shirya gobe juma'a mijinki zaizo ku
tafi,na soma kuka ina cewa don Allah kuyi hkr
wlh ya umar baya kaunar ganina, ahj ya taso xai
dake ni, abba ya rikeshi kadaka dake ta ba lafin
tabane ita momy dinta su ai itace ta daure mata
gindi, don haka kabr ta itama momy din tasu
auranta yana rawa. da saurina daga kaina dubi
abba,nace Allah abba ba ruwan momy, ahj
yakatseniki shiga shirin komawa gobesbd mune
muka haife kibakecekika haife mu ba,wannan
cemgn bama son jin komai daga gare ki,na tashi
ina kuka ban kai ga fitowa ba naji sallamar
mama,na tsorata sbd tun da nakea gidan nan zan
iya cewa zuwnmama baifi sau 3 ba, sumasai da
dalili, yau km nasan zuwanane tunda ga rigamr
da akeyi, na fito da sauri ta dube ni sannan tace
yayi mikikyau, wannan rashin mutuncin da kika
iya shi zaki mana yanxunko? to bari kijii in har
baza ki koma gidan mijin kiba,babu ni babu
ke,sannan ma ta aje ki ta kula dake ke kuma zaki
rabata da danta da kumaauranta,to maza kihada
kayankiance gobezaizo inyazoki bishi in kuma
kinki to ki nemi gidan uban da zakijeba zaki
zaunaki kashe mata aure ba, shibai guje ki ba
kace mai gudunsa? sakarya shashasha, mara
tunani, ta juya ta fita nabi ta da kallo a raina ina
raya wato daini kullum. cikin lafi nake? kila
mahaka zan koma ga ubangijina cikin bakin ciki
Allah ka dubeni na. shiga dakin momytna zaune
tayi tagumi nasan taji duk abin da mama tace na
zube a jiknta ina. kuka.
lallashi na ta shiga yi tare dacewa, in yarda in
koma, in naga abin da bai min ba toinkira ta zata
zo tataho dani ka dama nazo a galaifina,nace
shikenan zanje, tace shima zaizo ya sameni duk
yinin ranar lallashinamomy keyi, anty amarya
kuma ake har hada minkaya, ga wasu abubuwa
damomy tayi ta bani ina sha harda su na wanka
da sauransu. washe gari tun goma an gama
shirya minkayana tsaf naje salon suka wanke min
gashi naso zuwa gurin rahma amm ba dama,
domin momy tamin waya wai nayi sauri,ashe ya
isone dan ina zuwa kofar gida na ga motarshi,
sandana shiga dakn momy na same ta sai mishi
fada takeyi, banda hakuri babu abin da yake bata,
na shiga tace gata nan ta bika amma nace daka
muzguna mata to ta tahoko tayomin waya nazo
na dauketa. suko su abba fada suka min tare da
jan kunne ko gidanmu ban shiga ba muka dauki
hanya duk ni dashi bayan mota muka zauna, wani
soja ke janmu cikin wata galleliyarhenesi, tunda
muka shiga fuskarshi a turbune tamkar anaiko
mishi da sakonmutuwa, nace a raina kataras, zan
baka mamaki wannan karon ba waccan asma'u
daka sani bace, ba wadda ka gasa bace wannan
saedae ta gasaka, na bude jakata na ciro cingam
na bre na jefabaki naci gaba da tauna, sannan na
ciro waytana shiga neman layin rahma, tadauka
nace amarya kin sha kamshi, tace dole ne kice
nasha kamshi bakinki zuwa kema na dan sammiki
kamshinba?nace ke naso zuwa amma yanxun ba
rana dangani bisa hanyarabuja, tace haba nace
wlh,tace skul? nace a'a su ahj sun koreni in na
cemakiba'a sonakice karyane,tace gidan ya
umar?nace sai. kiyikuma, kadaki cinye min kudi
anjimakikirani gara ke kina da mai saka miki sai
na jiki tace shi kenan sai kin jini. na aje wayar a
kan cinyata, na bude volume dinta na kira mina
tace sai yau kika kirani?
Nace sorry mina bana cikn nutsuwa ne 2days,
shiyasa ko. su fatima ma bankira suba.ina ga yau
zan shigo abujanku, tace to queen sai naji kiran ki
bye. haka nan na kira fatima da bilkisu duk nayi
musu bangajiyan biki, yana jinana jefa wayata
cikin aljihun jaka na jingina, can aka kira shi ya
dauka naji yace, my farida kin dawo gida ne? ban
san amsar da taba shi ba, sai naji yace ok,
tonima hani nan bisa hanya kisa su joseph su
share BQ dinnan muna xuwa yanxun da bakuwa,
na dube shida sauri waton ni xa'a saka a BQ,
zaka sha mamaki, na raya a raina. kowace amsa
ta bashi?sai naji yace yarinyar nance, eh ita ya
sake yin shiru,tana ta mgn ba dai najin ko me
take fada sai naji yace,o no kada ki damu, kin san
ba zanja da mgnr su abba ba shine kawai ban da
su da ke tsakani mexanyi da ita?ka dama ki
damu. a raina nace, yau za'ayi ta donnima din
wlh ba zan dauk rainin hankali ba. muna isa wani
mahaukacin gida muka shiga acikin abacha
barak, na kula gurin duk manyan sojoji ne
donhaka tunfarkon unguwar har gidan da mukaje
sojoji ne, daya gama parking muka fito yasa
wasusojoji suka kwashi kayana zuwa BQ dan
sunce mishi sun gyara,yace min na bisu,ban
musa ba donkada na ba da shi naga sai wani
famankame mishi sukeyi, muna shiga naga wani
madaidaicin falo mai dauke da setin kujeru,duk
sun kode yadinsu naga dakunanbacci 2 na leka
duka da gadaje kanana sai kicin da bayi a duk
cikin falon ban zauna nan ba ai ni ba 'yar aikinshi
bace,nan na fita na bar kayan nan cikin falon na
nufi ainihin gidan nasu,tafiya ce mai shegen
nisa,kafin akai cikin gidan,a raina nace haka
kawa ba zan zauna ba cikin bishiyoyiba salon
maciji ya sare ni, na shiga falonsu ko sallama ban
y ba, farida nagani tana shirya abinci kandiin ta
ta kalloni taga inda zanje na samu kujera na
hakimce ina kallon TV, tabar abin da takeyi ta
nufi wani daki ina ganin nan ne dakin shi .
Jim kadan sai gasu tare ya cire kaki jallabiya ce
fara tas a jikinshi, sai gilas dinda nike zaton na
kara karfin ido ne don koda yaushe yana idon shi,
yazo warin da nake fuska tamke yace me kikazo
yi nan? Na mishi wani duba sannan nace kai zan
tambaya na maida idona ga kallon TV yace ke
bari kiji baza kizo ki dama min lissafi ba dan in
da nasa aka raka ki can ne mazauninki, nace
tabdijam wallahi ba zan zauna a can ba kuma ba
yar aikinku bace ni, ya daka min tsawa ke yimin
shiru mara kunya wuce ki koma, na gyara zama
nace nifa babu inda zanje. Farida ta dube shi,
sojana gaskiya yarinyan nan bata da kunya, ya
daka min tsawa ba zaki tashi ba? Nayi banza
dasu na daura kafa daya kan daya, na ciro
wayata na soma kiran layin momy, ya tsargu zan
kira momy ne sai yace farida jeki ci gaba da
aikinki, nace momy mun iso, tace kun iso lfy?
Nace lfy lau, sai dai kan in karasa ya amshe
wayar, na dube shi nace bani wayata don ba kai
ka saimin ba, ya soma fadin rufe min baki ko in
zane ki yanzun nan kina jina ko? Nima na mike
nace kai
Nima na miqe nace kai damisar takarda, ka sani
na daina tsoranka yanxu, da ka buga amma
yanxu mai dukana sai ruwan sama wlh, kallona
yakeyi na sani yana mamakin canxawar dana
yine, dama araina nace haukan tsiya xan musu.
komawa dakin matarsa yayi, taxo ta dubeni
qaryan rashin kunxa kike yi baxaki xauna min
gidana ba, na miqe na mata kallan banxa nace
gidan banxa da wofi gareki? to inasan ki sani da
gidanki da mijinki duk basa gabana,ni da xaki
taimaka min kisashi ya rbt min takarda,domin
baya cikin maxajan dana keso, ki daina kishi
basan mijinki nake yi ba,yanxuma ya baki lbrn
yanda akayi na yarda na biyo shi, tace ai shima
ba sanki yake yi ba,me xaiyi da karuwa? na dube
ta da sauri waye karuwa?tace ke,mai yawon
hotel..
*****************
[7:26PM, 17/10/2016] 🌹@lh@ji🌹 A R: Fuska Biyu 2----2
Tace ai shima ba sanki yake yi ba,me xaiyi da
karuwa? na dube ta da sauri waye karuwa?tace
ke,mai yawon hotel.. Takaici yaxo min kenan gun
mijinta taji? haushi daya kamani nace ni da
uwarki muke xuwa hotel din ko? ta nufo ni wai
xata dake ni, nace taba ni ki gani .hayaniyarmu ta
fito dashi yaxo ya ja matarsa tana fisgewa wai
saita duke ni suka tafi, na koma kan kujera na
xauna na ce wannan karan baxan dauki raini ba,
insha Allah

Leave a Review

You cannot submit review untill you Register or login